Sashe 10
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amatullah,Nusaiba, Nabila da Kabir ya hango suna karasowa wajen.
"Ke kaman Hamma Abdulkadir ne tsaye fa..."
Nabila ta fadi, tana saka Nusaiba kallon wajen a firgice
"Inalillahi...
Karfe nawa?"
Nusaiba ta tambaya, duk da tsiran sati biyune tsakaninta da Abdulkadir din, ajinsu daya ma a makaranta, amman hakan baya hanashi jibgarta.
Babu mai agogo a cikinsu balle ya amsata.
Sa'adatu kuwa kallon Kabir tayi
"Kabir dan Allah ce duk su fito..."
Juyawa Kabir din yayi da gudu, su kuma suka karaso wajen suna gaishe dashi a tsorace, amsawa yayi, da sauri suka shiga motar suka sami waje suna zama, Zahra ce ta fito itama, fuskarta a kumbure da kukan da tayi, ga shatin yan yatsun shi nan kwance saman fuskarta, ko da ta shiga motar babu wanda ya tambayeta, duk sunsan bazai wuce Abdulkadir ba.
Ba kullum yake binsu a tafi makaranta haka ba, ranakun duk da yahau machine yai gaba abinshi ransu wasai, motar kamar zasu tasheta da hira, in kuwa yana ciki ba zakaji bakin kowa ba.
Kabir bangaren Mama ya nufa, duk suna falon nata, wasu na daura takalma, wasu na saka safa
"Wallahi Commander ya fito..."
Ya fadi yana dariya, Commander shine sunan da suka laqaba ma Abdulkadir din, suke kuma kiran shi dashi a bayan idon shi.
Basu jira karin bayani ba da gudu suka kwasa, wani takalmi daya a hannu suna fita.
Kusan a tare suka karasa suna maida numfashi
"Wanne rashin hankali ne wannan?"
Abdulkadir din ya tambaya yana kare musu kallo
"Ina kwana Hamma..."
Suka fadi kusan su dukan su, madadin tambayar dayai musu, tsaki kawai yaja yana bude gaban motar ya shiga.
Suma soma shiga sukayi, tukunna Waheedah ta karaso wajen, hijabinta a hannu ko sakawa bata samu tayi ba.
Gabaki dayansu Sheikh Bashir sukeyi.
A bangaren Waheedah banda sunanta daya banbanta da nasu ko ita da kanta da ba zata taba sanin ba Alhaji Ahmad bane mahaifinta, balle kuma yan makarantar su, da rana daya bai taba nuna mata cewar bata fito daga jikin shi ba, kuma a cikin gidan ma babu wanda ya taba daga mata kai akan zaman agolancin da takeyi.
Sai kuma kalarta ta banbanta data su, fara ce har shiga ido takeyi, sukan tsokaneta da cewar da taku daya ta gujema zuwa duniya a zabiya, duk da suma akwai fararen a cikin su.
Zata iya cewa ta fara sanin labarinta ya canza ne a ranar, lokacin tana aji uku a sakandire, a gaban motar tagan shi a zaune, duk da gefen fuskarshi tagani saida zuciyarta tai wata irin dokawa da batada alaqa da tsoron shi da kusan su dukansu sukeyi.
Yanayine da ba zatace ga lokacin daya fara ba, ko muryarshi taji sai zuciyarta ta fara doka mata irin hakan, dan zata rantse wasu lokuttan har wani gashi ne yake miqewa a bayan wuyanta.
Jikinta da wani irin yanayi ta saka kafarta a cikin motar, dariya taga sunayi mata kasa-kasa, motar ta cika taf.
"Ku matsamun..."
Ta fadi cikin sanyin maganarta
"Babu waje fa"
Nabila ta amsa ta da murmushi a fuskarta, a raunane Waheedah ke kallon su, tana sauke idanuwanta kan Nazir da yake zaune a gefe, hararata yayi yana fadin
"Tab..."
Yazid da shine zai kaisu ya karaso wajen motar, cikin sanyin halinta ta gaishe dashi, ya zagaya ya bude gaban motar ya shiga yana mayarwa ya rufe
"Wai waye bai fito bane?"
Abdulkadir ya tambaya yana juyowa, Waheedah yagani tsaye
"Uban me kike da ba zaki shigo ba?"
Idanuwanta taji sun ciko da hawaye, ga zuciyarta naci gaba da dokawa da wani irin yanayi da bata da kalaman fassara shi
"Babu wajene anan din..."
Kabir ya amsa mata
"Baga waje anan ba?"
Abdulkadir ya fadi yana kallon su, hannu Nazir ya saka yaja murfin motar ya rufe, dan babu yanda za'ai ya koma gaba, bazai zauna waje daya da Abdulkadir ba.
Karma yaga shine a gefe yace ya tashi ya koma, ita Waheedah da bata fito da wuri ba, ita zata zauna kusa dashi, tsaye tayi a wajen tana rasa yanda zatayi.
Ba zama waje dayan dashi bane tashin hankalinta, luguden da zuciyarta takeyi duk idan ya wuce ta gabanta ma kawai, balle kuma ta zauna ga kugunta ga nashi tana jin kusancin shi.
Tunda take shine namiji na farko da batasan meyasa take jin hakan akan shi ba.
Hannu Abdulkadir yasa ya bude murfin motar
"Idan bakina ya sake magana sai ranki ya baci"
Batasan lokacin da kafafuwan ta suka motsa zuwa gaban motar ba, tana ganin ya kara matsawa, shiga tayi jikinta a sanyaye, kafin ta zauna ta dora hijab dinta kan cinyar shi tana rufo murfin kofar tukunna ta zauna a takure, tasa hannu tana daukar hijab din nata
"Baki ga inda zaki ajiye ba sai a jikina?"
Kai ta girgiza mishi, karamin tsaki yaja yana gyara zama, farinta yake ji yana shigar mishi idanuwa, a dakinsu shida Babban Yayan su Muhsin ne baqaqe, shi yadanfi Muhsin hasken fata ma, amman farin Waheedah na mishi wani iri, duk inya ganta tana kara saka shi yanajin yanda babu abinda zai hada mishi hanya da auren farar mace, ko kadan basa burgeshi.
Hijab din ta dayasha guga ta warware tana shirin fara sakawa
"Idan kika bigeni sai na mareki Waheedah, bansan iskancin dazaisa ba zaku saka hijab tun daga gida ba..."
Yazid dake tuqi ya girgiza kanshi yana murmushi
"Wallahi ka cika shegiyar masifa..."
A hasale Abdulkadir yace
"Hamma banaso..."
Waheedah kuwa hannuwanta ta sauke tana rike da Hijab din, numfashin kirkima ba sosai take yinshi ba, kar yaji iskar ta mishi yawa a kusa dashi ya sauke mata wata masifar tashi da bata karewa.
A haka suka karasa makarantar babu wanda yake ko motsin kirki.
Kitchen din Mama ta shiga, tana bude katuwar kular data zuba abincin a ciki taga ko rabi ba'a diba ba.
Jinjina kai tayi
"Kunma kanki Wallahi, gaba takaini"
Ta fadi tana dauko wasu manyan robobi masu murfi guda uku ta soma rage dafadukar shinkafar a ciki.
Daman bayan sun tafi makaranta, tunanin abinda zata dafa takeyi, tana bude fridge taga bata da cefane, dubu uku Abba ya bata kafin ya fita, zubin adashi zatayi da dubu biyu, akwai bikin da zasuje na bangaren kishiyar Ummanta, dole a kece raini a nuna banbanci, dan ba tun yau take ma bikin tanadi na gaske ba.
Sauran guntayen miya da tagani, wasu ma Allah kadai yasan tun yaushe suke ta dauko ta hade su waje daya ta sheqa ruwa ta kara mai da niqaqqen yaji a ciki, taga wani tsohon crayfish ta watsa a ciki, ko tsincewa bata tsaya tayi ba, tasan baci zatai ba, tai musu dafadukar shinkafa.
Da daddare tuwo zata tuqa, tana da sauran miyar kubewar da suka bar mata wancen girkin nata, ita zata juye ta karama ruwa ta kara kada wata kubewar ta tasheta, dan ita bata zubar da abinci, yanda suka barshi basuci ba, in wani girkin nata ya zagayo shi zataima kwaskwarima suzo su diba.
Dubu dayan zata aiki salim yayo mata cefane kona dari ne naman dari biyu tayi yar miya ta dafama Alhaji Ahmad taliya, damam hakan takanyi, dan idan yasan kalar abincin da take dafama yaran tashin hankali zai mata marar misaltuwa.
Shinkafar take kwashewa tana fadin
"Haba yara, wannan shinkafar ruwan jakara ce, in kunqi ci yau, kunci gobe"
Abdulkadir ya shigo, ya dan tsoratata dan ganin shi kawai tayi
"Kai dan ubanka baka iya sallama bane?"
Kallonta yayi rai a bace
"Karki sake zagina gaskiya tunda nayi sallama tun daga falo, ba laifina bane in bakiji ba"
Baki a sake Mama take kallon shi, rashin kunyarshi karuwa take duk rana
"Zaka rama zagin ne Abdulkadir?"
Rabata yayi yana dauko plate, ko Hajja inta zage shi ji yake kamar ta watsa mishi ruwan zafi, dan gani yake a shekarun shi ya girmi zagi, in yara sukaji ai saisu raina shi.
Balle kuma Mama da baiga dalilin da take dashi na zagin shi ba.
Wani ludayin ya dauko yana shirin sakawa cikin kular abincin da ko kadan yanayin shi bai kwanta mishi ba
"Karka batamun wani ludayin, ga wani nan..."
Ta fadi tana miqa mishi, karba yayi ya saka a ciki yana jujjuya abinci
"Meye wannan baqi-baqi a ciki?"
Ya tambaya yana daquna fuska
"Abin crayfish ne..."
Kallonta Abdulkadir yayi
"Crayfish kuma?
Meye yasa za'a saka mana a abinci...me yasa ba za'ai mana da nama ba"
Shisa taki fitowa tun dazun, ta dauka duk sun gama dibar abinda zasu diba tunda taga lokacin tafiya islamiyyar su ya kusa, duk a cikin yaran gidan shi kadai yake tsareta da tambaya kan abinda ta dafa musu, bamai mata wannan fitsarar sai Abdulkadir, har bataso yaganta ranar girkinta, tana kuma shakkar yaje ya samu Abba da maganar dan tasan tsaf zai iya.
Dan murmushi tayi
"To ai ana sakawa, yama fi nama zaqi..."
Ta fadi a fili a ranta tana
'Dan iska yaro mai baqin hali irin na uwar shi'
Cigaba da jagula abincin yake da ludayi, ranshi yake jin yana kara baci, duk kwana biyun da zatayi a jigashe suke yinshi, har yaranta, saboda kalar abincin da take dafa musu.
"Nikam gaskiya bazanci wannan jagwalgwalon ba"
Ya fadi yana ajiye plate din daya dauka yabar mata ludayin cikin kular ta juya ya fice daga dakin
"Karkaci dan ubanka, in girkina ya zagayo ita din zaka sake dawowa ka samu, shegen iyayin banza da wofi.
Yaro ga rashin kunya malam..."
Mama take cewa tana kwashe sauran shinkafar a robobin ta rufe su ta saka a fridge, harta koma daki bata daina kwashe ma Abdulkadir albarka ba.
Shikam bangaren su ya koma yana samun Zahra ta dauko uniform din islamiyar ta a hannu
"Sannu Hamma"
Tace mishi, dan baka isa ku hadu ka wuce bakai ma koda sannu bane ba.
"Zahra ki dafamun ko taliya"
Ware mishi idanuwa tayi
"Hamma guga zanyi...
Lokacin islamiyya kuma ya kusa, dan Allah kayi hakuri"
Ta karasa maganar idanuwanta na cikowa da hawaye.
Agogo ya kalla, uku da rabi harda wasu yan mintina akai
"Tsayuwar me kike?