← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 94

Sashe 77

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Waheedah na tsaye tana kallon shi, yanda yakeyi kamar shi yayi watanni da ciwon da tayi fama da shi, a karo na farko halin da yake ciki bai taba zuciyarta ba, tana jin dadin yanda yake jin kadan cikin quncin da zuciyarta take fama dashi
"Kirjin ka kamar zai bude ko Sadauki?"
Ta bukata cikin wani irin sanyi murya da yasa AbdulKadir daga idanuwan shi da har sun canza launi yana kallon ta, rausayar da kai tayi
"Haka nake ji duk idan naganka tare da Nuriyya..."
Mikewa AbdulKadir yayi yana karasa inda Waheedah take, hannuwan shi yasa ya kama kafadunta yana dan dannawa cikin alamun ta zauna, batayi mishi musu ba tayi kasa tana zama kan kafet din dakin, shima zaman yayi a gefenta, dan dakin ya fara jujjuya mishi da jirin tashin hankali.

Idan taci gaba da magana baisan inda zai saka rayuwar shi ba, ya bude bakin shi ya kai sau biyar amman ya kasa furta komai.

Sai da yaja numfashi yana fitar dashi, kafin ya iya cewa
"Waheedah..."
Kalmar na fitowa daga wani sashi na zuciyar shi da yau dinne ranar farko daya san da zaman shi, runtsa idanuwan shi yayi yana bude su, cikin kan shi yake ji babu komai, baisan ko yanajin alamun kwakwalwa ba a baya, amman a yanzun bayajin komai sai kokon kan, balle yayi tunanin kwakwalwar shi zata taimaka mishi da wasu kalamai, amman kirjin shi ciwo yake kamar zai bude, da gaskiyar zancen Waheedah, bai gane yanda zai fassara abinda yakeji ba sai da ta fada, kan shi babu komai, amman zuciyar shi cike take fam da yanayoyi daban-daban, bude bakin shi yayi yana barin zuciyar shi ta mulki abin zai fito daga bakin shi
"Ina da son kai, ban taba sanin ina da son kai ba sai yau, kina da rashin adalci..."
AbdulKadir ya karasa maganar cikin muryar da ta dira kunnuwanshi kamar ta wanda yasha gudu, yana saka kwayar idanuwan shi cikin na Waheedah da take ware mishi nata cike da maiqon hawaye, kai ya daga mata a hankali
"Me yasa baki fadamun ba?

Me yasa baki fadamun ba Wahee?

Kince kina sona, ni nagani kina sona, me yasa kika boyemun?"
Kai Waheedah take girgiza mishi, idanuwan ta na tsiyayo wasu hawaye masu dumi, ba zai mata haka ba, ba zata bar shi ya dora mata laifin da bata da shi ba
"Me yasa ka boyemun za kai aure?

Ka boyemun kayi aure har wata daya?

Ka boyemun Kawata ka aura sai da ka shigomun da ita cikin gida?"
Jinjina kai AbdulKadir yayi, kalamanta duka suna dirar mishi kamar zubar ruwan gishiri a sabbin ciwukan da kalamanta na baya sukai mishi, yasan tana da muhimmancin a rayuwar shi fiye da yanda zai misalta da kalamai, bai dai san a tattare da muhimmanci akwai iko akan abubuwa da yawa da suka shafe shi ba, ciki harda zaman lafiyar shi, kwanciyar hankalin shi, nutsuwar shi gabaki dayan ta
"Hakane..."
AbdulKadir ya iya furtawa yana kallonta da wani nisantaccen yanayi, muryar shi yakeji na fitowa da wani sauti da baida fasali
"Ba uzurin da ya sani yin abinda nayi nake so in baki a kurarren lokaci irin yanzun ba..."
Ya fadi yana maida numfashi kafin yace
"Banda komai, ko kalaman ban hakuri bani dasu, wallahi banda kalaman baki hakuri"
Dan har zuciyar shi yakejin hakuri yayi kadan ya wanke girman laifin da yayi mata
"Shisa zan baki wani abu daban, zan baki dukkan gaskiyata, ban san zanyi aure ba, lokaci daya tunanin ya zo mun..."
Kai Waheedah take girgiza mishi, bata son ji, bata son jin yanda yayi aure, tunda ya rigada yayi, shima kan yake girgiza mata
"Za kijini, ba zaki yanke mun hukunci gabaki daya ba, kimun adalcin da ban miki ba dan Allah, na rokeki"
Cikin rawar murya data fito cike da sautin kuka Waheedah take girgiza mishi kai
"Son kai Sadauki, son kai ne wannan"
Kafada yadan daga mata, ita hawayenta sun zuba, ance kana samun sauki duk idan ka zubar da su, shi bai samu wannan zabin ba
"Nasani, halina ne daman..."
Cewar AbdulKadir din yana dorawa da
"Da sanin zanyi auren da auren duka a kwana biyu ya faru, na samu awanni 48 da zan dauki mintina talatin in fada miki zanyi auren, banyi ba, kuskurena ne wannan da zai zauna dani har karshen rayuwata..."
Hannunta ya kamo yana hada yatsunsu waje daya, yanajin yanda ta dumtse nashi cike da neman alfarmar da ba zai iya mata ba, idan bai fada mata na shi bangaren ba, yana da tabbacin kirjin shi budewa zaiyi
"Amman ni ne, bana tunani, ban fara tunani ba sai bayan nayi auren, na kasa fada miki, banji maganar su Hajja da suka fadamun akwai rashin kyautawa a abinda nayi ba saboda ina ganin addini ya halarta mun, banyi tunanin ke yanda zakiji ba har lokacin, nayi tunanin ban kyauta ba da ban fada miki ba, kin san me yasa?"
Kai ta girgiza mishi a hankali, akwai yanayin da yake tattare da muryar shi da bai hana gwiwoyinta yin sanyi ba duk da a zaune take
"Saboda ban saba boye miki abu ba, lokacin ya kamata in san ban kyauta ba..."
Wannan karin ajiyar zuciya mai nauyin gaske ya sauke
"Ina miki maganar Nuriyya ne saboda kece, badan na raina ki ba Wahee, ba dan in nuna miki na isa ba, Wallahi babu ko daya a ciki, ki yarda dani..."
Ya karasa maganar muryar shi na karyewa, kafin ya ci gaba da fadin
"Ina fada miki ne saboda ke ce"
Ya sake maimaitawa kamar 'Ke ce' din ta isa ta fassara mata abinda yake nufi, shi kuma kalaman da zaiyi amfani dasu dan ta fahimta yake nema
"Tun ban san zan aureki ba kike sanin abubuwa a kaina da ba kowa ne yake sa
ni ba, saboda ke ce, ke kadai kikejin maganata idan raina yana bace, saboda ke ce, su Hajja na so na, amman basa son da yawa cikin halayena, suna magana a kai, baki taba ba, kina so na da komai nawa, shisa nabari kika sanni yanda kowa bai sanni ba"
Idanuwanta Waheedah ta runtsa tana kokarin hadiye yawu ko zai wuce mata da abinda take jin ya tsaya mata a kirji, shagwabe mata fuska AbdulKadir yayi cikin yanayin da bata taba gani ba, sai da taji zuciyarta ta doka da tunanin ko kuka zaiyi
"Ban miki maganarta dan in sosa ranki ba, na miki maganarta saboda komai nawa ina fada miki, banyi tunanin kishin da zakiji ba, saboda ina son kai na da yawa, wannan ma kuskurena ne...

Auren kawar ki"
AbdulKadir ya karashe maganar yana runtsa ido kamar kalaman nashi sun raunani shi, kafin ya bude su yana ci gaba da fadin
"Wahee ina so ince ki yafe mun, amman ina jin hakan ma zai kara zama rashin adalci..."
Kai ta daga mishi tana tabbatar mishi da ta yarda da kalaman shi, hawayen da suka zubo mata na kara tafasa shi, numfashi ya sauke yana dago hannun su da yake hade yakai kan goshin shi, ya lumshe idanuwan shi yana kara sauke numfashi mai nauyi, duniyar ta mishi tsaye waje daya, yakai mintina biyu a haka, kafin ya iya dago da kan shi
"Son kai halina ne, shisa zan fada miki ba zan iya rabuwa da ke ba....Wallahi ba zan iya ba, da tunanin aikina zaiyi sanadiyyar mutuwata nake kwana nake tashi kullum, cikin sati daya kin nuna mun kinfi aikina wannan hadarin, Wahee zaki kasheni in kika barni...."
AbdulKadir yake fadi a susuce, babu komai cikin kan shi har lokacin, ba lallai bane kalaman da yake fadi suna da wata ma'ana tunda bayajin taimakon kwakwalwar shi a fitarsu, zuciyar shi ce kawai take haukanta
"Idan lokaci kike bukata zan baki...

Komin tsayin lokacin da kike so ki huce zan baki..."
Kallon shi Waheedah take tana girgiza mishi kai cikin rashin yarda da cewar zai bata duk lokacin da take so, shi kuma yana fahimtar hakan da cewa tana nufin bata yarda ba, ya saukake mata auren shi, hakan yasa shi kara rikicewa da fadin
"Ba zan dinga zuwa ba, ba zan dame ki ba, duk lokacin da kike bukata..."
Dayan hannunta tasa tana goge fuskarta, taja hancinta da takeji yana mata radadi kamar ta shaqi barkono
"Shekara daya..."
Ta furta cikin dakusasshiyar murya, wannan karin dokawar da yaji zuciyar shi tayi da a kasar wajene ya tabbatar likitoci zasuji mishi tsoro bugun zuciya na farat daya
"Shekara biyu"
Waheedah ta sake fadi da wani nisantaccen yanayi a muryarta
"Uku...

Hudu...

Biyar...."
Taci gaba, ba iska kadai yakeji ta mishi kadan ba, hasken dakin yaga yana raguwa, ga zuciyar shi da take cigaba da dokawa tana mishi barazanar tsayawa, hannun Waheedah ya saki yana dafa gadon dake kusa da shi ya mike dakyar.

Batace mishi komai ba, asalima da idanuwa take bin shi harya fice daga dakin, baiko ja mata kofar ba, bai taba ganin nisan daga cikin gidan Yassar ba zuwa harabar gidan inda ya ajiye motar shi.

Wannan tashin hankalin bakon abune a wajen shi, kamar yanda tunanin da yai mishi daurin goro yake bako a wajen shi.

Dakyar yakai wajen motar shi, dishi-dishi yake gani lokacin daya bude ya shiga, bakomai na cikin tuqi yake iya tunawa ba, ya taka motar ne ta baya ya fita daga gidan, yana jin yanda ya daki gefen gate din dako gama budewa maigadin baiyi ba, haka yahau titi yana nufar hanyar gida, a ran shi yake karanto duk wani sunan Allah da yazo mishi, cike da yabo saboda yanda yake jinjina ikon Allah, yasan ba hankalin shi ya kai shi gida ba.

Lokacin da yayi parking din motar cikin gidan lumshe idanuwan shi yayi yana girgiza kan shi, ya sake bude su yana ganin duhun da yake son lullube mishi su ruf, dakyar ya fito daga cikin motar yana wani irin mayar da numfashi.

Dishi-dishi yake gani duk yanda yake kara ware idanuwan shi, ga jiri da yakeji yana dibar shi.

Ganin kamar Khalid yake hangowa yasaka shi kara ware idanuwan shi sosai, amman sai yake ganin Khalid din na rabe mishi gida wajen hudu.
Chapter 77 · 0% Book details