← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 94

Sashe 86

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da taji zuciyarta ta doka, dan tunda ta kwaso kayan daga wajen shanya, kulle su tayi a cikin zanin gado ta ajiye can gefe
"Magana nake dake fa"
AbdulKadir ta fadi a kule, saukowa tayi daga kan gadon tana kunna fitilar wayarta ta taka zuwa inda ta ajiye kullin kayan ta kama su taba kwancewa
"Ki mikomun gajeran wando da singlet"
Daukowa tayi, duk sun zama kamfala, musamman gajeran wandon da yake ruwan madara, mayar dashi tayi ta dauko mishi na kakin sojoji shima duk yayi rodi-rodi.

Tana dunkule su waje daya ta karasa ta mika mishi, kamar hakan yan nepa suke jira da bugun agogo na alamun cikar karfe tara na dare suka kawo wuta, haske ya gauraye dakin, yana dai-dai da sauke idanuwan AbdulKadir akan kayan ya kuwa ware su yana bude kayan sosai.

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Ya fadi yana jujjuya wandon shi
"Bansan akwai kaya masu zuba ba, na hada duka"
Kai AbdulKadir yake girgizawa
"Aikin ki kenan, kullum bakisan abu ba, ko yaushe uzurinki baki sani ba.

Hankalin ki bai baki ba'a hade gabaki daya kaya wajen wanki ba?

Idan kin hada wandon nan da sauran kaya, me yasa zaki hada farare da masu kala?

Ke mahaukaciya ce?"
Ya karasa maganar yana kallon ta
"Kuskure ne kowa nayi"
Nuriyya ta fadi cike da gajiya
"Karki fara mun rashin kunya, wallahi karki fara cewa zaki fadamun magana Nuriyya, baki sanni ba ko?

Bakisan halina ba har yanzun, shisa nake magana kina kokarin mayar mun"
Shiru tayi idanuwanta na cika da hawaye, gefen gado ta koma ta zauna, ta dauka yayi shiru, ai kamar lokacin ya fara fada, sai da yayi mai isar shi tukunna ya koma bandakin, ranta inyai dubu a bace yake, kwanciya tayi tana tsiyayar hawaye masu zafin gaske, ko kadan ba wannan rayuwar ta hango ba, bata saba ana mata fada ba, duk bala'in Anas ba koyaushe yake kulata ba, sai ta kaishi karshe, shima in yaga ta hayayyaqo mishi sai yayi shiru ya kyaleta koya fice daga gidan.

Amman yanda AbdulKadir ya nuna yana gab da kwada mata mari shisa tayi shiru, ba sai kowa ya gaya mata ba zai dauki kaso daya cikin abinda Anas ya dauka ba.

Fitowa yayi har lokacin ran shi a bace yake ji shisa ya karayin wanka.

Ya zagaya kan gadon ya hau yana kwanciya, baya Nuriyya ta juya mishi, tsintar kan shi yai da bai damu da hakan ba, Waheedah ce dai bata isa ta juya mishi baya ba kome yai mata, ko gajiya tayi da kwanciyar zata juya hannu sai dai suyi musayar waje.

Ko a jikin shi take kuwa, sai dai in bacci yayi, daya tashi ya ganta saiya kamata ya juyata.

"Ki kashe mana fitila"
Ya fadi yana juya kwanciyar shi, yana jinta ta sauka daga kan gadon ta kaso fitilar ta dawo.

Alarm ya saka a wayar shi ya ajiyeta gefe, Addu'ar bacci ya tofa a jikin shi yana lumshe idanuwan shi duk da alamun yunwa da yakeji.

Karfe uku da rabi alarm din daya saka ya tashe shi, sai da yayo brush da alwala tukunna ya tashi Nuriyya.

Rigar kirki ya dauka yasaka a jikin shi, yana ganin yanda ta koma kamar Kampala itama, sallar nafila ya tayar yanayin raka'a hudu.

Sai lokacin ma Nuriyya ta sauko daga kan gadon dakyar ta shiga bandaki ta wanko fuskarta, ta wuce kitchen.

Mikewa AbdulKadir yayi yana fita shima ya nufi bangaren Waheedah ya tura hadi da sallama ya kuwa same shi a bude, kwan dakin ya kunna yana sakata runtsa idanuwanta sosai alamar hasken ya shigar mata cikin su, kafin ta bude su tana kankancewa akan AbdulKadir
"Nace ki dinga kulle kofa, bakyajin magana ko Wahee?"
Cikin bacci ta turo mishi bakinta da har lokacin da alamun janbaki ja, mika tayi, muryarta cike da bacci tace
"Na manta ne"
Hararta AbdulKadir din yayi yana sakata yin murmushi
"Kinfi so inta surutu kan abu dayane kawai"
Ya karasa ya dauki Qur'ani daman shi yaje dauka, ya tako yana kashe fitilar
"Kabar mun a kunne"
Waheedah ta fadi, sake kunna mata yayi yana jan numfashi kamar yana son zuqar iya kamshin da zai iya da yake cikin dakin kafin ya fita hadi da ja mata kofar.

Dakin Nuriyya ya koma ya samu waje ya zauna yana bude Qur'anin shi ya soma karantawa cikin sanyin murya, yana wajen har Nuriyya ta shigo ta ajiye musu plate din shinkafa sai miya data zuba a wani kwanon, sai da AbdulKadir ya karasa shafin da yake karantawa tukunna ya rufe Qur'anin, su Hajja kawai yaiwa Addu'a sai iyalan shi da yan uwan shi, Yassar ne na farko.

Janyo jikin shi yayi yana matsowa inda Nuriyya take zaune, yanayin shinkafar a idanuwan shi yaga kamar bata dahu ba, hakan yasa shi dan dibowa da cokali ya saka a bakinshi ya dan tauna yaji ta giri-giri
"Wallahi bazan ci shinkafa a tsai-tsaye haka cikina ya kumbura ba, bata dahu ba"
Ya fadi yana ajiye cokalin, kallon shi Nuriyya tayi
"Kici a bakin ki, da tun jiya kika dafa mana yanzun saiki yi warming kawai"
Plate din Nuriyya ta dauka tana mikewa da sauri ta fice daga dakin, dan duk wani abu na zuciyarta gaya mata yake ta juye mishi shinkafar sannan ta kwantara mishi farantin tangaran din saman kai kowa ma ya huta.

"Kece da asara Waheedah, danni bawai ya dameni bane"
Nuriyyar ta fadi a fili da bala'in bacin rai, da tayi tunanin kwantara mai faranti ya mutu duk su huta.

Cikin tukunya ta mayar da shinkafar ta kara ruwa tayi tsaye.

Idan ta koma dakin ya sake magana tanajin kome ya fito daga bakinta fada mishi zatayi sai dai in gabas zai saka kanta ya yanka yayi.

Tagaji har cikin kasusuwan ta, ya fara fita daga ranta daga shi har auren, a wuya takejin su sun mata tsaye.

Takai mintina sha biyar har saida ta fara jin kaurin shinkafar tukunna ta kashe gas din, ko ta dahu ko bata dahu ba haka zai hakura yaci, ko ya fito ya dafa wata.

Sake zubawa tayi ta dauka tana komawa dakin ta ajiye.

Dan diba AbdulKadir yayi yana sakawa a bakin shi, tadan rissina ba kamar dazun ba.

Duk da bata kai yanda Waheedah take dafa musu laushi ba, kallon shi Nuriyya takeyi tana jiran taji ya sake cewa bata dahu ba, dan tabbas wannan karin zata kwantara mishi farantin tangaran din.

Sai taga baice komai ba, miyar ya dibo yana zubawa a gaban shi hadi da cakudawa, ba sosai yake son abinci mai zafi ba, hakan ne yasa shi baiyi saurin kaiwa bakin shi ba, ta riga shi zuba miyar ta juya ta diba ta saka a baki.

Wani irin karni taji cikin kofofin da suka hada bakinta da hancinta, sannan miyar ta sauka cikin bakinta da wani dandano marar kan gado, tana taunawa dakyar ta hadiye.

AbdulKadir ta kalla daya ciko cokali tanajin kamar tace mishi karya ci, ya kuwa auna cikin bakin shi, lokaci daya yanayin fuskar shi ya sauya, bai tauna shinkafar ba ya hadiye yana wani irin sauke numfashi har lokacin bakin shi a gauraye yake jin shi.

Mama na musu abinci marar dadi, amman yana ciyuwa, bakajin kamar zaka shaqe ka wuce lahira
"Kasheni kike so kiyi Nuriyya...

Da raina kike so ki kasheni"
AbdulKadir ya fadi yana dorawa da
"Baki iya abinci ba, bansan ya akai ban taba sani ba sai yanzun...

Wacce irin miyace wannan?"
Kai Nuriyya ta saddar kasa tanajin kunyar data shiga ta danne bacin ran da take ciki
"Shisa kike cewa in daukar miki yar aiki?"
Kai tadan daga mishi a hankali, kai AbdulKadir ya jinjina dan abinda ba zai taba yiwuwa bane ba, badan kar a tayata aiki ba, ko dan baya goyon bayan mazan da suke daukar ma matan su yan aiki ba, ko da babbar sallah yana ma Hajja magana a dauko ma Waheedah ta soya mata nama.

Baiga dalilin da zaisa shi yaci abincin yar aiki ba
"Ki koya dan ni ba zanci abincin yar aiki ba"
Kallon shi Nuriyya tayi sosai, tana tunanin ta inda yake so ta fara koyon girki, kowa yake so taje ta samu ya koya mata
"Kafin ki kasheni dan Allah ki dinga mana mai da maggi"
AbdulKadir ya karasa maganar da sigar roko yana dorawa da
"Yanzun ma tashi zakiyi ki zubomun da mai..."
Batayi musu ba ta mike, numfashi AbdulKadir ya sauke yana jin komai ya birkice mishi, fada yaso yayi sosai, amman kananun maganganu ba halayyar shi bace ba, bai kuma saba komai sai yayi magana a kai ba, sun sami matsala da yawa yau Da Nuriyyar bayaso su kara samun wata cikin daren nan.

Dan yasan halin sune, kome zai faru iya sune, babu shaidan din da zasu labe a bayan shi tunda watan azumi ne.

Bai shirya sanin yana da halaye marassa kyau ba, gara tasan yanda zatayi ta koya, ya dai cika da mamaki, ya dauka koyayane mata sun iya girki tunda abune da sukeyi yau da kullum.

Da mai yaci kuwa yana mayarwa da ruwa ya mike, yanajin yanda idanuwan shi sukai zuru-zuru duk da bai kallo mudubi ba.

Bacci suka dan koma kafin asuba.

Sanda ya dawo masallaci Nuriyya harta sake komawa bacci.

Shikam zama yayi yana yin azkar har rana ta fito ya mayar da sallah raka'a biyu ta nafila.

Sai daya wuce dakin Waheedah yana samunta tana linke dardumar ta da alama itama sai lokacin ta tashi.

Dan ita ta saba mishi da yin nafilar bayan asuba, ko kadan bata wuce ta, ta tunasar dashi tarin ladan da yake cikin hakan.

Yanzun harta zame mishi jiki, cikin sanyin muryarta ta gaishe dashi, ya amsa
"Kun tashi lafiya?"
Sai da ta fara jinjina mishi kai tukunna ta amsa tana dorawa da
"In kaje gida yau ka taho da Fajr"
Kallonta AbdulKadir yayi, sosai take kewar yaron nata
"Ni nace miki zanje gida ne?
Chapter 86 · 0% Book details