Sashe 75
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Tayi kyau das da ita, yunwa ta fara addabarta, kitchen ta wuce ta dafa ruwan zafi a kettle tana hada shayi mai kaurin gaske ta duba biscuit ta dauko, shima ya kusan kare mata, gashi babu wasu kudi a hannunta, zatai ma AbdulKadir maganar kudi idan an kwana biyu, tasan bazai hanata ba.
A kitchen din ta tsaya ta fara shan shayin dan yunwa take ji sosai.
Takun tafiyar AbdulKadir din taji, kafin ya rungumeta ta baya
"Yunwa nakeji Nuriyya"
Yatsine fuska tayi dan tasan baya ganinta, muryarta ciki-ciki tace
"Me zan baka Masoyi?
Nima yunwar ce ta tasheni...
In hada maka shayi?"
Sake matseta AbdulKadir yayi yana sauke numfashi
"Shayi da me?"
Ya tambaya
"Da biscuit"
Nuriyya ta amsa, tana sa AbdulKadir din sakinta ya kama hannunta yana juyo da ita, ta mishi wani irin kyau mai ban mamaki
"Ni zaki ba shayi da biscuit Nuriyya?
Na miki kama da Fajr"
Shagwabe fuska tayi
"Bansan me zan baka ba wallahi, me kake son ci?"
Kafadu AbdulKadir yadan daga mata, shima baisani ba, Waheedah bata tambayar shi abinda zaici, bashi kawai takeyi
"Ni dai bazan ci biscuit ba, bari inyi wanka.
Kimun koma menene"
Ya karasa maganar yana juyawa ya fice daga kitchen din, kamar hakan Nuriyya take jira tayi wani irin juyi tana buga kafarta a kasa, ko kadan wannan wahalar ce ba zata iya ba sam, a gidansu ma ba girki take ba, can da babu kudi, gidan Anas ma sai ranar da tayi ra'ayi tunda in bai bata kudi ba, inya ajiye dauka take, duk bala'in da zasuyi, ko kudin waye.
Daya daina ajiyewa kayan abincin shi take diba ta siyar, akwai gidajen da ake abincin siyarwa kala-kala a unguwar, wani lokacin ma danyen take kai musu, sai a dinga aiko mata dafaffe har kudinta ya kare.
Ranta a bala'in bace ta karasa shanye shayin nata, kitchen din Waheedah ta wuce tana dauko duka kwalin indomie din da ko rabi ba'ayi amfani dashi ba.
Batasan abinda zata dafa mishi ba banda indomie din, in zaici yaci, in ba zaici ba kam batasan ya zatayi dashi ba ita.
Wannan wahalar ko kadan jikinta ba zai dauka ba, tasan Waheedah zata dawo babu dadewa, tunda mayyar AbdulKadir din ce bata iya nisa dashi.
Tana ta kwashema Waheedah albarka a ranta tana dora indomie din, ta duba, albasa ma bata da ita sai da ta sake komawa kitchen din Waheedah ta dauko ta dawo.
Lokacin da AbdulKadir ya fito harta karasa ta kashe gas din, ta samu plate tana juye mishi ta saka cokali mai yan yatsu a ciki.
Ta dauka zaiyi magana, baice komai ba ya saka cokalin ya fara ci, kitchen ta koma dan tayi wanke-wanke, a kasan ranta takejin yanda harta fara gajiya da zaman gidan.
Mami da kanta tace mata takoma gidan Yassar ta huta abinta, babu wanda zai dameta a can din, dan tunda yan gidan suka ga tana nan sai hirar ta dawo bangaren Mamin.
Ita kanta Waheedah din tana bukatar shirun, tasan in tana nan gidan ba zata same shi ba, duk da sosai taji nauyin da kirjinta yayi ya mata sauki, musamman da aka hadu anata hira, sun rage mata kadaicin data jima tana fama dashi.
Sun kuma rage mata zafin zuciyar da take tare dashi, sai gab da Magriba Yassar yazo ya dauketa daya dawo daga wajen aiki ya biyo.
Fajr ma bata ganshi ba, bata kuma bi ta kanshi ba, tunda ba bakon waje yake ba, ballantana yana wajen Hajja inda babu wanda ya isa ko murya ya daga mishi ai bazai nemeta ba.
Da suka koma tadan samu taci abinci dakinta ta koma, tana sallar isha'i ta haye gado taci gaba da kallon film din daya rage mata tunani ba kadan ba.
Har saida taji dakyar take bude idanuwanta sannan ta hakura ta kwanta.
Badan taji kiran sallah ba, kawai sabo da tashin asuba dinne yasa tun kafin lokacinta ya karasa harta tashi.
Tana gabatar da sallah Ikram ta dauka tabata tasha sukayi kwanciyarsu suna komawa bacci.
Sanda ta tashi goma tayi, wanka ta shiga, ta fito ta dauki Ikram dan tayi mata itama, da kuka aka gama wankan, daman in dai kana son jin kukanta to wanka ko yunwa, kafin wani lokaci harta shirya kanta cikin riga da zani na atamfa da dinkin ya zauna mata sosai, kwalliya tayi tana saka jambaki a labbanta, Ikram ta shirya tsaf tana kallon yanda kamanninta da AbdulKadir suke kara fitowa
"Ikram ki rufamun asiri mana, dan Allah banda idanuwan"
Waheedah ta fadi tana gyarama Ikram din riga da ta dauka wasa take mata ta dashe mata baki tana dariya, itama dariyar ta tsinci kanta dayi
"Dariya kike ko?
Da gaske banda idanuwan..."
Waheedah take fadi tana jijjiga Ikram dake dariya sosai
"Kuma karkiyi irin rigimar shi, macece ke wahala zaki sha"
AbdulKadir da tun daga bakin kofa yakejin dariyar su, hakan yasa shi murza hannun kofar yana shigowa ya tsaya yana kare musu kallo da murmushin daya manta rabon da yayi shi a fuskar shi yace
"Ki daina hure ma yarinyata kunne...Fajr da ya biyo rigimarki me nace?"
Juyawa Waheedah tayi fuskarta dauke da mamakin ganin AbdulKadir din, duk da ya saba shigowa waje bataji shi ba sai dai ta ganshi, kare mishi kallo tayi ya saka gajeran wando iya gwiwarshi na sojoji sai farar riga a jikin shi, kamshin turarukanta yakeyi.
Fuskar shi har lokacin da kumburi, kare mishi kallo tayi kafin ta dauke idanuwanta daga kan shi tana janye Ikram ta matsar da ita tsakiyar gadon ita tana zama a bakin gadon, ta dora hannuwan ta daga gefe da gefe.
A hankali AbdulKadir yake takawa zuwa inda take, tsintar kan shi yayi da tsugunnawa saboda Waheedah ta sunkuyar da kanta.
Hannun shi yakai yana dago da habarta, agogon dake daure da hannun shi tabi da kallo, shine kyauta ta farko data shiga tsakaninta da shi, duk tarin agogunan shi, wannan din shi yafi daurawa fiye da ko yaushe, lokutta da yawa wanka da alwala duk dashi yakeyi, fatar duk ta koke, in tai mishi magana sai yace agogon na da muhimmanci a wajen shi, har wani ta siya mishi, amman dai yafi son wannan din.
Bama aiki yake ba, batasan me yasa yake yawo da shi ba.
AbdulKadir idanuwanta yake son gani, so yake yaga ko da giccin tarin soyayyar da take mishi ne.
"Wahee..."
Ya kira yana wani irin sauke murya cikin yanayin da baisan zuciyar shi zata taba iya jin shi ba balle ta fito dashi, idanuwan nata kuwa ta saka cikin na shi, maganganun Mami na dawo mata suna saka wani abu da batasan yana kulle a kirjinta ba budewa.
Komai takeji yana dawo mata kamar a lokacin yake faruwa, tana jin wasu irin hawaye da suke fitowa daga wani waje a zuciyarta daya jima yana ciwo kafin su fara zuba kamar an bude su, dumin su ya fara ji a jikin hannun shi da yake kan habarta kafin ta sake sunkuyar da kanta.
Da sauri AbdulKadir ya tashi ya zauna gefenta yana kama hannunta ya juyo da ita ta fuskance shi
"Waheedah..."
Ya kira yanajin yanda kukanta ya karasa birkita mishi tunani, wani irin dana sani yana saukar mishi kamar ruwan sama, ba ita ba, yanajin zai jima a rayuwar shi bai dagawa wani hannu ba a yanayin da yakejin shi.
Hannu yasa yana kamo fuskarta ta ture shi tana saka nata hannun ta goge hawayen da sunqi daina zubowa, hannu AbdulKadir ya sake kaiwa, kafin ya taba fuskarta ta sake ture shi
"Ka kyaleni....kabar ni"
Ta fadi cike da kashedin da AbdulKadir bai taba tunanin tana da zuciyar fito da shi ba, dan sanyin halinta yayi yawa, wani kuka na sake kwace mata.