Sashe 80
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kana kishinta amman baka iya kula da damuwar ta ba"
Runtsa idanuwa AbdulKadir yayi yanajin kamar Yassar ya watsa mishi ruwan zafi, kafin ya bude su a kan shi da fadin
"Karka karamun ciwon da nakeji"
Kujerar shi Yassar yaja yana matsawa gab da AbdulKadir din sosai
"Ba Hamma Yazid ya so Waheedah zaka duba ba AbdulKadir, ka duba yanda ya zabi farin cikin ka a kan nashi, ka duba yanda mu duka muke a shirye da dora farin cikin ka akan namu, ka fara yarda da fadanmu ba nuna isa bane a kanka, fadan mu na tare da yanda muke son ka"
Wannan karin kamar AbdulKadir din zaiyi kuka yake kallon Yassar, idanuwan shi sun kara kankancewa
"Sau nawa abinda nayi yai hurting din ku?
Rashin tunani da rashin duba abinda halayena suke yiwa na kusa dani, Hamma sau nawa?"
Dan murmushi Yassar yayi
"Ba zai lissafu ba"
Ya amsa a taqaice yana sa AbdulKadir din runtsa idanuwan shi yana bude su, zuciyar shi na wani irin ciwo
"Harda su Hajja ko?
Halayena na taba su suma"
Kai Yassar ya daga ma AbdulKadir din da dan murmushin karfin hali a fuskar shi
"Ta ina zan fara?
Taya zan fara baku hakuri Hamma?
Ban taba tunanin nan ba, ban taba tunanin dan nayi abinda ni ya shafa zai taba mutanen da nafi kusanci da su ba, mutanen da nake kauna da dukkan zuciyata"
Numfashi Yassar ya sauke
"Ka fara da sauraren shawarwarin mu, ko da baka dauka ba, ka nuna mana yanda muka isa ka saurara"
Kai AbdulKadir yake jinjina, kome suke so shikam zaiyi, tunanin yana cutar dasu ba karamin karyar mishi da zuciya yake ba
"Ka bude bakin ka kaba Waheedah hakuri, tana son ka, shisa kishinka yai mata yawa..."
Kai AbdulKadir din ya sake jinjina, muryar shi a karye yace
"Bansan ya akai kuke so na ba har yanzun Hamma, bana tunanin idan nine a matsayin ku zan manta duk abubuwan nan inci gaba da zama daku"
Wannan karin murmushin Yassar daga zuciyar shi ya fito
"Ba zabi aka bamu ba kafin ka kasance dan uwan mu, akwai alakar da bata baka wannan zabin, haka kaunar da muke maka, ba muna tare da kai dan mun manta abubuwan da kayi da bamu so ba, muna tare da kai saboda mun yafe maka hakan tun kafin kagane kuskure ne ka roke mu"
Hannu AbdulKadir din yakai yanajin kamar maiqo a gefe-gefen idanuwan shi, yasa yatsun shi yana dangwalowa, Yassar din naci gaba da fadin
"A kasan duk rashin kunyar ka, dan uwane kai da ko an bani zabi bazan taba daukar irin shi ba, kana da halaye da bana so, halayen da zanso ka sake su, amman shine cikar dan adam din, duk idan zamu fadama kan mu gaskiya akwai halayen da muke dasu da muke son canzawa saboda ba masu kyau bane ba"
Ya dauka zuciyar shi tagama karyewa da maganganun Waheedah, sai yanzun da yakejin hawayen daya dauka sunyi bankwana dashi cike taf da idanuwan shi, kaunar Yassar din na taba shi tana karya sauran abinda ya rage a zuciyar shi, ko yau rayuwa ta kare mishi yana da tabbacin kaunar su zata cigaba da samun shi a kabarin shi, saboda addu'o'in su ba zasu taba yankewa ba.
Baisan ya mike daga kan gadon ba saida yaji Yassar yasa hannu yana ture shi ya mayar dashi ya zaunar
"Rungumeni za kai dan ubanka?
Meye haka?
A india muke ko America?
Bana son iskancin banza da wofi fa"
Dariya AbdulKadir yake sosai yana goge idanuwan shi da yakeji cike da hawaye
"Nagode Hamma"
Ya fadi da dukkan zuciyar shi, kai Yassar ya daga mishi, AbdulKadir din na dorawa da
"Kai musu magana su zo su sallameni, ni bazan kwana anan ba"
Kallon shi Yassar yayi
"Faduwa fa kayi AbdulKadir..."
Kafadun shi duka biyun ya maqale ma Yassar
"Wallahi Hamma bazan kwana ba, in basu sallameni ba zan tafi da kaina"
Kai kawai Yassar ya girgiza hadi da sauke numfashi ya mike, mai hali akace baya taba canzawa, akwai halayyar AbdulKadir din da a jinin shi take, bazai iya canza ta ba, taurin kai na cikin wannan
"Kai kam ko Sheikh Mufti aka saka a ruwa aka girgiza aka baka kasha kayi wanka ba zaka canza hali ba Wallahi"
Dakuna mishi fuska AbdulKadir din yayi yana hade girar sama da ta kasa, babu wanda zai saka shi zama a asibiti, banda zazzabi bayajin komai, sai ciwon kai sama-sama, kirjin shi da yakeyi kamar zai bude ba asibiti yake bukata ba, Waheedah yake bukata, in ya riketa a jikin shi zai samu saukin duk wannan abubuwan da yake ji.
Da ido yabi Yassar din harya fice daga dakin, kafin ya sauke ajiyar zuciya yana jin tunanin Waheedah daya baibaye shi.
Ruwa ta watsa bayan tafiyar Hajja, ta sake kaya.
Wata nutsuwa take ji data kwana biyu bataji irin ta ba, WhatsApp dinta ta bude tana shiga sakon da Hauwa ta turo mata na littafin Farin Wata na Zahra Tabi'u.
'An saka mata sunan mace ba dan ana tunanin ita din cikakkiyar mace bace'
Ta karanta layin farko, maganganun na saka ta tunani barkatai, tun daga kan maitafiya take son marubuciyar, saboda tana tabo labaran da bako yaushe ake tabo su ba a cikin duniyar rubutu, tallar kawai ta ja hankalinta sosai.
Dari uku batai mata tsada ba, account number din ta dauka tana tura kudin kafin ta dauki lambar marubuciyar 08065156303 dan ta tura mata shaidar biya.
Tana karasawa ta mike, tana tunanin shiga kasuwane dan tayi siyayyar azumi tunda yau dinne ake sa ran fara duban fitowar watan, duk da anata gardama kan hakan kamar ko da yaushe.
Abin na daurema Waheedah kai, yanda ake shafe watanni goma cir ana tafiya kai a hade, sai ance watan Ramadan ya gabato sai a fara rikici kan lissafi, yanda aka saki sunnah da Manzo SAW ya doramu a kai na tsoratar da ita, shisa abubuwa sukai mana yawa, wahalhalun mu suka yawaita.
Shagon da takanyi siyayyarta guda dayane, dan sun saba sosai, lokutta da dama duk abinda take so ma list takeyi saita tura musu text, wanda sai an shiga kasuwa cikin yaran shagon ake sakawa yaje ya siyo mata, kafin ta shiga duk sun hada mata kayayyakinta, kudin kawa za tayi musu transfer, sai a nemo mata mai napep a saka mata kayan a baya.
Wasu lokuttan kuma mai napep din da taje dashi ne bata sallama.
Yanzun ma komawa tayi ta zauna tana tunanin abubuwan da take bukata, list dinsu tayi gabaki dayan su, sai doya da dankali da ta saka na adadin da zasu siyo mata, daya daga cikin yaran shagon Tasi'u ta kira, bazai wuce shekaru sha tara ba, amman hankalin shi har mamaki yake bata, ga girmama mutane, tace ya duba whatsapp din shi ga kayyakin da za'a hada mata nan, yanzun zata shigo kasuwar, ya kuma taimaka inda yakan siyo mata doya da dankali ya siyo mata doya ta dubu biyu sai dankali na dubu uku.
Tasan zata kwana biyu bata nema ba.
Kayan su ta hada a jakar da Yassar ya kawo musu.
Ta kara gyara dakin tsaf tukunna ta saka Ikram a jakar goyanta, tasa hijab tana goya yarinyar ta gaba, ta dauki jakar da mukulli ta wuce, a falo suka ci karo da Hauwa, da mamakin ganin ta dawo da wuri a tattare da Waheedah tace
"Yau da wuri haka?"
Dariya Hauwa tayi
"Nagaji fa, gudowa nayi nace banda lafiya"
Murmushi Waheedah tayi, daman tayi niyyar karbar kayanta a kasuwa ta sauke a gida ta dawo, sai tayi musu sallama tukunna ta wuce.
Cikin sanyin murya tace
"Ina son zuwa kasuwa ne, sai in biya gida in kai kayan nan"
Hauwa batasan lokacin data hade space din dake tsakanin su da Waheedah ta rungumeta ta gefe ba, saboda Ikram da take rike da ita, tukunna ta dago tace
"Inata kokari kar in miki magana Wallahi, inakuma kokari kar in wuce gidanki daga wajen aiki in jibgi Nuriyya ko zan huce haushina...
In kika bar mata gidan harni kin cuceni, bata isa kibar mata gidanki ba wallahi"
Dariyar karfin hali Waheedah tayi, Yassar yasa ta sami kawa a tare da Hauwa.
"Nagode Hauwa"
Ta fadi a sanyaye, kai Hauwa ta jinjina mata
"Muje in kaiki, ba abinda zanyi sai kwanciya ko na zauna gidan daman"
Tare suka fita da Hauwa din, har kasuwa sukaje tare tana ta tsegumin yanda motarta take bukatar ganin bakanike saboda tana mata wata kara da Waheedah bataji ba, tunda ba sanin kan mota tayi ba.
Da suka dauki kayan gidan Waheedah din suka wuce ta kai, bataga Nuriyya ba, bata kuma damu da hakan ba, har bedroom dinta ta wuce ta ajiye jakar kayansu, ta dauki mukullan data manta ranar karshe da tayi amfani dasu, ta kulle dakin baccin nata da sauran dakunan da suke bangarenta, dawowa tayi ta rufe kitchen dinta ma, dan siyayyar duk da tayi a tsakiyar kitchen din ta ajiye su, inta dawo ta shirya komai.
Suka sake ficewa da Hauwa din.
Saloon tace zataje ta wanke kai, tare sukaje, itama Waheedah kan aka wanke mata akayi mata kitso, yanda suka dameta da a saka mata bakin lalle akan jan da yake hannunta zaiyi kyau, harda Hauwa din yasa ta bari, da yake babban saloon ne, har su gyaran jiki anayi.
Lokacin da suka gama, wani yawon Hauwa ta sake janta, wai zata kai dinki.