← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 94

Sashe 52

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai yanzun da Nuriyya ta katse mishi baccin da yakeyi, ga yunwar da yake ji har hanjin shi kullewa yake.

Fitowa yai ya wuce dakin Waheedah.

Cikin jakunkunan ta ya dauko ya duba, dari biyar ya dauka a ciki yasaka a aljihu yana ficewa.

Mai babur ya tara zuwa gidan man, jikin shi har bari yakeyi daya karasa ya samu wanda zai jibga, ko canji bai tsaya karba ba, ya shiga cikin gidan man, inda take yake neman, kafin ya hango motar shi, da kuma Nuriyyar da take jingine a jiki.

Har yayi hanyar ya hango kamar Major M.

Alkali a tsaye jikin wata golf, sake dubawa yayi kuwa, shi dinne, dan sunyi aiki tare a Lagos.

Mutum ne shi da matsayin shi da kakin shi bai taba sa ya wulakanta kowa ba, duk da yana da zafi in an tabashi, kuma yana cikin sojojin da AbdulKadir yasani da suka tsani wanda yake amfani da kakin shi yaci zarafin mutane.

Fasa karasawa yayi inda Nuriyya take, sai da ya karasa can wajen shi yana kai gaisuwa, amsawa yayi baima iya tambayar AbdulKadir din abinda yake a gidan man ba.

Ganin kamar ran shi a bace yake yasa AbdulKadir din yi mishi sallama yana takawa ya karasa wajen Nuriyya da ta fara fifita fuskarta da mayafin jikinta tun daga lokacin da ta hango AbdulKadir din ya karasa ya sarawa mutumin da ta wanke da mari.

Hawayen ne wani nabin wani yake saukar mata
"Ki daina kuka...

Su waye?

Waye ya tabaki?"
AbdulKadir yake tambaya, sai dai ta kasa amsa shi, kuka take kamar zata shide mishi, baki ya bude zai sake magana, kamar daga sama yaji muryar Major M.

Alkali yana fadin
"Matarka ce ta wanke ni da mari kenan?

Shine ta kiraka kazo kayi amfani da kakinka kaci mun mutunci..."
Cikin tashin hankali AbdulKadir ya juya yana kallon Major, kafin ya juyo ya kalli Nuriyya da ta ja mishi bala'in da baisan ta inda zai fara fita daga cikin shi ba.

"Nuriyya..."
Ya kira muryar shi dauke da wani yanayi.

Kuka take tana girgiza mishi kai, dan ita kanta batasan kalar tashin hankalin da zai biyo baya ba kenan, da tasan soja ne, sojan ma da alama yaiwa mijinta fintinkau da bata fara tsayawa ba, tun sanda ake cewa ta tafi, da lokacin ta shiga motarta ta wuce.

"Muje ko..."
Major ya fadi yana kallon AbdulKadir.

Shikuma ya kalli Nuriyya kafin yabi bayan Major din, da sauri Nuriyya take shirin bin bayansu, wani irin kallo AbdulKadir ya watsa mata daya saka ta jin gabaki daya kayan cikinta na yamutsawa, idanuwanta cike taf da sababbin hawaye take kallon su, har suka karasa wajen golf din su Major da ta raina har tayi musu dibar albarka, boot din motar taga ya bude, AbdulKadir ya shiga ya kwanta, ya kuma mayar da murfin ya rufe, suna shirin shiga su tafi.

Ai bata san lokacin da ta kwasa da gudu tayi wajen su tana fadin
"Ina zaku kai shi?

Ina zaka tafar mun da miji?

Ka rufamun asiri, dan Allah kayi hakuri...

Ka rama marinka ka kyalemun miji"
Wani irin kallo Major ya watsa mata
"Marin zai fita a jikin mijinki, karki damu"
Ya bude motar ya shiga, suka wuce suna barin Nuriyya nan tsaye ta dora hannunta saman kai tana fadin
"Na shiga uku na..."
#TeamAbdulKadir
#TeamWaheedah
#LubnaSufyan[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
MAFARI
Rigima ce ta saka shi biyo mota daga Lagos zuwa garin Kano, dan tashi motar in ba hutun karshen shekara zai zo ba, baya tahowa da ita, babu yanda Waheedah batayi dashi akan ya biyo jirgi ba, yace mata bashi da kudi, wata yayi nisa, ga hidimar gida da sauran hidindimun dake gaban shi.

Saida tace mishi ya biya kawai, akwai kudi a hannun ta, Abba ya bata kyautar kudi, batayi amfani dasu ba, akwai kuma kudin da shima yake bata, duk bata siyi komai ba, amman yaki.

Jikin shi babu inda baya ciwo, ga rashin wadataccen bacci tunda motar dare ya biyo, da safe ya iso garin Kano.

Tunda Waheedah ta hada mishi ruwan wanka ta tafiyarta kitchen taci gaba da aikin kifin da ta fito dashi dan ya huce tun da asuba, tunda yayi kankara a fridge.

Sanda ya fito daga wanka, ta dauko mishi riga da wando marassa nauyi, sakawa yayi yana binta kitchen din.

Bude-buden kulolin duk da yagani yakeyi, ko kallon shi Waheedah batayi ba, kifinta take gyarawa, tana jinshi ya karaso inda take, yana dora kanshi a kafadarta, ta baya.

Ture shi tayi
"Sai na saka maka karnin kifi ko?"
Kankance mata idanuwanshi yayi
"Ni kike ta sharewa ko Wahee?

Yunwa nakeji, ki bani abinci, tun jiya banci komai ba"
Kwandon da ta zuba kifin a ciki ta dauka ta dora cikin wani kwano, tana saka omo ta wanke hannuwanta da sink din wanke-wanken ma, tana son kifi, amman sosai karnin shi yake damunta, shisa duk abinda zatayi amfani dashi bata iya ajiyewa, saita wanke.

Karamin towel ta dauka ta goge hannuwanta, sai lokacin ta kalli AbdulKadir sosai, daya biye mata, tun jiya da suna tare, yanzun idan ya tafi tana iya wata uku ko fiye da haka bata saka shi a idanuwanta ba, dan ma manhajar Imo data shigo, suna video call sosai, amman ba kamar dai yana kusa da ita ba.

"Duk lokacin dana samu na ganinka yana da muhimmanci a wajena, kamun asarar kwana daya saboda bakajin maganata"
Ta karasa tana hararshi, murmushi yayi yana fadin
"Kin san wa kika aura Wahee, kinsanni"
Kai ta jinjina mishi, ita kuwa ta san shi fiye da kowa da yake da kusanci dashi, wucewa tayi ta gaban shi tana fita daga kitchen din
"Da gaske yunwa nake ji, Allah banci komai ba"
Wannan karin ita tayi dariya, har mamakin yanda yake rayuwa a matsayin soja takeyi, da wajajen da ya shiga, da wanda tasan zai shiga anan gaba.

In yana bata wasu labaran, takan tambayeshi ya yakeyi da abinci.

Dan daga mata kafadu yakan yi
'Tunanin ko zan sake ganinku, ko zan sake samun damar rike ki a jikina baya barina yin wani tunanin, Hajja kan zo mun a rai, amman tana da wasu yaran, rashina zai mata sauqi duk idan ta kalle su, bana son barinki, tunanin yanda zakiyi yana sani jure komai, ciki harda rashin abinci ko na tsayin kwanaki nawa'
Ranar farko daya fada mata hakan, kasa magana tayi, sake shigewa jikin shi tayi, tana kokarin mayar da hawayen da suke cike da idanuwanta, banda nemawa kanta sauqin mutuwa da kariya daga azabar kabari, ta manta ranar karshe da tayiwa kanta wata addu'a, dukkan sujjadarta cike take da neman Allah ya tsare mata mijinta.

Matan sojoji ne kawai zasu iya fahimtar wannan fargabar da take ciki a duk ranar da baya kusa da ita, ko bata ji muryar shi ba, ko ta nemi wayarshi bata shiga.

Zuwa yanzun zata iya cewa sai zazzabi yayi da gaske yake kwantar da ita, dan sunyi wani irin sabo na ban mamaki.

Wajen cin abincin ta, sai dai ta janye kujerun ta goge, ta kakkabe su, inba randa tayi baqi ba.

AbdulKadir ba so yake takai mishi abinci can ba, yafi so ya zauna a kan kafet, harya saba mata itama, ko baya nan kan kafet take zama taci abincin ta.

Yanzun ma ta riga ta fito da kulolin da flask din shayi.

Saida ya zauna tukunna yace mata
"Ina yaro na?"
Numfashi ta sauke, tana zama itama
"Hamma Yassar ya dauke shi tun jiya"
Daquna mata fuska AbdulKadir yayi
"Kinsan zan zo....

Me yasa zaki bar shi ya tafi dashi?

Ni zanje in dauko yaro na"
Bata ce mishi komai ba, dankalin da ta soya ta zuba mishi a plate, ta samu dan kwano data fito dashi ta zuba farfesun naman da du
mamawa tayi da safen, dan tun jiya da rana tayi ta saka a fridge.

Bata san yanda AbdulKadir yake so ta fara cewa Yassar karya tafi da Fajr ba.

Wannan aikin sai shi, dan akwai dawowar da yayi yaje har gaban Hajja ya dauko yaran shi.

Wani abin idan yayi sai dai ita taji kunya, shikam ko a jikin shi.

Hira suke danyi sama-sama harya gama cin abincin ya miqe, tayata kwashe kwanonin yayi ya wanko hannun shi a kitchen din, ya fito yana fadin
"Zanje mu gaisa da Hajja...

Sai in biya in dauko Fajr...ko zaki rakani?"
Kai Waheedah ta girgiza mishi
"Aiki zanyi wallahi, dan Allah karkai mun rigima Sadauki, kaga kifi na gyara, aiki zanyi...

Kaje ka dawo"
Waheedah ta karasa tana shagwabe mishi fuska, dan ya fara kankance mata idanuwanshi cike da rigima, zai iya cewa ta ajiye kifin suje su dawo.

"Shikenan tunda ba zaki rakani ba"
Langabe kai tayi
"Ba kin rakaka nayi ba, aiki zanyi.

Anjima kadan zaka fara kira mun yunwa"
Murmushi yayi, dakinta ta wuce tana dauko wallet din shi da wayar shi da suke ajiye kan gadon ta, bude wallet din tayi taga da kudi a ciki, ta fito tana kawo mishi.

Numfashi ya sauke, zai iya rantsewa daya gan shi a kusa da ita yake manta yanda zaiyi abubuwa da yawa.

Da bata dauko mishi ba, ya manta wallet din da wayar basa jikin shi.

Har bakin kofa ta raka shi, tukunna ta dawo ta shiga kitchen.

Da Mami kawai ya gaisa, dan bai samu Hajja ba, yarinyar kanwarta ta haihu, tunda safe ta tafi Aminu Kano.

Tunanin ya kira wayarta bai zo mishi ba, da bai sha wahala ya fito ba, yayi kwanciyar shi yai bacci.

Inya tashi sai yazo ya dauki Fajr din.

Fitowa yayi daga gida, yana sakko kafarshi bakin kofa yana cin karo da ita, wani irin tsalle zuciyar shi tayi daga kirjin shi, kafin ta koma mazauninta tana ci gaba da wani irin dokawa da yakeji har cikin kunnuwan shi.

A duk tsayin shekarun nan, bai taba barin kan shi yayi tunaninta ba, saboda yasan matsayin hakan a addinin shi, ya kuma san darajar kan shi, fadin garin Kano zai musu kadan da duk namijin da yasan yana mishi tunanin Waheedah.

Kuma ko ba komai, shi mutum ne da baya tunani akan abinda ya wuce.
Chapter 52 · 0% Book details