Sashe 22
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko daya fita yai sallah a masallaci wajen karfe daya, yana dawowa daki ya cire dogon wandon ya mayar da iya gwiwar shi, kwanciya ya koma yayi.
Idan abu ya riga ya wuce baya tunanin shi, baya wannan asarar, shisa baisan dalilin da Nuriyya zata manne mishi cikin kai haka ba, ko idanuwan shi ya rufe ita yake gani, ta addabe shi, ta hanashi sakat, ya riga da ya fadama kanshi tana da kyau, baiyi ma kanshi karya ba tun farko, amman taki barin shi, wani in yagani saiya rantse da Allah hotonta ya dauka ya samu waje ya rataye cikin kanshi.
A hankali yaja karamin tsaki yana juya kwanciyar shi, yunwa yaji ta fara mishi sallama, duk da bai karya da wuri ba, saboda shi mutum ne da baya wasa da abincin kwata-kwata.
In har baici ba, to damar hakan ne bai samu ba.
Ya mike yasa wani ya kawo mishi dinne yake mishi wahala yau, lumshe kananun idanuwan shi yayi, har lokacin Nuriyya na manne cikin kanshi, bacci ne ya fara fisgarshi a hankali.
Cikin kunnen shi yaji an turo kofar hadi dayin sallama a hankali
"Hamma..."
Muryar dayai tunanin Nazir ne ta dirar mishi.
Shiru yayi bai amsa ba, yana fatan shirun tasa kowaye ya tafi.
"Hamma kazo inji Hajja..."
Nazir ya fadi yana riqe da kofar ko da almatsutsan Abdulkadir din zasu tashi.
Bazai tsaya ya sauke su akan shi ba
"Kaina namun ciwo"
Abdulkadir ya fadi batare daya bude idanuwan shi ba, baisan kiran me Hajjon take mishi ba, bangaren ta yasan a cike yake da mutane, ta kuma san bason hayaniyar yake ba, zata fara sakawa a kira shi.
Ba kanshi yake ciwo ba, jikin shine bayajin dadin shi.
Turo baki Nazir yayi dan saida Hajja ta balbale shi da fada tukunna yazo kiran Abdulkadir din
"Tace kazo..."
Sake runtsa idanuwan shi Abdulkadir yayi
"Zanci ubanka idan na bude idanuwana kana cikin dakin nan"
Yanajin karar rufe kofa, batare daya bude idanuwan shi ba ya gyara kwanciyar shi yana kwantawa kan bayan shi hadi da dora hannuwan shi duka biyun kan cikin shi, bacci ne mai karfi ya dauke shi wannan karin duk da yunwar da yake ji.
Ba zaice ga lokacin daya dauka ba, baccin kuma yau yayi karfin da baiji turo kofar ba sai bubbuga mishi kafa da yaji anayi, a tunanin shi Nazir dinne ya sake dawowa, raini yasa shi harda bubbuga mishi kafa wannan karin.
Cikin zafin nama yai amfani da inda yake jin hannun na bubbuga shi ya hasaso inda fuskar yake tunanin fuskar Nazir din zata kasance yakai mishi wani barin makauniya.
"Umm um um umm..."
Yassar ya fadi yanajin wani yawu da yake tunanin jinine na tattarowa yana cika mishi baki, dan a mummuke Abdulkadir ya same shi
"Ba zaka fita ba kenan dan uban ka?"
Abdulkadir ya fadi jin gurnanin da Yassar din yayi yana bude idanuwan shi hadi da mikewa ta sauke su kan Yassar dake dangwalo mummuken shi yana dubawa, ware kananun idanuwan shi Abdulkadir yayi
"Inalillahi...
Hamma...
Wallahi na dauka Nazir ne..."
Hannu Yassar ya daga mishi kawai yana wucewa bandaki ya kuskure bakin shi yana zuwa saitin mudubi, wajen harya tara jini daga waje, bude bakin shi yayi yana zira dan yatsa ya tana hakorin shi na sama da yaji kamar ya fara girgidi, sosai ya tattaba hakoran duk da yake tunanin sun fara girgidi yaji suna zaune dam, dubawa ya sakeyi yaga babu jini tukunna ya fito daga bandakin yana samu waje gefen gadon ya zauna, bazai karya ba, ya maku yanda ya kamata.
"Hamma..."
Abdulkadir ya kira da alamun dariya a muryarshi ganin yanda Yassar din ya nutsu.
Gabaki daya fuskar shi Yassar yake ji ta dauki dumi kamar tana zazzabi ita kadai.
Saida ya tabbatar idan yai magana muryarshi ba zatai rawa ba tukunna yace
"Dan ubanka ba zaka bude idon ka ba?
Daka cire mun hakori me zaka fadamun?"
Sosai Abdulkadir yake son danne dariyar shi amman ya kasa, sauka yayi daga kan gadon yana mikewa tsaye, sosai yake dariya
"Inda Nazir dinne haka zaka kai mishi wannan dukan?
Saboda kai baka da tausayi?"
Dariya Abdulkadir yakeyi
"Wallahi bansan kai bane ba"
Kai Yassar ya jinjina yana yin qwafa kawai.
Gabaki daya duk wani karfin gwiwa daya shigo dashi dakin ya gama sacewa.
Bandaki Abdulkadir ya wuce yana wanko fuskar shi ya fito, nesa da Yassar din ya zauna, dan yasan in ya yanke hukuncin rama dukan shi zaiji jiki.
Tukunna yace
"Menene kake tashi na?"
Sai da Yassar ya watsa mishi wani kallo tukunna yace
"Hajja tace zaka dauki mutanen da zasu kai Khadija, saika tabbatar ka tattaro su Zahra dan kar suce zasu kwana..."
Dakuna fuska Abdulkadir din yayi
"Gaskiya babu inda zance...bari in kira su Zahra din in musu kashedi kawai"
Tsare shi da idanuwa Yassar yayi cikin yanayin daya sashi qara daquna fuska yana fadin
"An shiga rayuwa ta wallahi...
An takurani gaskiya"
Kallon shi dai Yassar yaci gaba dayi batare da yace komai ba.
Abdulkadir din bayason yana kallon shi haka, bayaso yana kallon shi kamar yayi wani laifi.
Meyasa za'ace ya fara kai mutane wani waje, Hajja tasan a gidan in ba ita ba sai Abba, ko yara ba'a sakawa yakai makaranta.
Balle yazo ya fara dibar wasu mutane kamar direba.
"Ba zaka je ba kace Abdulkadir?
Kai tsaye ba zakaje ba?
Ince maka Hajja tace kayi abu kana fadamun ba zakaje ba?
Dan Ubanka ba zaka shiryu ba, ba zaka gane girma kakeyi ba ko?"
Yassar yake fadi ranshi a bace, baisan lokacin da Abdulkadir din zai gyara wannan muguwar dabi'ar ta rashin ganin kan kowa da gashi ba.
Kicin-kicin Abdulkadir din yayi da fuska
"Nidai an shiga rayuwata gaskiya"
Ya sake maimaitawa yana saka Yassar fadin
"Yayi kyau..."
Yaja kafafuwan shi yana dorawa kan gadon, wayar shi kirar blackberry curve 2 ya zaro daga aljihu yana ci gaba da dannawa.
Sake daquna fuska Abdulkadir yayi yana kallon Yassar din, yasan ranshi ne ya baci, bayan Abba a gidan babu wanda yake kokarin gujema fushin shi irin Yassar, fiye da Hajja dan yasan ita da wuri take sakkowa
"Wanne unguwa ne?"
Ya bukata muryar shi can kasan makoshi, inda yake Yassar bai kalla ba, ballantana yai kokarin kula shi.
"Hamma kaji...
Wacce unguwa?
Karfe nawa za'a tafi?
Shirun Yassar ya sake mishi
"Bana so ina magana ana mun shiru, kasani kuma, ina tambayarka kayi banza ka kyaleni"
Yanayin yanda yai maganar yana sa Yassar fadin
"Fada zakai mun Abdulkadir?"
Kankance idanuwa Abdulkadir ya sakeyi
"Magana nake maka kai shiru ka kyaleni"
Kai kawai Yassar ya jinjina
"Ya maka kyau"
Ya karasa maganar yana mikewa ya fice daga dakin, Abdulkadir nabin shi da fadin
"Kaifa kaqi bani amsa, banyi fushi nabar maka dakin ba kaine zaka fita?
Hamma bana son irin haka...
Hamma...
Ok ya maka kyau"
Wucewa Yassar yayi, yana jin 'Ya maka kyau' din da Abdulkadir din ya fadi da tasa shi jin son komawa yasa belt ya zane jikin Abdulkadir din, sai dai alkawari yaima kanshi bazai biyema Abdulkadir din ba, dan idan akwai mashi a kusa, tsaf takaicin dazai qunsa maka zai saka soka mishi batare daka sani ba.
Idan ya biyema Abdulkadir zai dake shi saiya karya shi, yana kuma da tabbacin duk da bazai rama ba, bakin shi bazai shiru ba.
Addu'ar shiriya yai mishi kamar ko da yaushe.
Saida ya dauro alwala tukunna ya fito daga dakin da nufin zuwa masallaci dan yaga la'asar ta kusan qarasawa, yana da tabbacin ana gab da kiran sallah.
"Zahra..."
Ya kira daya hango ta taho, tun jiya yake mamakin girman yarinyar, wai har ta gama sakandire, Yassar ne yake fada mishi ta nemi gurbin karatu a jami'ar Bayero dake nan Kano din ma da yake mishi zancen girmanta.
Duk da ta tsallake aji uku, kasancewar tana da kokari sosai.
Takowa take a hankali tana nufo inda Abdulkadir din yake
"Yanga zaki tsaya mun?"
Ya fadi yana kallon ta, kai ta girgiza mishi tana saurin fadin
"A'a..."
Ta karasa inda yake tsaye da sauri.
Kallon ta Abdulkadir yayi, dankwalin lace din dake jikinta ne ta dora saman kanta batare data daura ba, indai Zahra ce ba zata taba yin abu irin na mutane ba yasani, ko makaranta zataje hijab dinta in baya hannu lokacin zakaga tana saka shi.
"Ki kawomun abinci...da ruwa, kikai mun dakina a bude yake..."
Amsa shi tayi tana shirin juyawa Abdulkadir yace
"Ki fada musu ni zan dawo daku daga wajen kai Adda...
Duk wanda na nema sai yaji a jikin shi"
Ware idanuwa Zahra tayi, gabanta yana faduwa, kafin ta dakuna fuska
"Baki jini ba saina watsa miki mari"
Sake dakuna fuska tayi, da gaske Hajja take ba zasu kwana ba din dai, bayan Adda Khadee din da kanta tace musu zasu kwana tun kafin bikin.
"Zan fada musu"
Zahra ta amsa tana wucewa, yana kallonta tasha kwana, tunawa yayi baima tambayeta wacce unguwa ko kuma karfe nawa ba, bin bayanta yayi tunda ta rigada tasha kwana ko kwala mata kira yayi ba lallai taji shi ba, gashi yau bayajin hayaniya kwata-kwata.
Zahra kuwa tana shan kwana taci karo da Amatullah
"Kinsan Hajja tasa Commander ne yakai mu?"
Dafe kirji Amatullah tayi
"Kice mun wasa kike?
Haba dai Commander...
Ina ce Hamma Yazid zamu bi"
Kai Zahra ta girgiza ma Amatullah din
"Yanzun yaimun magana da kanshi, wai karma mu bari ya neme mu idan an kaita din"
Buga kafafuwa Amatullah tayi cike da rashin jin dadi
"Allah dai ya hadamu da jarabu da qwai..."
Turo baki Amatullah tayi tana fadin
"Ai gara Jarabu da qwai akan Hamma A..."
Hadiye maganar tayi ganin Abdulkadir din a tsaye ya diro musu kamar mikiya.
Yanda ya tsareta da idanuwa yana tabbatar mata da maganar yake so ta karasa, wani abu da taji ya tsaya mata a wuya ta hadiye, a daburce tace
"Hamma A...
Hamma Aminu"
Zahra da yanayin Amatullah din ya tabbatar mata da Abdulkadir din ne ya karaso wajen yasa ta juyawa ta kuma matsa kamar zata hade da bangon wajen, da yanayin fuskarshi ya tabbatar mata da yajita.
"Yaushe Aminun ya zama Hamman ki?"
Abdulkadir ya fadi yana tsare su da idanuwa.