Sashe 32
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallon shi Waheedah takeyi
"Kanka na ciwo fa Hamma..."
Dakuna mata fuska Abdulkadir yayi
"Nifa bazan sha wani magani ba"
Yazid Waheedah ta kalla da yake tsaye yana kallon su, shima Panadol din yake bukata, ji yake kamar yai ihu ko zata ga yana bukata fiye da AbdulKadir din ta bashi
"Hamma kai mishi magana.
Kan shi yana ciwo wai bazai sha magani ba"
Kallonta Abdulkadir yayi yana tunanin idan Zainab ce da yanzun ya kwada mata marin da bakinta bazai sake gigin kai karar shi ba, amman Waheedah ce, batayi hakan dan ta raina shi ba, yana ganin damuwa tattare da muryarta.
"Ki kyale shi tunda bazai sha ba"
Yazid ya fadi, yana kuma jin tun maganar ta fito daga zuciyar shi dake wani irin ciwo.
"Hamma..."
Waheedah ta kira cikin sanyin muryarta da yasaka Yazid din juyawa yana dana sanin fitowar da yayi.
Bazai yiwu yanajin azababben kishin Abdulkadir ba, AbdulKadir ne, kanin shi, dan uwan shi ciki daya.
Amman zuciyarshi batasan wannan ba, kishi yakeji har idanuwan shi na lumshewa
"Me yake faruwa ne?"
Yassar daya karaso wajen ya tambaya
"Bakomai..."
Abdulkadir ya fadi a lokacin da Waheedah tace
"Kanshi ne yake ciwo kuma wai bazai sha magani ba, har na ballo kuma"
Kallonta Abdulkadir yayi ciwon kan da yake ji na karuwa
"Bazan sha ba, ni babu maganin dazan sha.
Nace ki ballo mun?"
Yake fadi cike da masifar shi
"Karbi maganin nan kafin inci ubanka, tunda ta ballo sai kasha wallahi.
Kaji na
rantse"
Hannu Abdulkadir ya mikama Waheedah da take murmushi tana sakashi kankance ido cikin son watsa mata harara.
"Mincika..."
Yassar ya fadi yana kwashewa da dariya hadi da dorawa da
"Anya ba'aima Hajja musayarka a asibiti ba?
Abdulkadir wanne irin idone wannan?"
Maganin Abdulkadir ya saka a bakin shi ya bude robar ruwan ya hadiye tukunna ya watsama Waheedah da Yassar din harara, yana saka Yassar sake kwashewa da dariya, mukullin motar shi ya saka a jiki ya bude.
Bayan motar Abdulkadir ya bude ya shiga, yana dakuna fuska, tsakanin shi da Allah fushi yake an sakashi shan magani.
Yazid ma bayan ya bude ya shiga ta bangaren shi.
Hakan yasa Waheedah bude gaban motar zata shiga, hango Nuriyya tayi ta shigo gidan, dan tare da ita sukan tafi tunda Babansu bazai taba jerawa ya tafi idi da ita ba.
Irin atamfar jikin Waheedah ce ta saka itama, dan tare Abba yai musu da duka sauran matan gidan.
Hijab ce dako gwiwarta bata kai ba, daga inda Waheedah take tana hango kwalliyar da take fuskar Nuriyya, musamman jambakinta.
Tana kuma hango yanda kugunta ya fito cikin skirt din da take sanye dashi, dan ita riga da skirt tayi.
Kai kawai Waheedah ta girgiza dan in tai mata magana kan cewa hijab din tayi karama fada zasuyi da safen nan.
Daman sunyi wani kan Anas.
Karasowa Nuriyyar tayi
"Wallahi na dauka kun tafi, inata sauri"
Kai Waheedah ta girgiza mata
"Yanzun dai zamu tafi.
Na dauka ba zakije ba"
Hararata Nuriyya tayi, tana ganin ta mata wani irin kyau naban mamaki.
Dariya Waheedah tayi ta bude gaban motar ta shiga.
Zagayo Nuriyya tayi ta bude bayan motar ta bangaren Abdulkadir da tunda yaji muryarta ya runtsa idanuwan shi yana budesu da wani irin bugawa da zuciyarshi tayi.
Har addu'a yayi karya ganta harya tafi, yanzun ma kokarin kin juyawa yake yaji ta bude kofar, baisan lokacin daya juya ba, yana nasarar sauke idanuwan shi cikin nata.
Janbakin ta na saka wani abu cikin kanshi yamutsawa.
Tsarin kwalliyar da take fuskarta na samun wajen zama cikin kanshi.
Kallon shi Nuriyya tayi, bugun zuciyarta nayin dai-dai da nashi.
Yayi mata wani irin kyau cikin farin yadin shi, ga wani irin kamshi da yake, yau kam sosai take jin kasancewarta sallah.
Murmushi tayi tana zama cikin motar ta rufe murfin tukunna tace
"Ina kwananku"
Yassar ne ya amsa yana dorawa da
"Nuriyya anyi sallah lafiya?"
Amsa shi tayi, turarenta na cika hancin Abdulkadir din, yana saka shi sauke numfashi a wahalce da yanayin da yakeji.
Dan matsawa ya sakeyi jin yanda tayi kusa dashi da yawa, amman hakan bai rage mishi komai ba, saima hannunta daya kalla da take gyara hijabinta dashi, itama kunshine, ja da baqin lalle daya saka shi runtse idanuwan shi yana kirga daya zuwa hamsin, har yaji Yassar ya tayar da motar ya juyata suna ficewa daga gidan.
Idanuwan shi ya bude yana gyara zaman hannun shi daya dauke babu shiri jin ya taba na Nuriyya, ta gefen idanuwan shi yaga ta kalle shi da idanuwanta da taja da eyeliner suna kara fitowa.
Wani abu Abdulkadir yake ji tun daga dan yatsan kafarshi zuwa tsakiyar kanshi da kusancin da Nuriyya tayi dashi.
Ita kam yau ranta kal ta zauna kusa da Abdulkadir, ta kuma lura da a takure yake, zataji dadi idan ya zamana itace tai affecting dinshi haka, yana nufin koyayane ya damu da zamanta.
Inda idanuwan shi suke kallo take nema kafin ta kula da hannunta ne, dayan hannu ta zaro tana ci gaba da wasa da yatsunta.
Abdulkadir na kula da yanda har cikin tafukan hannuwanta itama kunshine, sai dai nata da ratsin baqi, na Waheedah kuma gabaki daya jan lalle ne.
Dakyar ya raba idanuwan shi da hannayenta.
Dan yana gab da rike su, ita kanta ji yake kamar yasa dan yatsa ya dangwali jambakin da yake lebenta yaji yana da maiqo ko idanuwan shine kawai suke gane mishi har kyalli yake.
Da gaske zuciyar shi raini take neman ja mishi, yana da wannan tabbacin yanzun.
'Kar muyi haka dake, dan Allah, terma four na shiga.
Ba yanzun zan settling ba, saina gama NDA na fito, an posting dina wajen da zanyi aiki na nutsu tukunna'
Abdulkadir yake magana da zuciyar shi yana rokonta data saurare shi, bashida wajen soyayya yanzun.
Baya komai a rayuwarshi babu tsari.
Wannan ne karo na farko da hakan ya kwace mishi akan Nuriyya, shisa yake jin komai ya cunkushe mishi, komai baya mishi dadi dan baisan yanda zai da ita ba.
Ya rasa yanda zai da ita.
Kokawa yake da kan shi da zuciyarshi akanta, yanzun kasancewarta kusa dashi yasa shi jin komai ya kara kwacewa daga hannun shi.
Motar yaji Yassar ya tsayar alamar sun karaso.
Kokarin bude kofar Nuriyya take amman ta kasa
"Hamma na kasa, kofar taki budewa"
Nuriyya ta fadi tana kallon shi cike da wani irin rauni da yake ji har bayan zuciyarshi.
Baisan lokacin dayakai hannu ya bude mata kofar ba.
"Nagode..."
Ta fadi tana ficewa, idanuwan shi ya runtsa ya bude su, yana dan dafe kanshi da yake kara sarawa
"Yazan yi ne wai?"
Yai tambayar yana dukan jikin motar kamar ita tai mishi laifi...!
*#TeamAbdulKadir*
*#FWA*
*#AnaTare*[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732:
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
"Mutumin da kike so na tare da uniform din nan, ban san waye ni batare dasu ba, ban taba son kaina babu su ba, bana tunanin zaki iya"
Kai ta girgiza mishi, hawaye ne cike da idanuwanta amman sunki zuba, in haka masu ciwon zuciya suke ji zasu kasance cikin addu'arta a ko da yaushe, saboda ciwo ne mai matukar radadi.
"Ba soyayyar nake tsoro ba Sadauki, ba mika maka dukkan zuciyata bane yake mun wahala, rashin tabbacin ka a rayuwa ta ne, bazan damu da raba soyayyarka da Uniform dinka ba, shi din da yafi ni muhimmanci ne matsalar"
Ta karasa maganar tana jin dacin son kan da take son yi a harshen ta, zabi take bashi, ita da take bakuwa a rayuwar shi ko Uniform dinshi daya girma da soyayyar shi?
Tana jin idanuwan shi na yawo a fuskarta cike da son ta dago nata su sauka cikin su, amman taki yarda hakan ya faru.
"Waheeda..."
Ya kira sunanta, yana jan haruffan cikin sigar da shi kadai yake iya hakan.
"Karki ce mun in zaba...
Ba zaki so amsar ba"
Runtsa idanuwanta tayi tana bude su da wani irin ciwo.
Me yasa yaki ganin abubuwan data sadaukar saboda soyayyar shi.
"Duk abinda kike tunanin kin sadaukar saboda soyayyata bai kai uniform dina muhimmanci ba...karki so kanki da yawa haka"
"Adda!
Addaa!!"
Idanuwanta da take ji sun mata nauyi ta bude, tana jin Amatullah ta kwashe da dariyar da ta sata jan karamin tsaki, dan mafarki take, kamar yanda a kwanakin nan mafarkan AbdulKadir din suke addabarta.
A cikin daya daga mafarkan ta kira shi da Sadauki, tun bayan tashin ta tsinci kanta da kiran shi Sadaukin dan sunan ya dace dashi ta kowanne fanni.
Batasan murmushi ya kwace mata ba saida taji Amatullah ta sake kwashewa da dariya
"Addaaaaa!"
Hararta Waheedah tayi da yasa Amatullah din sake yin dariya
"Jiba inda kike bacci fa, cikin kaya"
Miqa Waheedah tayi hadi da yin hamma tana miqa hannu ta dauki wayarta qirar Nokia Symbian E5 dake ajiye a gefe ta danna dan ta duba lokacin, karfe biyu harda kwata.
Gabaki daya jikinta a gajiye take jinshi.
"Anata nemanki fa..."
Kai Waheedah ta dagama Amatullah din, tana kallo ta fice daga dakin.
Zaune tayi a wajen tana tunanin ta inda zata fara miqewa, gajiyar da take ji har cikin tsoka da kasusuwan jikinta.
Idanuwa ta lumshe, fuskar Abdulkadir na mata yawo, wata irin kewar shi take ji taban mamaki, zata alaqanta hakan da jimawa da tayi bata ganshi ba, tun hutun da yazo na sallah, shima ranar idi ne, tun da suka dawo daga masallacin idi bata sake sakashi a idanuwanta ba harya tafi.
Satin da zata fara zuwa makaranta, Babban Yaya ya basu wayoyi, taga cikin mazan gidan ma kusan duk ya ba 'yan matasan.
Matanne yace sai sun gama aji shidda.
Sosai taji dadin kyautar wayar har ranta.
Yassar ya saka mata manhajar kafofin sada zumunta, ciki harda Whatsapp, har kati Yassar din ya saka mata.
Lambar Abdulkadir ce ta farko da tazo sakawa taga Yassar duk ya saka mata lambobin su.
Sunan kawai ta sake zuwa Sadauki.
Shi kuma ta fara dubawa a whatsapp, sai lambar ta nuna bayayi.
Sosai zuciyarta taji tai mata nauyi, lambar Yazid ta nema taga Yassar ya saka mata, shi kuwa yana Whatsapp.
Sallama tayi mishi tana fada mishi itace.
Shima tayi kewar shi ba kadan ba.