← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 94

Sashe 67

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dai akwai bangaren shi da takejin bata sani ba, sannan mutum ne shi mai wahalar sha'ani duk da ba sosai zaman su yake tsayi ba, inya dawo kwana biyune, ita daya, Waheedah daya, amman zatai karya idan tace bata takura da kwana dayan.

Bata cika tsawaita tunaninta akan abin bane kawai, amman AbdulKadir din da Waheedah kanyi magana ko da yaushe daban yake da ita wanda take gani.

AbdulKadir din Waheedah namiji ne da ko a littafin hausa batajin akwai irin shi, dan mazan littafin hausa miskilai ne, AbdulKadir din Waheedah ba haka yake ba, AbdulKadir din Waheedah kan mata abu batare da ta tambaye shi ba, yana girmamata fiye da yanda take nunawa, dan Nuriyya da idanuwanta taga hakan.

AbdulKadir din Waheedah bashi da wani hali marar kyau, ita shine mutumin da take so, mutumin da tayi tunanin ta aura.

Sai bayan auren da ta fara cin karo da kashedi a darenta na farko taji zuciyarta ta tsinke, sai kuma lokutta da dama da zaiyi tunanin tayi mishi abu tayi kokarin bayani ya rufeta da wani irin fada mai cin rai, kananun abubuwa masu tarin takaici da ba zaka gani daga nesa ba, ko kuma take tunanin AbdulKadir din Waheedah ba zai tabayi ba, sannan yana surutai cikin baccin shi, yana firgita sosai, ranar farko da hakan ta faru tsoron shi ta dingaji, musamman da tayi kokarin taba shi bayan ya farka ya hankadeta yana mata wani irin kashedi da har yau bata sake kokarin zuwa kusa dashi in yana surutan shi a bacci ba.

AbdulKadir na da matsalolin da take da tabbacin bata gama gani ba.

Sai dai batasan ita kadai yake nunawa ba, ko harda Waheedah.

Falonta ta koma ta zauna tana jin wasu hawaye masu dumi na zarya kan kuncinta.

Ita dai yanzun koma me zaiyi indai bazai saketa ba da sauqi.

AbdulKadir yana sake kaya, dakin Nuriyya ya koma ya shiga bandaki yana daukar wandon daya cire ya zaro wayarshi da wallet, wayar da take a kashe ya kunna yana fitowa.

Sakonni ne guda biyar suka shigo tana gama loading, budewa yayi, biyu daga MTN ne, daya bankin shine, yasan albashi ne, biyu kuma Yassar ne, ya shiga na farkon
'Lafiyar ka kuwa?

Wayarka a kashe.

Duk da ba ina so ka zo ka dame ta bane, lafiyarka ko?'
Fita yayi yana shiga dayan
'Ka kashe wayarka ne, kayi shiru dan in daga hankalina in goyi bayanka ko AbdulKadir?

Yayi maka kyau'
Murmushi yadan yi duk da nishadi na daya daga cikin karshen abinda yakeji.

Wallet din shi ya saka a aljihun shi.

Ya samu waje gefen gadon yana zama, dan dayaga albashin shi bayaso su kwana baiyi hidindumun da zaiyi dasu ba.

Waheedah ya fara turama kudin nata hidimar na wata kamar yanda ya saba, sannan ya tura ma Nuriyya ma, saiya tura wasu cikin account din shi na ajiyar kudin tsaron lalura.

Ya turana Abba da Hajja.

Kati ya tura ma sauran yan gidan kamar yanda ya saba duk watan duniya, ko yayane yakan tura musu.

Wata natsuwa yaji ta daban daya sauke wannan nauyin.

Wancen watan daya fita ya karo musu kayan abinci, dan shi yake siyan su shinkafa da su taliya, sai mai.

Kananun abubuwa ne yake basu kudin a hannunsu.

Haka suke tsarin da Waheedah, Nuriyya ma data shigo bai canza ba.

Duk da ita tana tambayar shi kudi, Waheedah kuma bazai tuna ranar karshe da ta tambayeshi kudi ba, inya dauka ya bata tana karba, in baibata ba bata taba tambayarshi.

Na Nuriyyar baya damun shi sam, yakan yi mamakin abinda takeyi da kudi ne kawai wasu lokuttan.

Mikewa yayi ya saka wayar a aljihu, mukullin motar shi yagani ajiye akan drawer din kusa da gadon ta, ya dauka ya fito, ko inda take bai kalla ba ya taka yana ficewa daga gidan.

Motar ya shiga ya tayar, kan shi tsaye gidan Yassar ya nufa, yana kallon yanda maigadin Yassar din ya kara sauri wajen bude gate din ganin motar tashi.

Saurayine matashi, daga yanayin shi AbdulKadir din ya fuskanci yaron tsoron shi yakeji.

Har cikin harabar gidan ya shiga da motar yanayin parking, tukunna ya taka yana karasawa cikin gidan.

Sallama yake tayi baiji alamar akwai mutane ba.

Ranar aiki ce yasani, Yassar din zai yiwu yana wajen aiki, matar shi ma tana aiki a asibiti, bangaren accounting tunda abinda ta karanta kenan.

Sai dai yasan Waheedah na nan, dan haka ya taka zuwa bangaren da ya sameta zuwan karshe da yayi.

Kwankwasa dakin yayi tukunna ya tura hadi dayin sallama, kamshi na dukan hancin shi, duk da bana turarukanta bane ba, kamshin yai mishi dadi sosai.

Wani irin tsalle zuciyar shi tayi naban mamaki ganin Waheedah a zaune, doguwar rigace ta atamfa a jikinta wani irin dinki da bazaice ga yanda yake ba, ta saka Ikram cikin jakar goyo ta goyata ta gaba tana tallabe da yarinyar da take bacci.

Kwalliya ce a fuskarta da ba koda yaushe takeyi ba, ta daura dankwalinta ya zauna das a saman kanta kamar a jiki akayi.

Tana zaune gefen gado ta dora kafa daya kan daya, da plate din soyayyen dankali a gefenta da cokali mai yatsu a ciki, ta dora system din da yake zaton ta Yassar ce akan wani dan tebir tana kallo.

Kafafuwanta yake kallo da suka sha zanen flower tayi wani irin ja mai duhu, kafin ya yawata da idanuwan shi yana tsayarwa kan hannunta daya dake tallafe da Ikram da shima yasha kunshin.

Kai ta dago tana kallon AbdulKadir din, zuciyarta na wata irin dokawa da wani sabon tashin hankalin da ta kwana biyar bataji shi ba, duk wani abu da su Yassar suka san zai dauke mata hankali ya rage mata tunani shi sukeyi mata.

Har system din Hauwa dake cike da fina-finai daga American zuwa na indiya harda na korea da tafi so ta kawo mata, ta manta lokacin karshe data huta haka.

Ji takeyi kamar tayi wata takwas rabonta da samun bacci mai nutsuwa, wata takwas rabon da ta zauna ta huta ma rayuwarta, rabon da tayi wani abu don kanta kawai.

Taji dadi da AbdulKadir din bai dameta ba, shisa ta kashe wayarta ta ajiye.

Bashi kadai ba, har yan gidan su batason kowa yayi mata maganar, kuma kowa ya kyaleta.

Yanzun ganin AbdulKadir din na mata barazana da dan kwanciyar hankalin da ta samu, dan jiya da akazo yiwa Hauwa kunshi itama yi mata akayi, jinta takeyi daban, kamar tabaro waccen Waheedahr a gidan AbdulKadir, yanzun kuma watace daban da batasan akwaita bama.

"Wahee..."
AbdulKadir ya kira da wani irin sanyin murya mai tattare da mamakin ganin hankalinta a kwance yake.

Dan ganinta yasa komai dawo mishi, dukan da yasha a barikin sojoji da yake nan garin Kano, yunwar da yake tattare da ita ta kwanaki na rashin samun wadataccen abinci, rashin bacci, da duk wani rauni da baya iya nunawa a gaban kowa.

Itama Waheedah kallon shi takeyi, tana kallon kumburin dake kasan idanuwan shi da tasan rashin bacci ne, da kuma wasu kumburin na alamun duka.

A karo na farko a rayuwarta da taji halin da yake ciki bai dameta ba, ballantana harta tambaye shi ya akai ya shiga ciki.

Dauke idanuwanta tayi daga kan shi tana mayar da hankalinta kan kallon da takeyi, tana kai hannu ta dauki plate din dankalinta tana cigaba daci
"Waheedah..."
AbdulKadir din ya kira wannan karin cike da rashin yarda cewa ita din ce ta nuna mishi halin ko in kula, ita din ce ya shigo waje ta kalle shi taci gaba da wata hidimar kamar baya nan.

Takawa yayi yana karasawa inda take ya zauna gefenta yana son ta sake ganin shi dinne
"Baki ganni bane?"
Ya tambaya yana kallon fuskarta da babu kowanne irin yanayi akai, dankalin data tauna ta hadiye tana tsayar da film dinta dan batason komai ya wuce ta.

"Naganka...

Menene?

Takardata ka kawomun?"
Wata irin dariya mai sauti AbdulKadir yaji ta subuce mishi, tabbas Waheedah na da aljanu, yana mamakin yanda akai basu taba tashi ba sai yanzun, film dinta ta dannama play tana mayar da hankalinta a kai.

Hannuwan shi AbdulKadir ya saka fuskar shi a ciki yana fitar da wani irin numfashi, bashi da karfin yin ko hayaniyar kirki, duk wani kashi da yake jikin shi ciwo yake, yasan yanda ake dukan ma'aikata in na horo ne, sun san inda suke duka da zai shigeka batare daya ji maka ciwon da zai hanaka zuwa aiki washegari ba.

Lokutta da dama ko fuskarka ba zata gwada alamun dukan da kaci ba.

Suna dukan inda uniform zai kare shatikan ko ciwukan.

Sauke hannayen shi yayi yana rutsa idanuwan shi da yanda hakarkarin shi ya amsa, yasan ba karaya ko daya a jiki, amman wajen ya tara jini saboda dukan da yasha, bashi bane na farko, Waheedah kan sa towel da ruwa mai zafi ta gasa mishi ta bashi panadol ko da bayason sha.

"Kwanana biyar a barikin sojoji..."
AbdulKadir ya tsinci kanshi da fadi da wani irin sanyin murya, Waheedah batama ji shi ba, dan gabaki daya hankalinta ya tattaru kan kallon da takeyi, hannu AbdulKadir yakai yana rufe system, hakan yasa ta kalle shi
"Bana so, banma ga dalilin da zaka shigomun daki ka nemi dagamun hankali ba"
Murmushi AbdulKadir yayi
"Ina da duk wani dalili da zan shigo dakin nan, hankalina ba'a kwance yake ba, banga dalilin da zai sa naki ya kwanta ba Wahee, ke kika zabar mana wannan rayuwar...sannan ba dakinki bane wannan...

Dakinki yana gidana"
Da kalar rigimar dake cikin idanuwan shi take kallon shi tana jin dai-dai take da duk wani abu daya shirya tarar ta dashi, gabaki daya yagama fita daga ranta, ko ganin shi batason yi, auren shi takeji kamar wata igiya data shake mata wuya tana hana mata yin numfashi a walwale, shisa take so ya datseta ya warware mata ko zata samu ta shaqi iska mai nutsuwa.

"Bani da daki a gidanka, bani da komai a gidan ka sai kayan da nake gab da zuwa in kwashe dan takardata zaka bani tunda babu inda aka taba aure dole"
Mikewa AbdulKadir yayi, ya dauka bashida karfin yin hayaniya, amman tunda can Waheedah tafi kowa damar bata mishi rai, bata amfani da wannan damar ne sai yanzun.
Chapter 67 · 0% Book details