Sashe 40
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yar dariya Yassar yayi
"Lallai yaron nan, to kaima kayi auren mana"
Girarshi duka biyun AbdulKadir ya daga ma Yassar
"Da wa?"
Ya tambaya yana kurbar shayin daya kware shi dajin amsar Yassar din
"Waheedah..."
Tari yake sosai dan shayin yabi mishi ta hanyar da bai kamata ba, sosai yake kara kurbar shayin ko zai samu sauki, muryarshi a dishe ta fito daga kasan makoshin shi
"Wanne irin wasa ne wannan?"
Ya bukata yana sa Yassar din hararshi
"Karka rainamun hankali AbdulKadir, shekara nawa kana yawo da hotonta a wallet?
Dan banyi magana ba baya nufin ban kula ba, itama kuma ina kallonta, bata kula kowa, ban tana ganin ta fita zance da wani ba..."
Kallon Yassar yake da dukkan alamu Hausa yake mishi, amman da wani yare daban yakejin maganganun Yassar din na dira kunnuwanshi saboda yanda ya kasa fahimtarsu, yanayin fuskar AbdulKadir din Yassar yake kallo, mamaki na bayyana akan tashi fuskar
"Tsaya...
Me kake son ce mun?"
Ya tambaya yana kasa gasgata abinda yake gani a fuskar AbdulKadir din, kai Yassar yake girgizawa
"AbdulKadir..."
Ya kira yana cigaba da girgiza kai, AbdulKadir din bai magana ba har lokacin, kallon Yassar din kawai yake kamar qaho ya fito mishi a tsakiyar kai
"AbdulKadir..."
Yassar ya sake kira a karo na babu adadi, yana jinjina abinda yake gani a fuskar kanin nashi, har ranshi, duk tsayin shekarun nan ya dauka soyayya suke da Waheedah din, yana kuma da tabbacin bashi kadai bane yake zaton hakan.
Wani zafi yaji kirjinshi nayi, ya hana Yazid furta mata yana sonta saboda a tunanin shi AbdulKadir din nasonta, yana kuma da tabbacin idan shi baya sonta ita tana son shi, dan yanda take tambayarshi akan AbdulKadir din kawai ya tabbatar mishi da haka daga nata bangaren.
"Me yasa?"
Yassar ya tambaya, sai lokacin AbdulKadir yace
"Me yasa me?"
Kai Yassar ya jinjina
"Tana sonka AbdulKadir..."
Yassar yai maganar can kasan makoshin shi, tausayin yarinyar na cika zuciyarshi, plate din dankalin shi AbdulKadir ya dauka yana diba ya cika bakin shi dashi taf yana cigaba da taunawa, maganar Yassar din na mishi yawo a duk ilahirin jikin shi
'Tana sonka AbdulKadir'
Ko a mafarki mai nisa bai taba hango soyayya da Waheedah ba, ko kadan, soyayya fa, da Waheedah, tana da muhimmancin dashi kanshi baisan iyakarshi ba a rayuwarshi, amman soyayya da ita, shine karshen abinda yake hangowa.
Sai dai soyayya da kowama a yanzun ba abu bane da yake tunanin zai faru, bayajin yana da wannan lokacin.
"AbdulKadir..."
Yassar ya kira ganin yanda yake cin abincin
"Karka kware..."
Bai kulashi ba, dankalin kawai yake zubawa a bakin shi yana taunawa.
Hakan yasa Yassar mikewa ya fice daga dakin da tunani kala-kala a ranshi.
Tari AbdulKadir ya somayi yana fita, babu shiri ya dauki shayi yana kora dankalin bakin shi dashi, hadiyewa yayi yana sauke numfashi.
Kafafuwan shi ya ja yana dorasu kan gadon hadi da kwanciya yaja bargo ya rufe jikin shi.
Pillow din daya dora kan shi yaji ya soma isar shi, dan ba haka yake kwanciya da pillow ba, dagawa yayi yana dora pillow din akan hannun shi tukunna ya dora kan shi a sama, yadanji dai-daito a kwanciyar.
Yassar yasa kashi abinda bayason yi, idan akwai abu na biyu da bayason bayan raini, tunani ne, ko kadan bayason ya zauna yana tunani, taya Yassar zaice Waheedah na son shi, ita Waheedah din bata da bakin da zata fada mishi kome yake faruwa, kanshi ya bala'in daurewa cikin yanayin da bai taba tsintar kanshi a ciki ba, komai yake ji ya cakude mishi haka kawai.
Tun ran daurin auren Nuriyya rabon dayai tunanin wani aure, yanzun kuwa gabaki daya tunanin ne a ranshi.
Ta ina zai fara?
Wacce yarinya zai fara tunkara?
Yaushe ma zai ganta?
Duk da yasan indai yana da rai da lafiya aure abune da ya zame mishi dole, ko dan gujin fadawa halaka, tare da Waheedah yana da tabbacin ba zata taba raina shi ba.
Asalima raini na daya daga cikin abinda yasan bazai taba shiga tsakanin su ba.
Kuma a yanda yakeji bazai iya kallon idanuwan kowacce yarinya da sunan soyayya ba a yanzun, bashida ma da wannan lokacin, da anyi posting dinshi zuwa inda zai fara aiki kuma zai kara samun karancin lokacin duk wannan abubuwan.
Tashi yayi zaune, karo na farko a tsayin lokaci da yaji zuciyarshi na dokawa da abinda yake shirinyi.
Wayarshi ya dauko yana kunna data din, WhatsApp dinshi ya bude, sunan Waheedah ne farko da saqonninta da suketa shigowa, sosai bugun zuciyarshi yake karuwa, bude sakkonin yayi:
'Me kaci?'
'Karka kwanta da yunwa Hamma'
'In dafa maka indomie?
Ko zaka sha Tea?'
'Shine baka fadamun zaka zo ba ko?'
Dubawa yayi yaga tana online, rubutu ma takeyi, jikinshi yakeji har kyarma yake mishi, a hankali ya soma rubutu yana tura mata:
'Waheedah...'
Rubutun da take yaga ta tsayar, hakan yasa shi cigaba:
'Waheedah...'
Runtsa idanuwan shi yayi yana sake budesu kan screen din wayar
'Hamma'
Ta amsa, ya karanta sunan nashi da muryarta, bayason yin abinda zai dana sani, sanin ba zata taba raina shi bane abinda yabashi kwarin gwiwar rubuta
'Kina so na?'
Karanta tambayar tashi yayi, ganin bata fara ko typing ba, ba lallai ma tagane kan tambayar tashi ba
'Ba so na yan uwa ba Waheedah...
So na aure.
Kina so na?'
Tana online har lokacin, amman bata ko fara rubutu ba, kuma yaga ta karanta, zuciyarshi yakeji har cikin makoshin shi saboda dokawar da take mishi.
'Ki amsani, zan kirga daya zuwa goma.
Karki amsa sai kina da tabbaci, idan bakida shi karki amsa, nida ke zamuyi kamar ban tambaya ba, maganar ba zata sake hadamu ba har abada'
Ya fadi yanajin yanda maganganun nashi suka zauna mishi, ita dashi suna da daqiqan da zasu dauke shi ya kirga daya zuwa goma, amman zai karya idan yace baya tsoron shirunta.
'Daya...'
'Biyu...'
'Uku..."
Rubutu yaga ta soma, hakan yasa shi barin kirgar da yake, can kuma yaga ta daina
'Hudu...'
'Biyar...'
'Shidda...'
Rubutun ta sake cigaba dashi, tana sake dakatawa bayan wani lokaci
"Ki kasheni kawai Waheedah"
AbdulKadir ya furta a fili, yana jin alamar zufa a goshin shi da bayan wuyan shi
'Bakwai...'
Zuwa lokacin hannuwan shi kansu zufa suke fitarwa, shi baima taba tunanin soyayya da ita ba, yanzun hakan baisan rashin hankalin daya kaishi yin abinda yayi ba, baisani ba, gashi yazo yanajin bugun zuciyar da bai taba tunanin zai iyaji bama akan jiran amsarta, Yassar bai tabbatar ba, hasashe yakeyi, bai tabbatar da Waheedah nason shi ba, kilama tana da wanda take so, yai tunanin yanajin wani tuquqi na tokare mishi makoshi.
'Takwas...'
Ya tura, yana jin yanda zaibar garin Kano da sassafe, yanajin yanda yaima kanshi karya da tunanin amsarta ko rashin amsarta bazai canza komai ba, da gaske baya tunanin zai iya hada idanuwa da ita idan bata amsashi ba.
Duk da bayajin yana dana sanin tambayarta din, Yassar yasa shi son sanin ko tana son shi ko bata son shi.
'Tara...'
Ya tura yana gyara zaman shi hadi da fitar da wani irin numfashi mai nauyin gaske, idanuwan shi ya runtsa a hankali ya bude su kan screen din wayar.
'Ina son ka, ina son ka da aure Hamma AbdulKadir'
Sake karantawa yayi yana sauke numfashin da baisan yana rike dashi ba.
Wayar ya ajiye gefe yana dafe kanshi da hannuwanshi duka biyun, wani irin numfashi yake saukewa mai nauyin gaske, kafin ya mike yana zira takalman Yassar dake bakin kofa ya fice daga dakin yanayin hanyar wajen bangaren nasu.
Takawa yake zuwa bangaren Abba yanajin shi kamar wanda yake tafiya a gajimare, jinshi yake kamar yana yawo a wata duniya da batashi ba, kamar yana gefe yana kallon wani mafarki dashi a ciki.
Dakin Abba ya shiga da sallama, ya same shi a tsakiyar falon a zaune, Mama nakan kujera
"AbdulKadir..."
Abba ya fadi da fara'a yanajin dadin ganin dan nashi.
"Abba..."
AbdulKadir yace yana karasawa ya zauna gefen shi.
"Abba zanyi magana dakai"
Murmushi Abba yayi
"Soja manyan kasa, ina saurarenka ai"
Daga kai AbdulKadir yayi yana kallon Mama dake zaune, yana saka Abba kara fadada murmushin shi, mikewa Mama tayi, batason sake shiga hancin AbdulKadir din kafin ya tona mata asiri wajen Abba.
"Bari in baku waje kuyi sirrinku"
Cewar Mama tana dora murmushi kan fuskarta, lokacin daga fice daga dakin.
Kallon Abba yakeyi a nutse yace
"Aure zanyi Abba...
Kafin in koma nake so a daura"
Da mamaki bayyane a fuskar Abba yake kallon AbdulKadir din, kafin ya numfasa da fadin
"Aure AbdulKadir?"
Kai AbdulKadir ya daga mishi, yana jin maganganun na fitowa daga zuciyarshi
"Eh Abba..."
Wannan karin Abba ne ya jinjina kai, maganar na dirar mishi da wani yanayi, yana kuma son karbarta da budaddiyar zuciya, idan har AbdulKadir din zai bude baki da maganar aure to yana kokarin ganin ya gujema fadawa halaka ne, kuma yanzun yana da sana'ar da Abban yake da tabbacin zata riqe mishi mata, sai dai shi bayason yin abu cikin gaggawa, musamman magana ta aure.
"Yaushe zaka koma?"
Jim AbdulKadir yayi kafin ya amsa
"Sati biyu in na dade"
Numfashi Abba ya sake saukewa
"Maganar aure a sati biyu AbdulKadir, abune da bazance bazai yiwu ba, amman gaggawa ba abu bane mai kyau.
Aure kuma yana bukatar shiri.
Nasan kana da aikin dazai rike maka mata, amman wajen zama fa?
Lefe da sauran hidindimun biki"
Dakuna fuska AbdulKadir yayi shi baiyi wannan tunanin ba kwata-kwata.
Yama manta ana wani abu waishi lefe a maganar aure, ya kuma manta ana neman wajen zama.
Magana Abba yaci gaba dayi
"Ana iya maganar auren, idan kana ganin zaka iya shiryawa nan da watanni shidda sai a hada dana su Yazid duk ayi..."
Kai AbdulKadir ya jinjina, hakan ya mishi, zai tara kudin da zasu ishe shi yin lefe, wajen zama zasu iya farawa da barikin sojoji tunda yasan za'a bashi muhalli, amman ko kadan ba dadewa zai ba, kafin ya tara kudin dazai mallaki nashi ne zasu zauna.
Baya son yaranshi su tashi cikin bariki, badan wani dalili ba, ra'ayin shine kawai hakan.
Dariya maidan sauti yaji ta kubce mishi, yadan girgiza kai.