Sashe 13
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har Mubarak ya shigo ya bama kowa yoghurt din shi, tata karba tayi tana zage aljihun jaka ta jefa a ciki, haka yalon ma, dan ji take sun takura yanayin ta, kanta ta jingina da jikin motar tana lumshe ido, kafin ta daina jin hayaniyar da suke a cikin motar dan ta bace cikin duniyar tunani.
Jikinta gabaki daya a sanyaye take jin shi, banda yanayin fuskar Abdulkadir din lokacin daya rikota babu abinda take hasasowa, so take taji ta a kwance a daki, ta janyo bargo ta rufe jikinta gabaki daya har hakanta, ba zataki bacci ya dauketa cike da tunanin shi ba, dan a dakine kawai take da tabbacin babu wanda zai uzzura mata balle ya katse mata tunanin ta.
"Waheedah..."
Taji an kira ana tabota, juyawa tayi fuskarta babu walwala
"Dallah anata miki magana, mu kwance kai yau, kinga alhamis babu islamiya, gobe in Allah ya kaimu sai muje kitso gabaki dayan mu..."
Da sanyin murya tace amsa Zahra da
"Kuje kitson ku, Nuriyya zatai mun"
Hararta Zahra tayi
"To mai Nuriyya data iya kitso, sai kita zuwa ai"
Tana kallon Amatullah ta tabe baki, juyawa tayi ta gyara zamanta tana kyalesu, batasan me Nuriyya ta tsare musu da basa sonta har haka ba, ko wani abin ake in tace da Nuriyya zatayi takan ga kiyayya shimfide a fuskarsu, musamman Amatullah da takance tama fi son Nuriyya akan ta, bata raba duk wani lokacin da ta samu tare da ita saida Nuriyya, zata iya cewa dukka yan uwan nata kan yi mata wannan mitar, kamar suna kishi da Nuriyya din, dariya takan yi musu kawai, yau kam ko dariyar basu samu ba, dan tunanin Abdulkadir ya addabeta fiye da kowanne lokaci, dashi manne a kasan zuciyarta kuma suka karasa gida.
Bai shigo gidan ba sai gab da Magriba, bangaren su ya wuce yana tura kofar dakin da sallama ya shiga, kafafuwan shi da jikin shi cikin shigar kayan ball.
Bangaren da gabaki daya mazan gidan suke daban yake, daka shiga falo zaka samu da kujeru a ciki, sai kofofin dakuna a zagaye, dakin bacci hudune a cikin wajen manya-manya, sai karamin nashi da yake tunanin anyi shi na baki.
Da shi da Mubarak suke kwana, kafin ya tattara yana bar mishi dakin, bai damu da kwana shi kadai ba, asalima hakan na mishi dadi, da dakin ya kasance nashi ne shi kadai, amman baisan dalilin da yasa kowa yake gudun hada daki dashi ba, abin na bata mishi rai wani lokacin, ko kujera mai zaman mutum biyu ya zauna da wahala kaga wani ya zauna kusa dashi.
Kusan su hudu yagani a falon suna kallo, baibi takan su ba, kitchen ya fara wucewa ya bude fridge din da yake kitchen din ya dauki ruwa, ba wani amfani suke da kitchen din ba, banda kwanonin da in suka shiga cikin gidan sukan zo su jibge, sai ya gaji da ganin su yake sa wani ya kwashe ya mayar cikin gidan.
Dakin shi ya wuce yana cire kayan jikin shi ya shiga bandaki, ruwa ya watsa cikin hanzari dan yasan ana gab da kiran sallah ya dauro alwala ya fito, kananun kaya ya saka, dan Hajja harta gane shi, in ya saka manyan kaya to sallar juma'a zashi, kayan duk da za'a dinka musu manya da sallah, yana dawowa idi yake zare su daga jikin shi.
Fitowa yayi yana jin ana kiran sallah, har yakai kofa ya juyo yaga su Yasir a zaune.
"Kuna ji ana kiran sallah, kuna kara gyara zama"
Yassar ne ya dago daga cikin kujera yana kallon Abdulkadir din
"Ka wuce abinka kai dai..."
"Badai kyau wallahi"
Cewar Abdulkadir din, dan yagane Yassar ne a yanayin shi, kusan duk gidan zai iya kwantanta zafin ranshi dana Yassar ne, baya tunanin ko Mama tana iya banbance su in bada hakan ba, kamannin su ya baci, gashi ya rasa jarabar da tasa komai iri daya sukeyi, har askin kansu, in suna tare ka kira daya su dukan su suke juyowa.
Da zafin ransu ne kawai ake ganewa.
"Karka bari in taso Abdulkadir..."
Yassar ya fada, amman ko motsi Abdulkadir baiyi ba
"Hamma Yasir kaima biye mishi zakayi?
Dan kun fito a yan biyu bazai sa a rufeku a kabari daya bafa, wallahi jibgar banza zaka sha..."
Mikewa Yassar din yayi yana fara takawa inda Abdulkadir din dayake dariya yake tsaye, sai dai kafin ya karasa harya bude kofar ya fice da gudu
"Dan banzan yaro marar kunya, daka tsaya ai"
Yassar ya fadi, yana sa Yasir yin dariya
"Banda kai a gidan nan, banga wanda Abdulkadir yake wasa dashi haka ba"
Mubarak ne ya jinjina kai yana miqewa
"Halin sune yazo daya shisa, yaron can ko tsokanar shi na gwada yi zaice mun bayaso, zansa yara suji su raina shi"
Dariya kawai Yassar yayi yana wucewa yabar su anan, banda Yasir da suka fito rana daya, bayajin akwai wanda yake ji har kasan ranshi a gidan kaman Abdulkadir, duk da kusancin su baya hana yai mishi rashin kunya sosai, amman kuma shi kadai yake daga ma Abdulkadir hannu ya sauke batare da Abdulkadir din ya gwada ramawa ba, sai dai ya sake fadar maganganu ya wuce, ko rikici akeyi dashi, Yassar din ake kira dan shi kadai yake iya raba rikicin Abdulkadir.
Alwala duk sukayi suna fita masallaci tare.
Abdulkadir bai shigo gidan ba sai bayan sallar isha'i, bai samu kowa a falon ba sai Yassar da yake cin abinci, kamshin da wake da shinkafar da ya hango yaji busashen kifi yake yasa shi sanin girkin Mami ne, dan duk ranar baici abinci a gidan ba, da safe ya rigasu fita makaranta dan shi yake da duty, acan ya siyi abinda ya sakama cikin shi, daya dawo kuma sunje gidansu Imran, acan sukaci abinci rana.
Cikin shi yaji ya murda da yunwa, ya karasa yana zama kusa da Yassar din, hannu yakai zai dauki cokalin Yassar ya doke hannun shi
"Tashi ka zubo naka"
Daquna mishi fuska Abdulkadir yayi
"Hamma mana..."
Abincin Yassar ya kara diba ya cika bakin shi yana fadin
"Zanci ubanka wallahi"
Sake daquna fuska Abdulkadir yayi
"Saika dinga zagina, ko a gaban yara saika zageni, salon kasa yara su rainani.
Ni kam bana so kana mun irin haka"
Hannu Yassar yasa yana kai mishi duka saboda bakin shi da yake cike da abinci, miqewa Abdulkadir yayi, duk gidan babu wanda yake mishi irin wannan cin mutunci sai Yassar, ya rasa kuma menene tattare da Yassar din da yakan sashi daga mishi kafa tunda ba tsoron shi yake ba, baya tunanin idan fada ya hadasu Yassar zai iya dibar wani abu a jikin shi, amman saiya barshi yana ci mishi mutunci haka, ko Abba bai taba dukan shi ba, balle kuma Hajja, Yassar ne mutum na farko a duniyar shi daya fara dauke shi da mari bai iya ramawa ba, lokacin da fada ya kaure tsakanin shi da Babban Yaya, kan ya mare shi ya rama.
Amman da Yassar din ya kafe shi da idanuwa tsintar kanshi yai da barin wajen, yana mishi kwarjini naban mamaki.
Yanzun ma kallon da yake mishi yasa shi fita daga dakin.
Kanshi tsaye bangaren Mami ya wuce yana shiga har tsakiyar falon tukunna yai sallama, Mami din data fito daga kitchen ta amsa shi
"Ina wuni"
Ya furta a hankali, duk cikin matan Abba yafi ganin girmanta, ita kadaice bata taba shiga harkar shi ba, asalima banda gaisuwa babu abinda yake hadasu, yanzun ma wucewa tayi hidimar gabanta, shi kuma ya taka yana karasawa har kitchen din, inda yaga Waheedah a tsaye, juyowa tayi tana kallon shi, kafin a dan daburce tace
"Hamma..."
Ludayin da yake hannunta ya karba, jajayen kayane a jikinta daya kara fito da farin ta yana saka shi daquna fuska
'In shaa Allah babu abinda zai hadani hanya da farar mace'
Ya fadi a kasan ranshi, plate ya dauko batare daya kulata ba, yana kallo ta matsa tana hade bayanta da kantar kitchen din, abincin da yake tunanin zai iya cinyewa ya zuba
"Ina miya?"
Ya tambaya yana kin kallonta dan farinta na shigar mishi ido, da hannu ta nuna mishi tana sake matsawa dan zuciyarta dokawa take sosai, da tunanin shi manne ta yini, har fita tayi harabar gidan ko zata ganshi batare da tasan dalilin hakan ba, ta gaji da leqe-leqenta ta dawo cikin gida, ko sallar isha'i sai yanzun ne tayi alwalarta, a falo ta zauna tana jiran ko zata ga ya shigo dibar abinci, sai yanzun da yake tana da rabon tagan shi din.
Cokali yasa hannu ya dauka hadi da wani plate din daya dora kan abincin ya rufe yana ficewa batare daya sake kallon inda take ba.
Bangaren su ya koma, abincin ya fara ajiyewa tukunna yaje ya dauko ruwa ya dawo ya zauna.
Daga shi sai Yasir da Yassar, Ahmad da suke kira da Babangida, sai Mubarak a falon.
Film din da lokacin ake rubuta sunaye alamun farawa ya tsayar da idanuwan shi akai.
'Paheli'
Ya karanta sunan film din da tun daga kidan daman yagane indiya ne.
Abinci yake ci yana nutsar da hankalin shi kan film din, dan sosai yake jin dadin shi, kafin yaji an harbar mishi baya da kafa, ya kuma san Yassar ne
"Sojan gobe ne yake kallon soyayya haka?"
Yassar yai maganar yana dariya
"Babu abinda zai hana insa a rufemun kai ko kwana biyune, saboda babu wanda ya rainani a gidan nan kamar ka"
Dariya Yassar ya sake yi
"Lallai ma yaron nan.
Ka zama sojan tukunna"
Juyawa Abdulkadir yayi yana kankance mishi idanuwa
"Na kusan applying NDA ai, in shaa Allah.
Kuma wayaki soyayya?"
Wannan karin Babangida ne yace
"Tambaye su dai, kaman suma ba kallon suke ba"
Murmushin gefen fuska Abdulkadir yayi
"Allah Hamma bazan auri matar da bana so ba, ina da buri mai yawa kan matata"
Dariya sukayi gabaki daya
"Hmm, tadai shiga uku da masifarka, aikai mai zama dakai tana da aiki wallahi"
Mubarak ya fadi
"Shisa nace zan auri wadda nake so..."
Murmushi Yasir yayi mai sauti
"Yaron da ko tafasa baiyi ba yana maganar soyayya da mata.