← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 94

Sashe 88

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kitchen din ta koma ta samu kwando ta juye kubewar a ciki, tana da yawa, inta ajiyeta ma kafin ta sakeyin wani tuwon zata iya yin yaushi, gara tayi miyar ta saka a fridge.

Tasan zata waiwayeta.

Ajiyewa tayi ta wuce daki ta dauko wayarta ta dawo, Tafsir din Sheikh Albani ta kunna kan yanda zaka kara gyara ibadunka.

Ta rage karar dai-dai kunnenta tunda ba earpiece ta saka ba, duk da ita kadai ce ta riga ta saba.

In akwai abinda yake saurin sosa mata rai bai wuce tana zaune waje wani ya kunna waka ko wani abin ya kure sauti ba.

Sam mutane basa tunanin ko wanda yake kusa dasu baya jin dadin su abinda suke saurara din, ko baya cikin yanayin son saurarar komai.

Wasu suna ganin ai karatun Qur'ani ne, musamman lokacin azumi, kuma zaka iya shiga hakkin wani, shisa aka saukaka da akai earpiece, ka saka kaji duk abinda kake so dai-dai kunnuwanka batare daka takura kowa ba.

Kubewarta ta wanke tana dauko abin gogawa ta dauraye shima ta ajiye su gefe dan taga naman ya saki, gara ta dora shi ta dafa, har cefane ta dauko, lokacin ba wahala gare shi ba, gashi tana son dafa zobo.

Aikinta take a nutse taga giccin AbdulKadir da wani irin sauri da ya sakata leqawa, yanayin tafiyar shi ya tabbatar mata da ranshi a bace yake sosai.

"Allah ya rufa asiri"
Ta furta a hankali tana komawa taci gaba da aikinta.

AbdulKadir kuwa duk azumin da yake bai hana shi zira kai ta murfin mota yana ma mutane masifa a hanyar shi ta zuwa gida ba, dan gani yake sun tare mishi hanya, sun hana shi isowa da wuri, wayar shi ma da Yassar ya ishe shi da kira kasheta yayi.

Ba zai tuna ranar karshe da yaji kunyar Yassar irin yanda yaji ba yau.

Tunda can ma akan Yassar ne fara sanin yana iya jin nauyin wani dan adam haka, kan shi tsaye zai iya fadama Hajja abu, har Abba ma, koya tambaye su abu, amman Yassar saiya jima yana juya maganar kafin ya samu ya fito da ita.

Lokutta da dama yanajin kamar shine ya kamata ya fito ciki daya da Yassar, su kwanta a mahaifa daya saboda kusancin da yake tsakanin su.

Sai dai haka Allah Ya kan tsara lamurra, wani lokacin ma sai kaga shakuwa a tsakanin mutanen da basu hada jini ba, Yassar na daya daga cikin abinda yake godema Allah da samu a duk sallar shi ta duniya tunda ya mallaki hankalin shi.

Ta ina Nuriyya take so ya fara hada idanuwa da Yassar din?

Me take so yace mishi bayan yau?

Ta mishi abubuwa da yawa, kanana da manya da ya dauki idanuwa ya saka
mata, abubuwan da duk ya tsarama kan shi ba zai dauke su a wajen macen da yake aure ba.

Sai dai ita din ba Waheedah bace ba, yanajin ranar da duk zai waiwayi abinda tayi mishi da wahala alaqarsu ba zata samu tangarda ba, shisa yake kauda kai yana kyaleta.

Yau ne ta kai shi saman kanta ga ba jikin bango bama, da shi ta taba, da kudin shine, watakila ba zai ji abinda yakeji ba yanzun, da kudin ma na wani ne daban da yasan in ya mayar mishi zai karba duk abin zai zo da sauki.

Kudin na Yassar ne, kuma ko jiya sai da yai mishi mitar bashi da kudi, yai ma Hawwa gyaran mota, yana so ya kara tara wasu kudin itama ya sake mata wata, zai iyayin abubuwa da dubu arba'in da biyun shi, ko kayan abinci zai siya ya ajiye, ko yayi hidimar sallah da take gaban shi cikin kwanaki kasa da talatin.

AbdulKadir na da tabbacin bashi kadai bane yake tsara komai na rayuwar shi.

Ciki harda yanda kashe kudin shi yake tafiya.

Bakin kofar dakin Nuriyyar ya tsaya yana rike da handle din kofar, idanuwan shi ya lumshe ko zai tuna wani dalili da yasa zuciyar shi doka mata tun daga farko amman ya rasa, ba halayenta bane, saboda baisan su ba lokacin da ya fara son ta, bai san su ba lokacin da zuciyar shi ta sake doka mata bayan ya rufe shafinta daga rayuwar shi.

Baisan ko kadan cikin halayyarta ba lokacin da ya amince ma aurenta, halayenta sun fito mishi ne bayan ya aureta, a kasa da sati daya bayan ya aureta ya fara kula dasu, sun sake fito mishi bayan ta tare a cikin gidan shi, zama ya hada su, tana saka shi fahimtar dalilin da yasa mutane ke cewa zaka iya shafe shekaru da mutum ba kasan ko da kashi ashirin cikin halayen shi ba, saboda akwai boyayyayun halayen da ba mutum bane yake boye su dan kar a sani, basa fitowa ne sai zama na a kwana a tashi karkashin inuwa daya ya kama suke bayyana.

Auren Nuriyya yasa ka shi fahimtar abubuwa da dama duk da ba zama yakan yi yai tunani akan hakan ba.

Akwai kuma dalilin da yasa akan auren Nuriyyar bayan ta tare Hajja ta kira shi a waya tana ce mishi
'Soyayya ce take dibarka yanzun AbdulKadir, kuma ita kadai bata isa ta rike aure ba, akwai lokacin da zaku tashi ku duka ku nemi digon soyayyar nan ku rasa, wallahi idan har baku gina zaman ku akan abinda ya girmi soyayya ba, in kuka shiga cikin irin yanayin nan zai muku wahala ku samu dai-dai to.

Ba zance maka kacokan zaman aure kan ginu akan halaye bane kawai, amman su din kan zama ginshiqi mai girma na zaman aure.

Ga ka ga Nuriyyar nan, itama ga ta ga ka nan, ba baki zan maka ba, amman akwai halayenka da nake da yaqinin Waheedah ce kadai macen da zata iya jurewa'
Bayason ya tsaya tunanin hakanne a baya, dan zai saka tunanin cewa sai da kowa da yake son shi yai mishi magana akan auren Nuriyya din yai biris da su, ko Yasir da ba shiga harkar juna suke ba sai dole sai da yace mishi
'Da yawan lokutta mukan so abinda ba alkhairin mu bane ba, zaka iya son abu ka rayu babu shi, zaka iya kin abu ka rayu dashi AbdulKadir.

Dan kana son yarinyar nan baya nufin in baka aureta ba wani abu zai sameka, da yawan lokutta mukan yi hakuri da abinda muke so dan zaman lafiyar mu'
Shima yai watsi da shi, kashe wayar shi ma yayi.

Shisa duk wani karamin abu da Nuriyyar zatai mishi baya daga kai, yasan tunanin maganganun da kowa ya fada mishi kan aurenta ne zai danne shi.

Ya kuma tsani kalaman dake biyo bayan dana sani na 'Sai a wane ko wance suka fadamun ban ji ba' wani lokuttan kuma sai kaji ana 'Daman ance mun kaza da kaza'.

Duk bayason wannan tunda ba zasu canza abinda ya riga da ya faru ba, shisa yau yake tsaye bakin kofar yana so ya tuna koma menene da zai saka shi yadan sauka daga dokin zuciyar da yake kai, ko da kuwa sharrin shaidan ne, amman azumi akeyi, babu wani shaidan a cikin abinda yake ji sai Nuriyya.

Numfashi yaja yana fitar dashi da wani irin bacin rai ya tura kofar, a tsaye ya sameta tana linke hijab.

Kan lace din da tayi saurin jefa hijab din sama idanuwan shi ya fara sauka kafin yaji kamar ta watsama wutar da take ci a zuciyar shi galan din fetir..

"Me yasa?"
Ya tambaya muryar shi can kasan makoshi yana kafeta da idanuwa
"Me yasa me?"
Nuriyya ta tambaya tana son yin kamar bata fahimci abinda yake nufi din ba, duk da yanayin shigowar shi yasa ta gane yasan ta dibi kudin, ita tabarmar kunya da hauka akan nadeya.

Tana bacci ma wayarta ta fara ihu, ta dauka taga Hajiya Kaltume ce tana fada mata yanzun za'a kawo lace din ma, dan ya iso, ta dauka sai dare.

Ta karbo kenan ta shigo ta tsaya waya da Asma, ta manta shaf bata kulle kofar ta dauke lace din ba taji shigowar shi, da yasa zuciyarta yin wani irin tsalle, shisa ta jefa hijabin a sama tana fatan Allah yasa baigani ba.

Tana kallon yanda yasa hannun shi ya dafe goshin shi yana runtsa idanuwan shi kafin ya sauke hannun yana ware su a kanta.

Sosai yake kokawa da duk wani abu dake zuciyar shi yana tuna mata da in ta manta akwai igiyar aure a tsakanin su da Nuriyya da ta hana mishi dukan ta saiya fitar mata da yanda ko a gaba ba zatai kokarin raina hankalin wani mai suna irin nashi ba, akwai azumi a bakin shi, watan Ramadan ne, wata mai albarka da yake cike da son yafiya da aikata alkhairai.

Amman tafin hannun shi har kaikayi yake ya amsa tambayar rainin hankalin da tayi mishi akan kuncinta, marin da sai taga taurari
"Ki tauna maganar da zaki fadamun Nuriyya, Wallahi gab nake da wanka miki mari.

Karki gwada wasan banzar ki a kaina yau, ba zai mana dadi ba.

Me yasa kika daukar mun kudi?"
Kallon shi Nuriyya tayi tana jin zuciyarta na ci gaba da dokawa, bata taba ganin shi cikin irin wannan yanayin ba, amman a kasan tsoronta akwai yanda maganganun shi suka bata mata rai, taya zaice zai mareta tana matar shi, ita alkawari taiwa kanta daga ranar da namiji zai tabata ya taba auren shi tunda ita ba jaka bace da zai kamata yana duka.

"Wai wanne kudi?"
Ta tambaya tana karasa kwance sauran hankalin da AbdulKadir yakeji yana rike da kwakwalwar shi ya kuwa dauketa da wani irin mari da yasa tajin kamar idonta daya ya fado, da sauri ta saka hannu ta dafe idon tana lalubawa taji kwayar na cikin shi, wani irin numfashi take ja tana son kukan ya kwace mata ko zai rage mata radadin da takeji, AbdulKadir na kallon ta, wani irin dana sani yake ji yana shirin lullube shi, alkawari yaiwa kan shi da ba zai sake taba wata mace da zata kasance karkashin igiyar auren shi ba, saboda yanda addini ya haramta mishi hakan, yanda al'ada bata yardar mishi da hakan ba, amman Nuriyya ta saka shi ya karya alkawarin nan da azumi a bakin shi.
Chapter 88 · 0% Book details