← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 94

Sashe 21

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanzun fa kake fadin kagaji"
Waheedah tai maganar tana dauke idanuwanta daga kan Abdulkadir din
"Zan huta Waheedah...bari inzo"
Yazid ya karasa dan yaga ba'a fara rarraba abin ci a wajen ba, dare nayi, sunce kuma ba zasu jima ba sosai, ya kamata ayi abinda za'ayi a tashi kowa ya kama gabanshi.

"Wai ta ina kuka zauna, nima inata duba ku"
Waheedah ta tambaya, hararta Nuriyya tayi tana matsawa ta zauna inda Yazid ya tashi taja kujerar kusa da Waheedah sosai, dai-dai kunnenta tace
"Ko ko fadamun Hamma ya dawo"
Dan murmushi Waheedah din tayi, muryarta can kasa ta amsa Nuriyyar
"Bamu zauna bane shisa, kuma dawowar bazata yayi"
Dan tabe baki Nuriyya tayi, kamar rashin zaman su na hana Waheedah din mata zancen Abdulkadir, ba tun yanzun tagane Waheedah nason Abdulkadir din ba, ita daice har yanzun take son raina mata hankali kamar yanda ta saba, take nuna kamar bata san abinda take ji akan Abdulkadir din so bane.

Ko dan tasan ba samun shi zatayi ba shisa take son nuna kamar batasan tana sonshi ba oho.

Duk idan Nuriyya tai wannan tunanin takanji sanyi a ranta, a karo na farko Waheedah bata samu abinda take so ba, wannan karin itama zataji yanda zafin rashin samun komai da kake so yake.

Abdulkadir zaice ya kwana biyu wani abu bai gwada karfin halin shi irin yau ba, kokawa yake da idanuwan shi karsu kalli inda Nuriyya take zaune amman hakan na neman gagarar shi.

Ita kanta Nuriyyan ta kasan idanuwanta take kare mishi kallo tana ganin yanda fuskarshi take a daqune babu alamar wasa ko kadan akanta.

Zungurin Waheedah tayi da alamar su tashi subar wajen.

Dan kallon Abdulkadir tayi itama, tana son zama dashi din ko ba zasuyi magana ba, tana kuma son zagayawa ta zauna cikin su Zahra dan nan ne kawai zatafi more bikin, wannan ne karonta na farko da ta taba zuwa wata hidimar biki.

Duk da anayi a dangin Abbah sosai, su Amatullah kanje harsu kwana, ita kam tana zama gida, duk da ko a fuska babu wanda ya taba nuna mata banbanci, kawai dai hayaniyar ce bata cika so ba.

Mikewa Nuriyya tayi tana kara taba kafadar Waheedah din data mike itama, hakan naba Abdulkadir damar da yake nema ta kallon su biyun, sai dai idanuwan shi nakan Waheedah.

"Zamuje wajen su Amatu..."
Ta fadi tana kallon shi, kai Abdulkadir ya girgiza mata yana fadin
"Idan na tashi tafiya wallet dina fa?"
Sai lokacin Waheedah ma ta tuna wallet din shice a hannunta, bin hannun nata da kallo Nuriyya tayi wani abu na tokare mata kahon zuciya dan alamu sun nuna tare suka zo da Abdulkadir din.

'Allah ya rabaki da naci Waheedah'
Nuriyya ta fadi kasan zuciyarta.

Wallet din Waheedah take shirin mika mishi, yanda ya kafeta da kananun idanuwan shi nasata kasa motsa hannunta, kallonta Abdulkadir yake har saida ta koma ta zauna.

Baisan dalilin shi na hanata tafiya ba, kawai yanda yakejin zuciyarshi na dokawa har lokacin cikin bakon yanayin daya kasa fahimta yasa bayason ya zauna shi kadai.

Ganin ta Waheedah ta koma ta zauna yasa Nuriyya din fara shirin zama itama.

"Ki wuce inda zakije"
Abdulkadir ya fadi yana watsa mata wani kallo dayasa ta barin wajen batare data ko yima Waheedah sallama ba, ta tsorata sosai, ranta kuma inyai dubu ya gama baci, meyasa zaima Waheedah magana kamar tana da muhimmanci a wajen shi, ita kuma yai mata magana kamar ita din bakomai bace, yana nuna kamar Waheedah yar uwarshi ce, bayan babu wanda baisan agola bace a gidan nasu, itama din bakomai bace a wajen shi.

Harta koma inda ta fito ta zauna ranta a bace take jinshi, bikin gabaki daya yagama fita daga ranta.

Numfashi Abdulkadir ya sauke da barin Nuriyya wajen, gabaki daya abinda yakeji baqone a wajen shi, bakuma zai yiwu yar mitsitsiyar yarinya kamar Nuriyya ta saka zuciyarshi wannan gudun ba, kawai dan tana da kyau.

Baya son raini, komai tattare da Nuriyya na nuna mishi idan ta samu fuska zata raina shi.

"Sai muzo tare ki tafi kibarni..."
Yai maganar yana kallonta, a lokaci daya yana rasa yanda akai ita kadai take ganin bangaren shi haka, yanda yakejin ita kadai zai iya nuna ma bangaren shi haka batare da tunanin zata raina shi ba.

Dan kallon shi Waheedah tayi tana sauke idanuwan ta dan akwai wani abu tattare da nashi idanuwan da yake karya duk wata garkuwa ta jikinta, komai tattare da Abdulkadir daban take ganin shi.

Batasan me zatace mishi ba, dan haka shiru tayi kawai tana lafewa cikin kujerar da take zaune a wajen.

Abinci aka kawo aka ajiye kan teburin da suke zaune, abincine wajen kala uku a cikin faranti daya, sai tsire a tsinke, harda hadin salad a gefe, a koshe Abdulkadir yake jin shi dan yaci abinci kafin ya fito, tsiren kawai ya dauka yana ci, kallon shi Waheedah takeyi harya cinye, nata tsiren ta dauka daga cikin plate dinta ta sake dorawa a nashi batare da tace komai ba, kallonta Abdulkadir yayi, ba dokawa zuciyar shi tayi ba, dumi yaji ta dauka wannan karin, hannu yasa ya dauki tsiren baice komai ba ya fara ci.

Lemo Waheedah ta dauka na roba da aka ajiye musu guda biyu, bata taba ganin shi da coca-cola ba tunda take, hakan yasa ta sanin ba zabin shi bane, dan haka ta bude mishi sprite din tana daukar abin zuqa ta saka a ciki tana turawa gaban shi.

Dauka Abdulkadir yayi, banda Hajja da Yassar, babu wanda ya taba mishi abinda Waheedah din take mishi yanzun.

Kowa a gida yana daukar baya bukatar kulawa, ko Hajja takan yi wannan tunanin wasu lokuttan.

Sosai zuciyar shi ta sake daukar dumi, baice komai ba.

Tsiren ya cinye, yana ganin Waheedah ta dauki abin goge hannu tana mika mishi, karba yayi ya goge hannun shi tukunna ya dauki robar lemon yasha kusan rabi ya ajiye
"Ruwa fa?"
Ta bukata, kai ya girgiza mata a hankali, yana kallon ta gyara zamanta kamar shi din dayaci wani abu kawai ya isheta, ita ba saitaci ba, numfashi ya sauke, yana kallon yanda fitilar wajen ta karama fuskarta haske.

Haka suka zauna shiru, ita tunanin shine fal cikin ranta, shikuma bazaice ga abinda yake tunani ba har mutane suka fara hada-hadar fita, da alamu anyi abinda za'ayi an fara shirin tashi.

Yazid ne yazo yana jansu biyun a cewar shi za'ayi hotuna, binshi sukayi akayi hotuna sosai dasu tukunna Abdulkadir din ya damqi hannunta yana fara janta.

Binshi take tana kallon hannun shi da yake rike da nata, zuciyarta kamar zata fito waje take jinta.

Su duka biyun basu kula da Nuriyya da take bin bayansu tanajin kamar zuciyarta zata fado, karshen abinda zai faru shine Waheedah ta samu abinda take so, fuskar Abdulkadir din take kallo ko zata ga alamun so, kamar yanda yake bayyane a fuskar Waheedah, amman bataga komai ba, asalima kamar ranshi a bace yake.

Ita dai komai zai faru kar Waheedah ta taba samun Abdulkadir din.

Tana jin zatayi komai dan kar hakan ya faru.

Wajen motar shi suka karasa tukunna ya saki hannun Waheedah din, yana bude motar da mu
kullin, har lokacin basu ga Nuriyya da take tsaye a gefe ba.

Zagayawa Abdulkadir yayi ya shiga motar, ya miqa hannu ya budema Waheedah daga ciki, jikinta babu karfi ta shiga cikin motar tana rufe murfin, su dukansu juyawa sukayi ita da Abdulkadir din ganin an bude murfin bayan motar.

"Nuriyya..."
Waheedah ta fadi cike da mamaki tana dorawa
"Banganki ba"
Cikin takaici Nuriyya tace
"Ya zakiyi kiganni daman"
Saida taji sautin muryarta tukunna tasan a fili tayi maganar da tayi.

Yanayin muryarta Abdulkadir yaji bayaso, yanda tai maganar kamar Waheedah ta mata wani laifi ya mishi wani iri, saboda yana tare da Waheedah din bai kuma ga abinda tai mata ba.

Baisan dalilin da yasa ta bude mishi mota tana shirin shigowa ba, shisa yake da tabbacin idan ta samu fuska zata raina shi, ga zuciyar shi da yaji tana shirin ci gaba da dokawa.

"Ki rufe mun mota..."
Ya fadi a tsawace, yana saka Nuriyya mayar da kafarta data dago, tana jin wasu hawayen bakin ciki sun tarar mata lokacin data rufe mishi kofar tana matsawa gefe ganin ya fisgi motar kamar zai bigeta.

Cike da rashin jin dadi Waheedah tace
"Hamma..."
Saida yai baya da motar sosai yai kwana tukunna ya kalli Waheedah din idanuwan shi cike da rikici
"Tare nazo da ita?

Meyasa zata budemun mota?

Sa'anta ne ni?"
Kai Waheedah take girgiza mishi idanuwanta cike da tsoro, batason fada, musamman nashi
"Meyasa zaki kirani kamar ban kyauta ba then?

Sa'ankine ni da zaki kira sunana kina tsareni da idanuwa kamar ban kyauta miki ba?"
Kai Waheedah ta sake girgiza mishi, yanda take jin ranshi ya baci nasa idanuwanta cika da hawaye.

Tsaki Abdulkadir yaja, shi kanshi idan za'a tambaye shi asalin abinda ya bata mishi rai bazai ce gashi ba.

Yasan Nuriyya na da hannu a cikin bacin ran nashi, baisan tayaya bane kawai.

Tunda Waheedah ta lafe cikin kujerar motar ko motsin kirki batayi, ta gefen idanuwan shi yake kallon tana goge fuska, yasan kuka take.

Inyai magana ta amsa yaji kuka take tabbas zai watsa mata mari ya bata dalilin da zata saka shi a gaba tana mishi kuka, shisa baice mata komai ha har suka karasa gida.

Ita ta fara fita daga motar, tukunna ya fito shima, zagayawa yayi ta gefen da take, cikin sanyinta ta dago da hannu tana mika mishi wallet din shi, karba yayi yanajin shi wani iri.

Bude wallet din yayi tukunna ya sa hannu yana zaro duka kananun hotunan da suke cikinta, sosai ya matsa daf da Waheedah din ya kamo hannunta yana ware tafin ya saka mata hotunan a ciki tukunna yasa dayan hannun shi yana rufe yatsunta akan hotunan ya saki hannunta yana juyawa abinshi...!
*#TeamAbdulkadir*
*#TeamWaheedah*
*#TeamNuriyya*
*#FWA*
*#AnaTare*
[7/27, 1:13 PM] +234 816 124 4732:
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
Washegarin ranar a kwance ya wuni, tunda yai wanka, karin safe ma baiyi ba sai wajen karfe sha daya na safe.
Chapter 21 · 0% Book details