Sashe 50
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Numfashi Yassar ya sauke, yana hango AbdulKadir din ya ziro kai ta window din motar ya kalli maigadin da bai bude mishi kofa da wuri ba, da sauri Yassar ya taka ya karasa kafin ya jibgi yaron mutane a banza.
"Dan kanwar uwarka bakaji karar mota bane halan?"
AbdulKadir din ya tambaya yana kallon yaron da yake a tsorace, da hannu Yassar yai mishi alamar ya matsa, da kanshi ya bude ma AbdulKadir din mota yana fadin
"Allah ya tsare Samarin Hajja..."
Tsaki AbdulKadir yaja
"Idan na zageka a fili yanzun zakace na maka rashin kunya"
Wata irin dariya ta kubce ma Yassar din, har AbdulKadir din ya figi mota, Yassar na tsaye ya rike gate din yana kwasar dariya, dakyar ya samu ya shiga cikin gida, har lokacin da murmushi a fuskar shi, a rayuwar shi bai taba hango abinda zai saka AbdulKadir susucewa a yini daya haka ba, har Waheedah din da kanta kuwa...!
#AnaTare
#TeamAbdulKadir
#TeamWaheedahFacebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
TAQABALALLAHU MINNA WA MINKUM
Tana kitchen din har aka kira sallar Magriba, bata mike ba saida ta karasa yanka dankalin tukunna, wanke shi tayi ta tace a kwando, tana ganin kamar yankan yayi girma, amman ta riga ta gaji, ko bata gaji bama ba zata sake tsayawa yankawa ba, ranta a bace take jin shi.
Gas ta kunna ta dora kasko ta zuba mai a ciki, tunanin ta barbadama dankalin gishiri bai zo mata ba, man ma ko dumi baiyi ba, balle yayi zafi, ta dibi rabin dankalin ta zuba a ciki tukunna ta fice daga kitchen din.
Dakinta ta wuce tana shigewa bandaki ta dauro alwala ta fito, sallah ta gabatar a nutse, bata tsaya addu'a ba ta tashi ta nufi kitchen din dan ganin halin da dankalin ta yake ciki.
Danqare ta same shi, kasancewar man da yasha yayi luntsum, haka ta cigaba da cakuda shi, duk ya kakkarye ya dame cikin man, yana kara jagula mata lissafi gabaki daya.
Batajin a cikin abubuwan da mata sukeyi na zaman aure akwai wanda yakai girki bata lokaci da wahala.
Bata taba tunanin suyar dankalin zatai mata wannan rashin mutuncin ba, barin shi tayi yadan karayi, tukunna ta kwashe, bata jira man ya tsane ba ta juye a wani kwano da ta dauko.
Sauran dankalin ta zuba, tana komawa falo ta zauna.
Da fitilar wayarta take ta amfani, kasancewar har lokacin basu dawo da wuta ba.
Ga AbdulKadir ya jima, balle yazo ya kunna musu generator, ko kallo tayi ta rage zafi.
Shima sauran dankalin haka taita juya shi duk ya dagargaje mata, ta kwashe tana kallon yanda a ido ma baiyi kyawun gani ba.
Gashi sai tayi wata sauce kuma.
Badan tana tsoron fadan AbdulKadir din ba, kwai zata soya su hada dashi.
Sauran kayan miyar da ta dauko kitchen din Waheedah ta fito dashi ta juye a tukunya tana dorawa kan gas.
Tukunna ta dauko albasa ta fara yankawa, ga yajin albasar daya cika mata ido, ga kayan miyar daya fara kamawa, banda tsakinta bakajin komai na tashi a kitchen din, sai kuma kauri.
Albasar ta zuba ciki, tukunna ta zuba mai wajen ludayi takwas, dan kusan na kaskon da tayi suyane ta kusa juyewa, cakudawa tayi, taga kamar ta mata yawa, ta fara saka ludayi tana rage man.
Ganin miyar na kara konewa yasa ta kashe gas din
"Wanne irin bala'i ne wannan?"
Tai maganar kamar zata saka kuka, tunawar da tayi bata saka maggi ba, guda takwas ta dibo ta bare, dandanqa shi tayi ta zuba a ciki tana cakudawa, sai taga kamar miyar ta kara baqi.
Tabe baki tayi, dan kanta harya fara daukar alamar ciwo.
Sanda ta fito daga kitchen din ana Isha'i, tana da alwalar ta, hakan yasa ta wuce daki, tana idarwa ta fara kiran lambar AbdulKadir, sau hudu tana kira bai daga ba.
Na biyar dinne ta ji ringing din wayar a cikin gidan ta bangarenta.
Hakan yasa ta fito tana dora murmushi a fuskarta
"Sannu da zuwa..."
Kai kawai AbdulKadir ya iya daga mata yana zama kan kujera, wayar shi ya ajiye a gefe.
"In zubo mana abinci?"
Da kai ya sake amsata, ta wuce kitchen din, plate ta samu ta juye dankalin a ciki, tana samun karamun wajen zuba miya ta zuba, ta hado ta fito, a kan kafet ta ajiye.
Tana kallon AbdulKadir da gabaki daya hankalin shi ba'a kanta yake ba.
Kafarshi ta taba, ya sauke wani numfashi mai nauyi.
Waheedah ba zata saka shi kin cin abinci ba, bata isa ta daga mishi hankali yana zaune lafiya ba.
"Meye wannan Nuriyya?"
Ya bukata yana kallon dankalin da ya koma kamar dambu a cikin plate.
Zuciyarta taji ta doka a cikin kirjinta, nan take idanuwanta suka ciko da hawaye.
Ranshi AbdulKadir yaji ya kara baci, inda Waheedah ce ya shigo tana kallon shi zata gane halin da yake ciki, kuma kome zaice mata ba zata nuna ranta ya baci ba dan tasan nashi a bace yake, balle tayi shirin mishi kuka.
"Bana son Kukan banza da bashida dalili, tambayarki nayi, ki bani amsa, meye wannan?"
Hawayen take kokarin dannewa, amman sosai suke mata barazana.
Muryarta can kasan makoshi tace
"Wallahi bansan ya akayi yai haka ba nima..."
Kai AbdulKadir ya jinjina, yasan ana samun akasi wajen girki, a ranakun da ranshi ba a bace yake ba, zai mata uzuri da cewar dan Adam baya wuce kuskure, amman yau haushin shi yake son hucewa akan kowa ya samu, ita kadai ce kuma a gaban shi.
"Hannu zan saka?"
Ya sake bukata yana kankance mata ido, kai ta girgiza mishi da sauri, tana mikewa ta wuce kitchen din, sai da ta matse kwallar da ta taru cikin idanuwanta, tukunna ta dauko cokula guda biyu ta dawo, mika mishi tayi ya karba, yana sakawa cikin miyar daya rasa gane wace iri ce, ga man da yake kwance a miyar zai iya ganin fuskar shi in ya leqa cikinta.
"Me yasa baki saka mana nama ba?
Wacce irin miya ce wannan?"
AbdulKadir ya karasa tambayar yana jujjuya cokalin shi cikin miyar, kafin Nuriyya ta amsa ya sake fadin
"Ni sauce nace kiyi mana, ita Waheedah takeyi idan ta soya mana dankali"
Yau ne karo na farko da Nuriyya taji takaicin rashin iya girki a rayuwarta, dan shine karo na biyu a rana daya da AbdulKadir ya hada girkin ta dana Waheedah, kishin da takeji kuwa kirjinta har zafi yake mata.
Shikuwa sunan Waheedah daya fadi yasa ranshi kara baci, babu shiri ya dibo miyar ya zuba akan dankalin daga gefe yana cakudashi kamar shinkafa ya dibo da cokalin yakai baki, yana jin kaurin daya cika mishi hanci daga cikin bakin nashi.
Hadiyewa yayi batare daya tauna ba, dakyar ya iya cokali hudu, yunwar da yake tunanin yanaji ya nemeta ya rasa.
Mikewa yayi kawai, Nuriyya na binshi da ido harya fice daga falon.
Tsoron kar yai mata fada yasa bata tambaye shi inda zaije ba.
Ita kanta a dole takecin dankalin, sai da taji cikinta ya cika tukunna ta kwashe kwanukan ta mayar kitchen, ta dawo ta zauna, jin har lokacin AbdulKadir bai tashi generator yasa tayi tunanin ko ta kira wayar shi, sai taganta ajiye akan kujera.
Salama ta sakama ranta taci gaba da danne-danne wayar da rashin abin kallo ya sakata.
Dan ita ba ma'abociyar chatting bace ba, daman karatu ne, nan tafi kwarewa, to duk litattafan da take bi, ba'a dora sabon cigaba ba.
AbdulKadir kuwa waje ya fita yana samun waje kan matattakalar shiga gidan ya zauna.
Yana kallon farin watan da ya haske harabar gidan, yana kuma daukar tunanin shi ya watsa satin su na biyu da tarewa a gidan shi da Waheedah.
Tunda sukaje gida ta samo fina-finai wajen Nabila, data gama aiki bata komai sai kallo, daya tambayeta wanne irin film ne tace mishi Korean, jiya daya farka yaganta tana kallo, da kan shi ya kashe system din, sai da ya zare mata ido da gaske tukunna ta hakura ta kwanta, da ta shagwabe fuska zatai mishi kuka.
Yau ma aikin kallon takeyi da gab yake da haramta shi saiya bar gidan, tunda ta rage samun lokacin shi.
Hidimar shi ya gama yi ya fita sallar isha'i.
Fajr na dakin shi yana bacci, dan shi da anyi Magriba cikin shi ya dauka sai bacci, inba yanajin rigima ba.
A matattakalar shiga gidan ya sameta zaune, jikinta sanye da rigar sanyin shi da ba hannun bane kawai yai mata yawa, har da rigar gabaki daya, sai dai Waheedah ce, haka take mishi, sai dai yaga rigunan shi a jikinta, inyai magana zata ce kamshin turarukan shi take so, kuma gasu a ajiye.
Yakan ce ta fesa ta ajiye mishi rigar shi, dariya takeyi kawai
"Kamshin ai ya hadu da naka...."
Shine amsarta lokutta da yawa.
Murmushi kawai yakanyi, a duniyar shi gabaki daya, ita kadai take mishi abinda take so, ita kadai yake cewa tayi abu ta maqale mishi kafada alamar ba zatayi ba, kuma ya hakura, wani lokacin ma kai kawai zata girgiza, idanuwanta na cikowa da hawaye, sai yaji gabaki daya gwiwoyin shi sunyi sanyi.
"Me kike a waje?"
Ya bukata yana karasowa ya zauna kusa da ita.
Hancinta da sanyi ya cika ta ja, tukunna ta amsa shi
"Wata nake kallo"
Murmushi ya kwace mishi mai sauti
"Wata?"
Ya maimaita cike da alamar tambaya, yana kallon ta, kai ta daga mishi.
Gabaki daya film din da ta gama kallo ya tafi da imaninta, duk wani abu da akai a film din taji tana sonyi itama, balle kuma kalar soyayyar da aka zuba.
Sai dai akwai haukan da ita kanta tasan ba zata fara tunkarar AbdulKadir da shi ba.
Shisa ta fito ta kalli watan abinta.
"Me yasa zaki fito kallon wata?"
Ya kara tambaya har lokacin yana kallon ta, shagwabe fuska tayi
"Ba'a magana fa Sadauki, shiru akeyi a kalli kyan watan...
Da yan....Subhanallah...."
Waheedah ta karashe tana mikewa babu shiri tana fara zazzage skirt din dake jikinta tana dorawa da
"Cinnaka...
Hamma cinnaka wallahi..."
Skirt din take zazzagewa tana murza cinyarta da take da tabbacin cizon daya manna mata ya wuce biyu.