Sashe 15
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har wanke-wanke ma duk zamuyi"
Tanajin zungurin da Zahra tai mata
"Naganki dan ubanki, wato tace wanke-wanke shine kike zungurinta ko?"
Cewar Antyn tana dorawa da
"Maquyatan banza da wofi, sai kace ba mata ba"
Ta juya ta koma dakinta, harara Nabila da Zahra suka zabga mata, Nabila na fadin
"Adda Wahee ke zakiyi wanke-wanken?"
Kai Waheedah ta daga musu tana ajiye cokalinta cikin abincin dan ta riga ta koshi tuntuni, hanyar kitchen din ta nufa tana ganin jibgin kwanonin wanke-wanken da ko kadan basu daga mata hankali ba, indai aikine da zatayi da jikinta baya mata wahala, duk da Mami kance ta cika yin abu da sanyin jiki.
Saida ta fara share kitchen din tukunna ta fara wanke-wanken, tafiyar Abdulkadir tayi mata tsaye a makoshinta.
Shekara daya na mata wani irin nisa naban mamaki, a wani bangaren kuma tana mata saurin zuwa, duka yaushe yagama jarabawar aji shidda harta fito, ita kanta aji biyar take shirin shiga yanzun hakan.
Ranar lahadin da saura kwana daya su koma makaranta, kuma yai dai-dai da litinin din da Abdulkadir din ma zai tafi Kaduna.
Wani iri take jinta, dan haka tanayin wanka tagama abinda takeyi ta fito zata shiga gidan su Nuriyya ko hira suyi, ta fito harabar gidan taci karo da Abba.
"Abbah..."
Ta kira fuskarta dauke da fara'a cikin yanayin da ita kadai take kiran shi da hakan.
Shima muryar shi dauke da fara'a yace
"Waheedah..."
Murmushinta ya kara fadada
"Ina kwana..."
Amsawa yayi yana dorawa da
"Har za'aje islamiyya ne da wuri haka?"
Kai Waheedah ta girgiza mishi, kafin ta amsa yace
"Wajen Hassanarki zakije kenan"
Dariya Waheedah tayi
"Abba mana"
Jinjina kai yayi yana saka hannu a aljihu
"Aina sani....itama goben suke komawa makaranta ko?"
Kai Waheedah ta dan daga mishi, dubu uku ya zaro daga aljihunshi yana mikama Waheedah din
"Na manta ne wallahi, ki bata saita dinka sabon kayan makaranta itama, abin na raina tun randa na bayar da naku dinkin..."
Da fara'a a fuskar Waheedah ta karbi kudin
"Allah ya kara arziqi Abba...
Angode sosai"
Murmushi kawai Abba yayi, hankalin yarinyar yasa yake jinta kamar daga cikin shi ta fito, ko kadan bayaso taji maraicin rashin mahaifinta, alkawari ya daukarwa mahaifiyarta na cewa zai riqeta, ko da mahaifinta na raye, nauyin alkawarin daya dauka zai cigaba da danne shi.
"A dawo lafiya.
Allah ya tsare mana kai"
Waheedah ta fadi, Abban ya amsata, tsaye tayi saida taga ya shiga mota ya juyata ya fice daga gidan tukunna ta karasa takawa tana isa kofar gidan ta fice tana shiga gidan su Nuriyya din.
Bata ma sameta a gidan ba, Mama ta aiketa, kudin da Abban ya bata ta mikawa Mama tana mata bayani, sosai Mama ta nuna jin dadinta hadi dayin godiya mai yawa, tukunna Waheedah ta koma gida.
Bangaren su ta nufa ta shiga dakinsu ta kwanta.
Bata da abinda zatayi, gashi sunqi kawo wuta balle tayi kallo ta rage zafi
Tunawa tayi da wani littafi da tafi wata shidda da karba wajen Nuriyya, amman bata karanta ba, dan har yanzun ita karance-karancen littafin Hausar nan basa kanta, saukowa tayi daga kan gado tana dauko tsohuwar jakar makarantarta, aikam tana saka hannu ta bincika ta janyo littafin, kan gado ta dora shi tana mayar da jakar tukunna ta koma tahau gadon ta kishingida tana daukar littafin.
ABIN DA AKE GUDU na BATUL MAMMAN ta duba sunan littafin da marubuciyar, sosai takan ji Nuriyya na maganar marubuciyar da yanda tsarin rubutunta yake tafiya a nutse, dan takance bata da gwana a marubutan Hausa kamar matar.
Shafin farko ta bude tana nutsawa cikin labarin ASMA'U.
Ko da suka dawo islamiyya so take kawai ta gama duk wata hidima da zatayi tai sallar isha'i ta koma daki ta karasa jin yanda za'a kare da labarin ASMA'U, da ta dauka Nuriyya zuzuta marubuciyar kawai takeyi, sai yanzun da labarin ya tabata fiye da tunani.
Ga tarin darussan da iya tsayin rayuwarta bata taba hango faruwar su ba, tashin hankali abune da sai dai taji labarin shi a waje ko a fina-finai, sai kuma yanzun da take karanta shi a littafin BATUL MAMMAN.
Kayan makarantar su duk ta hada ta goge.
Dauka tayi tana nufar daki, taga Amatullah a kwance a kasa kan kafet.
Tunda zasu fita islamiyya take fadin cikinta na ciwo, har suka dawo, dan Waheedah ba zatace taga taci abinci ba
"Ki tashi ki fadama Mami ko magani sai ta baki...
Ya zaka zauna ciwo na cinka"
Waheedah ta fadi tana ajiye uniform din a gefen gado, hadi da taba Amatullah din, zuciyarta tai wata irin dokawa ganin kamar bata motsi, tsugunnawa tayi tana kamota
"Amatu...
Amatullah..."
Take fadi tana jijjigata, idanuwanta cike taf da hawaye, dakyar Amatullah ta daga idonta
"Adda Wahee cikina, cikina ciwo yake..."
Hannu Waheedah tasa tana share kwallar da take shirin zubo mata, muryarta a karye tace
"Bari in kira Mami...sannu"
Ta kara maganar tana zame Amatullah daga jikinta, ta fice daga dakin da sauri, koda taje wajen Mami dinma hannunta kawai ta kamo dan ta kasa magana, saboda kukan da take, dakin nasu Mami tabita hankali a tashe, a kafada ta sabe Amatullah din tana daukar hijab din Waheedah da tagani inda tai sallar Magrib tana nufar hanyar fita daga bangaren nasu, Waheedah na rufa mata baya.
Bangaren Hajja ta nufa da Amatullah dan tasan Abban su bai isa dawowa ba.
"Subhanallah, me ya faru haka?"
Hajja ta tambaya, Mami na amsata da
"Cikinta ne yake ciwo..."
Hajja batace komai ba ta koma cikin dakin da hanzari, Hijab dinta ta dauko itama ta saka ta dauko mukullin motar ta tana fadin
"Muje...
Bari in dubo cikin yaran nan, ko wani yana nan.
Tafiya asibiti da namiji nada dadi, kodan zirga-zirga..."
Basu ma karasa bangaren nasu ba saiga Muhsin ya shigo gidan.
Motar Hajja ta bude tana karbar Amatullah da take fitar da numfashin wahala ta sakata a bayan motar tana shiga.
Ganin Waheedah dake kuka ta kama murfin motar yasa Mami fadin
"Ina zaki ke kuma?
Wuce ki koma gida..."
Rau-rau ta sakeyi da ido, wani kallo Mami ta watsa mata dayasata sakin murfin motar, tana kallo suka rufe, gefe ta matsa, Muhsin din ya juya motar suka fice.
Tsaye tayi a wajen tana share hawaye, hadi da sauke ajiyar zuciyar da take jin tana mata zafi.
Ita kam da sun tafi da ita hankalinta zaifi kwanciya.
A wajen ta zauna ko sauron dake gartsa mata cizo bataji, danma da haske, kasancewar an kunna musu gen.
Bata san iya lokacin data dauka a wajen ba, ta hada kai da gwiwa, kuka kawai take sharba.
Abdulkadir ne yazo wucewa, dan ranar ya wuni ne dasu Nawaf tunda washegari da sassafe zai wuce, ajiyar numfashin ta ya soma ji, kafin ya tsaya yana dakuna fuska, sosai ya saurara yaji daga inda kukan yake fitowa, dube-dube ya shiga yi, yana hangota rakube wajen ajiye motocin, daga hannuwanta yagane itace
'Me yarinyar nan take anan?'
Ya tambayi kanshi yana karasawa wajen, ta hade kanta da gwiwa da alama kuka takeyi.
"Waheedah..."
Ya kira, muryarshi na dukan dodon kunnenta da wani irin yanayi da yasata dagowa, fuskarta ta karayin ja, idanuwanta duk sun kumbura saboda kukan da takeyi, saiya tsinci kanshi da kasa yi mata fada.
Muryarshi dauke da wani yanayi yace
"Menene?
Waya dake ki?"
Kai Waheedah ta girgiza mishi, wani rauni takejin yana kara danneta da ganin shi, hawayen ta na kara zubowa.
"Me kike anan to?
Meya faru?
Mutuwa akai?"
Abdulkadir ya tambaya, wannan karin da damuwa a muryarshi.
Kan dai ta sake girgiza mishi
"Kimun magana Waheedah, kina son batamun raine kome?"
Ya karasa maganar a fadace, dakyar, muryarta can kasan makoshi tace
"Amatu...Amatullah ce bata da lafiya"
Numfashi ya sauke
"Shine kikazo nan kina kuka...ina Amatu din yanzun?"
Hannu tasa ta goge hawayen dake shimfide kan fuskarta tana jan hanci
"Sunje asibiti..."
Ta amsa muryarta na sake karyewa
"Me yasa basu tafi dake ba?
Mtswww"
Abdulkadir ya karasa maganar da jan karamin tsaki.
Kukan da take yana mishi wani iri
"Tashi daga nan"
Ya umarta, idanuwanta cike da hawaye take kallon shi
"Zan jira su dawone Hamma..."
Wani irin kallo yai mata yana fadin
"Zaki tashi ko saina watsa miki mari?
Cikin sauron zaki zauna da yake baki da hankali ko?"
Mikewa Waheedah tayi babu shiri, tana ganinta yar mitsitsiya a gaban shi, duk da halin damuwar da take ciki bai hanata jin yanda zuciyarta take dokawa ba.
"Ki koma cikin gida.
Idan naganki a wajen nan saina zaneki..."
Wasu sabbin hawayen taji sun zubo mata, duk da basu hanata kin bin umarnin shi ba, tsaye yayi a wajen yana kallonta harta sha kwana, dan dafe kanshi yayi, yana jin ranshi na baci babu dalili, bangaren su ya nufa, ko sallama baiyi ba ya wuce su Yassar da suke cikin abinci
"Ko shi da wa kuma?"
Yazid ya tambaya, Yasir ya amsa shi da
"Indai bakin ran Abdulkadir ya motsa ko babu dalili yin shi yake..."
Dariya sukayi, sai gashi ya fito, karamin tsaki yaja, dan baiga abinda zai basu dariya ba, ranshi yana baci suna dariya
"Ku komai na dariya ne"
Ya fadi yana kara jan tsaki
"Kai da uban wa?"
Yassar ya tambaya, bai samu amsa ba, Abdulkadir din yazo ya wuce yana yin ciki da kafafuwan Yazid da yace
"Ikon Allah...bani na kar zomon ba"
Shima bai samu amsa ba, Abdulkadir din ya fice daga dakin, yana doko musu kofar kamar zai karyata.
Haka kawai ya tsinci kanshi da nufar bangaren su Waheedah dan bai yarda cewar ta koma ba, hangota yayi tsaye bakin kofa tana kai hannu tana goge fuskarta
"Yarinyar nan bata da hankali"
Ya furta a hankali, kukan da takeyi ma zai saka mata wani ciwon kan, ga sauro daya gama moreta a wajen da ta zauna.
Da alama bata ganshi ba, dan saida ya kure mata tukunna ta ruga da gudu tana shirin komawa cikin dakin, Abdulkadir ya damqo hannunta
"Hamma dan Allah..."
Waheedah ta fadi idanuwanta kamar zasu fado, ga wani lugude da zuciyarta take mata
"Me nace?"
Kai ta girgiza mishi, hawaye na silalowa daga idanuwanta
"Me nace miki?"
Ya tambaya a tsawace
"Kar in fito...