Sashe 23
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alamun motsi yayi su biyun suka kwasa da gudu, kai ya girgiza murmushi na kwace mishi
'Jarabu da qwai'
Ya maimaita cikin zuciyar shi wani murmushin mai sauti na kwace mishi
"Sai naci uban yaran nan Allah..."
Yai maganar a fili yana juyawa.
Masallaci ya fita abin shi.
Sanda ya dawo hanjin shi har nadewa suke waje daya.
Dakin shi ya nufa kai tsaye yana tunanin ganin abinci baiga komai ba, tabbas saiya zane jikin Zahra.
Fita yake shirin yi yaji an kwankwasa kofar hadi dayin sallama cikin sanyin muryar daya tabbatar mishi da Waheedah ce.
"Shigo..."
Ya fadi
Da kafa ta tura kofar saboda farantin da yake hannunta, tukunna ta shiga dakin.
Zahra ta sameta tace Commander yace ta kai mishi abinci.
Hakan yai mata dadi, tun safe take jin ganin shi, ta fito yafi a qirga amman bataga giccin shi ba, batason fito da hotunan daya bata jiya daga inda ta adana su, saboda gidan cike yake da mutane.
Farantin ta ajiye mishi a kasa tana mayar da hannunta daya baya kamar mai boye wani abu
"Ina wuni"
Ta gaishe dashi
"Lafiya..."
Ya amsata a taqaice yana jan farantin gaban shi
"Akwai wainar shinkafa, ban saka maka ba saboda nasan baka ci"
Da mamaki Abdulkadir ya dago yana sauke mata kananun idanuwan shi.
Baya tunanin ko Hajja tasan bayacin wainar shinkafa, dan da bakin shi bai taba cewa kowa yana cin abu kaza ko bayaci ba, idan yaje ya duba yaga ita akayi ficewa yake ya nemi wani abin daban yaci.
Ganin kallon da yake mata yasa tajin zuciyarta na bugawa, tana mamakin yanda idanuwan shi suke birkita mata lissafi, duk kankantar su.
"Ban taba gani kaci ba, idan ka shigo anyi baka diba kake fita"
Waheedah tai mishi bayani, Idanuwan shi ya dauke daga kanta, yana jin jikin shi ya dauki dumi na daban.
Abune da bai taba tunanin wani yai damuwar dazai kula ba.
Plate din shinkafa da miya harda lettuce data zubo mishi ya dago yana dora shi kan cinyar shi, yanda yake motsa abincin a nutse take bi da kallo, kafin ya diba abincin yana fara kaiwa bakin shi.
Idanuwanta Waheedah ta dauke daga kanshi, tana dan sa hannu ta dafe kirjinta da yake dukan uku-uku.
Passport dinta ne data gama bincika duk wasu da take dasu tana dauko wanda tai tunanin tayi kyau a ciki ta ke riqe dashi a hannunta.
Tun jiya da tunanin ta bashi yazo mata zuciyarta take dukan uku-uku da tunanin abinda zai iya biyo baya.
Tasan babban cikin su bazai wuce tasha mari yace ta raina shi ba, amman son ya tafi da wani abu da nata ne yafi karfin duk wani tunani da takeyi, yanda yabar mata wani abu nashi duk da ko baiyi ba tasan zai kasance manne a zuciyarta harya dawo, haka take so ko yayane itama ya tuna da ita, ta gama tattaro karfin gwiwarta amman ganin shin da tayi ya tuna mata yanda a kasan komai
akwai tsoron shi a shimfide.
Kalle-kalle take cikin dakin, a drawer din gefen gadon ta hango wallet din shi, karasawa tayi wajen tana zama.
Sai lokacin Abdulkadir ya dauke idanuwan shi daga kan abincin da yake ci ya kalleta, ganin wallet din shi yayi a hannunta ta bude
"Kin ban ajiya ne?"
Ya bukata yana tsareta da idanuwa, tunda ta shigo yake tunanin ta kara haske, sai lokacin ya kula da lace dinta farine da ratsin ja ko stones din jikine ja bazai tantance ba, shiya kara fito da haskenta dayai mishi yawa a ido.
Kai Waheedah ta girgiza mishi zuciyarta take ji ta dawo wuyanta, idanuwan shi ya dauke daga kanta yana ci gaba dacin abincin shi, hakan ya bata damar saka mishi hoton cikin karamin wajen da zaka iya ajiye hoto tukunna ta balle wallet din tana ajiye mishi inda taganta.
Sosai zuciyarta take dokawa har wani zazzabin faduwar gaba take ji a jikinta.
Ga zufa da tafukan hannunta sukeyi, mikewa tayi
"Ina zakije?"
Abdulkadir ya tambaya, bai jira amsarta ba ya dora da
"Ki jira in gama ki tafi da kwanonin"
Komawa Waheedah tayi ta zauna, idanuwanta kafe a kasa, shirunta Abdulkadir yaji ya mishi yawa, hakan yasa shi kallon ta, kanta a kasa yake
"Waheedah?"
Ya kira cike da alamun tambaya, ta dago tana sauke mishi manyan idanuwanta da yake da yakinin za'a cire hudun nashi a ciki har a samu ragowa, har mamakin yanda za'a ce idanuwan mutum ne da wannan girman yake, yana son ganin tsoron shi cikin su saboda girman da sukan qara yi mishi.
"Lafiyar ki?"
Ya tambaya, tambayar shi kanshi tana bashi mamaki, haka kawai yana son jin tana lafiya, da bata mishi surutunta yau.
Kai Waheedah ta iya daga mishi, yanda ya kira sunanta nasa har lokacin zuciyarta dokawa take har cikin kunnuwanta.
Numfashi ya sauke, ita kadai take amsa mishi magana haka, surutun nata yake son ji, tana amsa mishi magana da kai.
Abincin shi ya karasa ci yana cire robar ruwan daga kan farantin ya dago dashi ya miqama Waheedah data miqe tsaye, gara ta fita, kan shi yake jin ya mishi nauyi yau din nan, Nuriyya taki ficewa daga cikin shi, bazai kara da tunanin ko lafiyar Waheedah kalau shisa take mishi shiru-shiru ba.
Tsaye yake jikin mota Abba yana jiran wanda zaikai din su fito, ance mishi sharada ne, yagane ta wajen dan akwai abokin shi a gurin unguwar.
Waheedah ya hango tana takowa inda yake, tafiyarta yake kallo kamar batason taka kasar dakyau karta tsage ta rufta da ita.
Hijab ce mai hannuwa a jikinta har kasa.
Yana son hijab, dan matar shi ba zata saka mayafi ta fita wani qaton banza na kallonta ba, kwalliyarta a cikin gida zatayi iya idanuwan shi.
Kalar hijab din ruwan kasa mai cizawa, a ranshi yake tunanin ko Waheedah batasan tana da gaske bane, duk kayan da zatasa kara mata haske suke suna saka ta shigar mishi ido.
Yana son mace mai duhu
'Kamar Nuriyya'
Wata murya cikin kanshi ta furta mishi tana saka shi sauke numfashi, duk da ba karya ta fadi ba, yanayin kalar Nuriyya haka yake son macen shi ta kasance.
'Har yanayin jikinta da komai nata'
Muryar ta sake fada mishi tana saka shi girgiza kai, kamar yana son fada mata kartai musu haka shi da ita, karta ja musu raini.
Karasowa Waheedah tayi tana fadin
'Hamma baka shirya ba, yanzun fa za'a tafi, dangin su Angon har sun zo"
Sosai yaji dadin saukar muryarta da ta katse mishi tunanin da yake da yake da tabbacin babu abinda zai ja mishi sai rainin dayafi tsana a rayuwar shi.
Kafin maganganub Waheedah din su zauna mishi suna saka shi kallon ta cike da rashin fahimta
"Wanne irin shiri?"
Dan kallon shi Waheedah tayi tana rausayar dakai, tagan shi da wando iya gwiwa sai riga blue mai haske datai mishi kyau naban mamaki a idanuwanta, amman duka cikin abokan angon da suka zo da motocin da kuma yan gidan nasu da zasu taya hidimar daukar amaryar manyan kaya ne a jikin su.
"Baka sa kaya ba"
Ta fadi, tana saka shi kankance mata idanuwan shi.
Haka Yassar yai mishi maganar sake kaya dazai fito, itama tazo tana mishi yanzun
"Tsirara kika ganni?
Meya sami kayan da suke jikina?
Me yasa bazan je da wannan din ba?
Su ba kaya bane"
Kallon shi Waheedah take yanda ya kankance ido yana mata masifa kamar jiranta yakeyi daman, ita bada tunanin komai tai mishi magana ba, idanuwanta taji sun cika da hawaye.
Batare da tunanin komai ba ta sake cewa
"Allah ya baka hakuri..."
Wani murmushi Abdulkadir yayi mai sautin dake fassara ya kasa yarda shi Waheedah tace ma 'Allah ya baka hakuri'.
Duk da baiji raini a muryarta ba, baqar magana ce ta fada mishi saboda yana magana mai tsayi da ita
"Bakar magana zaki fadamun?
Saboda kinga hakorina?
Maganar da nake dake tasa zaki fara rainani ko?"
Hawayen da take tarbewa ne suka zubowa, yana kara harzuqa Abdulkadir din saboda bayason kuka marar dalili, idan zaka saka shi a gaba kana mishi guga gara ya tabbatar ya baka dalili me karfi nayin kukan
"Me nai miki?"
Kai Waheedah ta girgiza mishi, hawayenta na sake zuba, fadan shi take ji har kasan zuciyarta, inda tasan zai mata fadan ba zata soma mishi maganar kayan da yasa ba.
"Raini ne yasa kike mun kuka?"
Abdulkadir ya sake tambaya yana tsareta da qananun idanuwan shi.
Kafin yaja tsaki yana wucewa ya nufi bangaren su, kayan da Yassar din ya fito mishi dashi dan ya saka yaqi ya dauka hadi da jan wani karamin tsakin, dan baisan dalilin da yasa shi yake sake kayan jikin shin ba, tunda baiga abinda sukai ba.
Ko motsi Waheedah batayi ba daga inda yabarta, hannu take sakawa tana share kwallar da taqi daina zubar mata har lokacin, fuskarta tayi wani irin ja, abinka da farar fata.
Anan Nuriyya da tun jiya da suka dawo ta kwanta batare da tace mata komai ba ta sameta.
Tunda aka fara hidimar a gidansu Waheedah din take kwana, duk da ko babu hidima tana kwana wasu lokuttan, kusan rabin da kwata na rayuwarta tare dasu takeyin ta a gidan.
Yau da safe data tashi ma bata kula Waheedah din ba, saboda haushinta take ji, haushin kowa da komai take ji, data isheta catai mata kanta ke mata ciwo, harda bata paracetamol din rainin hankali.
"Ke kuma lafiya?
Me akai miki?"
Nuriyyan ta tambaya tana tabe baki, hannu Waheedah tasa tana share kwallarta, muryarta a dishe tace
"Hamma Abdulkadir ne ya sauke mun fadan shi"
Dariya Nuriyya tayi saboda har ranta taji dadi, Abdulkadir din ya tabbatar mata da Waheedah kamar kowa ce a wajen shi, babu wani special treatment da take samu
"Abin dariya ya baki ko?"
Waheedah take fadi tana hararar Nuriyyan data sake yin wata dariya tana riqo Waheedah din hadi da dora kanta kan kafadar Waheedar
"Sorry kawata.
Halin Hamma wanne ne baki sani ba?"
Jinjina kai Waheedah tayi, tasan shi fiye da zaton kowa, fadan shine ba zata taba sabawa dashi ba, duk yanda take da tsoron duka gara ya daketa dayai mata fadan shin nan mai tsaya mata a rai.