Sashe 20
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Waje ya samu yayi parking yana bude motar ya fice.
Hoton Waheedah ta mayar inda ta dauko shi, tukunna ta bude murfin motar itama tana ficewa.
Sai da yaga ta fito tukunna ya rufe motar ya soma tafiya, bin bayan shi Waheedah tayi dan gani tai yana sauri sosai
"Kaji Hamma, in dauka?"
Take fadi tana mayar da numfashin daya sashi juyawa ya kalleta, sauri take kamar zata fadi tana kai hannu daya ta dafe mayafin dake jikinta, dayan riqe da wallet dinshi tana kokarin tattare doguwar rigarta ko zata kara sauri, juyawa yayi yanajin murmushi na shirin kwace mishi, bai taba ganin kalar Waheedah ba, baisan meyasa yaji yana so ya kure rashin hankalinta ba.
Sauri ya kara yana bi ta duk inda yaga turmutsun jama'a duk da ga hanya nan dazai iya wucewa, sai da yai wajen mintina biyar a hakan har yana hango kofar wajen tukunna ya tsaya yana juyawa, hangota yai can cikin jama'a an matse ta, sai kokarin turmutsowa take da hannuwanta da suke mishi kama da sandar siririn rake.
Murmushin da yake ta dannewa ne ya kwace mishi, kai ya girgiza
"Wallahi yarinyar nan bata da hankali..."
Abdulkadir ya fadi yanajin nishadin da ya rasa daga inda yake fitowa, komawa yayi baya dan yaga alamar mutane na gab da ture Waheedah ta fadi kasa, in wani ya takata yana da tabbacin karyewa zatai bal, hannunta ya kama yana janta, banda maida numfashi babu abinda takeyi, hanyar da babu mutane yabi da ita, dakyar take tafiya saboda batasan wahala irin wannan a rayuwarta, dakyar ta iya cewa
"Hamma sauri kake kamar zaka tashi sama wallahi...."
Dariya yaji ta kubce mishi
"Lalaci ne yai miki yawa"
Ya fadi yana ci gaba da janta, binshi take da duk saurin da zata iya har suka shiga wajen daya qawatu babu laifi tukunna Abdulkadir din ya rage saurin da yakeyi yana sakin hannunta, numfashi ta mayar tana fifita fuskarta da wallet din shi saboda zufar wahalar da take jin tanayi.
Kankance idanuwan shi yayi a kanta, kafin ya mayar da hankalin shi kan harabar wajen yana nemo tebir din da yaga babu kowa da kuma kujerar mutum hudu tukunna yaja hannun Waheedah batare daya damu da mutanen dake binsu da kallo ba suka karasa wajen, kujera daya yadan ja baya yana jan hannunta ya zagaya da ita, zama tayi dan tagaji kam.
Ta gefenta Abdulkadir ya zagaya ya zauna yana kallon yanda take mayar da numfashi.
Hannunta Waheedah ta sauke kasan tebir din tana murzawa da dayan, tana jin kamaf Abdulkadir yabar mata shatin nashi hannun a wajen da yanayin dayai mata tsaye a zuciya.
"Bakace in dauka bafa"
Ta fadi tana kallon Abdulkadir daya dauki robar ruwan da take ajiye a wajen yana murzawa da nufin budewa da alama.
Kananun idanuwan shi ya kafeta dasu da yasata sauke nata idanuwan, zuciyarta naci gaba da tsalle a cikin kirjinta.
Ruwan shi Abdulkadir ya kwance, yana son ganin yanda tsoro kan cika idanuwanta, kai robar yai bakin shi yana shan ruwan sosai tukunna ya mika robar kusa da Waheedah yana fadin
"Ki sha ruwa..."
Hannu tasa ta dauki robar ta cire murfin dabai daure ba sosai tana kaiwa bakinta ta kurbi ruwan tukunna ta mayar ta rufe, ba kishi take ji ba, tasha ne kawai dan yace tasha, dan shine ya bata bazata iya ce mishi batajin kishi ba.
A hankali ta ajiye robar tana soma kalle-kalle ko zata hango su Nuriyya.
Amman ko alamun su bata gani ba.
Yazid ne ya karaso wajen yana jan kujera ya zauna hadi da fadin
"Kai jama'a, wallahi jikina ciwo yake mun"
Kallon shi Waheedah tayi cike da tausayawa, abinda yafi ciwon jiki ma tasan zaiyi, tunda hidimar bikin ta fara shi yake zirga-zirga.
Cikin sanyin muryarta tace
"Sannu...
Kaine baka huta ba ai Hamma..."
Murmushi yayi yana sauke idanuwan shi akanta, tun dazun ya kula da yanayin fuskarta kafin su taho, baisan lokacin da abinda yake ji ya fara ba, kawai ta gitta ta gaban shi ya tsinci zuciyar shi da doka mata.
Tunda yazo wajen yake cin karo da yan mata kala daban-daban, dukkan su fuskokinsu dauke suke da kwalliya taban mamaki.
Yanda tata take fayau ya mishi, lokaci zuwa lokaci taken sake gyara zaman mayafinta a kafadarta, ya kula da a takure take jinta saboda rashin hijab dinta
"Me yasa baki saka hijab ba?"
Ya bukata, bayason ganin yanda take a takure, dan murmushi tai mishi cikin yanayin sanyinta, baisan koshi kadai yake ganin kyanta ba, da dan bakinta da yasan mata da yawa zasu shafa abubuwa da dama dan kalar labbansu tayi ruwan hoda haka kamar nata, idanuwanta sunfi komai daukar hankalin shi a fuskarta, yanda suke maiqo kamar da hawaye a cikin su koda yaushe kan saka shi murmushi koshi kadai ne.
"Su Zahra zasu dameni"
Kai Yazid ya jinjina
"Ki daina yin abinda zaki takura saboda mutane..."
Kai Waheedah ta rausayar gefe, bazai fahimta ba, bata takura kanta bane saboda su, idan ta saka hijab din yanda zasu takurata zaifi yanda take a takure yanzun, ta zabi abinda yafi mata sauqi ne kawai.
Abdulkadir hankalin shi ya mayar kan hidimar da ake wajen dinner din, ganin hirar Yazid din da Waheedah ta fara dakushe mishi nishadin da yake ciki.
Dan mudubin da ta saka a cikin yar jakar hannunta ta dauko tana saka shi ta karkashin teburin wajen ta duba fuskarta, kowa yace mata tayi kyau, daga yan gidansu Waheedah zuwa abokan wasan su da suka zo bikin, sai dai kamar koda yaushe akwai murya a kasan ranta da take fada mata kyawunta bai kaiba, kyawunta bazai tana isa ba, kamar yanda bazai cike mata gurbin abubuwa da yawa da bata dashi a rayuwarta ba.
Ta jima tana tsara kwalliyarta yau, amman Waheedah na fitowa saita raina duk wani kyau da take tunanin tayi.
Batasan menene a tattare da fuskar Waheedah din dako hodar kirki bataji ba.
Tana da tabbacin ba ita kadai take ganin wani sanyi da yake cikin idanuwan Waheedah a koda yaushe ba, yau dinma batare da wani yunkuri ba taga Waheedah din tayi kyau, da pink lips dinta da take jin kamar ta cire ta mayar a tata fuskar, duk da inta kalli yanda zubin kirarta yake takan ji sanyi ta wani fannin, duk kyan Waheedah da hasken fatarta ba zata nuna mata dirin jiki ba, duk da itama a sirantakarta Allah yai mata wadattacen cikar kirji da Nuriyya take jin bai kamace taba, yanda take siririya yakamata komai nata ya zamana a shafe, ta fito a asalin zanen lamba dayanta.
Tunda suka zo takan tashi ta yawata a cikin wajen ko zata ga Waheedah din, amman ko alamunta bata gani ba, yanzun ma zagayawar take tana dube-dube, kafin idanuwanta su sauka kan Waheedah din da take murmushi cikin yanayin da yakan kara mata kyau.
Karamin tsaki Nuriyya taja, tana jin wani daci har a kasan zuciyarta da batasan daga inda yake taso mata ba.
A hankali take karasawa, idanuwan mazan duk data gitta yana kanta, amman ko kadan bata kula dasu ba, gabaki daya hankalinta yana kan Waheedah da Yazid da alamu ya nuna hira sukeyi, akwai wani namijin tare dasu da batasan kowaye ba, saboda ya bata baya.
Takawa tayi harta karasa inda teburin yake tana fadin
"Inata neman ki tun dazun"
Saukar maganar Abdulkadir yaji saman kanshi, dan a bayan shi Nuriyya ta tsaya, gyara zaman shi yayi tukunna ya juya a hankali dan yaga wacce marar tunanin ce take mishi magana tsakiyar kai, batare dako sallama tayi musu na ballantana ta gaishe su tukunna tai maganar da zatayi, idanuwan shi ya fara saukewa kan fuskarta, kafin ya kankance su yana kare mata kallo, wani abu yake ji yana dokawa cikin kunnuwan shi daya rasa daga inda yake jin sautin shi, dan bashida alaqa ko kadan da kidan da yake tashi a wajen.
Zai karya idan yace bai manta da wata Nuriyya a shekarun nan ba, saurarawa yayi dan gane inda yake jiyo sautin, kafin yagane zuciya shi ce take dokawa a kirjin shi, alaqanta hakan yake da mamakin girman da yarinyar tayi.
"Baki iya sallama ba?"
Abdulkadir ya fadi har lokacin yana rasa dalilin da zaisa zuciyar shi ba zata daina bugawar da take ba.
Ware idanuwanta Nuriyya take akan Abdulkadir din, batasan yazo ba, Waheedah batace mata yazo ba, duk da a shekarun nan biyu daya tafi, ta tabbatar babu wanda Waheedah take damu da zancen shi idan ba ita ba.
Bata taba ganin shi cikin manyan kaya ba tunda take, ba tun yanzun yake mata kyau ba, hankalin data kara yasa kyawun nashi bayannar mata sosai yanzun.
Gashi yayi wani irin girma.
"Hamma..."
Nuriyya ta fadi tana murmushin da Abdulkadir din yaji zuciyarshi ta kara gudun dokawar da take.
'Tana da kyau'
Wata murya ta fada a cikin kanshi.
Sake kankance idanuwan shi yayi kamar zata iya karantar abinda yake tunanin akan fuskar shi, idan akwai abinda ya tsana a rayuwar shi bai wuce raini ba, yara kuma a shekarun su Nuriyya sukafi jin tashen raini, saboda kuruciyar girma na dibarsu, shi bai saba yima kanshi karya bane kawai, yaga tana da kyau, ya kuma yi acknowledging kyan nata a ranshi.
"Sannu da dawowa"
Nuriyya ta fadi tana shirin dorawa da
'Yaushe kazo'
Yanda Abdulkadir din ya daure fuska ya hanata fito da maganar a fili, juyawa yayi batare daya amsa Nuriyyar ba hadi da gyara zaman shi, tukunna kamar an mishi dole yace
"Yawwa"
Wani abu Nuriyya taji ya tsaya mata a makoshi, har ranta taji dadin ganin nashi, ya tuna mata yanda yake mata kyau naban mamaki, a lokaci daya kuma ya tuna mata yanda daga kawar Waheedah da suke gaisawa kan dole bata wuce nan ba, bakuma zata taba wuce nan ba, batasan meyasa yanayin yai mata ciwo na gaske ba.
Waheedah kuma Abdulkadir din take kallo, yanayin shi na nuna alamar gajiyar da yai da zaman wajen.
Inda idanuwan Waheedah suke Yazid yabi da kallo, kafin ya sake mayar da kallon shi kan fuskarta, yana runtsa idanuwan shi ya bude su hadi da kauda tunanin da yake shirin dirar mishi
'Duka nawa Waheedah din take'
Ya fadi a ranshi yana mikewa
"Ina zaka je?