← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 94

Sashe 91

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakin Hajja ya sake komawa yai kwanciyar shi.

Tana shigowa tagan shi tace
"Wai kai AbdulKadir ba zaka tashi ka tafi gidan ka ba?"
Sake juya kwanciya yayi
"Yanzun Hajja dan nayi aure shikenan bazan zo gida duk sanda nake so in kwanta in huta ba?"
Ya karashe maganar kamar zaiyi kuka, dan baiga dalilin da zaisa Hajja ta dinga korar shi shida gidan Abban shi ba, amman da Waheedah tazo babu wanda yace ta koma sai da yazo ya dinga binta yana bata hakuri
"Idan kuma yaji nayo fa?

Sai ki koreni kice in koma?"
Dariya Hajja take da AbdulKadir din baiga dalilinta ba, dan shi da dukkan gaskiyar shi yake maganar da yakeyi din.

"Allah ya shiryamun kai AbdulKadir"
Hajja ta fadi har lokacin tana dariya ta fice daga dakin, sai da yagaji da kwanciyar tukunna ya fito zuwa falon yana zama Fajr na shigowa da nama a hannun shi yanaci
"Paapi kaga, Mami tabani"
Ya karasa maganar yana zuwa ya zauna a jikin AbdulKadir din
"Mami ta kyauta, ka gode"
Sake shigewa jikin AbdulKadir din Fajr yayi yana kwanciya sosai, yana sa AbdulKadir din fadin
"Kaifa ka cika son jiki Fajr, baka azumi zaka bini ka danne"
Baisan inda yaron ya koyi son jiki ba, gashi dan mitsitsi dashi abinda yake so shi zaiyi, maganar shi ba zata sa Fajr din ya sauka daga jikin shi ba, sai dai in dukan shi zaiyi.

Amman wani ido ko magana ba ko yaushe suke tasiri akan Fajr ba, baisan inda ya kwaso halayen nan ba, dan shi ba haka yake ba.

Anan ya zauna har aka kira sallah, dabino da kankana ya dan sha yayi alwala, Fajr na rigimar sai ya bishi
"Ka tafi dashi mana"
Cewar Hajja
"Baiga takalmin shi daya ba, har anyi raka'a daya"
AbdulKadir ya fadi yana zame hannun Fajr din daga cikin nashi, yaron na bude baki ya fara kuka, wani irin mari Abdul ya dauke shi dashi da yasa Hajja fitowa daga kitchen ta kama Fajr din
"AbdulKadir baka da hankali?

Wannan ai sai ka ji mishi ciwo"
Ta karasa tana daukar Fajr da jikin shi ko ina ke bari, yama kasa fitar da sautin kuka.

Ficewa daga gidan AbdulKadir yayi dan baida amsar ba Hajja, bayason kukan banza marar dalili, Fajr ya cika rigima har ta banza, inda Hajja tasan dukan da yake sha da ba zatai magana dan ya mare shi ba.

Daya dawo masallaci ma ruwan shayi kawai ya iya sha, dan ko yunwar ma bayaji, tukunna yaima Hajja sallama ya sake ficewa ya shiga motar shi yana nufar gida.

Ba zatace ga iya lokacin da ta dauka a kofar gidan ba, zafin ranar da ake kwallawa shi yasa ta yanke hukuncin takawa zuwa bakin hanya ta tare wata napep din ta shiga zuwa gidan su.

Lokaci zuwa lokaci take saka hannu tana share kwallar dake zubo mata.

Bayan kayanta da aka gudu dasu, tasan akwai wani abin da yake nuqurqusarta da bata son tsawaita tunani a kai.

Dari biyu ta ba mai adaidaita sahun tana wucewa ta shiga gida da sallamar da Mama ta amsa mata.

Tana zaune kan kujera a kofar daki tana tsintar shinkafa.

"Ki dauko tabarma mana"
Mama tace mata ganin Nuriyya din na shirin zama kasa kan siminti, batayi musu ba ta shiga daki ta dauko tabarma tazo ta shimfida.

Gaisawa sukayi, Mama taci gaba da tsintar shinkafarta batare da ta ko kalli inda Nuriyyar take ba, ballantana kuma tace mata wani abu.

Gabaki daya jikinta Nuriyya taji ya kara mutuwa, wasu sabbin hawayen na kara zubo mata da ba zatace ga dalilinsu ba.

"Mama ya sakeni, AbdulKadir ya sakeni"
Ta furta wani abu na tasowa daga dan yatsan kafarta yana zuwa kirjinta ya samu wajen zama.

Sosai yanzun abinda hakan yake nufi ke zauna mata, ga yunwar azumin dake bakinta data fara kulle mata ciki, ga shinkafar da taga Mamar na tsinta ta kuma tabbar da ita dince abincin buda bakinsu, sai dan kunu da kosai da ba kullum ake samu ba.

Da yanzun tana daki a kwance da fanka in sun kawo wuta, komin ta lalace kuma akwai nama a fridge dinta, ko soyawa zata iya yi.

Watanta kusan tara rabonta da shinkafar hausa.

"Allah ya rufa asiri ya kyauta"
Mama ta fadi tana mikewa da farantinta takai dan karamin kitchen din gidan ta ajiye.

Itacen ta iza tana bude waken taga ko alamar dahuwa baiyi ba, shisa ta dora shi da wuri inta dafa saita ajiye.

Anjima ruwa zata kara daya tafaso ta zuba shinkafa.

Badan tayiwa auren Nuriyya da AbdulKadir din baki ba, amman har a kasan ranta taji alamun babu inda zaije, ko badan auren cin amana bane, Nuriyya na da son zuciya da son abin duniya da in batai wasa ba zai hanata zaman aure, dan zata cigaba da gina aurenta akan hakan, duk namijin daya gane kuwa da wahalar gaske yaci gaba da zama da ita.

Hidimarta Mama ta karasa ta shige daki tana barin Nuriyya anan zaune, ganin hakan yasa itama ta tashi tana komawa dakinta na da, yana nan yanda yake babu abinda ya canza, banda yan kayan sawa da aka ajiye.

Ta kuma san na Mama ne, tunda ita bata da yara mata, nata duk mazane, dakin su kuma daban yake.

Jakarta ta ajiye ta samu waje kan katifa tana kwanciya, a jikinta take jin banbancin katifar da ta gidan AbdulKadir.

Wasu sabbin hawayen na sake silalo mata, musamman da tunanin Waheedah nacan kwance a daki tana jin dadin tabar mata gidan, sai taji wani malolon bakin ciki ya taso mata kamar zata hadiyi zuciya ta mutu ta huta.

Kafin yamma wani zazzabin tashin hankali ya rufe ta, banda tsinuwa da fatan tifa ta take mai napep din da yai mata dibar albarka babu abinda takeyi.

Ga kuma tashin hankalin abinda zai faru idan Baba ya dawo gidan ya ganta, dan sosai kashedin shi yake dawo mata.

Ita kam bataga inda zata fara zuwa ba a yanzun, bata da wani waje daya wuce nan din, haka ta wuni juye-juye.

Ta kulla ta saka, hadi da addu'o'i kala-kala, cikin su harda na samun mijin da yafi AbdulKadir komai tana gama iddarta tayi aure inda zata huta ta shakata, amman tasan hakan bazai yiwu babu suttura ba.

Ta yanke hukuncin siyar da duka kayan kitchen dinta, ta siyi kaya saita ajiye sauran kudin tana kashewa a hankali kafin ta samu garan da zata wanka.

Wannan tunanin shiya nutsar da ita har aka kira sallar Magriba, tukunna ta fito daga dakin tayi alwala tana sake komawa, sanda ta idar da sallah, Mama ta kawo mata kunu da kosai da taketa jin kamshin shi tana kwance, hakan ya tabbatar mata da ba siyowa akayi ba, Mama ta soya da kanta.

Ci tayi dan ya mata dadi sosai, rabon da taci abu mai nutsuwar wannan tun girkin Waheedah.

Tas ta shanye kunun ma da yasha kayan kamshi ta samu waje ta zauna, wata nutsuwa da koshine kadai ke samar da ita na saukar mata.

Tanajin sallamar Baba taji hanjin cikinta ya hautsina, komai ya tsaya mata.

Tashi zaune tayi, daman dakin fitilar wayarta ce ta haska, itama kashewa tayi, tai zaune cikin duhun tanajin zazzabinta ya dawo sabo.

Ba zatace ga iya lokacin da ta dauka a dakin ba kafin taji Baba na fadin
"Auren ta kaso?

Shine kika barta ta zauna mun a gida?

Ban gaya mata ta nemi wani wajen ba?"
Baba ya karasa maganar yana daga labulen dakin da Nuriyyar take ciki
"Fito....aina fada miki idan kika kaso auren nan ki nemi wani wajen, na fada miki bazan kaffarar rantsuwa ta ba"
Wani irin kuka Nuriyya take tunda Baba ya fara magana.

Mama ce ta kama labulen daga hannun shi tana saukewa da fadin
"Aikam hakuri zakayi kai azumin kaffara saboda babu inda zataje"
Da matukar mamaki Baba yake kallon Mama, kai ta daga mishi, dan sosai iyaye suke wannan kuskuren, tasan bacin rai abune da ba'a iya guje mishi idan yazo.

Amman bataga dalilin da zaisa iyaye su gindaya sharadi kan cewar idan yara suka tsallake su nemi wasu iyayen ko kuma su bar musu gida ba.

Akwai dalilin da yasa Allah ya zabi ya basu amanar yaran, batace babu hakkin iyaye akan yaransu ba, amman akwai hakkin yara akan iyaye suma.

Amana ce mai wahalar rikewa, amana ce da rikonta yake cike da kalubale kala-kala.

Amman korar yara daga gida da nufin son su gane kuskurensu ba hanyar gyara bace ba, lokutta da dama hakan baya janyo komai banda kara lalacewar su, ga fushin iyaye da ko basu koresu ba zaici gaba da bibiyarsu har sai lokacin da suka furta sun yafe ko suka kudurta a ransu, ga tangaririya a filin duniya batare da tudun dafawa ba.

Ba mata kadai hakan yake faruwa dasu ba, ha
r mazan, da yawa in basu fada sace-sace dan su sami abin ciyar da kansu ba, zasu fara shaye-shaye dan rage damuwa, da duk wani abinki da zai iya fin wanda yai sanadin korar su daga gida muni.

Akwai kaddarar da take tafiya da son zuciya, kamar ta Nuriyya, halin da take ciki laifinta ne, amman hakan baya nufin ba kaddararta bace ba.

Da yawan mutanen da zasu zageta idan sunji halayenta marassa kyau su kansu basu wuce jaranta da irin kaddararta ba, bata saka musu baki a cikin al'amuran su, amman tana da yara, duk da maza ne, ba za'a hadu da ita ayi wannan kuskuren da Baba yake shirin yi ba
"Ina kake so taje?

Idan tabar gidan nan ina kake so taje?

Bazan maka magana akan cewa hannunka baya rubewa ka yanke ka yarda ba, saboda ban taba yarda da wannan kalaman ba, lokacin da azaba zata isheka, idan baka roki wani ya yanke maka ba, zaka sami wuka ka yanke da kanka, neman sauki abune mai ban mamaki"
Cewar Mama tana dorawa da
"Amman nasan yara amana ne a wajen iyayen su, nasan idan tasa kafa ta fita daga gidan nan ka gaza a rikon wannan amanar.
Chapter 91 · 0% Book details