Sashe 27
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ki fadamun Waheedah..."
Ya umarta cikin yanayin dayasa ta fadin
"Nuriyya ce daman, Waec din da aka fara registration, shine nake so ince ma Abba da kudin da zai biyamun a sheikh Bashir, in da hali ya cika saiya biya mana mu biyun muyi a Green Olive, nasu da sauki na tambayo"
Murmushin shi Yazid ya fadada, ya dauka matsalar tata mai girma ce, kaunar da take ma Nuriyya na tsaya mishi a rai, yana musu addu'ar dorewar zumuncin su, dan kamar yanda rayuwa bata da tabbaci hakama mutanen cikinta sukan kasance, yana tsoron aminantaka irin haka, yana tsoron yai kusanci da mutane su shiga jikin shi su cutar dashi, dan yasan yana da raunin zuciya, ba komai yake da karfin dauka ba.
"Su Green Olive din nawa ne?"
Ya tambaya, cikin sanyin murya tace
"Dubu talatin da uku"
Kai Yazid ya jinjina yana mikewa tsaye hadi da fadin
"Kiyi mata magana, ta shirya gobe in shaa Allah da na daukoku daga makaranta, kafin lokacin sallah yayi sai muje ni dake da ita Green Olive din muji ya abin zai kasance"
Da wani irin murmushi da yasa zuciyar shi kumbura ta cika kirjin shi taf Waheedah ta kalle shi
"Zakai ma Abban magana ne?"
Kai Yazid ya girgiza mata, sosai yake jinta a ranshi har jikin shi yakejin yana daukar dumi da halin da zuciyarshi take ciki a kanta
"Zan biya mata"
Ware idanuwa Waheedah tayi da mamaki, kafin ta dago hannuwanta duka biyu tana rufe bakinta data bude cikin mamaki, kafin ta sauke su, tana sake kallon shi, dariya Yazid yake sosai
"Ki fada mata yau dan ta zama cikin shiri, kina ji?"
Yai maganar yana juyawa, farin cikin dake fuskarta zai jima yana tare dashi.
"Hamma!"
Waheedah ta kira tana jin yanda yagama mata komai a yar karamar duniyarta, idanuwanta cike taf da hawayen farin ciki take kallon Yazid daya juyo
"Nagode da karamcinka...
Nagode fiye da yanda zan iya fada da kalmar..."
Kai kawai Yazid ya jinjina mata yana juyawa, yanzun kam yanda yake jin zuciyar shi a cike ba iya kirjin shi ta tsaya ba, har ko ina na jikin shi yake jinta.
Da gaske yana son Waheedah, yana mata son da yake tunanin dakyar ya iya hakura ta karasa aji shiddan nan bai furta mata ba.
Sai dai yana duba kankantar Waheedah din, yana ganin kamar yayi wuri, amman har Abba da bikinsu Babangida saida yai mishi magana cewar me yake jira?
Idan aikine yana dashi, yana da muhallin dazai zauna tunda Allah yai mishi budi dai-dai gwargwado Kasancewarshi Engineer yana kuma aiki da kamfanin gine-gine babba da yake nan garin Kano.
Bai fadama Abba cewar matar tashi a gida take ba, saboda yana son ya fara furta mata tukunna.
Idan suka san wacece zasu daina mishi surutu kan aure, sosai yake jin lokacin da zata sani yayi.
Da wannan tunanin a ranshi ya nufi bangaren su...!
*#TeamAbdulKadir*
*#TeamYazid*
*#TeamWaheedah*
*#AnaTare*
*#FWA*
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732:
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
Mami ce data fito daga daki ta kalli Waheedah da take kwance, tana murmushi tace
"Ki tashi an kusan kiran sallah"
Hannun kujerar Waheedah ta kama tana miqewa dakyar, kanta take jin kamar baya liqe da jikinta saboda rashin nauyin da yai mata.
Tunda aka fara azumi babu wanda ya bata wahala kamar na karshen nan, ita bata damu da duk wani aikin gida ba.
Amman tana azumi ace ta fita sosai take wahala.
Gashi a dakinsu kowa zai sha ruwa ranar tunda girkin Mami ne.
Amatullah da zata tayasu wani abin wuni tayi gidan kitso, bata jima da shigowa gidan ba.
"Mami hanjina kamar an kwashe"
Waheedah ta fadi tana taba cikinta da yake a shafe.
Dariya Mami tayi
"Idan wani yaji saiya dauka zakici wani abin kirki..."
Kai Waheedah ta jinjina tana fadin
"Haba ai yau yunwar da nakeji zan baku Mami"
Murmushi kawai Mami tayi tana shiga kitchen ta dauko robar dabinon data dauraye ta fito da ita tana dorawa kan hannun kujera.
Kitchen din ta sake komawa tana dauko babban kwanon tangaran din da yankakkun kayan marmari ne a cikinsu ta ajiye tsakiyar dakin.
Ta miqa hannu ta dauko robar dabinon daga kan hannun kujera, samarin gidan na soma shigowa da sallama, dai-dai lokacin da aka kira sallah.
Wasu dabinon kawai suka dauka suna ficewa daga dakin dan tafiya masallaci, Mami ma daki ta shige dan gabatar da sallar Magrib.
Dakyar Waheedah takai hannunta tana daukar kankana hadi dayin Bismillah tukunna ta saka a bakinta.
Zata rantse da Allah inuwar shi ta banbanta da ta kowa, shekara daya da kwanaki
"Assalamu alaikum..."
Muryarshi ta daki kunnuwan ta, tana sa tari kwace mata saboda ruwan kankana da yabi mata ta hanyar da bata shirya ba, zuciyarta da take wani irin dokawa bata taimaki yanayin da take ciki ba.
Yace mata zaizo da sallah, tun satin take baza ido ta inda zai bullo amman shiru, kallo daya Abdulkadir yai mata yana ganin yanda take tari sosai, takawa yayi zuwa kitchen yana dibo ruwa a cup ya dawo ya mika mata.
Karba Waheedah tayi tana shan ruwan hadi da sake yin tari, tukunna tayi gyaran murya.
Maqoshinta kamar zai ciro take jin shi.
A hankali ta dago tana kallon Abdulkadir din da yake tsaye yana kallon ta, ta dauka akwai shekarun da mutum yake kaiwa ya daina kara tsayi ko girma, amman banda Abdulkadir din.
Zata rantse yafi lokacin dayazo tsayi da girma.
Kalar askin da yazo dashine wancen karin, jikinshi sanye da farar riga mai dogon hannu sai wando daya rufe gwiwar shi da kadan, baqi yana da igiyoyi daga jikin kafafuwan.
Wani irin kyau yai mata har zuciyarta na matsewa waje daya.
Hannu taga ya miqo mata, dube-dube take tana neman abinda zata bashi
"Kofin...
Kiban kofin Waheedah..."
Abdulkadir ya fadi a gajiye, babu abinda ya canza a tattare da ita, sai girma da ta kara mishi.
Kofin ta miqa mishi ya karba yana wucewa ya mayar kitchen, yana fitowa hanyar kofa ya nufa, sai lokacin Waheedah ta samu bakinta ya motsa saboda wani irin yanayi da take ji da bazai misaltu ba
"Baka dauki komai ba"
Dawowa yayi ya dauki kankana guda daya yasa a bakinshi tukunna ya fice daga dakin.
Cikin sanyin jiki Waheedah ta miqe daga falon, har wani zazzabi-zazzabi take ji yana shirin kamata, yanayi ne da kusanci da Abdulkadir ne kadai yake haifar mata dashi.
Gama aji shidda, cin nasara a duk matakin da daliban da suke son samun gurbin karatu a jami'ar Bayero suke bukata baisa Abdulkadir yabar zuciyarta ko na minti daya ba.
Bataji dadi ba da Nuriyya bata samu gurbin karatu a Bayero ba itama, sai nan Poly Abba yai mata cuku-cuku ta samu Business administration, kuma karfin karatun tun daga kan kudin makaranta da komai shiya fadama mahaifin Nuriyyan zai biya, hakan ba karamin zumunci ya kara tsakanin gidajen nasu ba.
Su dukan su sai bayan sallar zasu fara registration.
Zuwa yanzun tasan cewar son Abdulkadir din take, wani irin so take mishi da rashin algus din da yake ciki har mamaki yake bata.
Son Abdulkadir take irin soyayyar da ta ginu domin Allah, soyayyar da babu wani tsammani a cikinta, soyayyar da take jin ko ta samu kwatankwacinta ko akasin hakan duk ba matsala bane ba, zuciyarta abu daya take gane mata, shine son Abdulkadir.
Nuriyya kadai ta furta ma data kalleta sau daya tana ci gaba da abinda take a lokacin, bata sake mata maganar ba, itama kuma Nuriyyar bata tayar mata da zancen ba.
Hakan yasa Waheedah dauka ko Nuriyya tana tunanin wasa take mata.
Dakyar ta iya wucewa dakin su, inda ta samu Amatullah na sallah.
Bandaki ta wuce itama ta gabatar da alwala, dakyar tayi gefe da tunanin Abdulkadir ta gabatar da sallar Magriba.
Ko da ta fita falo duk suna nan, an cika falon ko ina tarkace ne ana hidimar shan ruwa.
Kan kujera Waheedah ta zauna, Yazid na tashi daga inda yake ya koma kusa da ita, hannun shi riqe da kofin shayi
"Na dauka ai ba zaki fito ba"
Ya fadi yana kallon Waheedah, da tunda Mami ta aike su cefane da yamma take fada mishi yanda azumin yake wuju-wuju da ita.
Murmushinta tai mishi da yake jin yana nutsar da wani abu da baisan a tashe yake ba cikin kirjin shi.
Duk idan tai mishi murmushi haka yakan ji kamar ya bude bakin shi ya furta mata yanda ya gama tsara gabaki daya rayuwarshi da ita, amman ya rasa abinda yake danne shi, gani yake kamar har yanzun da sauran yarinta a tattare da Waheedah din, hakan kuma nada alaqa da tazarar shekarun da yake tsakanin su.
Waheedah tasan ya kamata taci wani abu, amman idanuwanta kafe suke kan kofa tana jiran shigowar Abdulkadir
'Dan Allah Hamma baka shigo ina sallah ka sake ficewa ba.
Dan Allah karkai mun haka, bamu gaisa ba, ban gaisheka ba'
Take fadi cikin zuciyarta.
Yazid fuskarta yake kallo yana tunanin abinda yasa ta nutsuwa haka
"Waheedah..."
Ya kira a hankali yana sata raba idanuwanta daga kan kofar tana sauke su akan shi
"Kici wani abu...
Tun dazun kike kiran yunwa"
Batare da tace komai ba ta miqe tana nufar kitchen.
Akwai wake da shinkafar da Mami tayi musu jiya, jallof ce tasha busashen kifi da nama, sosai tayi mata dadi shisa data rage ta kwashe ta saka a fridge.
Daukowa tayi tana saka robar a microwave ta kunna dan ta dumama.
Tsaye tai a kitchen din har saida ta fara jin kamshin abincin alamar yayi, ta fito da robar kenan taji muryar Abdulkadir
"Menene kike dafawa?
Ina ci..."
Juyowa tayi da murmushi a fuskarta, tana jin kusancin shi fiye da tazarar dake tsakanin su, tana jin shi har kasan zuciyarta.
"Hamma..."
Kananun idanuwan shi ya kankance mata
"Yaushe kazo?
Ashe zaka zo"
Numfashi Abdulkadir ya sauke yana amsa ta da
"Banyi niyyar zuwa gida ba yanzun.