Sashe 64
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yinin ranar babu inda ya fita sai masallaci, duk da tana iya kokarinta na ganin jikinsu bai hadu da juna ba, ko hannunta bataso ya rike sai taji ya kara mata ciwon da take ji a kirjinta.
Abin har tsoro ya fara bata.
Bai mata zancen auren ba, ita kuma tama kanta alkawarin in bai tayar mata da maganar ba, ba zatace mishi komai ba.
Inya tayar mata dinma maganar data fada mishi jiya ita zata maimaita mishi, bata da wasu kalaman banda wannan.
Sai da daddare ya samu ya turama Nuriyya text
'Ya kika wuni?
Zan zo sai gobe in shaa Allah.
Waheedah bata jin dadi.
Zan kiraki goben, ki kula da kanki'
Bai jira amsarta ba yasa chargy ya kwanta gefen Waheedah da duk idanuwanta data rufe bai hana shi kakume mata ba.
Ta godema Allah da bai jima ba bacci ya dauke shi, amman koya ta motsa sai taji ya sake riketa kamar zai shige jikinta.
Ta jima sosai saboda yanda kusancin da yayi da ita yake kara ma kirjinta ciwo, kafin barawon bacci ya saceta.
Washegari da karfinta ta tashi, babu abinda takejin yana mata ciwo banda zuciyarta.
Doya ta dafa, Anty ta aiko mata da wani yaji mai dadi, lallaba shi takeyi karya kare, tata doyar ta diba dan da mai da yaji takejin ci.
AbdulKadir ta soya mishi tashi.
Tana gamawa ya fito shikuma suka ci karo a bakin kofar kitchen din
"Ni ban isa ba ko Waheedah?
Bazan ce karkiyi abu kijini ba"
Kai ta girgiza mishi
"Yayi kyau, yanzun kuma karya nayi.
Me nace miki dana dawo masallaci?
Ko shara karkiyi...
Amman ban isa ba shisa kika fito"
Numfashi Waheedah ta sauke, tasan zaiyi fada daman, amman ta kasa komawa bacci, aikin da ga fito tanayi yana rage mata tunani tunda babu wuta balle ko kallo tayi, ko da wutar ma batajin yin wani kallo ita.
"Kayi hakuri, ba wani aiki nayi ba, doya kawai na dafa na soya"
Yanda tai maganar yasa shi jin wani iri, karasawa yayi yana kama hannunta
"Dan kinga bana iya miki fada shisa kika daina jin maganata"
Murmushin karfin hali tayi tana ware mishi idanuwa
"Dan Allah karki karayin komai, ki huta, inkin ji sauki sai kiyi"
Kai ta daga mishi.
Ya sumbaci gefen fuskarta, ya dago hannunta yana shafa inda yai ja da alamar hudar zaman allurar karin ruwan da akai mata.
"Sannu..."
Ya furta cike da kulawar da ta ragema kusancin da yayi da ita kara mata ciwon da takeji.
"Zaka karya yanzun?"
Kai ya daga mata, ta dora da
"Ina da zobo a fridge, ko zaka sha Tea?"
Da sauri ya girgiza mata kai
"Yaushe kikayi zobo?"
Hannunta ta zame daga cikin nashi tana bude fridge din ta dauko roba daya
"Tun shekaranjiya, da yawa nayi, Fajr duk yamun barnar shi"
Tare suka fita da kayyakin, AbdulKadir a kular ma yaci tashi doyar.
Itama tayi mamakin wadda taci dan lokacin da suka zauna ko yunwar bataji.
AbdulKadir din ya kwashe kayan tana zaune.
Tanajin shi yana ta kwaramniya da kwanoni.
Sai daya fito taga hannuwan shi duk ruwa
"Me kayi?"
Ta tambaya
"Wanke-wanke...
Har gogewa nayi"
Murmushi tayi mishi da yake ganin kamar bai kai idanuwanta ba.
"Sannu da aiki..."
Amsawa yayi da
"Yawwa"
Yana dan nazarin yanayinta kafin ya wuce dakin.
Wayar shi ya dauka ya kira Yassar, yau dinma sai da yayi tunanin ba zai dauka ba tukunna ya daga.
"Ina jin ka"
Numfashi AbdulKadir ya sauke
"Gaba babu kyau Hamma...Kuma yanzun mun girma mu ba yara bane, bai kamata muna irin wannan..."
Bai karasa ba saboda Yassar din ya kashe mishi waya a kunne, lumshe idanuwa AbdulKadir yayi yana budesu hadi da furzar da wani numfashi ran shi a bace, wayar Yassar din ya sake kira, wannan karin yana dagawa yace
"Wai meye?"
Numfashin AbdulKadir ya sake fitarwa, zai dauki girman yau, girman da Yassar din ya kasa dauka
"Motar ka daman, in ba zaka bukata ba, zanyi abu da ita"
Dan shiru Yassar yayi
"Me yasa baka zo da taka ba?
Wanne abu zakayi?"
A ranshi AbdulKadir yayi niyya tun jiya, daya koma akwai abokan aikin shi da zasu taho Kano su biyu satin sama, zai basu motar su taho mishi da ita, yabarta a gida tunda sai yazo yake gane yafi bukatarta anan din fiye da can Lagos.
Tunda inba wani dalili ba sunfi fita da motar aiki.
"Da gaske kana son sanin abinda zanyi da ita?"
Murya a dakile Yassar yace
"Inka gama ka dawomun da motata gaskiya"
Yana kashe wayar.
A karo na biyu a rana daya daya kashema AbdulKadir din waya a kunne, inda wani ne a gidan ba Yassar ba, kome zaiyi da motar ya hakura, amman shi kan shi Yassar din yasan ba zaiyi zuciya ba.
Shi kadai AbdulKadir yake tambaya abu, ya zageshi, kuma ya bashi abin ya karba.
Shakuwar dake tsakanin su ta daban ce, Yasir ne suka kwanta a ciki daya a lokaci daya, amman zai iya rantsewa babu shaquwa mai karfi irin wannan a tsakanin su.
Dan zai iya kwana biyu ma basu gaisa da Yasir din ba, musamman yanzun da shi yana Katsina, tunda aiki ya mayar dashi can ya samu yar Katsina ya aura.
Falo AbdulKadir ya dawo yana samun Waheedah a zaune inda yabarta.
Zama yayi ya zame jikin shi ya kwanta yana dora kan shi a cinyarta.
Jin yana gyara kwanciya yasa ta fadin
"Karka danne mun hancin yaro Sadauki"
Dariya AbdulKadir yayi
"Yarinya dai"
Shiru tayi ta kyale shi, cikin Fajr ma haka sukai ta wannan gardamar, sai ta haifi namiji.
Kuma shi yace bayason sani a asibiti, wannan dinma yace mata ko an tambayesu zasuce basa son sani, sai ta haihu tukunna.
"Ina so in fita, amman banaso in barki ke kadai"
Hannunta ta dora kan fuskar shi, tana jin maganar shi can nesa, da wani yanayi a fuskar ta tace
"Ka fita abinka, naji sauki ai.
Ka tahomun da kwakwa inka ganta"
Kai AbdulKadir ya jinjina mata
"Bacci zanyi yanzun.
Sai azahar tukunna, kwakwa kawai?"
Ya karasa maganar yana juya kwanciyar shi, ta daga mishi kai.
Baice komai ba ya lumshe idanuwan shi.
Kanta Waheedah ta jingina jikin kujerar dake bayanta.
Tunani take, amman ba zatace ga ko na menene ba, kawai tasan ta lula tsakiyar wata duniya da bata ganin falonta balle tayi tunanin karshenta.
Jikin shi ya mishi nauyi saboda baccin da yayi, dan sai da Waheedah ta tashe shi da aka kira sallah.
Hamma kawai yake a mota, harya karasa kofar gidansu Nuriyya yayi parking, gida yake son shiga, amman bayaso su bata mishi rai, kan shi a cunkushe yake jin shi, bayason hada abubuwa da yawa waje daya, tunanin zai iya damun shi.
A cikin motar yai zaman shi yana kiran wayar Nuriyya ya fada mata yana kofar gidan.
A cikin motar ta same shi, tana zama da wani irin bugun zuciya naban mamaki.
Turarenta daya cika motar na mishi daban
"Ina wuni"
Ta gaishe dashi cike da kunyar da batasan tana da ita ba.
"Lafiya kalau.
Ya kike?"
Kanta a kasa tana wasa da yatsunta da suka sha kunshin jan lallen da rashin aikinyi yasa ta daura shi shekaranjiya.
Ta mishi maganar tarewa ne saboda zaman gidan ya isheta, kwata-kwata Mama bata hira da ita, gaisuwa ce kawai take hadasu, ko dariya take inta hangota zata daina, Baba ma inta gaishe shi dakyar yake amsawa.
Gashi babu damar ta fita daga gidan ballantana ta sha iska.
Yanzun ma maganar take sakeyi mishi, amman kunya ta hanata.
"Alhamdulillah"
Ta amsa, AbdulKadir din na tsintar kanshi da kamo hannunta yana wasa da yatsunta da suka sha kunshin da yai mishi kyau sosai.
Sai yake ganin hannun ya mishi daban, ko a mafarki bai hango rike hannun wata macen da zata kira kanta da matar shi banda Waheedah ba.
Komai bako yakejin ya dawo mishi, duk da hannun Nuriyya din a cikin nashi yasa wani abu tsirga mishi cikin kai yana yamutsa mishi tunani.
"Kin shirya ne?"
Da sauri ta dago kanta tana sauke idanuwanta cikin nashi tana kasa yarda da cewar shi din mijinta ne.
"Eh na shirya, amman ban fadama su Mama ba tukunna"
Kai AbdulKadir ya jinjina mata
"Ki fada musu to, saiki kirani inji yaushe...
Gobe in shaa Allah zan wuce"
Shagwabe fuska Nuriyya tayi
"Gobe?
Da wuri haka Masoyi?
Jiya banganka ba"
Kallonta yake, sunan da take kiran nashi dashi na mishi banbarakwai a lokaci daya kuma yana saka mishi wani irin nishadi.
Murmushi yayi da yasa gwiwoyin Nuriyya yin sanyi.
Tasha ganin murmushin a fuskar shi, amman yaune karo na farko da yayi shi domin ita, wani shauqin kaunar shi taji yana fisgarta.
"In dauko wasu kayan ka tafar mun dasu?"
Nuriyya ta bukata da sauri tana dora dayan hannun nata saman nashi, tanajin dadin yanda take da damar yin hakan yanzun.
Kai AbdulKadir ya daga mata, ya fada mata inda zata zauna akwai komai, kitchen ne kawai ba kaya.
Ta siyi kayan kitchen sosai, kusan abinda tayi da kudin da ya bata kenan, daman akwai sauran kudin kayan dakinta wancen da ta siyar bayan ta fito daga gidan Anas.
Da su da sadakinta ta hada ta siyi fridge.
Yana gidan Asma'u kawarta, dan duk kayyakin ma ita ta dinga turama kudin tunda sana'arta kenan, siyar da kayan kitchen din.
Ta kuma kawo mata komai da ta siya, fridge dinne da babu inda zata ajiye.
Hannun AbdulKadir ta saki tana fita daga motar cike da zumudin kayanta zasu isa gidan AbdulKadir din, itama kuma zata bi bayansu babu jimawa.
Ganin ta fara fitowa da kaya yasa AbdulKadir fitowa daga motar ta bude mata boot, yana taimaka mata ta zuba wanda zasu shiga, wasu kuma a bayan motar.
Tukunna sukai sallama, yana wucewa gida.
Da niyyar inta kirashi ba ranar zata tare ba, saiya tura mata kudin abinci, daman wancen watan bayan tafiyar shi saida ya tura mata kudin abinci tunda tana karkashin kulawar shi, yasan hakan hakkinta ne.
A hanya yai la'asar tukunna ya wuce gida.
A mota yabar kayan.