Sashe 3
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yanayin kaddarar su na mata nauyi
"Ba zaka shigo kaganta ba?"
Abinda yake son yi kenan, amman ya kasa, yanzun dinma kunyar Mami tasa shi sadda kanshi kasa yana kasa cewa komai.
"Ka shigo ka ganta..."
Mami ta umarta, sai da taga ya mike tsaye tukunna ta dawo da kanta cikin dakin, a hankali ya tako yana shigowa, daga bangon kusa da kofar ya tsaya yana jingina bayan shi a jiki, inda Mami take zaune ta koma tana zama, idanuwan shi ya tsayar kan Waheedah da nata suke a rufe da alamun bacci, duk da haka yana jin gabaki daya idanuwan su na yawo a jikin shi, ya zabi yaki kallon sune kawai dan bayason yaga kallon tuhumar da suke mishi.
Zuciyar shi yaji tayi tsalle tana shirin dawowa cikin makoshin shi, kafin ta koma mazauninta tana ci gaba da wata irin dokawa da yake ji ba cikin kunnuwan shi kawai ba, har a ko ina na jikin shi, bai tsammaci Waheedah zata bude idanuwan ta data sauke cikin nashi ba.
"Waheedah...
Alhamdulillah..."
Yaji muryar Anty ta fadi, yana kuma jin motsin kannen shi da suke mikewa suna tahowa sukai ma gadon Waheedah din rumfa, yadai daina gane me suke ta fada, saboda har lokacin idanuwan Waheedah na cikin nashi, kallon shi take da wani irin yanayi da yasa zuciyar shi rawa.
Yasha ganin yanayi da dama cikin idanuwanta, kaunar shi na daya daga cikin yanayoyin da suka rinjayi sauran, suka rinjayi lokuttan da ko a kasan bata mata ran da yakan gani akwai kaunar shi.
Wannan yanayin bakone, kuma bazai ma kan shi karya ba, ya soma ganin alamun shi wajen kwana hudu da suka wuce.
Sai dai duk idan yaga giccin yanayin yakan ga alamun kaunar shi da yake son rinjayar ko meye din yake gani.
Yau kam kallon ta yake, duba idanuwanta yakeyi sosai yana neman alamar kaunar shi a cikin su ya rasa, a hankali yake girgiza mata kai, akwai inda ta boye soyayyar shi, ba zatai mishi haka ba, Waheedah ce yasani, kaunar shi bangare ce na rayuwarta da bata boye mishi, ba zata fara ba yau, bakin ta yaga ya fara motsawa kafin yaji dirar muryarta cikin kunnuwan shi da fadin
"Mami dan Allah ku ban waje inyi magana dashi..."
Bazai ce ga asalin abinda yake ji ba, amman yasan bayason subar dakin, bayason fuskantar ta, a karo na farko da yake son gujema fuskantar wani abu, bai taba hango zuwan ranar nan ko a mafarkin shi ba.
"Ko ruwa ki sha..."
Anty ta fadi, yana kallo Waheedah ta girgiza mata kai, har lokacin shi take kallo da yanayin nan cikin idanuwan ta.
"Ina son magana da shi dan Allah..."
Ta sake furtawa, yana kallon daga Mami har Anty suna mikewa, su Salim suka fara wucewa suna fita daga dakin.
Anty ce karshe, bata fita ba sai da ta dan tsaya tana mai wani irin kallo kamar tana son yawo da idanuwanta cikin zuciyar shi ne taga abinda yake boyewa kowa, tukunna ta fice tana turo musu kofar.
"Ka zo ka zauna..."
Waheedah ta fadi, daga inda yake taga ya girgiza mata kai.
Zuciyarta take jin ta daskare a kirjinta, ta dunqule waje daya kamar dutse, ta dauka datai hakan ba zatai mata ciwo ba, ba zata ji yanda take dukan kirjinta da wani yanayi da yake barazana da numfashin ta ba.
"Magana zamuyi Abdulkadir..."
Ita kanta saida taji sunan ya dira cikin kunnuwanta da wata murya da tasa jikinta bari, balle Abdulkadir da yake jin kafafuwan shi na rawa, yaune karo na farko a tsayin rayuwar shi data furta sunan shi kai tsaye haka.
"Waheedah..."
Ya kira da bayanannen mamaki a fuskar shi da muryar shi.
"Idan ba zaka zauna ba shikenan"
Cewar Waheedah cikin sanyin muryarta din nan, da yau yake taba shi a wajajen da baisan akwai su a jikin shi ba.
"Waheedah..."
Ya sake kira yana jiran hakan yai tasiri a kanta kamar ko da yaushe.
Sai dai cikin idanuwanta yake ganin katangar daya kasa ko motsi balle yayi wani abu akanta tana ginuwa a tsakanin su, kai yake girgiza mata a hankali, kamar hakan kadai ya isa ya hana abinda yake faruwa ya faru.
"Aurenka zaka saukake mun!"
Maganar ta jima tana mishi yawo kafin ta samu wajen zama tana sa shi kokawa da shaqar numfashin da yakeyi ta hanci, bude baki yayi yana soma shaqar iskar ta bakin shi ko zata wadace shi, yakai mintina biyu a haka kafin yaja wani irin numfashi, budaddiyar muryar shi na sake budewa da wani yanayi yace
"Karki sake mun irin wasan nan, bana so, karki sake"
Wata dariya tayi da sautin ta yai mata wani iri har a cikin kunnuwanta, kafin wasu hawaye masu dumi da bata da iko dasu suka zubo mata
"Ba wasa nake ba, Sadauki ba wasa nake ba"
Lumshe idanuwan shi yayi yana bude su, Sadaukin da ta kira shi na rage bugun da zuciyar shi take yi, yana kuma bashi karfin raba jikin shi da bangon wajen yana karasawa inda take yaja kujerar ya zauna gab da gadon nata, hucin numfashin shi da taji kan fuskarta na sata runtse idanuwan ta, wani irin abu na tsirga mata har kasan zuciyarta, sanannen yanayin da takan ji duk idan yai kusa da ita haka take jira ya dirar mata, amman shiru, babu ko alamar shi, hakan yasa ta bude idanuwan nata tana jan jikinta ta mike zaune, bayanta ta jigina da gadon da take kai tana kallon shi.
A duk jikin ta take jin lokacin da take jira yayi, lokacin da batasan ta dibarma zama dashi ba sai yanzun take ji har a kasusuwanta ya cika
"Ka saukakemun auren ka"
Ta sake maimaitawa, wannan karin shi yai wata yar dariya yana kallon ta kamar ta samu tabin hankali
"Doctor din nan yace babu wata matsala, haka yace baki samu wata matsala ba..."
Abdulkadir yake fadi, maganganun Waheedah din na tabbatar mishi ta samu matsala a kwakwalwar ta, da hankalinta ba zata furta mishi wannan kalaman ba, bazai kusa da ita haka ta sake maimaita kalaman ya saukake mata auren shi ba.
"Ki kwanta ki huta sosai kina jina?"
Yai maganar yana daga mata girar shi, cikin yanayin da take jira hannunta da taji ya motsa ya sauka akan fuskar shi, sai taji shi akan tata fuskar tana shafa kuncin ta, cikin yanayin daya sashi saurin fadin
"Waheedah..."
Wasu hawayen taji da suka fi na dazun dumi sun sake zubo mata.
"A gaban yarana, Sadauki a gaban yarana..."
Take fadi tana jin wani daci na taso mata daga kirjinta, kalmar hakuri na daya daga cikin kalaman da baya amfani dasu, shisa yanzun da yake neman ta inda zai fara furtawa ya kasa, indai abinda take son ji kenan zai kokarin furta mata ko zata dawo cikin hayyacinta.
"Ka saukakemun auren ka, dan Allah ka saukakemun auren ka"
Take fadi tana kamo hannun shi, da sauri ya rike hannun nata yana dumtse wa, yanajin siraran yatsunta da suke barazanar ballewa kowanne lokaci cikin nashi, suna saka shi sassauta rikon dayai mata
"Bakisan me kike fadamun ba ko?
Baki san kalaman da suke fitowa daga bakin ki ba"
Abdulkadir yake maganar yana yawata idanuwan shi kan fuskarta, yana so tagan shi, yana so taga shine Abdulkadir.
Kamar tasan hakan yake nufi ta furta
"Nagan ka...ka yarda dani naganka, na kuma san me nake fadi.
Ka saukakemun auren ka nace, kuma wallahi da gaske nake...
Dan Allah sadauki"
Waheedah ta karasa maganar wani irin kuka na kwace mata, ji take in ta kara kwana daya da igiyar auren shi a kanta hauka zatayi.
"Kaji dan Allah..."
Hannun ta ya saki yana jan kujerar shi baya, kai yake girgiza mata, baisan akwai wani waje mai laushi daya rage a zuciyar shi ba sai yanzun da Waheedah tasa kalaman ta dai-dai wajen tana dannawa.
Yana alaqanta wannan hargitsin da yake ji da yanda ya jima baiji tashin hankali ba.
A gaban shi abokan aikin shi babu adadi suka tarwatse, wasu daga sassan jikin su na dukan jikin shi harda fuskar shi, a gaban shi harsashin bindiga yasha fasa kan abokan aikin shi, mutanen daya yarda dasu da rayuwar shi, mutanen daya kwashi shekaru yana kwana waje daya dasu a karkashin kasa ko a samanta.
Bayajin akwai sauran tashin hankalin dazai gani ya taba shi, asalima ya dauka ya jima da katange zuciyarshi da faruwar hakan.
Sai yanzun da Waheedah take karyata shi, take nuna mishi raunin katangun daya gina.
"Dan Allah Waheedah...kinji...
Dan Allah ki daina mun wasan nan"
Da mamaki take kallon shi, take hango raunin da bai taba bari tagani ba, da sati daya daya wuce ne taji taushi irin wannan a muryar shi, ta hango rauni haka a cikin idanuwan shi, da tana da tabbacin zuciyarta ta gama narke mata da soyayyarshi da ta jima tana dawainiya da ita, da yanzun tana jikin shi ta rike shi cike da tsoron kar tabar kofar da wani abu zai sake shiga tsakanin su fiye da yanda ya riga da ya faru, amman yau babu abinda hakan ya kara banda sa zuciyarta yin wani taurin fiye da yanda takejin ta a kirjin ta.
Ganin da gaske bai dauka cikin hankalinta take magana ba yasa ta fadin
"Mami..."
Cikin wani sabon hargitsin Abdulkadir yake kallon Waheedah da take hawaye kamar an bude wani abu.
"Mami!"
Ta sake fadi da karfin da yasa Mami turo kofar babu shiri, ganin kukan da Waheedah take yasa Mami fadin
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un....Waheedah?
Me yake faruwa haka?"
Salatin da Mami tayi yasa Anty biyo bayanta tana ma su Salim alamar dasu tsaya nan inda suke karsu biyo su, ita ta karasa da sauri gefen Waheedah din ta zauna tana rikota jikinta.
Kuka Waheedah take kamar numfashin ta zai dauke, kallon ta Abdulkadir dake zaune yake yana jin shi kamar a mafarki, yana jin shi shirun da yaji lokacin da bomb ya fara tashi da abokan aikin shi a karo na farko a gaban shi, shiru ne da bai taba fatan ya sake jin irin shi ba, bai dauka akwai abinda ya isa ya sake saka shi jin irin shi din bane bama, sai yanzun.
"An...Anty..."
Waheedah take fadi tana jin numfashin ta na mata wani sama-sama.