Sashe 45
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zai iya rantsewa da duk wani abu na jikinshi harta gashin dake bayan wuyanshi yana sane da zamanta a gefen shi.
Fuskarta yake son gani ko yayane, amman hular alkyabbarta ta kare mishi.
Ko kunshinta baigani ba sosai, ta turo mishi hotunan da tace ana mata, amman da aka gama baigani ba, yaita jira ko zata tura mishi amman shiru, sai bai tambayeta ba tunda zaizo yagani da kanshi.
A nutse yake tukin har suka karasa gida sannan ya samu waje cikin harabar gidan yayi parking.
Fitilar dake cikin motar ya kunna haske na gauraye su.
Gyara zaman shi yayi yana kai hannu yaja hular alkyabbarta yana sauketa daga saman kan nata.
Hakan yasa Waheedah da tayi zurfi cikin tunanin da ba zatace gashi ba ta juyo tana sauke mishi manyan idanuwanta da kwalliyar da akai musu ta saka su kara girma.
Wani irin numfashi AbdulKadir ya tsinci kanshi da ja yana furzawarwa hadi da yawata idanuwan shi akan fuskarta da tayi mishi kamar ba tata ba.
A hankali yake jin bugun zuciyarshi na karuwa musamman data motsa labbanta da yake komai dan ganin baisaka yatsan shi akai yaji ko janbakinta nada maikon da yake gani marar walqiya ko kuma idanuwan shine suke haska mishi hakan.
"Hamma..."
Ta kira cikin sanyin muryarta da yaji ya saukar mishi da wata kasala taban mamaki.
"Me yasa kika kashe wayarki?
Kinsan zan kira meyasa kika kashe?"
Maganar tashi ta fito a matsayin tsegumi maimakon fadan da yayi niyya, ta gama kashe mishi duk wani fada da yakeji, kanshi ya jingina jikin kujerar motar yana kar kankance mata idanuwanshi
"Banda chargy ne shisa, wayar mutuwa tayi..."
Waheedah ta fadi tana kallon yanda shaddar jikin shi tai matukar karbar kalar fatarshi.
"Kayan nan sun maka kyau"
Ta tsinci kanta da furtawa tana sakashi dakuna mata fuska
"Nama kayan kyau dai..."
Dariya tayi da ta saka shi runtsa idanuwanshi yana budesu akanta, wani irin kyau tai mishi da bai taba sanin tana dashi ba.
Kamar kullum ya dinga ganin fuskarta dauke da kwalliya haka.
Har shigar mishi ido da haskenta yakeyi yau ya nema ya rasa, farin nata yaji yayi mishi dai-dai.
"Kinyi sallah?"
Ya bukata yana kallonta har lokacin, kai ta girgiza mishi tana tuna mishi da yanda ita kadaice a fadin rayuwarshi da take amsa mishi magana batare data bude bakinta ba, kuma ya karbi amsar.
Ita tunda aka fara hidimar bikin a dai-danta take.
Ko zata samu tsarki sai zuwa washegari.
"Zaki je kiyi saiki dawo?
Lokaci na tafiya"
AbdulKadir ya sake fadi, dan sallah na daya daga cikin abubuwan da baya wasa dasu a rayuwar shi, bakuma yabari duk wani makusancin shi yayi wasa da ita.
Sai dai ga mamakin shi kai ta sake girgiza mishi, tana saka shi fadin
"Me yasa?"
Cike da wata irin kunya da rabon da tajita a tsakaninsu ta manta ranar ta sauke idanuwanta daga cikin nashi tana fadin
"Hamma mana..."
Dan ware idanuwanshi yayi cike da fahimta, da murmushi a fuskarshi yace
"Oh...okay...
Nagane.
Duk yau me kikaci?"
Ganin ta sake sadda kanta kasa yasa shi fadin
"Yau ma bakici komai ba Waheedah?
Jiya bance kici wani abu ba?
Meyasa bakici ba?
Saboda kin rainani ko?
Ban isa in sakaki abu kiyi ba..."
Dagowa tayi ta kalli fuskarshi da take dauke da yanda rashin yake a bace
"Hamma..."
Ta kira cikin sanyin murya tanaso ya fahimci badan ta raina shi yasa bataci abinci ba, ba kuma dan bataji yunwa bane ba, anata hidima ita basu bata abincin bane shisa, amman tasan halin shi, idan tace ba'a bata abinci bane shisa bataci ba fadan karuwa zaiyi.
"Ki jirani ina zuwa..."
Yai maganar yana bude murfin motar ya fice.
Gyara zamanta tayi sosai, tasan anacan ana nemanta watakila, ba zata iya rikicin AbdulKadir ba da tace mishi zata shiga cikin gidan dan kar a nemeta.
Tana wannan tunanin AbdulKadir din ya dawo ya bude motar yana shigowa, robar take away da abinci a ciki ya dora akan cinyarta yana gyara zamanshi cikin motar ya rufo murfin, robar ruwan a jikinshi ya ajiyeta yana daukar robar dake jikin Waheedah ya bude ya saka mata cokalin da bata kula yana hannun shiba a ciki, kamshin fried rice din da tasha kayan hadi da nama ta daki hancinta tana kara mata yunwar da takeji.
Batare da tunanin komai ba tasa cokalin ta dibo abincin takai bakinta ta tauna, Lumshe idanuwa tayi dan ya mata dadi na fitar hankali, batasan ko hakan nada alaka da yunwar da takeji ba, hadiyewa tayi tana kara dibowa, yanda take cin abincin da sauri yasa AbdulKadir fadin
"Slow down, karki kware Waheedah..."
Kai ta girgiza mishi, tana hadiye abincin da yake bakinta
"Hamma yunwa nakeji sosai, banci komai bafa duk yau...
Bazan kware ba"
Ta karasa maganar tana kai wani cokalin a bakinta.
Sosai taci abincin dan kadan ta rage da taji ta koshi har cikin makoshinta.
Ruwan AbdulKadir ya kwance yana mika mata, ta karba kuwa tana kaiwa bakinta.
Yabi kunshin da yake hannunta da kallo.
Ruwan data sauke ya karba yana sha shima, makoshin shi ya bushe batare da dalili ba tunda ba kishi yakeji ba.
Numfashi Waheedah ta sauke wata nutsuwa na saukar mata, cokalin ta gyarama zama cikin robar ta rufe, tana jin yanda AbdulKadir yake binta da idanuwa, kafin yasa hannu ya dauki robar abincin yana dorawa gaban motar ya ajiye.
Gyara zaman shi AbdulKadir yayi yana jingina da kujerar motar sosai ya lumshe idanuwan shi.
"Hamma..."
Waheedah ta kira ganin kamar shirin bacci AbdulKadir din yakeyi a cikin motar.
"Karki dameni da surutu Waheedah, hutawa zanyi"
Ya fadi batare daya bude idanuwan shi ba, gabaki daya bayajin karfi a jikinshi, saida yai sallar isha'i kafin ya karasa wajen kamun, amman bayajin shiga cikin gida ya kwanta a daki.
Anan cikin motar inda take yake son hutawa, kokawa yake da abinda keson dora koda kanshine a jikinta yayi bacci, ba sai yayi tsayi ba, awa daya ma ya isheshi.
Ba sosai yake samun bacci ba tunda ya tafi, yanzun ganinta yasa duk wata gajiya da yake rike da ita saukar mishi.
Ita kadaice a rayuwarshi yake iya nunama kasawarshi ko gajiyarwar shi.
"Za'a nemeni Hamma..."
Waheedah tai maganar kamar zatai kuka, tana saka shi bude idanuwanshi ya duba agogon da tun wanda ta sai mishine
"Karfe takwas da rabi, tara da rabi saiki tafi"
Duk da yayi maganar babu wajen musu bai hanata fadin
"Hamma tara da rabi"
Idanuwan shi ya sauke cikin nata
"Musu zamuyi dake?"
Ya bukata yana sata girgiza mishi kai.
"Good..."
Ya fadi ya gyara zaman shi cikin kujerar yana lumshe idanuwan shi.
"Ki zauna sosai"
Yai maganar batare daya bude idanuwan shi ba.
Ita kam bataga ta zama sosai ba, awa daya AbdulKadir yake son tayi a zaune cikin motar, badan batason zama dashi ba, har ranta awa dayama yai mata kadan tare dashi, amman za'a nemeta tasani, da ba'a hidima ba zata damu ba.
"Inajin sautin tunaninki har nan Waheedah...babu inda zakije kuma"
Shagwabe mishi fuska tayi duk da idanuwanshi a lumshe suke.
"To inje in dauko wayata?"
Ta bukata, ko wayar ta latsa kafin awa daya ta cika, zatafi mata sauri, hannu yasa a aljihunshi yana zaro wayarshi ya mika mata, hannu tasa ta karba ganin idanuwan shi a lumshe suke.
"Waheedah"
Ya fadi yana sauke numfashi.
Cike da rashin fahimtar kiran sunanta da yayi take kallon shi, kamar yaji hakan yasa shi fadin
"Password din Waheedah"
Zuciyarta taji ta kumbura ta cika fam, sunanta ne mukullin sirrin wayarshi, dannawa tayi kuwa taga wayar ta bude, murmushi tayi tana gyara zamanta, takasa daina murmushi, abinda batasani ba shine kowanne abu nashi da yake bukatar mukullan sirri sunanta ne, hotunan shi ta shiga tana dubawa, duk wanda tagani saita shiga WhatsApp dinta ta turawa kanta shi.
Batasan awa daya ta cika ba, batama san ya bude idanuwan shi ba, saida taji ya fisge wayar daga hannunta yana fadin
"Me kike mun da waya..."
Yana dubawa, hotunanshi yagani ta tura ma kanta ta WhatsApp, yana da tabbacin gabaki daya hotunanshi ne da suke cikin wayar.
Kai kawai ya girgiza, da tace yabar mata wayar ma taje ta tura ba saita karar mishi da data ba.
Mukullin motar ya zare yana zagayawa ya bude mata, fitowa tayi.
Hamma yayi saboda bacci yakeji sosai
"Saida safe..."
Yace mata yana murza idanuwanshi cikin yanayin da yai mata kyau.
Ganin ta tsaya tana kallon shi yasa shi fadin
"Ko in rak
aki?"
Da sauri ta girgiza mishi kai.
Zata lallaba ta shiga bangaren Anty, inta dan jima anan saita koma gida, ba saiya rakata kowa yasan tare suke ba.
Juyawa ma tayi ko saida safe batai mishi ba, kafin rikicin shi ya yanke mishi hukuncin rakata.
Washegari hidimar tafi hade musu, tun karfe bakwai aka gama musu kwalliya ita da Zahra, wata doguwar rigace ruwan kwai, wuyan rigar dogone irin wanda ake kira high-neck a turance, sosai ta karbi su duka biyun, daga daurin dankwalayensu zuwa yanayin lullubinsu zaka gane amare ne ko baka kalli kunshin dake hannuwansu ba.
A harabar gidan aka fito dasu dan ayi hotuna.
AbdulKadir yafi duka mazan dake wajen tsayi, shima yana sanye da shadda fara kal da babban rigarta kamar sauran angwayen.
Abin gwanin ban sha'awa, sosai akai musu hotuna, angwayen da amarensu su kadai, su duka gabaki daya, sai kuma da sauran mutane da abokan arziqi.
Kasancewar daurin auren na karfe takwas ne, Zahra kanta ba a Kano zata zauna ba, Katsina ne, ga Yazid da matarshi shima.
Dan haka aka saka bikin da safe don ana dawowa za'a tafi da amaren.
Suna gama daukar hotunan, babban masallacin dake nan kofar ruwa inda za'a daura auren suka dunguma suka nufa su dukkansu da abokan su.
Ran AbdulKadir a bace yake, tun da safe daya samu Hajja da tambayar
"Wai da gaske za'a kai Waheedah ne itama?"
Cikin rashin fahimta Hajja tace
"Bangane za'a kai Waheedah ba"
Dakuna mata fuska yayi
"Ina nufin rakiya...