← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 94

Sashe 24

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nasani Nuriyya, bana son fadan shine kawai"
Tabe baki Nuriyya tayi
"Nidai muje..."
Ta karasa tana kama hannun Waheedah din dan su samu mota, cikin abokan angon wani ya leqo kai yana ma Nuriyya murmushi
"Ya zaku wuce direban naku?"
Ya fadi yana dan daga mata gira, dariya Nuriyya tayi ganin baiko kalli inda Waheedah take ba.

Murfin motar zata bude dan ta shiga, kamar daga sama taji ance
"Ina zaki je?"
Juyawa tayi zuciyar ta na dawowa makoshinta, kamshin turaren shi na cika mata hanci, shaddar jikin shi tayi matuqar amsar shi, jikinta har wani bari yake, kafin ta kula da idanuwan shi tsaye suke kan Waheedah.

Wani tuquqi taji ya taso daga dan yatsan kafarta yana samun wajen zama a makoshinta.

Yana fitowa bai ganta wajen motar ba, hijab dinta ya hango, ranshi a bace yake har lokacin, baima san wayace tabar wajen ba.

"Nace ki bar wajen ne?"
Ya tambaya, kai Waheedah ta girgiza mishi, kalar fadan da yake ji yau na bata mamaki, tunda daman bashi ya kirata ba, ita ta same shi a wajen, yanda ya kafeta da ido yasa ta wucewa ta gaban shi kamar qwai ta fashe mata.

Wani kallo ya watsa mata mukullin motar dake hannun shi na subucewa ya fadi, kafin ya yunkura Nuriyya ta tsugunna ta dauko mishi tana sauke idanuwan shi cikin nata, wani irin abu na tsirga mishi dayasa gashin dake bayan wuyan shi miqewa.

Hannu ya miqa mata ta saka mishi mukullin a ciki.

Yana duk wani kokari dazai iya karya riqe hannunta ya jujjuya shi yaga kunshin ta dakyau.

Idan akwai abinda yake kara burgeshi bai wuce kunshi ba, ko baisan yarinya ba yaga hannuwanta dauke da kunshi saiya sake kallo, musamman na Nuriyyan da yake baqi da ja.

Gashi yan yatsun nata jan lallen ya kama.

Wani abu ya hadiye a dakyar yana tsintar kan shi da fadin
"Wa yai miki kunshi?"
Murmushi Nuriyya tayi saboda shine karo na farko da yai mata wata magana da ba amsa gaisuwa bace, banda jiya da yace ta rufe mishi kofa.

"Wata mata ce"
Ta amsa tana saka shi ware kananun idanuwan shi da ya tabbatar a waje yai maganar, kai yadan daga mata yana juyawa.

Takun tafiyar da yakeji ya tabbatar mishi da Nuriyyan na biye dashi.

Zuciyar shi dokawa take sosai, ga tsikar jikin shi da yake ji tana miqewa, bayaso ya juya ya sake fadin wata maganar da bai niyya ba, shisa ya kyaleta.

A tsaye wajen motar ya samu Waheedah.

Zagayawa yayi ya bude motar ya shiga, wannan karin baice ma Waheedah ta shigo ba, da kanta ta bude kofar ta shiga.

Bata kula da hararar da Nuriyya ta watsa mata ba, dan ita taso ta shiga gaban motar.

Babu yanda zatayi haka ta bude bayan ta shiga, duk da gabanta na faduwa kar ya koreta, baice mata komai ba, zuciyarta har wani tsallen murna take, murmushi yaki barin fuskarta har lokacin.

Dan tashi Abdulkadir yayi yana saka hannun shi a aljihu ya ciro links din dake cikin aljihun tukunna ya zauna.

Waheedah ya mikama links din, batace komai ba ta karba tana gyara zamanta dan ta saka mishi a hannun da ya miqo mata din.

Cikin yanayin dayasa murmushin da Nuriyya take ya bace bat daga fuskarta, kallon su takeyi har Waheedah din ta daura mishi link din, ya janye yana miqa mata dayan hannun nashi, saka mishi tai tukunna ta gyara zamanta batare da tace komai ba.

'links ne kawai, kema dan bazai yiwu ya baki bane kisa mishi shisa ya bata'
Nuriyya take fada ma kanta duk da wata murya na gaya mata
'Ita ma din ai ba kanwar shi bace, babu abinda ta hada dashi, agolar gidan su ce'
A karo na farko da taji daman Waheedah tazo a kanwar Abdulkadir din da hakan zaifi mata, saboda babu wani chance na soyayya a tsakanin su.

Kirjinta take jin yana mata zafi da abinda take jin kishi ne na fitar hankali, tasan Abdulkadir ya mata nisan da bazai misaltu ba, shisa duk kyan da yake mata, da yanda yake sak da zabin mijin da take burin samu bata taba daga burinta akan shi ba.

Haka take so yaima Waheedah nisa, ko kadan bata son wanni kusanci daya banbanta da wanda yake nunawa tsakanin shi da kowa.

Idan ba zata same shi ba, Waheedah din ma ba zata same shi ba.

Abdulkadir kuwa kokawa yake da yanda komai na jikin shi yake son juyawa ya sake kallon Nuriyyan, kafin kanwar Abba ta bude motar ta shigo tana fadin
"Abdulkadir..."
Damar yai amfani da ita ya juyo
"Anty...

Ina wuni"
Dan ware idanuwa Anty Maryama tayi, duk da taga Abdulkadir din ya girma, tana tunanin hankali ne yazo mishi har yau take samun arziqin gaisuwa
"Lallai Abdulkadir an girma..."
Ta fadi tana saka shi daquna fuskar shi.

Irin abinda bayaso kenan, saika gaishe da mata saita dinga nuna maka kamar an haifeka a gabanta, ko Hajja da ta haifeshi bayaso tana ce mishi yaro a gaban kannen shi.

Nuriyya ya dan kalla yana sata sauke idanuwanta daga kanshi babu shiri.

Juyawa yayi yana gyara zaman shi.

Anty Hafsatu ce ta shigo itama yanajin motar tai qasa saboda nauyin da sukai mata.

Tayar da motar Abdulkadir yayi
"Ka tsaya Hajiya Hassana ta karaso, gata can ta taho"
Anty Hafsatu ta fadi tana sa Abdulkadir fadin
"Inba saman motar zata shiga ba nan dai ai ya cika"
Abdulkadir yace yana yin baya da motar, ganin da gaske tafiyar zaiyi yasa Anty Hafsatu rufo murfin motar
"Mutum nawa suke zama a baya?

Ka jira tazo Abdulkadir"
Daquna fuska yayi yana fadin
"Gaskiya ta shiga wata motar.

Bakiji yanda motar tai kasa ba da kika shigo...

Inba so kike muna tafiya muna gurzar titi ba"
Bude baki Anty Hafsatu tayi cike da mamaki
"Kaci uwaka Abdulkadir, kana jina..."
Daquna fuska Abdulkadir din yayi, yana shirin yin magana Waheedah tace
"Hamma..."
Yanda tai maganar cike da roqo yasa shi harararta cike da alkawarin sauke mata wata masifar.

Bata damu ba indai zaiyi shiru, bata so su Anty Hafsatu suce ya musu rashin kunya, kuma tasan idan maganar tai tsayi ba a iya rashin kunya zai tsaya ba, Abdulkadir zai iya fita yabarsu a motar ko su su fita subar shi a ciki.

Batason hakan ya faru, Nuriyya dake gefe tana kallon su ta tabe baki.

'Allah yai miki baqin shishigi'
Ta fadi a ranta, koma menene din bata ga matsalar Waheedah ba tunda dai su Anty Hafsatun jinin shine, ita kuma bare ce, amman ji yanda tai mishi magana kamar tana da wani muhimmanci a wajen shi.

Tun su Anty Hafsat suna mita har sukai shiru, saboda radio din da Abdulkadir ya kunna yana qure maganar, basu ce ya kashe ba, tunda babu wanda inhar yana zuwa gidan baisan halin Abdulkadir ba.

A haka suka isa gidan Adda Khadija din, da duk da ba babba bane yanayin ginin yaima Abdulkadir kyau.

A cikin motar ya zauna bayan ya fadama Waheedah inta shiga cikin gidan tace ma su Zahra su fito su tafi...!
*#TeamAbdulkadir*
*#TeamWaheedah*
*#TeamAbindaAntyFatiTaHanani*
*#AnaTare*
[7/27, 1:13 PM] +234 816 124 4732:
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
Sai da yai wanka tukunna ya dauro alwalar sallar Asuba, yana kuma dawowa daga masallaci jakarshi ya hada tukunna ya kwanta.

Sai lokacin ya kunna wayar shi tunda yazo Kano.

Babban Yaya, Muhsin ne ya basu, dan shi harkar da yakeyi kenan, tun yana yaron shago da yake ubangidan nashi bamai baqin ciki bane, Muhsin din kuma akwai ladabi da kwantar dakai, kudaden duk da yake samu saiya tattara in za'a china saro kayayyaki saiya hada da nashi a dan saro mishi abubuwa.

A haka har Allah ya saka mishi albarka, duk da ya kammala karatun shi bangaren computer science, bai nemi wani aikin ba, da sana'ar ya dogara, sai babban caf
daya bude a wajen rijiyar lemo da shima yana kawo mishi rufin asiri.

Shima wayar hannun nashi blackberry din ce, danne-danne yake, yana ma rasa abinda zaiyi da wayar, lokutta da dama hakan yakan faru tunda aka bashi wayar, idan ya gaisa dasu Hajja shikenan, kashewa yake, tana iya kwana biyu a kashe.

Yazid ne ya turo dakin da sallamar da Abdulkadir din ya amsa mishi
"Ni banga amfanin wayarka ba"
Yazid ya fadi yana zama gefen gadon da Abdulkadir din yake zaune ya miqe kafar shi akai
"Ina amfani da ita mana..."
Kai Yazid ya girgiza cikin rashin yarda
"Kai dan BBM din nan da kowa yake yi ma bakayi"
Kankance mishi idanuwa Abdulkadir yayi
"Meye BBM din wai?

Nawaf ma ya isheni da maganar kwanaki"
Dariya Yazid yayi
"Kafar sada zumunta ce, amman wayar blackberry ce kadai take dashi.

Idan kayi register zasu baka wasu lambobi hade da haruffa, to sune zasu zama kamar..."
Hannu Abdulkadir din ya dagama Yazid, alamar baya bukatar karasa ji hadi da cewa
"Bani da ra'ayi..."
Yassar da yake wanka ne ya fito daga bandakij dan yanajin duk hirar da suke
"Ai idan kana son magana da Abdulkadir sai dai kai mishi text kawai, ko ka tura mishi saqo ta email dinshi.

Idan ba zaka iya jira ya kunna wayar shi kuyi magana ba"
Yassar ya karasa yana daukar mai dake ajiye a gefen Abdulkadir din ya kwance ya dangwala yana soma shafama hannuwan shi.

"Matar yaron nan tana da aiki"
Yazid ya fadi yana sa Abdulkadir din watsa mishi harara da kananun idanuwan shi
"Bafa naso Hamma, duka shekara baifi shekara hudu kabani ba"
Kai Yazid ya girgiza mishi
"Banma baka ko daya ba, yaro sai shegen son girma..."
Turo labba Abdulkadir yayi
"Kayi na girman ka Hamma, kar kai na ukku"
Mikewa Yazid din yayi
"Sallama nazo muyi, rasa kunya..."
Daquna fuska Abdulkadir ya sakeyi
"Wanne irin sallama sai kace wanda za akai kabari?

Ina ce makaranta zan koma ba wani wajen ba"
Numfashi Yassar ya sauke, Yazid na girgiza kai
"Ba za'a taba maka abin arziqi ba kai kam.

Allah ya tsare hanya, a kula, banda rashin kunya"
Idanuwa kawai Abdulkadir ya kankance mishi, baice komai ba harya fice daga dakin.

Hankalin shi ya mayar kan Yassar
"Wai shafa mai ne haka tun dazun.
Chapter 24 · 0% Book details