Sashe 5
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tabe baki tadan yi
"Allah ya bada lafiya..."
Ta fadi da wani yanayi a muryar ta da tasa Abdulkadir mikewa
"Me kikayi yanzun?"
Ya bukata muryar shi can kasan makoshi, ware mishi idanuwa Nuriyya tayi
"Me nayi nikuma?"
Hannun ta ya damqo yana janta kamar bata da wani nauyi zuwa gab dashi
"Abinda kikayi da bakin ki yanzun nake nufi"
Wani irin yawu Nuriyya ta hadiya, tasan halin shi, tun kafin dan zaman nan na auratayya ya hadasu, tunda kusan fiye da rabin rayuwarta a gidan su tayi ta, ta kuma san raini na daya daga cikin abinda baya dauka ko daga wajen yayyen shi, iyaye ne kawai Abdulkadir yake dagama kafa, sai dai ita din takan mishi abubuwa da yawa sai dai ya kalleta ya wuce, sosai ta shagwabe mishi fuska tana matsawa hadi da shigewa jikin shi.
"Yunwa nake ji Masoyi...dan Allah karkai mun fada...
Ni banyi komai ba, addu'a nai mata"
Yanda ta narke mishi yasa shi sauke numfashi, a hankali ya janye ta daga jikin nashi, yana dafe kan shi da hannu.
'Karka fita baka saukemun auren ka ba'
Maganganun Waheedah ne suke ta dawo mishi.
Tsintar kan shi yayi da saukowa daga kan gadon, asibitin yake son komawa ya tabbatar da bata samu matsala a kwakwalwar ta ba, bayajin zai samu wata nutsuwa in bai tabbatar ba
"Ina zaka je?"
Nuriyya ta bukata
"Zan koma asibitin ne"
Ya amsa ta, yana jiran yaji ko zata ce mishi su tafi tare ta duba jikin Waheedah din.
Baisan wani abu taji ya taso mata tun daga kirjinta har cikin wuyanta yana mata tsaye ba.
Bata son nuna mishi kishin da taji, dan haka tace
"Zaka dawo da wuri?
Kayo mun take away dan Allah..."
Kallon ta Abdulkadir yakeyi
"Me yake damun ki Nuriyya?"
Itama kallon shi takeyi
"Bangane me yake damuna ba, kar ince ka taho mun da take away idan zaka dawo da wuri?
Jikina yamun nauyi bazan iya girki bane shisa, kuma laifinka ne daka qi dauko mun yar aiki..."
Kai Abdulkadir yake girgizawa
"She was your BestFriend (Aminiyarki ce a baya)..."
Ya furta a hankali, yana mamakin Nuriyya din, yanda yake kallon ta yasa ta cire earpiece din daga kunnuwanta tana ture system din, saukowa tayi daga kan gadon tana takawa ta karasa inda take, ba zaka kirata gajerar mace ba, amman tsayin Abdulkadir na kwatance ne, ga girman da yake dashi kasancewar baya wasa da motsa jiki, sai ta ganta yar karama a gaban shi, matsawa tayi tana riko hannun shi, hadi da daga kanta tana sauke idanuwan ta cikin nashi.
"Masoyi yau kam laifina kake ta gani, bansan me nai maka ba"
Ta karasa maganar tana tattaro hawaye dakyar ta cika idanuwan ta dashi
"Karki mun kuka Nuriyya...
Karki mun kuka"
Dayan hannunta ta saka tana share kwallar data taru a gefen idanuwan ta
"Bansan me nayi maka ba..."
Yanda tai maganar cike da rauni ya taba shi, numfashi ya sauke, baisan me yake damun shi ba yau.
Ganin ya fara saukowa a fuskar shi kawai yasa Nuriyya dora kanta a kirjin shi tana sakin wani guntun murmushin da take da tabbacin baya gani, batasan meya faru ba yau, idan zatai fada dashi Waheedah ba zata zama sanadin hakan ba, yaune karo na farko daya jefeta da kalmar alaqar dake tsakaninta da Waheedah a baya, ba zata bari hakan ya faru ba, tana sane sarai saboda ba tace zataje duba Waheedah din bane.
"Kome nayi kaina a kasa Masoyi...kar a sauke sojan a kaina yau...
Umm?"
Tai maganar tana kara narkewa a jikin shi, dagota yayi yana sumbatar gefen fuskarta batare da yace komai ba ya juya yana ficewa daga dakin, bin bayan shi tayi tana leqawa ta tabbatar da yayi nisa tukunna ta dawo dakin tana turawa hadi da fadin
"Ni na dora mata ciwon...
Yanzun haka karya take...
Bansan yaushe Waheedah ta koyi munafunci da bakin hali ba..."
Da kan gadon zata koma taci gaba da kallon da take, sai kuma ta fasa saboda cikin ta dayai wata irin murdawa da yunwa.
Babu shiri ta koma tana ficewa daga dakin, kitchen din ta ta nufa, a dispenser ta dibi ruwan zafi ta hada shayi, kwalin biscuit ta dauka tana wucewa ta koma daki, ta kasa daina zagin Waheedah a cikin zuciyar ta, yau da safe Abdulkadir din ya koma bangaren ta, shisa ta zauna tana kallon film din ta a system dan kartai tunanin yanda Waheedah take manne dashi kamar mayya, yanzun ma ba zata bari tunanin Waheedah ya bata mata rai ba, hakan take maimaitawa kanta harta samu wajen zama tana gyara system din ta dauki earpiece din ta mayar a kunnuwanta ta kunna film din, tukunna ta dauki kofin shayin data ajiye tana janyo biscuit din gabanta.
A hanyar shi na zuwa asibitin yaga Apple, dan harya wuce yayi parking yana fita daga motar ya taka da kafar shi zuwa wajen masu Apple din, hannu ya saka a aljihunshi duk da yasan bai zuba kudi ba, amman Waheedah ta dauko mishi wandon, yana da tabbacin duk wani abu dazai bukata tasa a ciki, akwai kudin kuwa, biya yayi ya karbi ledar yana komawa mota.
Zai iya rantsewa da Allah duk idan ya dawo gida ya ganta, yakan manta yanda yake iya yin komai batare da ita a kusa dashi ba.
Dayan aljihun yakai hannu ya laluba yaji I.D cards din shi na ciki yana kuma da tabbacin har da ATMs din shi duk suna ciki.
Sai da ya sauke wani numfashi da baisan yana rike dashi ba tukunna yaja motar yana nufar asibitin.
Parking din motar shi yayi a inda akeyi yana takawa zuwa cikin asibitin, hannun shi rike da ledar Apple din daya siya, indan tashi ba za'a ci Apple ba, dan yana cikin kayan marmarin da baya kan shi sam-sam.
Zama da Waheedah ya sashi koyan ci, duk da haka badan yana jin dadin shi ba, duk idan ta yayyanka yanda takan yi ta miqo mishi bayaqin dauka, ko idan tana ci, data gutsura take miqa mishi shima ya gutsura saita sake karba, ko ruwa zata sha saita bashi shima.
Baya tunanin Waheedah na iya cin wani abin yana zaune ko yaci nashi bata bashi ba.
Sosai yake shiga cikin asibitin harya karasa bangaren da Waheedah din take, dan sun kama dakin da ita kadai ce, kan shi tsaye ya nufi dakin da yake lamba ta sha biyu, kwankwasawa yayi hadi da murza hannun kofar ya shiga batare daya jira an bashi izinin ba.
Baiga kowa a dakin ba sai Anty, da sallama ya karasa ta amsa shi a sanyaye.
Ledar Apple din ya ajiye a gefe kan abinda akan ajiye kayayyaki, tukunna ya kalli Anty da take zaune tana goye da Ikram yana fadin
"Ke kadai?
Ya jikin nata?"
Cikin sanyin murya ta amsa shi da
"Sun koma gida, ba'a son hayaniya ne ko kadan, saboda jininta yayi wani irin hawa.
Abdulkadir me yake faruwa?"
Kujera ya janyo yana samun waje ya zauna, fuskar shi da bata cika fara'a ba ya sake hadewa waje daya.
Tambaya na daya daga cikin abubuwan da bayaso, musamman wadda ta shafi matsalar iyalin shi.
"Tambayar ka nake, me yake faruwa?"
A daqile yace
"Tsakanin mune...
Komai zaiyi dai-dai..."
Sakin baki Anty tayi, na dan lokaci ta manta waye Abdulkadir, yanzun yake tuna mata.
"Tsakanin kune take rokon mu da mu karbar mata takardar saki a hannun ka?"
Dago da kan shi yayi yana kallon Anty
"Kaman yanda nace, tsakanin mune.
Anty karki wuce hurumin ki dan Allah"
Ya karasa yana mayar da kallon shi kan Waheedah da take bacci, hannun ta da yake daure da ruwa ya kama yana gyara mata zaman shi, baibi takan Anty da take kallon shi ba, rashin kunya ce Abdulkadir ya saba batun yanzun ba, batasan me yasa tai tunanin iyalin daya fara tarawa zasu saka halayyar shi canzawa ba.
Bata sake cewa komai ba, tasan halin rashin hakurin ta, kaca-kaca zasuyi ita dashi a asibitin nan, dan bakinta bazai shiru ba, Abdulkadir kuma ba zaiqi datsa mata duk maganar data fito daga bakin shi ba.
Yanke hukuncin tashi ta koma wajen dakin tayi, idan ya gama zaman shi ya fita ta dawo.
Yana jin bude kofar ta da rufewa, juya idanuwan shi yayi, yana kara matsawa kusa da Waheedah sosai, sam bayason baqar tambaya, baiga meya shafi Antyn da matsalar gidan shi ba, dayan hannun Waheedah ya kama yana zagayo dashi takan cikin ta hadi da riqewa.
"Wahee kinga me kika ja mana ko?"
Ya furta a hankali, yanzun yake kara samun tabbas akan ba cikin hayyacinta ta furta mishi kalaman dazun ba.
Numfashi ya sake saukewa, sosai ya ja kujerar yana kwantar da kan shi a cikinta, kan kuncin shi haggu ya kwanta yanda zai iya kallon fuskarta, har lokacin dayan hannun shi na cikin nata.
Wani numfashin mai nauyi ya sake ja yana fitarwa hadi da lumshe idanuwan shi.
Babu tunanin komai cikin kan shi, kallon ta yake wata irin nutsuwa na saukar mishi, a hakan bacci mai karfi ya dauke shi shima.
Kan ta takejin kamar an dora mata katon dutse, idanuwan ta dakyar ta iya daga su, nauyi taji saman cikin ta, a zaton ta Fajr ne, dan haka yakanyi mata, komin baccin da takeyi zata jishi yazo ya kwanta a jikin ta, bazai taba kwanciya kan katifa ba, ko ta sauke shi daya farka yake sake koma kan jikin ta ya kwanta.
Hannu takai tana dorawa kan cikin ta inda take jin nauyin, zata rantse dumin shi ya banbanta dana sauran mutane.
Dan dago kanta tayi, shi dinne ba magagin bacci takeyi ba.
Hannu takai tana murza kirjinta inda take jin yana mata wani irin ciwo.
A hankali komai yake dawo mata, hannu takai da nufin tashin shi ya furta mata abinda take son ji, saita tsinci kanta da kasa yanke mishi baccin nashi, tunda tasan bako da yaushe yake samu ba, duk da yazo hutune bayan shekara biyu sai yanzun ya sami hutu mai dan tsayi.
Kallon shi take, zuciyarta a dunqule waje daya take jinta, shisa bata motsa mata da duk wata kaunar Abdulkadir din.