Sashe 63
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sunayen Allah duk wanda yazo bakinta fadin shi takeyi ko zata samu saukin azabar da takeji.
Akan kunnenta akai kiran sallah na farko, har aka sakeyin wani aka shiga masallaci tukunna ta iya raba jikinta da kafet din.
Alwala ta sake zuwa tayi dan batajin ta cikin yanayin da zata tabbatar tana da alwalar.
Ta shiga wata duniya mai wahalar misaltawa.
Sallah ta dawo tayi, tana sake komawa ta kwanta kan kafet din.
Sai yanzun takejin dama ta kira Yassar jiya ya dauki Fajr, dan ko wanka ba zata iya mishi ba, ballantana abinda zata bashi yaci.
Wajen shidda na safe ko motsin kirki bata iyayi, ga wani irin zazzabi mai zafin gaske daya lullubeta.
A haka AbdulKadir ya shigo ya sameta, dan shi ya dauka bacci takeyi da yaita sallama yaji shiru.
"Waheedah..."
Ya kira yanajin gabanshi yayi wata irin faduwa, da sauri ya karasa yana tsugunnawa ya dagota, jikinta da yaji kamar garwashin wuta yasa shi fadin
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
Yana dorawa da
"Baki da lafiya?
Tun yaushe Wahee?
Me yasa baki fadamun ba?"
Dakyar ta iya bude idanuwanta ta kalle shi, da gaske kara mata ciwo yakeyi, daga muryarshi har tabatan da yakeyi.
Tana ji ya zameta daga jikin shi yaje ya tashi Fajr daya shagwabe fuskarshi cike da bacci zaiyi kuka, ganin AbdulKadir din yasa yaron wartsakewa dukkan shi
"Paapi"
Ya fadi yana riko AbdulKadir din daya kamashi ya sauko dashi daga kan gadon
"Fajr tashi, Omman ka zamu kai asibiti"
AbdulKadir ya karasa maganar yana yin bandaki da Fajr, fuska ya wanke mishi yaga abin bazaiyi ba.
Da kanshi yai ma yaron wanka ya goge mishi jiki da towel, kaya yazo ya dauko mishi yanajin dadin yanda komai yake a shirye, baisha wata wahala ba.
Yana gama saka ma Fajr kaya da yake ta mishi surutun da hankalin shi baya kai, yaga Waheedah taja jiki dakyar ta mike.
Muryarta na rawa tace mishi
"Nikam kabarni da zuwa asibitin nan"
Ko inda take AbdulKadir bai kalla ba, Fajr ya zaunar kusa da ita, ya koma ya dauko wayarshi dake cikin jaka.
Yassar ya kira, sai da ta kusa yankewa tukunna ya daga batare da yace komai ba, jin hakan yasa AbdulKadir fadin
"Hamma banzo da mota ba, Waheedah bata da lafiya kuma..."
Da sauri Yassar din yace
"Subhanallahi, ina zuwa yanzun"
Ya kashe kiran daga can bangaren shi, yana saka AbdulKadir din bata rai, bayaso a kashe mishi waya a kunne, ko kadan abin na bata mishi
rai, ya kuma rasa dalili.
Wayar ya ajiye kan gado yana karasa ya kama hannuwan Waheedah duka biyun, batayi mishi musu ba.
Kasa yai da muryarshi sosai saboda Fajr dake zaune a wajen
"In tayaki kiyi wanka?"
Kai ta girgiza mishi
"Zan iyayi...
Ka rakani bandakin kawai"
Taimaka mata yayi har cikin bandakin, duk da hankalin shi bai kwanta daya barta ita kadai din ba, fitowa yayi yai tsaye bakin kofar bandakin, duk bayan wasu daqiqa saiya kira sunanta duk da yasan babu kyau tayi magana a bandakin.
Badon Fajr ba shikam shiga zaiyi, karta fadi a ciki ya shiga uku.
Saida yaga ta fito tukunna hankalin shi yadan kwanta, kama hannunta yayi yana janta zuwa gefen gado ta zauna.
Da kan shi ya dauko mata doguwar riga da inners ya ajiye mata akan gado gefenta
"Sannu, Bari in hadama Fajr Tea"
Kai Waheedah ta daga mishi, ya kama hannun Fajr din suna wucewa kitchen.
Flask ya fara jijjigawa yaji akwai ruwan zafi a ciki, ya samu kofi ya zuba madara da milo ya hada mishi rabi, ya saka sikari yana juyawa.
Hannun yaron ya sake kamawa har falo ya zaunar dashi kan kafet yana ajiye mishi kofin shayin, Fajr na kama kofin yaga yana tiriri ya kalli AbdulKadir din
"Bamai zafi Omma take bani ba"
Kofin AbdulKadir ya dauka ya kurbi shayin, babu wani zafin da bazai iya sha ba
"Wanne irin shayine bamai zafi ba Fajr?"
Shagwabe fuska Fajr yayi
"Na Omma..."
Kai AbdulKadir ya jinjina yana ajiye kofin
"Bata da lafiya, sai kasha nawa yau"
Turo baki Fajr yayi
"Baka bani biscuit ba"
Runtsa idanuwa AbdulKadir din yayi, wajen matar shi yake son zuwa ya dubata, yaron yana da rikici, duk karancin shekarun shi baya hana AbdulKadir din zane shi.
Kitchen ya koma ya dudduba, baiga inda Waheedah ta ajiye biscuit ba idan akwai kenan.
Ya dawo yana fadin
"Ni banga biscuit ba"
Narai-narai Fajr yayi da idanuwa
"Kasan Allah idan kaimun rigima zaneka zanyi Fajr.
Ka zauna kasha Tea din ka kana jina..."
Ya karasa yana juyawa ya koma wajen Waheedah, harta saka kaya, da alama tadanji kwarin jikinta da tayi wanka.
Kusa da ita ya zauna yana taba wuyanta, da zazzabi har lokacin
"Shine jiya baki fadamun baki da lafiya ba?"
Idanuwanta ta ware mishi
"Zazzabi ne kawai, zai tafi"
Kai AbdulKadir ya girgiza
"Banaso...
Karki karamun wannan, idan baki da lafiya ki fadamun ni dai"
Kai Waheedah ta jinjina mishi, ba zata iya doguwar magana ba, kirjinta yayi nauyi, mararta na ciwo har lokacin.
Kiran Yassar yagani, hakan yasa bai daga ba ya mike yana ficewa daga dakin da falon gabaki daya.
Fajr na ajiye kofin shayin ya bishi da gudu ko takaa babu a kafarshi, yana kara gudun shi ganin Yassar ne, cike da farin ciki yake fadin
"Uncle..."
Daga shi sama Yassar din yayi yana dariya
"Fajr..."
Ya kira yana rike shi a jikin shi sosai
"Zan bika ni"
Kai Yassar ya jinjina
"Tare zamu tafi aikam"
Tukunna ya kalli AbdulKadir da yake mishi murmushi, hade fuska Yassar yayi kamar bashi ya gama dariya ba
"Ya mai jiki?"
Ya tambaya, kai AbdulKadir ya jinjina
"Yanzun kai ma Fajr dariya kana magana muryarka lafiya kalau..."
Mukullin dake hannun shi Yassar ya mikama AbdulKadir din yana juyawa tare da Fajr din tunda yana da kaya a gidan.
Kyaleshi AbdulKadir yayi ya koma cikin gida suna fitowa tare da Waheedah, da kanshi ya bude mata mota ta shiga ta zauna, ya rufe tukunna ya zagaya ta dayan bangaren, ya tayar da motar, yana ja suka fita daga gidan zuwa wani asibitin kudi na masu ciki da bashi da nisa sosai da gidan.
Har azahar suna asibitin, dan ruwa suka saka mata leda biyu.
Har Hajja ya kira bata daga wayar ba.
Sosai ran shi yaji bai mishi dadi ba, daman ya fada mata ne, sai a turo wani cikin yan gidan da zai tayasu aiki, Waheedah din ta huta.
Amman zaiyi komai da zai iya, kuma yaga Waheedah din da sauki, duk da ance ta samu wadataccen hutu, kafin a sallamesu su tafi gida.
Magunguna kala biyu ne kawai aka basu, duk zuwan da yake asibitin tare da ita, wannan ne karo na hudu magani sai dai yaga guda daya ko biyu, sam basa tila magunguna.
"Nikam kamar in dinga zuwa asibitin nan in bani da lafiya, sam basa bada magunguna masu yawa"
Ya fadi yana kwance takalman kafar shi, sai da Waheedah ta cire hijabinta tukunna ta kalli AbdulKadir din
"Asibitin masu cikin Sadauki?"
Dakuna mata fuska yayi
"Me yasa sai masu cikine kawai zasu je?
Basa bada magani da yawa"
Kai Waheedah ta girgiza
"Dan na masu cikine shisa basa bayarwa da yawa, bakowanne magani ake sha ba in ana da ciki"
Kai ya jinjina mata yana fahimta, ita kuwa hannunta take murzawa inda akai mata karin ruwa tanajin yana mata ciwo.
Har lokacin ba zatace ga asalin yanda takeji ba, kallon AbdulKadir din kawai takeyi duk inda yayi, kamar tana jira yace mata maganar da sukai daren jiya wasa ne, sai dai tasan akwai maganganun da badon ba'a wasa dasu ba, AbdulKadir dinne dai bazai taba mata wasa dasu ba.
Idanuwanta ta lumshe taji yace
"Me zaki ci?"
Budesu tayi a kanshi a hankali
"Taliyar Hausa nake so, zan dafa idan na tashi.
Kai me zakaci?"
Dan shiya kamata ta tambaya ma, daya kwaso tafiya, ko hutawa baiyi ba
"Nima ina ci, a ina kika ajiye in dafa mana?"
Tun kafin ya karasa take girgiza mishi kai, ita zata shaida dahuwar taliyar shi, narkewa ne kawai batayi ba, amman harshi kan shi bai iya yaci ba, daga ta tafi kitso, tayi miyarta take ce mishi taliya zata dafa, data dawo tunda babu wahala shine ya dafa, ta nadi uban ruwan da ta tabbatar bai tafasa ba ya zuba taliyar
'Kinga dana dauko daya sai inji kamar ta dahu, amman naga batai fari ba kamar yanda kike dafawa'
AbdulKadir din ya fadi lokacin da ta shiga kitchen din ta samu taliyar kan wuta.
Idan ya dafa taliyar hausa tabbas kunu zata koma.
"Nagode.
Allah ya bada ladan niyya Sadauki.
Zan dafa..
Kaje ka watsa ruwa ka kwanta.
Baka huta ba"
Kai ya girgiza mata
"Zanyi wanka, nikam banajin bacci.
Ke da baki da lafiya, ya za'ayi ki iya dafa taliya...naga yanda kikeyi.
Zan dafa nikam...
Bari in fito wanka"
Ya karasa maganar yana shigewa daki, bai jima ba ya fito, ya saka riga mai yankakken hannu da gajeran wando.
Rigima ce cike da idanuwan shi, barnar taliyar da take bala'in ji da ita zai mata
"Akwai sauran doya, a dafa doya kawai"
Murmushi AbdulKadir yayi
"Baki yarda dani ba ko?
To wallahi saina dafa..."
Ya fadi yana shiga kitchen din ya dauko tukunya.
Mikewa Waheedah tayi tana bin bayan shi
"Sadauki dan Allah nidai kabar shi, zan iya.
Kaga zazzabin ma ya sauka tun dazun"
Da gasken take tun kafin a cire ruwan farko da ta samu bacci zazzabin ya dauka, ciwon marar ma yai mata sauki.
Kirjinta ne dai takejin kamar zai bude da wani irin ciwo.
"Gara ki dauko mun taliya kije ki zauna.
Kuma ba wasa nake ba"
Taliyar ta dauko mishi, ta ajiye taja kujerar rubber da take ajiye a kitchen din in zata yanka wani abu tana jin qwiyar tsayuwa ta zauna.
"Ruwan sai ya tafasa"
Tace ma AbdulKadir din ganin duk mintina biyu saiya bude tukunya.
Da taimakon ta ya dafa musu taliyar, tana da soyayyen manja da zafi baisa ya kwanta mata ba.
A asibitin sukai sallah daman.
Dan haka Waheedah taje ta kara watsa ruwa itama ta sake rigar jikinta da takejin tana mata warin asibiti har lokacin tukunna ta fito sukaci abinci.