← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 94

Sashe 71

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yasan da baiyi rashin kunya lokacin da aka bashi damar yin bayanin karar shi da Major yakai ba, da wahala ma ya kwana, tunda bayani kawai zaiyi suce mishi yaja ma matar shi kunne, sai yaba Major hakuri, amman bazai iya wannan ba.

Rashin kunya ya tsula har Major din ya sa mishi hannu, da sukayi detaining din shi kuma ya sake jibgar wani a cikin cell din.

Shisa yai kwanakin da yayi, gashi sai yanzun yakejin ciwon da jikin shi yake mishi.

Waheedah ko wannan bata duba ba take kara kallon idanuwan shi tana cewa ya rabu da ita, shikam bashi da wannan zuciyar, hakuri zatayi ta yafe mishi ta dawo suyi zaman su.

Dan shi bazai taba iya rabuwa da ita ba.

Yanzun ma ji yake yanda ranshi yake a bace in bai ganta ba akwai matsala, wata irin kewarta yakeji tana danne shi kamar bai ganta awanni kadan da suka wuce ba, a gigice yakejin rayuwar shi da wata irin rashin nutsuwa da kusancin Waheedah kawai yake samar mishi.

Tashi yayi yana laluba aljihun shi yaji mukullan motar shi suna ciki.

Ficewa yayi daga gidan ya shiga mota, wajen Abba zashi, in Waheedah bata dawo gidan shi yajita a kusa dashi ba yau baisan yanda zaiyi da tunani ba.

Tsintar kan shi yayi da kasa nufar bangaren Abba kai tsaye, dan haka ya wuce wajen Hajja, a falo ya sameta zaune da remote a hannunta, Zainab da itace Autarta kuma tana aji daya a jami'a a yanzun tana zaune gefen Hajja din
"Hamma ina wuni"
Ta fadi bayan Hajja ta amsa sallamar AbdulKadir din, kai kawai yadan daga ma Zainab din data mike tabar musu falon.

Inda ta tashi AbdulKadir ya koma ya zauna, yana dafe kan shi cikin hannuwan shi dan ya rasa abinda zaice.

Kallon shi Hajja tayi, tunda ya shigo tagan shi a firgice, kamar ba AbdulKadir din ta ba, kamar ba sojan gidanta ba, cikin kwanaki bakwai gabaki daya ya fita hayyacin shi.

Ba zatace auren soyayya sukai da Alhaji Ahmad ba, asalima baifi sau biyu tagan shi kafin a tsayar da maganar auren su ba.

Ba kuma kasafai take fahimtar soyayya irin ta yaran yanzun ba, amman akan AbdulKadir da Waheedah tasan cewa kaddarar data hadasu mai girma ce, dan ko ita sosai ta jinjina al'amarin sanin yanda Waheedah take da sanyin hali, shekarun da taga suna wucewa batare da matsala ko daya daga gidan AbdulKadir din ba ya nutsar da hankalinta, ta sake jinjina kaddarar zamansu lokacin da taji ya auri Nuriyya, duk idan taga Waheedah a gidan sai taita kallonta tana mamakin yanda ta shanye wannan cin amanar.

Dan ita kam tasan ba zata iya ba, da saninta ma a auren Alhaji Ahmad saida takai zuciya nesa, har gobe kishin sauran matan shi kan motsa mata ba kadan ba, shisa batason wani abu ya sami auren dan nata da Waheedah, babu macen da zata iya zama dashi tana da wannan tabbacin, Nuriyyar ma ba baki tai musu ba, babu inda auren zaije ko bana cin amana bane, saboda ta kula da yarinyar tana da ji dakai da son abin duniya.

"AbdulKadir..."
Hajja ta kira tana ganin ya dago fuska yana sauke mata kananun idanuwan shi
"Kaci abinci?"
Kai ya girgiza mata, yunwar ma ya nemeta ya rasa.

Mikewa Hajja tayi, da sauri AbdulKadir din yace
"Hajja na rasa yanda zanyi...na bata hakuri Hajja...

Bansan ya zanyi ba kuma.

Wallahi bazan iya rabuwa da ita ba"
Numfashi Hajja ta sauke, tausayin shi na cika mata zuciya.

Kitchen ta wuce ta zuba mishi shinkafa da miya da lettuce.

Ta dawo tana mika mishi, karbar plate din yayi ya ajiye akan kafet
"Ba abinci ba Hajja...

Matata..."
Numfashin Hajja ta sake saukewa
"Kaci abincin AbdulKadir...

Zan roki Abbanku sai a bata hakuri kaji..."
Kallon Hajja yake
"Za'a bata hakuri da gaske?

Abba yace ba zai saka baki ba fa...

Hajja haka yace ya daina saka baki a lamurrana, dan Allah shima ki bashi hakuri...

Nikam rayuwata na cikin wani yanayi"
Yanda ya karasa maganar takeji har cikin ranta, bata taba ganin dan nata yayi laushi haka ba, da bakin shi yake kiran a bama Abba hakuri yau, tura takai bango.

Shisa take jinjina ma kokarin maza, zasu dauki shekaru suna musgunawa mace, ko a fuskarta da wahala a gane, amman rana daya idan ta ware ta rama sai kagani a fuskar shi namijin.

Sai kaji an fara bata rashin gaskiya saboda halittarta da juriya aka santa.

Yanzun wanda duk zaiga AbdulKadir din saiya tausaya mishi, da yawama zasu manta cewa koma me yake faruwa dashi yanzun laifin shine, wasu ma zasu ce me yasa Waheedah ba zata hakura ba tunda harya bude baki ya bata hakuri.

Amman yarinyar kawai tasan abinda ta hadiya tunda har take neman ya saukake mata
"Kaci abinci AbdulKadir, zan ma Abban naka magana"
Kai AbdulKadir ya jinjina mata, shi abincin ma yau ba damun shi yayi ba.

Sai da Hajja ta sake dauko plate din ta mika mishi a hannun shi, cakudawa yayi gabaki dayan shi ya fara ci, taunawa yake yana hadiyewa da wani irin nisantaccen yanayi shimfide a fuskar shi...!
#TeamAbdulKadir
#TeamWaheedah
#LubnaSufyan
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
AbdulKadir Comments
Zauren Biebee Isa
Wattpadians
Daukacin makaranta AbdulKadir
Godiya mai tarin yawa
#SonSo saboda Allah
A waya Hajja ta kira mishi Abba, amman ca yayi bayason ganin AbdulKadir din, idan sulhu yake nema yaje wajen Waheedah, shi kam ba zai saka musu baki ba.

Da wani irin sanyin jiki AbdulKadir yabar gidan.

Amman tsintar kan shi yayi da nufar hanyar gidan Yassar, ba zai iya zuwa gida ba, har a kasusuwan shi yakejin bukatar Waheedah a kusa dashi.

Bai taba zaton zaiyi kewarta irin haka ba, ko watannin da yakan shafe batare da ita ba, inya tuna cewar tana gidan shi, tana jiran komawar shi kan nutsar da wani bangare na zuciyar shi.

Amman yau yana gari daya da ita, da auren shi a kanta ace ta kwana bakwai bata cikin gidan shi, gidan su, abin yana ci mishi zuciya fiye da yanda zai iya fadi.

Gidan Yassar ya karasa yana parking din motarshi, a jiki yabar mukullin yana fitowa, ya karasa bakin kofa yaci karo da Yassar din da yake girgiza kai
"AbdulKadir..."
Katse shi AbdulKadir yayi da fadin
"Hamma dan Allah, banajin tashin hankali, magana kawai zan mata, dan Allah karka cemun wani abu, na roke ka"
Da bayanannen mamaki Yassar yake kallon AbdulKadir, yasan kaf gidan su daga su Hajja sai shi AbdulKadir kan dagawa kafa lokutta da dama, amman Yassar yasan su Hajja kawai yake saukewa murya irin haka, ya kasa yarda da AbdulKadir ne a gabanshi yake rokon shi alfarma yau.

Mutane kan ce in da ranka ka sha kallo, kallon yake sha yanzun.

Rabashi AbdulKadir yayi yana wucewa cikin gidan, yaji dadi da baici karo da Hauwa ba har ya karasa dakin da Waheedah take ya kwankwasa tukunna ya murza hannun kofar yana shiga.

Ta sake kaya, rigar bacci ce a jikinta, doguwa har kasa.

Kalar rigar bata dami AbdulKadir ba, idanuwan shi na kan fuskar Waheedah da take kallon shi da gajiya shimfide cikin idanuwanta, takawa yayi ya karasa gefen gadon yana kama hannuwanta ya dumtse cikin nashi
"Me yasa zaki karya alkawarin ki?

Kince ba zaki barni ba, da bakin ki kin sha fadamun zaki kasance tare dani....

Wahee in ke zaki iya barina ni bazan iya barin ki ba....

Wallahi ba zan iya ba"
Kallon shi Waheedah take tunda ya fara magana, amman zuciyarta a bushe take ballantana kalaman shi suyi mata tasiri, a hankali ta tara abinda ya kawota inda take yanzun, batajin akwai kalaman da zasu canza ra'ayinta.

Hakan AbdulKadir ya kula dashi, ya sake dumtse hannuwanta da ta fara zamewa daga cikin na shi.

"Waheedah ni ne fa, ki kalle ni, ni ne, ban aureki dan in rabu dake ba..."
Ya karasa maganar da wani nisantaccen yanayi a muryar shi, yana kasa yarda Waheedah ce take son barin shi.

Yana tuna lokacin da aiki ya kaishi tsakiyar inda ake tarzomar yan boko haram a Maiduguri.

Ta dauka tashin hankalinta kan aikin shi ya fara tsagaitawa, sai da aikin ya daukar mata miji yayi Maiduguri da shi.

Tana da cikin Fajr wata kusan bakwai.

Ko yaushe wajen awo ca suke mata ta kwantar da hankalinta, amman tasan ita da kwanciyar hankali sunyi hannun riga har sai AbdulKadir ya dawo gida.

Kasancewar in da suke babu network, duk Asabar yana samu ya fito ya kirata, idan bai kirata ba, wani idan ya fito cikin abokan aikin nashi zai turo mata da sakon AbdulKadir din.

Yanda kwanaki kan wuce mata tsakanin Asabar zuwa wata Asabar din ba zatace ba.

Sai dai duk wani tashin hankali da take tunanin ta taba shiga, ko ta taba jin labari bai kai wanda take ciki a yanzun da satika uku suka wuce batare da labarin AbdulKadir ba, wata na hudu yake nema lokacin a Maiduguri, bai kuma taba wuce sati biyu bataji daga wajen shi ba.

Ya fada mata idan sati hudu suka wuce bai kira ba, ko sakon cewar yana lafiya bai sameta ba, to wani abin ya faru dashi, tayi mishi addu'a.

Kukanta bai tsananta ba sai da satika hudun suka cika babu labarin AbdulKadir, musamman da su Hajja suka fara kiranta suji ko AbdulKadir din ya kira, Anty ma ca tayi zata zo ta dauketa su koma gida, tunda ga cikin ya tsufa, ga kuma tashin hankali, sai dai ba zasu gane ba.

Ba gida take son zuwa ba, mijinta take son sanin yana lafiya.

Ba zata ce ga abinda take tunani ba, safiyar asabar din da AbdulKadir ya cika sati biyar bai kirata ba.

Zata iya tuna sauka daga kan gado ta shiga bandaki, yanda tayi wanka bata sani ba, dan hankalinta yayi nisan da ba zata iya taro shi ba.
Chapter 71 · 0% Book details