← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 94

Sashe 79

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yassar yabita da kallo ganin babu takalma a kafarta, baice komai ba, ya koma inda ta tashi yana zama ya saka idanuwan shi a kan AbdulKadir da duk motsin da zaiyi sunan Waheedah ne a bakin shi, Yassar na jinjina ma kaddarar su, ya dauka yasan zafin so a kan Hauwa, yanzun AbdulKadir da Waheedah ke nuna mishi bakomai suka sani ba a soyayya, dan tasu kalarta daban ce.

Rabonta da gidan Yassar tun lokacin da matar shi tayi bari, da yake yarinyar ta sha wahala sosai.

Bata kuma zata zatazo gidan batare da wani dalili da zai kasance ya shafi Yassar din ko Hauwa ba, bata taba tunanin dalilin AbdulKadir zaisa tazo gidan Yassar din ba, a kofar gida tayi parking din motar, tunda tasan inta gama abinda takeyi sake fita zatayi, bataga wahalar saita shigo da motar ba.

Tsakuwoyin da ta taka na tuna mata cewar babu takalma a kafarta, haka ta shiga cikin gidan, maigadin kan shi kallon ta yake dan yana da tabbacin ba lafiya ba.

Har cikin gidan ta shiga, taci karo da Waheedah da take fita daga kitchen din, itama Ikram zata wankema jiki ta sake mata pampers taji ruwan da sanyi, tausayi yarinyar ta bata shisa ta dafa, tana sake mata kuma bacci ta koma, shine ta fito ta kawo kettle din taci karo da Hajja, sai da zuciyarta ta doka, musamman yanayin Hajja din
"Hajja..."
Waheedah ta kira cike da shakku da alamar tambaya, inda take Hajja ta karasa
"Alfarma na zo roka Waheedah"
Hawaye Waheedah taji sun cika mata idanuwan da suke a kumbure suna zubowa a hankali
"Nasan zaki ce na so kai na, zaki ce na duba bukatar 'dana sama da taki, amman banda wani zabi...

Wallahi yanzun ma yana asibiti, faduwa yayi Waheedah"
Hajja ta karasa maganar muryarta na karyewa, wasu hawayen Waheedah taji sun kara zubo mata, muryarta a sarqe cike da kuka tace
"Hajja nima naje asibitin gado zasu bani"
Kai Hajja ta jinjina mata
"Nasani, kiyi hakuri, dan Allah kiyi hakuri, ki duba yanda ya koma cikin sati daya...

Kina tunanin zai iya rabuwa dake?

Bakomai yake raunana AbdulKadir ba, banma taba ganin abinda ya saka shi shiga yanayi haka ba...

Shisa na zo in baki hakuri, koma menene yai miki dan Allah kiyi hakuri"
Hannu Waheedah tasa tana goge fuskarta, amman wasu hawayen ke zuba, itakam hakurin ne bataso su bata, saboda zuciyarta harta fara karyewa, musamman da Hajja ta dafa kafadarta fuskarta cike da roko tana fadin
"Ki yafe mishi dan girman Allah, ki duba rokona Waheedah..."
Kuka Waheedah takeyi, hakan yasa Hajja ta riketa a jikinta, kaddarar yaran na tsaya mata, ita kanta Waheedah din a idanuwanta zaka ga rauni, AbdulKadir dinne ya tabata sosai, amman rabuwa dashine karshen abinda take bukata.

Cikin kuka tace
"Hajja bansan ya zanyi ba...

Ban sani ba nikam"
Riketa Hajja tayi sosai
"Hakuri zakiyi, kiyi hakuri...

In yayi abinda ya nuna miki ke din bakida muhimmanci halin daya shiga yanzun ya isa ya karya shi...

Ke dince rayuwar shi Wallahi..."
Kai Waheedah ta girgiza tana kin yarda da kalaman Hajja, wani kishi naban mamaki na turnuqe zuciyarta, da itace rayuwar shi da bai hadata kishi da Nuriyya ba, da itace rayuwar shi da bai ci mutuncinta ya auri aminiyarta ba.

Dagowa tayi daga jikin Hajja tana saka hannuwanta duka ta share hawayenta
"Waheedah..."
Hajja ta fadi tana rasa da kalaman da zatayi amfani dasu dan rikici take gani shimfide a idanuwan Waheedah din, da gaskiyar mutane ka guji bacin ran mai hakuri
"Jinin shi ya hau"
Hajja tace tana saka Waheedah rausayar da kai, cikin sanyin murya tace
"Nima hawan jinin nake fama da shi Hajja"
Hawaye na zubar mata, duk idan tayi zaton hawayenta sun kare sai wani abin ya sake faruwa da zasuci gaba da zuba kamar an bude fanfo, numfashi Hajja taja tana fitar dashi kafin tace
"Shikenan Waheedah, Allah ya zaba muku abinda yafi alkhairi"
Ta juya tana ficewa daga gidan.

Daki Waheedah ta koma ta dauki wayarta, kuka take har bata ganin abinda ke rubuce a screen din wayar sosai, saida ta goge fuskarta tukunna ta lalubo lambar Abba ta kira, bugun farko ya daga da fadin
"Waheedah..."
Wani irin kuka ta rushe dashi da yasa Abba cewa
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un...

Waheedah me ya faru?

Menene?

Me akai miki?"
Ta dayan bangaren, kana jin tashin hankalin dake cikin muryar shi, numfashi take fitarwa kamar zata shide saboda kukan da takeyi
"Ab....Abba..."
Ta iya fadi dakyar tan dorawa da
"Kowa nata bani hakuri...

Abba har Hajja hakuri take bani, zuciyata ciwo take mun Wallahi...

Dana tuna zuciyata ciwo take mun...

Ab...Abba bansan ya zanyi ba"
Tanajin ya sauke numfashi, cikin taushin murya mai cike da lallashi yace
"Kiyi duk abinda zuciyarki zata nutsu da shi, karki bari hakurin da suke baki ya saki yin zabin da zaki cutu, karkuma ki bari fushinki yasa kiyi zabin da ba zakiyi dana sani"
Kai Waheedah take jinjinawa tana goge fuskarta da bayan hannunta
"Kina jina?"
Abba ya fadi yana sa ta sake jinjina mishi kai
"Zan zo in dubaki anjima, ki samu ruwa ki sha, ki daina kuka kinji Waheedah?

Komai zaiyi dai-dai"
Kai ta jinjina tana kara goge fuskarta, batace komai ba ta sauke wayar daga kunnenta, bata samu damar sanin mahaifinta ba, amman Abba ya bata kauna da kusancin da ko mahaifinta jinin shi dake yawo a jikinta ne kawai zai nunawa Abba.

Abu biyu ta sani, zuciyarta na mata ciwo na gaske na biyun a fili ta fade shi
"Kin yi kadan in bar miki mijina Nuriyya...

Nabar miki abubuwa da yawa a rayuwata, ban da shi, banda Sadauki na..."
Ta goge hawayen da suka zubo daga zuciyarta tana jin wani irin karfin gwiwa da bata taba jin irin shi ba...!
#LubnaSufyan
#TeamAbdulKadir
#TeamWaheedah
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
Hauwa A Usman Jiddarh
Nagode da kauna
Kunshin hannunta da yake rike cikin na farin matashin saurayin ya fara bi da kallo, kirjin shi na zafi kamar zai bude, kafin yaga saurayin ya mika kai saitin kunnen Waheedah yana rada mata wata magana da tasa tayin dariyar nan tata da take kashe mishi jiki.

Baisan ya karasa wajen ba saboda wani irin kishi daya turnuqe shi har duhu-duhu yake gani, tsakanin su ya shiga yana huci kamar kububuwa.

"Lafiya?"
Saurayin ya fada yana kallon AbdulKadir din kamar yaga mahaukaci.

"Lafiya kake tambayata?

Bakasan matata bace dan ubanka?"
Dariya saurayin yayi data kara bata ma AbdulKadir din rai
"Ka saketa din, na aura kana fadamun matar..."
Bai karasa maganar ba AbdulKadir din yakai mishi wani irin naushi a baki
Duka Yassar yakai ma AbdulKadir din da saura kadan ya gabje mishi hanci, duk da haka ya same shi kadan a gefen mummuqe, wani dukan ya kara jibga mishi yana fadin
"Tashi....

Ka warke shisa zaka kwantar dani ba..."
Mikewa AbdulKadir yayi yana dafe kan shi da yake sarawa, a zuciyar shi yake karanto
'Inalillahi wa ina ilaihi raji'un'
Yana neman tsari daga muguwar kaddara, tari ya sarke shi da yasa Yassar din mika hannu ya dauko robar ruwan da take gefe ya mika ma AbdulKadir din, da sauri ya karba yana sha.

Kishine yake turnuqe shi har lokacin, kowanne mahaukaci ne yake tunanin zai saki Waheedah ya aura yana fatan yazo da bargo da filo, dan zaici gaba da kwana a wajen ne, in yagaji ya kara gaba.

Karin ruwan da yake daure a hannun shi ya kalla yana son tuna lokacin da suka zo asibiti
"Karka kara tsoratani haka AbdulKadir, idan kana so in goyi bayanka ka zamana mai gaskiya, karka kara tsoratani haka"
Yassar ya fadi muryar shi can kasan makoshi, yanajin yanda har lokacin zuciyar shi bata daina rawa ba.

Ganin AbdulKadir din a kwance ya tsorata shi fiye da tunani, ya tuna mishi duk wani dalili da yasa bayason uniform din shi, a lokaci daya kuma ya tuna mishi da soja ko ba soja ba, mutuwa babu ruwanta, ba zabe take yi ba, kowa nata ne, lokaci kawai take jira ta cika aikin ta.

"Ashe kana so na"
Cewar AbdulKadir da murmushi a fuskar shi duk da kirjin shi da yake ciwo, hararshi Yassar yayi da yasa ya karayin dariya, sautinta na dirar mishi a kunne da wani irin yanayi
"Zuciyata namun ciwo Hamma"
AbdulKadir ya fadi yana dorawa da
"Kaman zata fito daga kirjina haka nake ji...amman Waheedah tace mun haka ta dinga ji harna wata takwas, Hamma ta ina zan fara bata hakuri?

Ta ina?

Yau kawai na fara jin hakan amman inajin kamar lokacin mutuwa yazo gab...

Wanne irin karfin hali gare ta?"
Kallon shi Yassar yake, yana jin kuncin dake tattare da muryar kanin na shi da yake tabashi sosai da sosai
"Kayi kuskure AbdulKadir...

Bance maka nayi dana sanin zama sanadin daka auri Waheedah dan bana son zaman ku ba...

A karo na farko kasa naji dana sani nabar Hamma Yazid ya aure ta"
Da mamaki AbdulKadir yake kallon Yassar din yana jin maganganun shi sun dirar mishi kamar saukar ruwan da babu hadari
"Hamma Yazid?"
Ya maimaita cike da alamar tambaya, kai Yassar ya jinjina mata
"Yana son ta, ya sota a lokacin, ni na fada mishi kuna soyayya saiya hakura...

Shisa yai nisa da Kano..."
Wannan karin ruwan da yake hannun shi AbdulKadir ya fisge duk yanda Yassar din ya kira sunan shi, kafafuwan shi ya sakko daga kan gadon yana jin shi wani sama-sama.

Yazid ya so Waheedah?

Ko kadan kwakwalwar shi ta kasa yardar mishi da maganar, muryar shi can nesa cike da tuquqin kishi yace
"Me yasa ta aure ni to?

Tunda yana son ta"
Ya karasa maganar yana kallon Yassar din kamar zai rufe shi da duka, numfashi Yassar ya sauke
"Ka taba ganin son wani a idanuwan ta?

Bai taba fada mata ba, bata taba son shi ba, kishin banza da wofi zaka nuna yanzun?
Chapter 79 · 0% Book details