← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 94

Sashe 4

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Waheedah dan Allah ki daina kukan nan...

Kinji...duk gamu nan, ko ma menene, muna nan tare dake, kina jina?"
Kai Waheedah take girgiza ma Anty tana ci gaba da wani irin kuka da yasa jikin Mami yin sanyi, dan ita kam tana tsaye ta rasa abinda ya kamata tayi
"Anty kuce ya saukake mun, dan Allah kuce Sadauki ya sakeni!"
Ba Abdulkadir din ba, har su Mami saida suka girgiza da kalaman da Waheedah din ta furta
"Kunji, kuce karya fita daga dakin nan bai rabani da auren shi ba..."
Wannan karin Anty nata idanuwan cike yake da hawaye, fuskar Waheedah din ta dago tana kallon ta
"Waheedah kinsan me kike fada?"
Anty ta tambaya cike da tashin hankali, tasan auren Waheedah da Abdulkadir wani irin aurene da yake cike da hargitsi, ta hango mutuwar shi a watannin kusan takwas da suka wuce, amman bai mutu ba, batasan dalilin da yasa sai yanzun ba.

Duk da zatai karya idan tace a watannin baya bataso mutuwar auren ba, ko dan kwanciyar hankalin Waheedah din, amman yanzun da take ganin abin na shirin faruwa a gaban idanuwanta, tashin hankalin da take ciki bazai misaltu ba.

Mikewa Abdulkadir yayi
"Ina zaka je?

Ka dawo fa, karka fita baka rabani da auren ka ba...

Ka dawo"
Waheedah take fadi tana kai hannu ta fisge karin ruwan dake jikin dayan hannun nata.

Mami kallon ta take tana da tabbacin ba a cikin hayyacinta take ba.

Hannu Abdulkadir yadan daga yana kasa magana, kafin dakyar yace
"Iskar dake dakin tamun kadan...

Zan fita in shaqi iska ne"
Yai maganar muryar shi can kasan makoshin shi.

"Ka saukake mun saika fita kasha iskar..."
Waheedah ta fadi tana sa hannu ta share hawayen dake fuskar ta, tana tsayar da idanuwan ta akan fuskar shi da wani irin yanayi da yasa bugun zuciyar shi karuwa.

Juyawa yayi
"Sadauki...

Sadauki!!"
Baiko juya ba, tafiya yaci gaba dayi yana ganin kofar dakin ta mishi nisa, kafin ya samu ya fice, ko kofar bai ja musu ba, Anty ta rike Waheedah gam, dan shirin sauke take daga kan gadon tabi Abdulkadir
"Anty ki sakeni, kuna kallo fa ya fita, Mami ki bishi ki karbomun takardata, idan bazai rubuta ba ya fada miki da bakin shi ki dawo ki fadamun..."
Kallon ta Mami takeyi
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
Ta furta a hankali tana ci gaba da maimaitawa, dan batasan wani abu daya kamata ta fadi ba.

Wannan tashin hankalin da yake faruwa a gaban idanuwanta yafi karfinta.

"Anty dan Allah ku kira shi, kinji...

Ku kiraa sh..."
Bata karasa maganar ba, ta sulale jikin Anty data saki wani irin sakati a firgice, cikin tashin hankali ta ke girgiza Waheedah
"Haj Sakina ba kallona zakiyi ba,ku kira likita mana..."
Da sauri Mami ta fita tana ma su Aminu magana dasu kira likitan, kafin kace meye saiga likitan da gudu, wani ma yana biyo bayan shi, dayan ne yace ma su Anty su fita daga dakin, ya rakasu har bakin kofa yaja kofar.

"Me yake faruwa wai?

Anty me yake faruwa?"
Zainab ta tambaya cike da damuwa.

"Meya sameta?

Naga Hamma ya fita a hargitse shima...

Dan Allah kuyi mana magana"
Cewar Nabila muryarta na karyewa.

Hamma da ta fadi yasa Anty kallon su Aminu da fadin
"Ku bishi dan Allah, kar yace zaiyi tuqi a yanayin da yake ciki..."
Tsayawa sukai suna kallon ta cike da rashin fahimta, tsaki ta saki tana kama hanya cikin sauri ta fita daga wajen, sai dai bata ga Abdulkadir din ba, ko alamun shi bata gani ba, har wajen asibitin ta duba amman bata ganshi ba, wajen da taga an ajiye motoci ta nufa tana duddubawa, duk da batajin tasan wacce irin mota Abdulkadir din yake da ita, kawai dai ta duba ne ko Allah zaisa tagan shi.

Dan dafe kai Anty tayi tana fadin
"Oh Allah na..."
Kasan zuciyarta take addu'ar Allah ya kaishi gida lafiya idan can din ya nufa, kafin ta juya tana nufar hanyar da za
ta mayar da ita cikin asibitin Aminu Kano din, a duk jikinta take jin wannan abin bana lafiya bane...!
#Abdulkadir
#FWA
#AnaTare[7/27, 1:13 PM] +234 816 124 4732:
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
A nutse yake tuqin shi, dan ba ranar bane karo na farko daya taka mota cikin rashin kwanciyar hankali, yana dai kula da yanda ake kauce mishi saboda katon tambarin bajon sojoji da yake manne jikin gefen motar, sai kuma sticker dinsu a gaban motar, ko babu kayan da suke jikin shi, kallo daya zakai ma motar kasan cewa ta soja ce.

A haka harya kara gidan shi da yake Rijiyar Zaki, kasancewar shi muqamin shi First lieutenant, akwai sojoji guda biyu masu tsaron shi a gida.

Daya daga cikin sune ma ya bude mishi gate, bai damu da ya tsaya ya gyara parking din ba, kawai kashe ta yai ana harabar gidan yana fitowa, mukullin ma a jiki yabar shi bai cire ba.

Cikin gidan ya karasa, har saida ya wuce tsakiyar falon da takalman shi, kaman daga sama yaji muryarta na fadin
'Babu sallama Sadauki?

Takalmi har tsakiyar daki, ina sallah a wajen fa'
Bai kokarin cire takalman nashi ba, sallamar dai ya tsinci kan shi dayi.

Jin shiru babu wanda ya amsa yasa shi takawa cikin gidan yana karasawa bangaren Nuriyya, hadi da sake yin wata sallamar, yasan tana can tana bacci, idan akace batai sallar Azahar ba bazai musu ba, ranar girkinta ma tana bacci, balle yau da tasan ba itace dashi ba.

Karasawa yayi bangaren dakin baccin ta yana kwankwasawa, tukunna ya tura ya shiga, tana zaune kan gado, kunnenta liqe da earpiece, ta tusa system a gaba, da alama kallo takeyi.

Jin shigar shi yasa ta zare earpiece din guda daya tana kallon shi a kasalance da idanuwanta da suka fi komai a tattare da ita jan hankalin shi.

Miqa tayi hadi dayin hamma tukunna tace
"Masoyi..."
Kamar yanda take kiran shi ko a gaban waye.

Ganin yayi tsaye yasa ta mika hannunta tana mishi alama daya karasa, tana sakeyin wata hammar
"Bacci nake ji Allah, jikina namun ciwo"
Tsintar kan shi yayi da tambayar
"Me kikayi?"
Daquna mishi fuska tayi
"Kallo nayi...

Me Waheedah ta dafa dan Allah?"
Zuciyar shi yaji tayi wata irin dokawa da sunan Waheedah din da Nuriyya ta kira.

Bai iya amsa ta ba ya wuce kan shi tsaye yana nufar bandaki.

Da ido Nuriyya ta bishi tukunna ta tabe baki tana mayar da earpiece din data cire daga kunnen ta daya taci gaba da kallon da shigowar shi ta katse mata.

Rigar jikin shi ya fara cirewa yana mamakin yanda akai Nuriyya bata kula da jinin da yake jikin kayan shi ba, bata ma kula da damuwar da take shimfide a fuskar shi ba.

Kan washing machine din da yake cikin bandakin ya ajiye kayan daya cire.

Ruwa ya bude ma kanshi yana yin tsaye, sanyin ruwan na nutsar da wani abu a tattare dashi, idanuwan shi ya kankance saboda bayason rufe su gabaki daya, baisan meya faru ba, baisan ya akai ba, yana da wata irin zuciya ta fitar hankali da bata da alaka da aikin shi, tun kafin shigar shi aikin soja yake da wannan zuciyar da har Abban shi yakan mishi addu'ar samun saukin ta a can baya, bayason rufe idanuwan shi ballantana yaga me zuciya ta saka shi aikata ma Waheedah yau a karo na farko tun auren su.

Bazai bata lokacin shi tunanin abinda ya rigada ya wuce ba, wannan ba halayyar shi bace sam, yau bazai zama na farko ba, idan abu ya wuce mishi ya riga ya wuce tunda ba zai iya komawa ya sake ba, gaba kawai zai duba ya kiyaye.

Da wannan tunanin a ranshi ya karasa wankan ya fito.

Baibi takan Nuriyya ba, kamar yanda bata bi ta kan shi ba, da towel din daure a jikin shi ya fito daga bangaren ta yana nufar bangaren Waheedah, dan nan yake da tabbacin zai sami kayan shi a nutse, dakin baccinsu ya shiga, kamshin ta na cika mishi hanci, tana son amfani da turarukan larabawa, sai dai bazaice ga wannne da wanne takan hada kamshin su ya bada kalar da yake bayarwa ba.

Kan gadon ta ya hango kayan shi data fito mishi dasu, ya karasa ya dauka, riga ce fara qal, sai wando iya gwiwa baki mai wasu igiyoyi.

Sai da ya fara saka singlet din da take ta zabga kamshi tukunna ya saka sauran kayan yana daukar towel din ya koma bangaren Nuriyya dashi.

Idan yace ga asalin abinda yakeji karya yake, kan shi dai yayi mishi wani irin nauyi.

'Ka saukakemun auren ka'
Maganar Waheedah ta dawo mishi tana saka shi kai hannu dai-dai kirjin shi inda yake jin wani abu na mishi kaikayi ya murza.

Bandaki ya koma ya mayar da towel din ya rataye, tukunna ya karasa kan gadon yana kwanciya gefen Nuriyya da ko inda yake bata kalla ba.

Hannun shi ya mika yana zare earpiece din kunnenta, ya sake miqawa ya zare dayan, juyowa tayi fuskarta babu walwala
"Kallo fa nake..."
Idanuwan shi ya kankance mata, yana sa ta fadin
"Dan Allah mana Masoyi, kuma wallahi yunwa nakeji, nace me matarka ta dafa muku kayi banza dani"
Runtsa idanuwan shi Abdulkadir yayi, duk idan yana tare da ita yakan sha wahala, komai saiya fito fili yayi magana tukunna zata gane, ba surutu yake so ba.

"Bata da lafiya...

Tana asibiti"
Sai yanzun tagane dalilin dayasa ya shigo mata, inda Waheedah din nan bata tunanin jarabar nacin ta zai sa tabari Abdulkadir ya shigo bangarenta haka kawai batare da wani dalili ba.
Chapter 4 · 0% Book details