← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 94

Sashe 84

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranta baci yake yi duk idan akai mata fada, balle kuma yanzun da take jin tayi girman da duk wannan abubuwan bai kamata ana mata su ba, ranta a bace tace
"Karka ce haka..."
Tunda shi ba zama yake gidan ba, kuma Waheedah din na wanke mata da, bai sani bane ba
"Dama can nake kaiwa, yaune kawai ta dawo dashi"
Sosai AbdulKadir yake kallon ta
"Wankin kike dauka daga nan, sai ki kai bangaren ta, sai ta wanke miki?"
Yayi tambayar yana saka Nuriyya jin kamar tayi wani laifine, wata yar dariya AbdulKadir yayi da ko kadan batada alaka da nishadi kafin ya sauko daga kan gado yana ficewa daga dakin ya doko kofar kamar zai karyata.

Bangaren Waheedah ya nufa ko sallama baiyi ba yanda ya tura dakin yasa ta bude idanuwanta daga baccin daya soma fisgarta
"Wanki kike ma Nuriyya?

Akan wanne dalili?"
Ya bukata yanajin yanda ranshi yakai koluluwa wajen baci
"Baka taba kula ba sai yanzun?"
Waheedah ta bukata a sanyaye, dan yana gidan Nuriyya take kwaso wankin ta kawo mata bangarenta, shisa ta dauka yasani.

"Karki amsa mun tambaya da tambaya, karki kara batamun rai Wallahi"
Yanda yai maganar da yanayin fuskar shi yasata sauke idanuwanta daga cikin nashi, akwai yanayin da tasan ba zata fara gwada hakurin shi a cikin su ba, yanzun na daya daga cikin su
"Ko ban sai mata engine wanki ba, akan wanne dalili zakiyi mata wanki?

Ajiyeki tayi?"
Numfashi Waheedah ta sauke
"Ina azumi nikam"
Kankance mata idanuwa tayi
"Ni nace miki bana azumin ne?"
Kai ta girgiza mishi a hankali, tana jin murmushin da yake shirin kwace mata, tayi kewar rikicin shi
"Allah ya baka hakuri Sadauki, yanzun ai zata wanke abinta kaga, kuma menene dan na hada na wanke?"
Kallon da yai mata yasa ta yin murmushi
"Yi hakuri"
Tsaki kawai AbdulKadir yaja yana ficewa daga dakin, su duka biyun haukata shi suke sonyi yaga alama.

Akwai halayen Nuriyya da yawa da yake kula dasu yanzun da baya ganin su da, dakin ya koma yana samunta inda yabarta, bandakin ya wuce ran shi a bace har lokacin, tsayen da Nuriyya taga yayi ne yasata bin shi, nuna mata yanda zatayi amfani da injin wankin yayi, bama komai tagane ba saboda a masife yake nuna mata komai, yana gamawa ya fice daga dakin, falo ya koma ya kwanta kan doguwar kujera yana huci shi kadai.

Ga hanjin shi daya tattaru ya kulle waje daya.

Bacci yake son yi, rana na karawa kuma, yana so yadan shiga kasuwa, dan ba zai ba Nuriyya kudin shi ba.

Komawa dakin yayi ya dauko wallet da mukullin mota sai wayar shi ya fita daga gidan.

Dakyar ya dawo gida, har wani haske-haske yake gani yana gilmawa ta cikin idanuwan shi saboda yunwa.

Ga makoshin shi kamar sahara, a bushe da kishi, a hanya ya tsaya yai azahar, kayan ma dakyar ya fito da su daga mota, daga dankali sai doya da cefane ya siyo, sai kuma kwai da dakyar ya samo shi.

Ga kasuwar a shaqare, darajar watan azumi shisa duk wanda ya take mishi kafa in ya bashi hakuri ko amsa baya samu, amman da mutanen da zai mara Allah kadai yasan yawan su, duk da haka saida ya watsa ma wani me napep zagi, baiko juyo ba illa kara gudun napep din ganin wandon sojoji a jikin AbdulKadir din.

Yana shiga ya wuce bangaren Nuriyya ya ajiye kayayyakin a bangarenta, tukunna ya koma mota ya dauko apple din daya gani yana shiga dakin Nuriyya, a falo ya sameta zaune, ta kwantar da Ikram a kujera tana mata wasa, sallamar shi tasa ta amsa tana dago da kanta, fuskar shi ta kalla taga gajiyar da take tattare da shi, ledar ya mika mata tasa hannu tana fadin
"Sannu da gajiya..."
Kai AbdulKadir ya jinjina mata, yana kallonta, jira yake tace mishi zata hada mishi ruwan wanka ya watsa ruwa, ko batace haka ba, ta fada mishi wani abin, ta nuna mishi damuwarta kamar yanda ta saba, amman ta ajiye ledar apple din tana mayar da hankalinta kan Ikram
"Wahee nagaji sosai, kuma yau ana rana"
Hancinta ta hada dana Ikram din da take wangale bakinta da babu hakora, suna saka zuciyar shi cika fam da kaunar su, hankalinta na kan Ikram din tace
"Sannu, akwai rana kam, ni da nake cikin gidama inajin zafi"
Kallonta yayi, muryar shi da wani irin sanyi yace
"Nasan nayi laifi, nasani Wahee, ki horani ta kowanne fanni zan dauka.

Amman wannan rashin kulawar banda ita, zuciyata ba zata dauka ba Wallahi"
Yanda ya karasa maganar ya sata yin shiru batace komai ba, tanajin shi ya juya ya fice daga dakin.

Numfashi ta sauke me nauyi, sai taji wani irin kadaici ya danneta, kewar Fajr takeji, da yana nan da ya dameta da surutun shi, addu'a take a kasan ranta, Allah yasa AbdulKadir din yaje ya taho dashi, tunda ita ba zata iya kira tace a dawo dashi ba.

Tana nan zauna aka kira sallah, ta tashi ta dauki Ikram suka koma daki.

AbdulKadir yana shiga dakin Nuriyya a kwance ya sameta kamar gawa, har saida ta tsorata shi ganin ko motsin kirki batayi
"Nuriyya..."
Ya kira, tana dago kanta dakyar ta kalle shi, dariya yaji ta kubce mishi
"Duk azumin ne?"
Ya tambaya yana zama gefen gadon, ta matsa mishi can, duniyar takeji ta hade mata waje daya, ga baqar yunwa da take addabarta, ga wankin da tayi akwai kayan da suke zuba, duk ta hade su da masu haske.

Harta zanin gadonta yayi kampala-kampala, zaman gidan takejin ya gundureta, ga kuma fadan AbdulKadir din.

Zama tayi tana tunanin rayuwar da ta tsarama kanta kafin shigowa gidan shi, da wannan da takeyi yanzun.

Ga kuma Waheedah ta kara sawa komai ya kwance mata, mamaki takeyi tana karawa, babu kalar tunanin da batayi ba, ko wasu kawaye Waheedah tayi masu mugun hali da suka bata shawarar canza mata haka.

"Wallahi bakaji cikina ba, kamar an mun sata"
Murmushi AbdulKadir yayi, zuciyar shi yakeji tayi nauyi a kirjin shi.

Kan gadon sosai yahau ya kwanta, idanuwan shi ya rufe yanajin gajiya sosai.

Bacci yayi har la'asar dan saida Nuriyya ta tashe shi tukunna yai alwala ya fita masallaci.

Sanda ya dawo sun kawo wuta, yai zaman shi a falo yana kallon namun daji a tashar discovery.

Har wajen biyar kafin yaga Nuriyya ya fito daga dakin tana bin bango, shima yunwar yakeji.

Kitchen ta shiga tana rasa abinda zata farayi, batama san abinda zata dafa ba, tunda bataga alamar Waheedah zatayi girki dasu ba.

Ita yau ma ba zataje bangarenta ba, alkawari taiwa kanta.

Zama tayi ta yanki doya ta fere tana samu ta dora, tunda taga kwai, gara ta soya musu doya da kwai kawai.

Bude fridge tayi taga babu lemo ko daya sai ruwa, falo tazo tana samun AbdulKadir din tace
"Masoyi bamu da abin sha fa a dakin
nan, ko fanta ka siyo mana"
Yana rike da remote, hankalin shi nakan tv ya amsa ta da
"Banda kudi"
Yana cigaba da kallon shi, abinda ya zame mishi dole yayi shi zaiyi, tunda tai mishi barnar kudi zata gane kuskurenta.

Tsaye tayi tana kallon shi cike da mamakin fadin bashida kudi da yayi, ranta a jagule takejin shi
"Me zamuyi buda baki da shi to?"
Har lokacin bai kalli inda take ba ya amsa da
"Nima ban sani ba"
Yana cigaba da kallon shi.

Kitchen Nuriyya ta koma, ta cika kamar zata fashe, dan ta kashe dubu arba'in shisa yake mata wannan wulakancin, wayarta ta dauka tana duba account dinta taga babu abin arziqi a ciki.

Kudin hannunta kuma bai wuce dubu hudu ba, shisa take karajin kamar batada lafiya, dan ta tsani taji babu kudin kirki a jikinta, in ba zai bata ba tasan zai ajiye, zata kuma diba idan ya ajiye.

Dan tana bukatar abubuwa na ciye-ciye.

Doyar ta sauke da tafasa daya tayi ta tace ta.

Ko gishiri ta manta ana zubawa balle dan sikari tunda sabuwar doyace, ko ba sabuwa bama taste din nayin dadi na daban inka dan saka sikari.

Ruwa ta maka mata, ta dauki cefanen ta juye wajen wanke wanke ta gyara shi, jiri ma takeji saboda yunwa.

Markadawa tayi duka ta juye shi a tukunya.

Tana da danyar kaza a fridge ta daukota, ba zata iya wata wahala ba, itama ruwa ta saka mata ta wanketa, da kankara a jiki har lokacin ta dauketa tana zundumawa cikin kayan miyar tunda a yayyanke take, kankara ce tayi, zata narke in taji wuta, ta zuba ruwa kofi biyu, duk su hadu su tafaso tare sai tayi miyar da yawa ta saka a fridge, diba kawai zata dingayi.

Mai ta dauko ta bulbula a kai, ta bare maggi ta zuba ta rufe tana komawa daki ta kwanta.

Mintina talatin ta ba miyar ta fito tana ganin ruwan ya tsane, jujjuyawa tayi ta sauketa tana kashe gas din.

Doyar ta yayyanka ganin yamma tayi sosai, ta kada kwai ta zuba maggi, ta dora mai.

Yar albasa ta dauka ta yanka cikin kwan tana tuna cewar bata zuba a cikin miya bama.

Karamin tsaki taja tana kara dauko wata albasar ta yayyanka a plate ta bude miyar ta zuba a ciki ta mayar ta rufe, tukunna ta zuba doyar cikin kwan ta cakuda ta juye ta gabaki daya a cikin mai tana komawa gefe ta tsaya.

Aikam ya fara tasowa yana zuba har kasa, gabanta yai wata irin mummunar faduwa, zuwa tai kashe gas din mai ya zubo mata ta saki ihun da yasa AbdulKadir shiga kitchen din da gudu.

Hannu yakai yana kashe gas din ya kama na Nuriyya zuwa wajen famfo ya sakar mata ruwa
"Mahaukaciya ce ke?

Me kikeyi haka?"
Hannunta ta cire daga cikin ruwan tana yarfewa saboda azaba.

Turo baki tayi kawai dan tanayin magana fashewa zatayi da kuka, batasan me yasa komai yake jagule mata ba haka.

Shi kanshi AbdulKadir din ranshi yaji ya kara baci, kananun fada haka ba halayyar shi bane ba, amman a kwanakin nan jin shi yake komai ma na fada ne, ganin idan ya tsaya a kitchen din fada zai mata yasa shi fita kawai ya koma ya zauna inda ya tashi.
Chapter 84 · 0% Book details