Sashe 58
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haramun ne in auri kawar ta?"
Dafe kai Yassar yayi da yakejin wani irin ciwon kai ya dirar mishi.
Ga zuciyar shi dake zafi, in har yanajin haka da abinda AbdulKadir yake shirinyi, baisan ya Waheedah zataji ba
"Ka daina yin kaman mai asthma Hamma, bazai sa in fasa auren nan ba.
Bansan me yasa Abba zai fada maka ba, tunda ai zan gaya maka da kaina daman"
Da hannuwa biyu wannan karin Yassar ya tallafe fuskar shi.
Da ance mishi akwai ranar da zata zo da zaiji bayason ganin AbdulKadir zai karyata, amman abinda yake ji yanzun, maganganun AbdulKadir din ko kadan bayason gani.
Dashi ake jinjina maganar matan da suke cakawa mazajen su wuka duk idan hakan ya faru, AbdulKadir yasa shi fahimtar kadan daga cikin dalilin da maza suke ba matansu har shaidan yai galaba akan su, su hau dokin zuciya su aikata abinda zaisa ka su dana sani daga doron duniyar har lahira.
Idan akwai mazaje dari irin AbdulKadir, yana da tabbas lahirar mata da yawa zata raunana, zasu zama barazana da kwanciyar kabarin mata da dama.
Fuskar shi Yassar ya bude yana jan wani irin numfashi ya fitar dashi rai a bace
"Babban kuskuren rayuwar Waheedah shine amince ma auren ka"
Wannan karin AbdulKadir ne yaja wani irin numfashi, kai yake girgizawa
"Baka fadamun maganar nan ba Hamma, ka janye kalamanka..."
Mukullin shi Yassar yake lalubawa cikin aljihu, ya kuwa yi nasarar ciro shi yasa a jikin murfin mota ya bude.
AbdulKadir ya mayar da murfin yana rufewa, ya kuma rike hannun kofar gam.
Muryarshi can kasan makoshi yake cewa
"Hamma ka janye kalaman ka, dan Allah ka janye ko zasu rage mun zafin da sukeyi..."
Tsaki Yassar yaja
"Ka matsamun daga jikin mota kafin in kwada maka mari AbdulKadir....
Wallahi yanda nake ji komai zai iya faruwa..."
Kallon shi AbdulKadir din yakeyi, a tsayin rayuwar shi yaune rana ta farko da Yassar ya fada mishi maganganun da yakejin ciwon su har cikin kasusuwan shi, akan maganar abinda addini ya halarta mishi ta kowacce fuska.
Yasha ganin ya ta mutu, kanwarta ta auri mijin, baisan me yasa nashi zai banbanta ba.
"Me yasa zaka fadamun haka?
Hamma me yasa?
Saboda nace zan auri Nuriyya?
Dan zanyi abinda Allah bai haramtamun ba...ya tana mutuwa, mijin ko bai nuna yana son kanwar ba a bashi, me yasa nawa zaiyi maka zafi haka?"
Ture shi Yassar yayi yana fadin
"Mahaukaci ne kai wai?
Dan ubanka allurar sojojin kai ka miqa musu suka caka maka ita?
Addini bai haramta maka auren Nuriyya ba, amman al'ada ta haramta maka shi, kunya ta haramta maka, ko mutuwa Waheedah tayi ka nuna kana son auren ta, akwai mutane da yawa da zasu ga rashin kyautawar haka...
Ka matsamun AbdulKadir, ka matsamun in wuce...mahaukacin banza marar tunani"
Yassar ya karashe yana kara sa hannu ya ture AbdulKadir din, ya bude motar shi ya tayar.
AbdulKadir nabin shi da kallo harya fice daga gidan.
Bai ce mishi komai ba, saboda yaga alama Yassar din marin shi zaiyi idan ya sake magana, a karo na farko kuma da yasan inya mare shi ramawa zaiyi, dan shima ran nashi ya gama baci.
Yafi mintina goma a tsaye a wajen, kafin ya iya wucewa ya shiga gida.
Kai tsaye daki ya shiga yana wucewa bandaki ya sakarwa kanshi ruwan sanyi ko zai samu sauqin abinda yakeji.
Daga shi sai towel ya fito, ya samu gajeran wando ya saka, Waheedah har tayi bacci ya hau kan gadon yana matsawa gab da ita.
A hankali yake girgizata
"Wahee....
Waheedah..."
Bude idanuwanta tayi cike da bacci tana jin fitilar dakin dake kunne ta shigar mata idanuwa yana sa ta mayar dasu ta rufe babu shiri.
"Ki tashi Waheedah....
Kinji...
Kimun hira"
AbdulKadir ya karashe yana kara girgiza ta, bude idanuwan ta tayi tana kallon fuskar shi
"Banajin dadi Sadauki...
Dan Allah kabarni inyi bacci"
Kai ya girgiza mata, ita batajin dadine, shi zuciyar shi zafi take mishi kamar kirjin shi zai bude, hannunta ya kamo ya dora kan kirjin shi inda yakeji yana mishi ciwo na gaske
"Wahee raina a bace yake, zuciyata zafi take mun wallahi, Hamma ya batamun rai"
Yanda ya karashe maganar yasa ta mikewa, sosai take kallon shi, idanuwan shi harsun canza launi saboda bacin rai, tashi zaune tayi tana jingina bayanta da gadon, zazzabine ruf a jikinta, tashin da AbdulKadir din yai mata yasa har amai takeji.
Ganin ta tashi yasa shi barin pillown shi yana komawa kan cinyoyinta ya kwanta, ya kama hannunta ya dora kan fuskar shi yana neman sauqi koya yake.
"Kayi hakuri dan Allah...
Kome zai fada maka nasan baya nufin kalaman, bacin rai ne kawai...
Daya huce shikenan, kayi hakuri"
Ta fadi a tausashe, kara naniqe mata yayi, ba zata iya hana shi ba, duk da zazzabin da take ji, yanayin shi ya gama raunana tata zuciyar, indai zata sama mishi sauki koya yake zata kokarta.
Biye mishi tayi, bata samu yayi bacci ba sai wajen karfe biyun dare.
A daddafe ta shiga bandaki tana dubawa ko da ruwan zafi dan basu bar wutar ta zauna ba.
Dakyar ta iya watsa ruwa, ga wata yunwa da take wujijjigata, kitchen ta wuce ta duba sauran abincin da yake tukunya, ba zata iya cin shi da sanyi ba, dan haka ta dora tayi warming.
Ta dauko plate kenan ta fara zubawa taji takun AbdulKadir din, kafin ta juya ya rungumeta ta baya, muryarshi cike da bacci yace
"Shine kike barni ko?"
Numfashi ta sauke
"Yunwa nakeji...ka koma ka kwanta, da naci abinci zan dawo..."
Tanajin shi yana girgiza mata kai, ko daya farka baiji ta a kusa dashi ba ranshine yaji yana shirin kara baci.
Ya duba bandaki bai ganta ba, shisa ya fito nemanta.
"Sadauki dan Allah...
Karka karyani"
Magana yai mata data tsaya iya kunnenta, ta ture shi tana dariya.
Abincin ta zuba, falo ta koma yabita ya zauna a gefenta.
Wani lokaci har bataso a bato mishi rai, in kuwa ya faru gara ta tambayeshi ya sauke mata fadan shi da ya shiga yanayin nan da ko bandaki ta shiga tabar shi saiya bita.
A kanta abin yake karewa, yanzun din kuma yaki fahimtar ba ita kadai bace itama, ko karfin kirki bata dashi.
Yabarta taci abincin a nutse yaki, sai murza ido yake yana hamma, gashi rabin jikin shi a kanta yake.
Samu tayi tagama suka wuce suke kwanta.
Tunda ya dawo sallar asuba yaga sakon Hajja
'Ka zo ina neman ka'
Wayar ya kashe gabaki daya.
Zai je inya tashi, saiya gama baccin safen shi amman.
Waheedah kuwa dankalin Hausa taji tana marmari, tana dashi dan haka ta fere bayan ta idar da sallah, ta yayyanka ta zuba a karamar roba ta saka ruwa.
AbdulKadir na dawowa Masallaci yaga tana karatun Qur'ani ya samu waje ya zauna a gefen gado, tana idarwa ta ajiye ta cire hijab din ta wuce kitchen yabi bayanta.
"Yanzun Waheedah sai kin soya dankalin zamu kwanta?
Bacci fa nake ji"
AbdulKadir da yake tsaye yace ma Waheedah da take share wajen da ta bata.
Indai bacci ne ta fishi bukata, tunda bai bari ta samu na kirki ba, yama fita samun baccin, batace mishi komai ba.
"Ke kadai nake ma magana kijini kuma kiyi shiru"
Abin kwashe shara ta saka cikin dustbin, ta wanke hannunta tukunna ta kalle shi da fadin
"Yi hakuri...
Muje"
Kankance mata idanuwanshi yayi da suke cike da rikicin da bata da karfin biye mishi.
Kwanciyar sukai, sanda ta tashi karfe goma, ruwa ta watsa ta saka doguwar riga ta material da farar hula tukunna ta wuce kitchen tana dora mai dan ta fara soya dankalin.
Idan AbdulKadir ya tashi zai fara mata maganar abinci ne tasani, kuma tashin zaiyi, dan daya laluba yaji bata kusa dashi tashi zaiyi.
Tana sauke kaskon farko AbdulKadir din na fitowa daga shi sai towel
"Baki dauko mun kayan da zan saka ba"
Ya fadi, in tace yaje ya dauko da kan shi dogon surutu zasuyi, kuma karshe ita zata dauko mishi, sauran dankalin ta juye ta wuce daki ta dauko mishi farar riga marar nauyi da wani three quarter mai igigoyi daga kasan, sai singlet da boxers, turare ta fesa mishi a jiki tana ajiye mishi kan gadon.
Murmushi yayi mata yana sa hannu ya taba fuskarta
"Ya kuka tashi?
Ya jikin ki?"
Murmushi Waheedah tayi
"Baka tambayi jikina ba sai da kagama sani aiki ko?"
Yar dariya yayi, ta gaishe shi da asuba, ya tabata yaji babu zazzabin, bai dai tambaya bane sai yanzun.
Ganin yayi shiru yasa ta fadin
"Mun tashi lafiya.
Kasa kaya, kar dankalina ya kone..."
Kafin ya amsa ta juya da sauri ta fice daga dakin.
Albasa ta yanka dan tana so, ta zuba a cikin wancen data kwashe, na biyun bai karasa ba har AbdulKadir ya fito, falo ya wuce ya zauna yana jiranta, tana gamawa ta hada mishi shayi ta zubo dankalin ta fito.
Ci sukayi suna hira, suna gamawa yace mata zaije gida.
Rakashi tayi har kofa tukunna ta dawo ta hada wanke-wanke tayi, ta goge kitchen din tukunna ta koma dakin su ta gyara gadon, batajin zata iya share shi tunda ba dauda yayi ba, kuma batama jin dadin jikinta.
Komawa tayi ta kwanta tana tunanin abinda zasuci da rana.
Gida ya shiga, bai samu Hajja a falo ba, ya wuce dakinta yana kwankwasawa, ya tura bayan ta amsa hadi dayin sallama.
A zaune ya sameta kan gado ta mike kafafuwanta ta saka glass din karatu da littafin 'Tarihin Annabi Kamalalle' a hannunta tana karantawa.
"Hajja..."
Ya fadi cikin sigar gaisuwa, littafin ta ajiye tana cire gilashinta shima ta ajiye shi a gefe.
A nutse take kallon AbdulKadir
"Menene matsalarka?
AbdulKadir yau kam ka gayamun menene matsalar ka"
Da mamaki a fuskar shi yake kallon Hajja yana girgiza mata kai
"Bani da matsalar komai Hajja"
Numfashi ta sauke
"Kawai wulakanci ne kenan ko?
So kake kaja mana abin magana shisa kake so ka auri Nuriyya...
Itama Nuriyyar dan ubanta idan tana da kunya ai ko mutuwa Waheedah tayi idan kazo mata da wannan maganar za ta dubi amintakar dake tsakanin su taki amincewa.