Sashe 25
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ka shiga uku kaikam, sai kace mace"
Murfin man Yassar ya jefa mishi yana fadin
"Fita daga dakin nan dan ubanka..."
Dariya Abdulkadir yayi
"Ba inda zanje, ni da dakina"
Ganin Yassar na ajiye robar man dake hannun shi yasa Abdulkadir din mikewa babu shiri, ya fice daga dakin yana dariya.
Daman yana da niyyar zuwa ya gaisa da Hajja kuma yai mata sallama, tunda inya koma baisan lokacin da zai sake dawowa ba kuma, sai dai ta waya.
Da sallama ya shiga dakin Hajja, yana samun wasu cikin dangin Abba da suma duk ranar zasu tattafi, yawancin su baya tunanin a garin Kano suke da zama, bai tabbatar ba, saboda ko taron dangi da akanyi duk karshen shekara zai iya qirga guda nawa ya taba zuwa, suma idan Yassar ya jashi.
"Sannun ku"
Ya fadi yana soma wucewa cikin dakin sosai, kamun wata mata da yasan yar uwar Abba ce, amman bazai tuna ya alaqar take ba, ko abokiyar wasan shi bai sani ba, tace
"Abdulkadir baka iya gaishe da mutane ba?"
Juyawa yayi yana kare mata kallo, kafin ya amsa da
"Sannun kun da nace bai miki ba?"
Daya daga cikin matan ta watsa mishi daquwa tana fadin
"Karbi wannan Abdulkadir, marar kunyar banza.
Yayar gyatumin naka kake mayarwa magana haka"
Kankance idanuwa Abdulkadir yayi yana fara bude baki ya tambayeta meta hada da Abban nasu da zatai mishi
zagin yara, Hajja ta katse shi da fadin
"Abdulkadir..."
Juyawa yayi ya kalli Hajja, ranshi ya gama baci
"Me yasa zatai mun zagin yara Hajja?
Wacce gaisuwa suke so in musu?
Bayan ta musulunci daya wajaba akaina har sannu na musu"
Runtsa idanuwa Hajja tayi, tana gujema Abdulkadir bakin mutane
"Abdulkadir..."
Ta sake fadi, wannan karin ranta a bace, da gajiya da halayenshi, ba zatace batayi kewarshi a shekarun nan ba, amman bakinta ya huta kwana biyu.
Kuma babu wanda yazo gidan yagan shi ballantana wani abu ya hadasu har yai musu rashin kunya.
Juyawa Abdulkadir din yayi yana ficewa daga dakin.
Hajja tabi bayan shi, sauri ta kara tana wuce shi, ganin ta nufi sashin Abba yasa ran Abdulkadir din kara baci, yasan kararshi zata kai wajen Abba, shi ba karamin yaro ba.
Bayanta yabi har dakin Abban data shiga da sallama, yana zaune akan kafet da alama karyawa yagama yi.
Hajja najin shi yana biye da ita, dan haka bata tsaya bata lokaci ba tace
"nagaji da halin yaron nan Alhaji.
Yanzun su Hajiya Salamatu ya samu a falo yai musu rashin kunya..."
Numfashi Abba yaja ya fitar yana kallon Abdulkadir din da yake tsaye.
Hakan yasa shi fadin
"Ni ba rashin kunya nai musu ba Abba"
Juyawa Hajja tai tana kallon shi
"Na maka ta kudin ka, kasan tambarin gidan muce"
Kai Abdulkadir ya sauke kasa, shisa daya tafi ya shekara biyu baizo gidan ba, sai angan shine za'a saka shi a gaba ana mai fada kamar karamin yaro.
Juyawa Hajja tayi tana ficewa daga dakin
"Ni ban musu rashin kunya ba Abba.
Nayi sallama fa, har sannu nayi musu.
Shine zasuyi mun surutu ban gaishe dasu ba"
Numfashin dai Abba ya sauke da maganganun Abdulkadir din, addu'a itace abinda yake bin yaron da ita, dan idan yace zai saka bacin rai da halayenshi matsala za'a samu.
Tunda haka Allah yayi shi da baudadden hali, idan zagin shi akai, ko akai mishi fada ba amfani yake ba, dukan ma ko sanda ake mishi baji yake ba.
Addu'a ita kadai ce abinda zai tausasa zuciyar Abdulkadir.
Hakan yake yawan kwatantama Hajiya Safiyya.
"Ka kyauta ai.
Inace tun jiya da daddare kaimun sallama cewar yau da sassafe zaka wuce"
Abba ya fadi, kallon shi Abdulkadir yayi yanajin wani sabon bacin rai, dan yaga alama, Abban nason nuna harya gaji dashi.
"Yanzun ma sallama naje in mata..."
Kai Abba ya jinjina
"Allah ya tsare ya kaiku lafiya.
A dinga tausar zuciya dai"
Sai da ya amsa da Amin tukunna ya fice daga dakin.
Sosai ranshi a bace yake, amman bazai tafi baima Hajja sallama ba.
Dakin ya sake komawa, yana buga kafafunshi cikin son sanar dasu Hajiya Salamatu baiyi niyyar gaishe su ba, babu kuma wanda ya isa yasa shi yin hakan, ba kuma yanda zasuyi dashi tunda ba haihuwarshi sukai ba.
Dakin Hajja ya fara shiga ya samu bata nan, fitowa yayi yana nufar kitchen.
Acan kuwa ya sameta tana hada shayi
"Hajja..."
Ya kira, inda yake bata kalla ba, aikin da takeyi taci gaba, dan sosai ya bata mata rai.
"Hajja mana...
Banaso fa..."
Abdulkadir ya sake fadi, ganin bata da shirin kulashi yasa shi kama hannunta
"Zan watsa maka ruwan shayi idan baka bace mun dagani ba"
Wani guntun murmushi ya kwace ma Abdulkadir din
"Nine fa Hajja..."
Harara ta watsa mishi, yanayin yanda ya kankance mata idanuwan shi nasa murmushin da batayi niyya ba kwace mata, tana son yaranta fiye da yanda zata iya fadi, amman Abdulkadir daban take jin shi, tun yana karami jin shi take har ranta, ko dukan shi tayi tana da tabbacin yanda hakan yake mata zafi a zuciya yafi yanda yake mishi a jiki.
Wasu yaran kan zama karfin ka, Abdulkadir rauninta ne.
"Hajja hanya zan hau, bana so in tafi kina mun fushi, bayan banyi komai ba"
Duka Hajja takai kishi a kafada tana yarfe yatsunta da suka amsa, dariya Abdulkadir yayi yana kama hannun nata data fisge tana hararshi, yasan ta huce dan yana ganin murmushi a idanuwanta
"Saura aita kiran wayarka a kashe"
Yar dariya Abdulkadir yayi
"Zan kunna in shaa Allah"
Kai Hajja ta jinjina mishi
"Dan Allah ka kula...kaga girma kake, banda rashin kunya"
Daquna mata fuska Abdulkadir yayi
"Nifa bana rashin kunya"
Rausayar dakai Hajja tayi
"Hmm..."
Kawai ta iya fadi, Abdulkadir din yai mata murmushi yana dorawa da
"Sai munyi waya..."
Kai ta jinjina mishi
"Allah ya tsare ya bada sa'a..."
"Amin.
Zahra fa?
Hamma Mubarak ma ni sau daya nagan shi tun da nazo"
Kofin shayi Hajja ta dauka tukunna tace
"Kasan wannan hidimarshi tafi karfin shi, nima da muke kwana gida daya, sai in yini ban saka shi a ido ba.
Zahra kuma tana bangaren Hajiya Halima nake ji..."
Kai Abdulkadir ya daga mata kawai, saida ya samu plate ya zuba soyayyar doya da kwai da tayi, ya dauki shayin da ta hada mishi, tukunna ya sake yi mata sallama yana ficewa daga dakin ya nufi bangaren su.
Tare suka fito da Yassar, jakar Abdulkadir din riqe a hannun shi, sai wallet dinshi a dayan hannun, gaban mota ya bude yana jefa jakar tashi kujerar baya ta gaban.
Ya fito da jikin shi kenan daga motar yaji ance
"Hamma..."
Sanyin muryarta yasa shi sanin itace tun kafin ya juya yana sauke kananun idanuwan shi akan Waheedah da take tsaye, jikinta sanye da doguwar riga ta atamfa, ta saka farar hular sanyi saman kanta, sai yaga fuskarta tai mishi fayau.
Kallon shi Waheedah take tana jin zuciyarta dake dokawa ta matse waje daya a kirjinta.
Yanayine da bata da kalaman da zatayi amfani dasu wajen fassara shi, bata taba jin kewar wani a rayuwarta yanda take jin kewar shi tun kafin ya tafi din ba.
Gaishe shi ya kamata ace tayi tasani
"Tafiya zakai?"
Ta bukata, bata bari ya amsa ba tace
"Hamma bakai mun sallama ba, tafiya zakai bakai mun sallama ba..."
Ta karasa maganar muryarta na karyewa tana jin hawayen da suke tahowa daga zuciyarta sun cika mata idanuwa taf.
Kallonta Abdulkadir yakeyi, banda Hajja da Abba, babu wanda yaima sallama a gidan.
Su kadaine yake jin ya zama dole yai musu sallama idan zai tafi, wanda yagani yanzun dazai fito dai sunyi sallama, baisan meye a yanayinta da yake son saka shi jin kamar bai kyauta ba da bai mata sallama ba.
Tsintar kan shi yayi da fadin
"Zan zo hutun sallah..."
Saida ta ware mishi manyan idanuwanta tukunna maganganun dayai suka zauna mishi
"Da gaske zaka zo?
Dan Allah kazo Hamma, kaji...
Kazo dan Allah"
Kai Abdulkadir din yadan daga mata, yana ciza fatar bakin shi daga ciki, baisan meyasa yace mata zaizo din ba, amman hawayen da yake gani cike da idanuwanta ne bayason su zubo.
Murmushi tai mishi da yasa fuskarta qara mishi haske.
Su duka biyun basu kula da Yassar ba harya wuce ya zagaya ya shiga mazaunin direba ya zauna yana jiran Abdulkadir din.
"Sai na dawo..."
Abdulkadir din ya furta muryar shi can kasan makoshi.
Wani irin yanayi kalmomin nashi suka jefata, ji take kamar zai tafi da wani bangare na zuciyar ta, lokaci daya ta nemi tsallen da zuciyarta take mata najin zaizo hutun sallah ta rasa.
Sai kewar shi da ta kara danneta
"Kamar karka tafi"
Ta furta muryarta a karye, tana saka shi runtsa idanuwan shi ya bude su hadi da kankance su akanta.
Hannun shi daya yasa ya laluba aljihun shi duka biyun, da alama baiji abinda yake nema ba, juyawa yayi sai lokacin yaga Yassar, kanshi ya zira ta jikin murfin motar yana fadin
"Dan bani biro..."
Cike da mamaki Yassar yace
"Biro kuma?"
Daquna fuska Abdulkadir yayi
"Idan zaka bani kabani kawai Hamma, meye namun tambaya kamar na maka wani yare?"
Kallon shi Yassar yayi
"Bazan bayar ba to"
Da alamun gajiya Abdulkadir yace
"Hamma mana...
Kabani nikam"
Kallon shi Yassar ya sakeyi, baisan me zai da biro ba, amman saboda Waheedah da take tsaye yasa shi dudduba cikin motar, yako samo wani baqi ya miqama Abdulkadir din, karba yayi yana takawa inda Waheedah take tsaye.
Bashida takarda, bashida kuma lokacin zuwa nemo wata.
Hannunta ya kamo, yana share yanda ta ware mishi manyan idanuwanta cike da mamaki, zuciyarta nayin wani irin tsalle ta dawo cikin hannun nata daya riqe, bin shi tayi da kallo tana mamakin yanda akai baya kyarma, dan tana jin yana kyarmar daga ciki.
Rubutu Abdulkadir din yai mata a hannun tukunna ya saki yana juyawa batare daya ce komai ba.