Sashe 60
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aure yayi, Nuriyya ya aura, ba wannan bane damuwar shi, bai fadama Waheedah ba, bai kuma san ta inda zai fara fada mata ba...!!!
#TeamWaheedah
#TeamAbdulKadir
#LubnaSufyan
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
BABBAN ASIRIN DA MUKE FAMA DA SHI A AL'UMMAN CE SHINE SON ZUCIYA.
LOKUTTA DA DAMA MUKAN DORA ALHAKIN ABUBUWA MASU YAWA AKAN KALMAR ASIRI DAN GUJEMA FUSKANTAR AINAHIN GASKIYA.
FOR ANTY FATINA (Batul Mamman) SonSo mai tarin yawa
Yakanji mutane na fadin gwiwoyin su sunyi sanyi, akwai lokutta da yawa da zaice ya taba jin irin yanayin, baisan asalin yanda yake ba sai yanzun da yake a bakin kofar gidan shi amman ya kasa shiga.
"Oh Allah na"
Ya tsinci kan shi da fadi ganin da gaske shine a tsaye bakin kofar gidan shi ya kasa shiga.
Lumshe idanuwan shi yayi yana bude su hadi da sauke numfashi, duk wani sauran karfi da yake jin ya rage mishi ya tattaro ya murda hannun kofar dashi.
Kafafuwan shi da yakeji kamar itace saboda nauyin da sukai mishi yaja yana shiga cikin gidan dayin sallamar da ta tsaya cikin makoshin shi.
Gyaran murya yayi yana sake yin sallama, amman duk da haka a hankali yaji muryar shi ta fito.
Dakyar yaja kafafuwan shi zuwa bedroom din su, ko sallama sai bayan ya tura ya shiga yayi ta.
Amsawa Waheedah tayi, tana jera kaya a wardrobe din dakin da take cikin bango.
"Takalma Sadauki...
Saboda kai bana sallah a tsakar daki saina saka darduma, ko ina shigarmun kake da takalma..."
Nan inda yake ya tsaya ya kwance igiyar takalman da suke kafarshi yana zame su tukunna ya karasa cikin dakin ya zauna kan gado.
"Sannu da aiki..."
Ya furta da wani irin sanyin murya da yasata barin abinda takeyi ta juyo tana kallon shi.
"Sadauki?"
Waheedah ta kira cike da alamun tambaya, dan yanayin shi gabaki daya ya bata tsoro, ganin bai dago ba, asalima sake sukunyar da kan shi yayi, yasa ta rufe wardrobe din tana karasawa ta zauna kusa dashi.
Kafadar shi ta dafa tana fadin
"Lafiya?
Me ya faru?
Menene?
Wani bashida lafiya a gida?"
Kai AbdulKadir yake girgizawa da duk tambayarta, amman ya kasa dagowa ya sauke idanuwan shi cikin nata.
A karo na farko da yake tir da gaggawa kan al'amura batare da tunani ba.
Saboda bai taba tunanin zaiji abinda yakeji din ba yanzun, ya rasa karfin gwiwar fuskantar Waheedah ya fada mata yayi aure, an daura mishi aure, matsalar shi ba gaya mata da wa aka daura mishi auren bace a yanzun, ta inda ma zai fara mata maganar auren.
Kan shi ya dora a kafadarta yana sauke wani irin numfashi
"Waheedah...."
Ya fadi cikin wani irin yanayi, hannunta ya kamo ya rike yana rasa kalaman da zaiyi amfani dasu.
Da Hajja bata mishi fushi sai ya kirata tazo ta taimaka mishi ta fadama Waheedah din, ko Yassar ma, wani dai ya fara fada mata dan shikam har wani zazzabin tashin hankali yakeji ya fara rufar mishi.
"Kana bani tsoro Sadauki...
Na kasa yarda komai lafiya"
Waheedah tace tana dumtsa hannun shi da yake cikin nata.
Idanuwan shi ya lumshe da maganganunta yanajin komai yai mishi tsaye cik.
Waheedah ce, Waheedahr shi.
Ta ina zai fara fada mata ya kara aure batare da saninta ba, sai yanzun tunanin ita ya kamata ta fara sani kafin kowa yazo mishi.
Dagowa yayi daga jikinta ya ja Kafafuwan shi kan gadon yana lankwashe su.
Numfashi ta sauke, tunda ya shigo gidan sai yanzun ya hada idanuwa da ita, duk da akwai wani abu da take gani tattare da yanayin fuskar shi da yasa zuciyarta yin rawa.
Fuskarta ya tallafa cikin hannuwan shi yana fadin
"Karki barni Waheedah, ki tabbatar mun da ba zaki barni ba"
Nata hannuwan ta dora kan nashi dake fuskarta
"Dan Allah ka gayamun me yake faruwa"
Ta karasa maganar idanuwanta na cikowa da hawaye dan gabaki daya ya tsoratata
"Wani waje mai hatsari zasu sake turamun kai ko?
Ka fadamun dan Allah..."
Cewar Waheedah muryarta na karyewa.
Wannan na cikin bangaren da tafi tsana a aikin shi, in duk aka turasu wajen da ake hatsaniya, tare da kwanciyar hankalinta yake tafiya, wayar duk da zataji sai gabanta yai wata irin faduwa, idan tayi sati daya bataji shi ba, ko baccin kirki batayi.
Tana da tabbacin matan sojoji tare suke raba duk wani tashin hankali dake cikin aikin mazajen su.
Mata da yawa nason auren sojoji, ita AbdulKadir take so, in da tana da yanda zatayi da baizo mata a soja ba.
Tashin hankalin dake cikin aikin shi yana da yawa.
Kai ya girgiza mata, muryarshi can kasan makoshi yace
"Babu inda aka turani, kawai ina son jin ba zaki barni ba"
Murmushin karfin hali tayi badan zuciyarta ta nutsu ba, amman shi dinma bata ganin nutsuwa a tattare dashi, bata so ya koma wajen aiki a haka.
"Ka taba ganin mata tabar mijinta?
Ina zanje nikam...ina tare da kai daga yanzun har sauran kwanakin da Allah ya aramun"
Numfashi AbdulKadir ya sauke yana barin kalamanta na samun wajen zama a kasan zuciyarshi.
Yakai mintina biyu tukunna ya saki fuskarta yana mikewa, bandaki ya shiga ya watsa ruwa, amman ko kadan baiji wani sauki ba, hankalin shi yakeji yaki kwanciya, ga wani bangare na zuciyarshi da yake azalzalar shi ya fadama Waheedah din kawai ya huta, amman ya kasa samun karfin gwiwar fada mata, baisan ta inda zai fara ba.
Kwanciya sukayi, Waheedah na jikin shi, ko kadan bacci ya kaurace ma idanuwan shi, ya rasa abinda yake mishi dadi a duniya, karfe hudu ya mike ya karayin wanka, shiya hada kayanshi, ya rasa karfin zuciyar tashin Waheedah din, kai kawon da yakeyi da motsin shi da yai yawa shiya tasheta.
Fuskarta kawai ta wanke tayi brush ta wuce kitchen tana fara fere dankalin turawa, iya wanda AbdulKadir din zaici ta soya.
Kafin biyar harta gama komai yaci, tana kula da yanda yake komai da wani irin sanyi da yake taba mata zuciya.
Kafin asuba yake fita daman, Yassar ne yake zuwa yana sauke shi tasha.
Amman yau kwata-kwatsa AbdulKadir din bai tsammaci zai zo ba, har saida yaji karar shigowar mota tukunna.
Jakarshi ya rataya Waheedah na rakashi har bakin kofa, ta kasa sabawa har yanzun, duk randa zai tafi sai tayi kuka.
Yanzun ma idanuwan ta cike suke da hawaye, muryarta na rawa tace
"Allah ya tsare mun kai a duk inda zaka shiga.
Ka kula da kanka dan Allah..."
Kai AbdulKadir din ya daga mata yana rungumeta a jikin shi, saman kanta ya sumbata da gefen fuskarta, tukunna ya dago ta daga jikin shi
"Zanyi kokari in dawo wata na gaba in shaa Allah.
Ki kulamun da kanku..."
Sake rungumeshi tayi tanajin kamar karya tafi.
Dakyar ta iya raba jikinta da nashi, tana sa hannunta ta share kwallar data tarar mata.
Shi kanshi yanajin barin nata, da son samun shine duk inda zaije da ita zai tafi.
Amman ya fahimce ta data fada mishi Fajr na bukatar samun ilimin addini mai inganci, zaman Lagos ba nata bane da yara, tafiso ta natsu waje daya.
Shisa ma ya dawo da ita Kanon, tunda shima wani lokaci aiki na dauke shi watanni, duk inda yakaita in hakan ya faru ita kadai zata zauna.
Gara a gida inda yasan tana zagaye da yan uwa.
Sai da ya sake sumbatarta tukunna ya fice daga gidan yanajin yau ba wani bangaren shi ya bari ba, harda wani irin nauyi mai girman gaske da rashin gaya mata maganar auren shi, tunda ta tashi yake motsa bakin shi, kalamai ne sukaqi fitowa.
Abba ya kamata ya tambaya ta inda zai fara tunda shi yayi hakan har sau uku.
Zaifi kowa sanin kalaman daya dace yayi amfani dasu, amman Abba fushi yake mishi, tunda bai kirashi yau ya mishi Allah ya tsare ba.
Wajen motar Yassar din ya karasa ya bude ya shiga yana fadin
"Hamma ina kwana..."
Inda yake Yassar bai kalla ba yaja motar yana fita daga gidan.
Numfashi AbdulKadir ya sauke
"Kai ma fushin kakeyi kenan har yau...
Ni banyi fushi na Hamma kaine kakeyi...
Ok"
AbdulKadir ya karasa maganar yana sauke wani numfashin
"Da Kawu Ali mukaje jiya...
An daura auren tun jiya...
Ban fadama Waheedah ba, Hamma na kasa fada mata, tunanin bai zo mun ba sam sai bayan an daura auren.
Ya kamata in fada mata..."
Katse shi Yassar yayi da cewa
"Wallahi, Wallahi idan kaci gaba da magana zan saukeka ka nemi abinda zai kaika tasha ko ka taka da kafa bai dameni ba.
Allah kadai yasan yanda nakai zuciyata nesa na fito...
Kayi abinda kake so, wannan matsalarka ce, tun jiya ka rigada ka nuna mun banda matsala da aurenka.
Kabar shi a haka kawai, bana son jin duk wani abu daya shafi tsakanin ka da Nuriyya, yanzun, anjima, gobe, kai har iya zaman rayuwar aurenku idan kana son zaman lafiya dani ba zaka kawomun zancen ta ba"
Muryar Yassar din ta tabbatar ma da AbdulKadir yana nufin dukkan kalaman daya fada, daga zuciyarshi yai maganar.
A karo na farko da yaji bayason kure hakurin Yassar din.
Shiru yayi, yana kara jin komai ya hade mishi waje daya.
Wayarshi ya laluba yana ganin text din Nuriyya.
Mayar da ita yayi ya ajiye, itama baisan me zaice mata din ba, baisan me zaicewa kowa ba.
A bakin tashar unguwa uku Yassar ya sauke AbdulKadir din yana fadin
"Allah ya tsare..."
Yaja motar shi ya wuce, da gaske fushi Yassar yake mishi, dan yakan samu waje yai parking, baya tafiya sai yaga AbdulKadir din ya shiga mota suna shirin tashi tukunna.
Wani irin numfashi AbdulKadir yaja yana fitar dashi a wahalce, zai karya idan yace ranshi bai sosu ba, amman Waheedah ta danne duk wani abu da yakeji yau.
Zai bi takan sauran al'amura idan ya samu hanyar fada mata ya kara aure.
Inda Baba ya fita yabarta, nan ya dawo ya sameta, badan bataso ta tashin ba, sai dan tanajin tsoron tashi ta farka daga mafarkin da takeyi na cewar AbdulKadir yazo neman aurenta wajen Baba.
Magana ce da takejin ta kamar almara.