Sashe 36
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kabarta ta huta idan an kwana biyu saika dawo kuyi magana, itama tahau dokin zuciya ne"
Kankance idanuwan shi Abdulkadir yayi, yana wani irin sauke numfashin bacin rai, Waheedah ita taja mishi tonon sililin nan.
Da ta saka kowa yazo yana tsoma mishi baki a cikin maganar iyalin shi
"Kiban yarinyata Anty..."
Abdulkadir din ya fadi yana kokarin danne sauran maganganun da suke kan harshen shi.
Itama Antyn ranta take ji yana kara baci
"Ba zakaji magana ba kenan ko?
Ba zaka ji ba ko Abdulkadir..."
Runtsa idanuwan shi yayi yana budesu
"Idan da naso jin ra'ayinki kan abinda yake faruwa ina da bakin dazan bukaci hakan...kiban yarinyata"
Hannu Anty ta saka tana kwance goyon Ikram din, mika mishi ita tayi tana furta
"Allah ya shirya"
Karbar yarinyar yayi da taketa bacci kamar komai bai faru ba, nutsuwar da take ciki na sakashi sauke numfashi, saida ya gyarata cikin hannun shi tukunna ya kalli Anty
"Amin"
Ya juya yana ficewa daga dakin, yanda ya doko kofar na saka Anty yin dana sanin marin da taki daukeshi dashi.
Sai dai tasan Abdulkadir idan bai rama ba, sai ya gaya mata maganganun da zatayi satika tana juyi dan kunar rai.
Wani abin da zai maka koda an samu igiya an kulle shi a baka kulki ka jibgeshi bazaka huce ba.
Kan gado ta koma ta zauna, zuciyarta na tafasa.
Shikam falon ya karasa yana kallon yanda Waheedah take kallon shi cikin sabon tashin hankali.
Hakan ya mishi dadi, gara taga da gaske yaranshi zai dauke, saita tashi su koma gida gabaki daya.
Idan rigima takeji zai bata dai-dai wadda zata isheta harda kari idan bukatar hakan ta taso.
Waheedah batasan ta mike ba saida taga kallon da Abdulkadir din yake mata.
Ta dauka zuciyarta ta bushe, ta dauka babu wani abu dazai sake taba ta, saida taga yarinyarta a hannun shi tukunna takejin yanda yake son rabata da sauran nutsuwar da ta rage mata, muryarta a karye ta soma magana
"Me kake so dani?
Sadauki me kake so dani haka?
Meye ban baka ba?
Lokacin da sukazo saura suka samu daga zuciyata, saboda kaso mafi girma na tare dakai..."
Shiru tayi tana mayar da numfashin daya taso mata mai hade da kukan da yasa ta kasa karasa maganar data fara
"Ki biyoni mu tafi gida, koma menene zamu gyara shi mu biyu..."
Abdulkadir ya fadi yana rokonta da duka zuciyarshi da ta amince, saidai a fuskarta yake ganin hijabin da baisan daga inda ta samota ta saka a tsakaninsu ba, hannu tasa ta share hawayenta tana girgiza mishi kai, yanayin daya kara mishi zafin da kirjin shi yakeyi.
Kai ya jinjina yana fadin
"Kiyi abinda kike so Waheedah..."
Ganin ya juya yana shirin barin dakin ya sata furta
"Takardata Sadauki..."
AbdulKadir bai nuna alamun yajita ba ya fice daga dakin.
Aurenta a hannun shi yake, yara nashi ne, zai dauka duk sanda yaga dama.
Ya dauka idan yayi amfani dasu zata hakura ta dawo hayyacinta daga rashin hankalin da take ciki.
Hakan bai faru ba, zai dauki yaran yanzun, zai tafi dasu.
Zai kuma ga wanda ya isa yasa shi sakinta, tonon asirine ta gama yi mishi, abinda bai taba tunanin zata tabayi ba, sosai ta girgiza shi, dan harya shiga bangaren Mami yana mamakinta, yana kuma duba cikin kanshi ko zai tuna asalin laifin dayai mata banda na ranar amman ya rasa.
Bai samu Mami a falon ba, Aminu ne zaune da Fajr da hankalin shi gabaki daya akan tom and jerry din da yake kallo a babbar talabijin din dakin.
Batare da yayi magana ba ya karasa yana saka hannun shi daya ya dago da Fajr din da a shagwabe yace
"Paapi..."
Gyara mishi tsayuwa Abdulkadir din yayi yana fadin
"Wuce mu tafi..."
Da rashin fahimta yaron yake kallon shi da idanuwan shi irin na Waheedah din
"Omma fa?"
Saida Abdulkadir ya sauke numfashi tukunna yace
"Banda ita..."
Maqale kafada Fajr yayi, yana shagwabe fuskarshi sosai
"Zan zaneka Fajr...
Ka wuce nace"
Wucewar Fajr yayi dan duk karancin shekarun shi yasan cewa Abdulkadir din zane shi zaiyi kamar yanda ya fadi, kukan shi ma bai bari ya fito ba, dan yana bala'in tsoron duka, ko tsintsiyar kwakwa yaga Waheedah ta fito da ita ta ajiye waje daya zai nutsu.
Abdulkadir kuwa ya taba saka charge ya zane shi, sosai yake tsoron yin wani abu a gaban shi.
Sai lokacin Aminu yace
"Tunda ba zashi ba ka kyaleshi"
Kallon shi Abdulkadir yayi yana kafe shi da idanuwa, bai manta maganganun daya fada mishi a asibiti ba dazun, kawai ya kyalene baice komai ba saboda a lokacin yana cikin jin kunyar Mami
"Ka mantani ko?
Aminu ka manta wanene ni"
Kai Aminu ya sauke kasa yana jin zuciyarshi na dokawa cike da tsoro.
Bai manta ko waye Abdulkadir ba, haushin shi da yakeji dinma a yanzun ya nemeshi ya rasa
"Zan dakeka, zan fasa maka bakin da saikayi sati magana da kowa na maka wahala balle kayi tunanin mun rashin kunya..."
Abdulkadir ya karasa yana directing bacin ran nashi kan Aminu.
Sosai yake jiran yaron yai motsin da bai mishi ba, ya ajiye Ikram kan kujera ya dake shi kamar ganga.
Zuciyarshi zatai mishi sanyi ko yaya ne idan ya zane wani, tunda bazai iya zane Waheedah da ta bata mishi ran ba.
Amman Aminu ko dago dakai baiyi ba ballantana yai kokarin cewa wani abu.
Kai Abdulkadir din ya jinjina ya juya ya kama hannun Fajr yana janshi suka nufi hanyar da zata kaisu harabar gidan inda motarshi take a ajiye.
Yassar ya hango ya bude motar shi ya fito, cikin shigar manya kaya da hula da suka kara mishi wani irin kwarjini.
Tsaye Abdulkadir din yayi batare daya san dalili ba, yana nan har Yassar din ya karaso ya same shi
"Ina kuma zakaje da yara?"
Yassar ya bukata, yana kai hannu ya dafa kan Fajr daya fada jikin shi yana fadin
"Uncle..."
Yana gidan shi a kwance yaga wayar Hajja.
Saida zuciyar shi ta doka, dan yasan ba lafiya ba, indai Hajja zata daga waya ta kirashi sai da wani babban dalili.
Baiyi mamakin jin dalilin Abdulkadir bane ba.
"Bakaimun sallama ba Hamma..."
Abdulkadir ya fadi yana kankance idanuwan shi, dan yaga yanayin Yassar din shima yasan abinda yake faruwa.
Wani irin kallo Yassar ya watsa mishi
"Yaran ka dauko?
Ka sake tan?"
Kai Abdulkadir ya girgiza mishi, hannu Yassar ya mika yana karbar Fajr da Abdulkadir din ya kasa hanashi
"Nasan baka da hankali ko kadan, amman banyi tunanin yakai haka ba.
Gidan ubanka zakaje da jaririya?
Ko Nuriyyar ce zata shayar maka da ita?"
Sosai Abdulkadir ya dakuna fuskarshi
"Karkai mun fada Hamma, idan zaka dauki sides saika tsaya kaji nawa bangaren tukunna"
Tsaki Yassar yaja, da yace bazai sake shiga matsalar Abdulkadir din ba, yanzun ma dan Hajja ta kirashi shisa ya dauko kafarshi yazo.
Hannun Fajr ya kama yana shirin raba Abdulkadir din da nufin wucewa
"Hamma ina zakaje mun da yara?"
Kallon shi Yassar yayi
"Idan ka biyoni saina watsa maka mari, mahaukacin banza..."
Murya can kasa Abdulkadir yace
"Yarana, a gaban yarana Hamma..."
Tsakin Yassar ya sake ja yana wucewa abin shi, yanajin Abdulkadir din na biye dashi.
Baiko juya ba harya karasa bangaren Anty, tunda Hajja tace mishi suna can data kira.
Waheedah ya samu ta hada kanta da kujera, yanayin ta nasa wani abu tsaya mishi a rai, dagowa tayi fuskarta harta tara jini saboda kuka.
Sosai Yassar yaji kirjinshi yayi nauyi.
Karasawa yayi ya zauna kan kujerar yana mika mata Ikram.
Da sauri ta karbi yarinyar tana riketa a jikinta, duminta na saukar mata da wata irin nutsuwa taban mamaki
"Nagode Hamma..."
Ta fadi cikin wata irin murya da tasa Yassar sake kallon Abdulkadir din yana watsa mishi wani kallo.
Kankance mishi idanuwa Abdulkadir din yayi, ya dauka Yassar na bayanshi, kamar ko yaushe akan abubuwa da dama.
Tun a watanni baya yagane cewa shima bayan Waheedah yake, bashida matsala dan Yassar yaso Waheedah, ko bakomai kanwarshi ce, amman shima kaninshi ne, kuma yana da kishin da bayaso a fifita soyayyarshi akan ta kowa.
Ko Hajja bayason yaga tana nuna ma su Yazid soyayya fiye da wadda take nuna mishi.
"Kiyi hakuri Waheedah..."
Kai Waheedah ta girgiza ma Yassar da takejin maganar shi kamar ya watsa mata ruwan zafi.
Shima kan yake girgiza mata yana saurin dorawa da
"Ba ina nufin kiyi hakuri da koma menene yai miki ba..."
Da mamaki Abdulkadir yake kallon Yassar
"Hamma?"
Ya kira, ko kallon shi Yassar baiba, asalima maganar da yakeyi yaci gaba
"Idan nan din zasu dameki ki tashi mu tafi gidana..."
Wani murmushi mai sauti Abdulkadir yayi da bashida alaqa da nishadi
"Kana magana kamar izinin fitarta yana hannun ka"
Zama Waheedah ta gyara tana daga Ikram ta mike, towel dinta ta zame ta sakata a bayanta.
Goya yarinyar tayi a bayanta.
Kamar yanda Yassar din ya fadi, tana bukatar hutu, bataso kowa ya dameta ko yayi kokarin bata hakuri, tana kuma da tabbacin Yassar bazai bar kowa yazo ya dameta ba.
Zata jira takardarta a gidan shi.
In yaso daga baya ta dawo gida.
Dan daman batayi niyyar zama bangarensu ba, balle Mami ta tambayeta meya faru.
Batasan ta inda zata fara ba, ya saukake mata shine abinda tafi bukata.
"Ina zakije?"
Abdulkadir ya bukata yana kallon ta cike da sabon mamaki
"Ka aikomun takarda ta gidan Hamma, ko kabama Abba, duk wanda yafi maka sauki dai"
Tai maganar tana kallon Yassar da fadin
"Hamma muje..."
Ta kama hannun Fajr, bai cika yawan magana ba, amman bai taba tunanin zai rasa abin cewa gabaki daya ba sai yanzun, dan ba kalaman shi bane kadai suka kubce mishi, harda abinda ya kamata yai tunanin da ya wuce tsananin mamaki.
"Waheedah tsinuwar mala'iku da duk takun da zakiyi batare da izinina ba..."
Ya tsinci kanshi da furtawa ganin ta saka kafarta daya wajen dakin.
Juyowa tayi da wani irin yanayi a fuskarta
"Tunda safiyar yau nake zubar da hawaye, kuma kaine sila, tsinuwar zatai balance Sadauki...
Ina jiran takardata"
Ta karasa tana ficewa daga dakin.
Wani murmushi Yassar yayi, tunda ya san yarinyar bai tana tunanin tana da kwarin gwiwar karbarma kanta 'yanci ba sai yau.