Sashe 29
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hijab dinta Nuriyya ta cire tana dorawa kan window din kitchen din, yanayin da yasa Waheedah kallon ta
"Naga kin cire hijab"
Kai Nuriyya ta jinjina
"Bazan cire in sha iska ba?"
Yar dariya Waheedah tayi, idan wani yaga Nuriyya ta cire hijabin zaiyi zaton aiki zata tayata, ita da yake tasan hali bata saka a rai ba, dan Allah ya zubama Nuriyya qwiya, ko aikin gida aka sakata sai ta zuba ha'inci a ciki, wani lokaci Maman su na kallonta zata tsallaketa tayi aikinta, a cewarta ko wanke-wanken Nuriyya ba fita suke ba, haka zakaga maiqo cikin kofuna.
"Ke jiya Anas yazo da daddare, saima bayan isha'i tukunna"
Nuriyya ta fadi wani tattausan murmushi na bayyana a fuskarta da yake nuna alamun Anas din ba karamar hidimta mata yayi ba.
Sun hadu ne lokacin da suka kai mishi dinkin uniform din Nuriyya na Green Olive, Yazid ne ya hadasu dashi a cewar shi yakan mishi dinki wasu lokuttan, basu da nisa dashi sosai tunda suna kofar ruwa ne, shikuma yana Kurna babban layi ta wajen yan doya.
Kusan tun lokacin ya manne ma Nuriyya, da yake ana barinta fita zance, sukam gidansu saika gama sakandire tukunna.
Anas ya gama diploma dinshi a yanda Nuriyya take fadama Waheedah, sai dai baici gaba ba, shine babba a gidansu, kuma Allah yaima mahaifinshi rasuwa, hakan yasa yai tsaye kan sana'arshi ta dinki da take kawo mishi rufin asiri dai-dai gwargwado.
Dan a cikin sana'ar yake ma kanshi da mahafiyarshi harma da yan uwanshi duk wata hidima, duk a yanda Nuriyya take sanar da ita, yana da gidanshi na gado mai daki falle-falle guda biyu, sai bandaki da kitchen, dan in yanzun Nuriyya ta bashi dama a shirye yake daya turo a tsayar da magana.
Abinda baisani ba shine ko kadan Nuriyya bata jinshi a ranta, duk da Anas bashida wata makusa a matsayinshi na matashi, yana da kyau na misali da cikar zarrah, ga nutsuwa da kamala shimfide a fuskar shi.
Ko kadan Anas ba tsarin aurenta bane ba, bashi bane mijin da take buri.
Tana kulashi ne saboda hidimar da yake mata, hannun shi a bude yake, ko yaushe cikin mata hidima yake, sau biyu yakanzo a sati, duk zuwan da zaiyi da kalar kayan ciye-ciyen da zai kawo mata.
Da sallar nan kaya yai mata kala uku, mayafi harda jaka da takalmi, shi yai mata dinkunan, ya kuma kawo dubu biyu ya bata tayi kitso da kunshi.
Sosai Waheedah take son Nuriyya da Anas din saboda yanda yake da nutsuwa da kuma son Nuriyyan da take gani a tattare da yanayin shi.
"Turarenki yana gida..."
Nuriyya ta sake fadi tana yar dariya.
Tana kara jin dadin yanda haduwa da Anas take bata damar yima Waheedah kyauta irin haka.
"Dan Allah fa...
Turare ya kawo miki?"
Waheedah ta tambaya cike da jin dadi itama, kai Nuriyya ta daga mata
"Har guda uku ma"
Dan bude baki Waheedah tayi
"Aikam baki isa ba saina zaba...
Mai kamshin cikin nake so"
Yar dariya Nuriyya tayi
"Banza in munje gidan duk wanda kike so saiki ta dauka.
Ina da wasu ai"
Karasa share kitchen din Waheedah tayi suna hirar Anas din da Nuriyya
"A fara poly Anas ya turo musha biki"
Hade fuska Nuriyya tai waje daya
"A'a kin manta, uwar biki zaku sha"
Dariya Waheedah takeyi
"Ki daina mun wannan wasan, nace miki ina son shine?"
Kai Waheedah take girgiza mata
"A'a amman kina karbe mishi kaya ai, wallahi Nuriyya kar Allah ya kamaki"
Tsaki Nuriyya taja tana daukar hijab dinta daga kan kofa tana sa Waheedah tambayar ta
"Ina zakije?"
Ko kulata Nuriyya batai ba, ta saka hijab dinta, dan ta gama bata mata rai, wato fatan ta auri Anas take mata, dan karta huta.
Ko a hanya aka ganta ansan batai kalar auren tela ba, diplomar da yake da ita ya fada mata bashida niyyar cigaba, tunda yana da tsayayyar sana'a, ita kam sai wanda yake zuwa office, babu abinda zatai da tela.
"Hamma yazo..."
Waheedah ta fadi cikin sanyin muryar da yasa zuciyar Nuriyya wani irin dokawa, da sauri ta juyo
"Haba dai..."
Kai Waheedah ta girgiza mata
"A'a ki tafi, ba tafiya zakiyi ba?"
Dan murmushi Nuriyya ta dora kan fuskarta
"Dallah ai kece kike son batamun rai.
Ban labari yaushe Hamma din yazo?"
Wannan karin wani tsadadden murmushine ya bayyana kan fuskar Waheedah
"Allah Nuriyya ina son shi fa..."
Wani zafi Nuriyya taji kirjinta ya dauka, ta fada mata kwanaki, bata kulata bane, saboda tayi kamar sai lokacin tasan tana son Abdulkadir, batasan meyasa take maimaita mata ba yanzun
'In shaa Allah ba zaki taba samun shi ba'
Nuriyya ta fadi a cikin ranta, a fili kuma tabe baki tayi tace
"Kina da hankali kuwa?"
Narai-narai Waheedah tayi da idanuwa, ita kanta tasan batada hankali, ta kuma san ta rungumowa kanta dala ba gammo
"Bansan yazan ba Nuriyya.
Nasan banda hankali, shisama ban taba tunanin samun shi ba, kawai dai nasan ina son shi"
Ta karasa maganar muryarta cike da rauni
"Yafi miki alkhairi..."
Nuriyya ta fadi a taqaice tana dorawa da
"Bari inje gida...
Zan dawo anjima"
Dan batasan Abdulkadir ya dawoba da ba zata shigo gidan haka ba, sauri zatayi taje gida tai wanka ta tsara kwalliya tukunna ta dawo, batasan me yasa ba, haka kawai taji bataso yaganta batare da tayi kwalliya ba.
Kai kawai Waheedah ta iya daga mata dan batajin zata iya wata magana, tunanin Abdulkadir ya cika zuciyarta fal.
Yassar na kula da yanayin Abdulkadir din tun jiya da yaje dauko shi, dayake sunyi waya a bakin gate ya same shi tsaye da jakar shi, batare da yace ma Yassar din komai ba ya zagaya ya shiga mota.
Hannu ya saka ya kunna radio din motar cikin nuna ma Yassar din alamar bayason yin magana.
Haka daren jiya duk wanda yazo dan su gaisa da masifa Abdulkadir din yake amsa su, kamar sannu da zuwan nasu na kara mishi bacin ran da Yassar ya kula yazo dashi.
To yau ma da alama da yanayin ya tashi, shisa tun asuba bai koma dakin nashi ba, duk da zai karya idan yace abin bai dame shi ba.
Maballan kayansu da tela bai saka musu ba Yassar din yake sassaka musu a jikin riguna, daga shi sai Aminu a falon, dan duk yawanci sun faffara shiga wanka.
Abdulkadir ne ya fito daga shi sai singlet da gajeran wando
"Ina kwana Hamma..."
Aminu ya gaishe dashi sanin halin shi, shiru Abdulkadir din yayi, hakan yasa Aminu sake gaishe dashi dan a zaton shi ko baiji bane, daquna fuska Abdulkadir yayi
"Karka dameni Aminu, meyasa zaka fara gaisheni tunda sassafe"
Numfashi Aminu ya sauke yana jinjina kanshi kawai, da idanuwa Yassar yai mishi alama da yabar falon, bai musu ba ya miqe ya nufi dakinsu, saida ya shiga ya turo kofar tukunna Yassar da bai dago daga maballin da yake sakawa ba yace
"Me yake damunka?"
Zagayawa Abdulkadir yayi ya zauna inda Aminu ya tashi, bayason yin magana, bayaso ai mishi magana, komai baya mishi dadi
"Da kai nake, me yake damunka?"
Yassar ya sake tambaya wannan karin yana sauke idanuwanshi kan fuskar Abdulkadir da babu alamar walwala a tare da ita
"Karka dameni Hamma, dan Allah.
Gidane ban niyyar zuwa ba"
Rigar dake hannun shi Yassar ya ajiye yana mayar da hankalin shi kan Abdulkadir din
"Ubanwa yace ka daga waya ka kirani inzo in daukeka to?
Idan kasan bakai niyyar zuwa ba saikai zamanka...meyasa zaka zo kana ma mutane bakin rai, ubanka akai maka?"
Yassar yake fadi dan shima ranshi ya fara baci, hakan Abdulkadir ya kula dashi yasa shi fara shirin mikewa dan yabar wajen
"Wallahi idan ka tashi ranka saiya baci, ka zauna ban gama maganar da nake ba..."
Komawa Abdulkadir yayi ya zauna, karshen abinda zaiso a yanayin da yake ciki shine bacin ran Yassar din, yana da zuciya yasani, abinda yake bata mishi rai a kusa yake, amman yana sauka da wuri, wasu lokuttan idan yai duka ko yai fada shikenan.
Amman na Yassar daban ne, yakan jima ranshi bai baci ba, amman idan ya baci duka gidan sai hankalin kowa ya tashi
"Meke damunka?
Bazan sake maimaitawa ba"
Numfashi Abdulkadir ya sauke yana rasa amsar dazai ba Yassar din, bashida wata kwakkwarar amsa, me zaice mishi?
Ranshi a bace yake saboda zuciyarshi nason ja mishi abinda su dukansu bazai musu dadi ba?
Ko kuma fada mishi zaiyi yanda yake ta kokarin ciro Nuriyya daga duk inda take a cikin jikinshi kafin ta zame mishi matsala amman ya kasa?
Wanne daga ciki zai fada mishi da bazai mishi kallon marar hankali ba, ko zai fada mishi yanda Waheedah ta saka shi zuwa gida bai niyya ba, yanda alkawarin dayai mata yai mishi tsaye a wuya saida ya janyoshi garin kano.
Amsar da tafi mishi sauki yaba ma Yassar din
"Bansani ba, komai bayamun dadi"
Numfashi Yassar ya sauke, yanayin da Abdulkadir din yai maganar na saka bacin ran da yake ji soma dishewa.
"Kayita istigfar, tana yaye damuwa"
Kai Abdulkadir ya jinjina mishi yana mikewa tsaye
"Bari inyi wanka...
Kayana fa?
An dinkamun?"
Dan kallon shi Yassar yayi
"Da bikin su Hamma ai masifa kaimun, na maka dinkin da bai maka ba...."
Daquna fuska Abdulkadir yayi
"Da wanne kayan zanje sallar idi?"
Dan daga mishi kafadu Yassar yayi
"Bakazo da kaya ba?"
Idanuwa ya kankance ma Yassar
"Gajerun wanduna ne fa..."
Maballan shi Yassar yaci gaba da sakawa, ganin AbdulKadir din na tsaye har lokacin yasa shi fadin
"Kamun tsaye a kai"
Da mamaki Abdulkadir yace
"Hamma da gaske baka dinka mun ba?"
Wani kallo Yassar ya watsa mishi daya tabbatar mishi da gaske yai maganar.
Kuma da gangan yaki dinka ma Abdulkadir din kaya, saboda rashin kunyar dayai mishi wancen karin, har cayai shi bazai saka wasu manyan kaya ba.
Ya fadama kanshi bazai sake dagama Abdulkadir din hannu ba, tunda ba yaro bane yanzun, amman hakan baya nufin bazai nuna mishi kuskuren shi ba.