← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 94

Sashe 69

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yafi mintina talatin a cikin motar kafin ya tayar da ita yana nufar gida...!
#TeamAbdulkadir
#TeamWaheedah
#LubnaSufyan
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
To UMMU ABDUL, Hajjan AbdulKadir, Chairlady ta yan Fikra, Tauraruwar MSU.

Thank you, SonSo a ko da yaushe.

Tun daya tunkari kofar yake jin kauri ya cika mishi hanci, yana bude kofar ya saka kafafuwan shi cikin falon Waheedah yakejin kaurin na karuwa, bangaren Nuriyya ya karasa yana ganin hayakin dayake fitowa daga kitchen din ya turnuqe falon, gaban shi yaji yayi wata irin mummunar faduwa, da gudu ya shiga kitchen din, hayakin na shaqe mishi kafofin shige da ficen iska, yana soma tari, ta inda kaurin yake fitowa AbdulKadir ke nema.

Kafin idanuwan shi sukai kan tukunyar da tayi wani irin baki.

Hannu yakai yana kashe gas din ya fito daga kitchen din yana takawa zuwa dakin baccin Nuriyya.

Tunda AbdulKadir din ya fita, ta tashi tana dora ruwa ta zuba shinkafa a ciki dan ita ba tsayawa zatayi sai ruwan yayi zafi ba.

Dawowa tayi ta dauki wayarta tana ganin text, dubawa tayi taga dubu arba'in, murmushi tayi hankalinta da yake a tashe taji ya kwanta.

Daman ko da AbdulKadir din bai dawo ba ita ba tunanin abinda ya same shi ko abinda ake mishi ne a gabanta ba, tunanin abinda zai mata idan ya dawo shine matsalarta, tunda kuma ya tura mata kudi kamar yanda yakanyi duk wata, hakan na nuna alamar babu abinda zai faru.

Ko fadama bai mata ba, shisa ta wuce dakin baccin.

Akwai wasu takalma da aka turo a group dinsu na mata da kawarta Safara'u ta sakata ciki, takalman sun mata kyau, har ta private Safara'u tai mata magana ko zata siya, sai dai ta kashe kudin hannunta tas, tayi niyyar ta nunama AbdulKadir din daman inya kwana biyu ya huta, sai ga Waheedah tazo tana asibiti ita kuma.

Batasan cutar da har yanzun take damunta da bata warke bama, takalmin tace tana so dubu bakwai da dari biyar, ta tura kudin, saita turama Safara'u balance din atamfofin da ta dauka wancen watan dubu goma, ta kuma turama mai dinkinta shima dubu goma.

Kafin wani lokaci dubu hudu ce ta rage mata a banki.

Kwanciya tayi kan gadon da yake a hargitse tana manta cewar ta dora wani girki tunda ba sabawa tayi ba.

Hankalinta ya nutsu kan littafin DAN ADAM na Rufaida Omar da take karantawa, dan littafin saika nutsu zaka fahimce shi yanda ya kamata.

Ranta kal take jin shi, ko kadan bataji shigowar AbdulKadir daya nutsar da hankalin shi kanta ba, ya dauka ma wani abinne ya sameta harta dora girki yai wannan kamun ko kaurin shi bataji ba.

"Nuriyya..."
AbdulKadir ya kira ranshi a matukar bace, da alama batama jishi ba, dan tayi rufda cikine da waya rike a hannunta
"Nuriyya!"
Ya sake kira da karfi wannan karin yana sakata juyowa a tsorace, ganin shine yasa ta tashi zaune tana ajiye wayar hadi da fadin
"Sannu da zuwa"
Da idanuwa AbdulKadir ya kafeta
"Bakida hankali ko?

Baki da hankali zaki dora girki ki dawo daki ki zauna kina danna waya.

Gobara kike son ki hadamun a gida Nuriyya?"
Gabanta ne yai wata irin mummunar faduwa tana mikewa tsaye
"Ina zakije?"
AbdulKadir ya bukata
"Wallahi na manta ne"
Ta amsa tana wani irin sauke murya da ya kara bata mishi rai
"Saboda girkin bashi bane a gabanki, ya zaki dora girki har yai wannan konewar kina fadamun kin manta"
Idanuwanta Nuriyya taji sun ciko da hawaye, ta manta ranar karshe da aka tusata gaba ana mata fada haka, daman shine in yana nan baya rasa abinda zatayi da zai mata fada.

"Masoyi mantuwa ce, kowa nayi kuma"
Idanuwan shi AbdulKadir ya kankance a kanta, yanajin yanda ranshi yake kara baci, bazai dauki wata rashin kunyar bayan wadda Waheedah ta gama sauke mishi ba.

Karasawa yayi ya kama hannunta yana fara janta zuwa hanyar da zata fita dasu daga dakin, binshi kawai Nuriyya take har kitchen din tana ganin hayakin da har lokacin bai gama fita ba
"Meye a hancinki?

Danna waya yafi miki muhimmanci, ki kalli kitchen dinki, yaushe rabonki da shara Nuriyya?

Wanke-wanke fa?"
Hannunta daya damka take murzawa da dayan, tana jin wani hawaye mai dumi ya zubo mata
"Karki mun kukan banza da bashida dalili wallahi..."
AbdulKadir din ya fada, dan bayason kukan banza.

Rabata yayi ya wuce yana fita daga kitchen din, daki ya koma ya shiga bandaki, yana ganin yanda farin tiles din yai duqun-duqun, bangon har wani dallakin daudar da baisan ko tun ta yaushe bace ba, ga kayan wanki kaca-kaca.

Tsintar kanshi yayi da kasa amfani da bandakin, ya fito yana ganin bedroom dinma a hargitse.

Kai kawai ya girgiza yana tunanin kalar Nuriyya, inda zaman kallone ko danna waya babu wanda zai nuna mata.

Bangaren Waheedah ya wuce yana shiga bandakin ya gama abinda zaiyi ya fito.

Bangaren Nuriyyan ya koma ya zauna a falo yana dora kafafuwan shi kan kujera dan jin kasar da yake takawa kan kafet din.

Yanajin kacafniyar kwanoninta a kitchen din.

Da alama wanke-wanke take, aikam abinda takeyi kenan, ranta a bace yake, batasan yanda zata sake mishi maganar yar aiki ba, idan azumi yazo mata Waheedah bata dawo ba ta gama yawo tasani.

Kugunta taji ya gaji lokacin data gama tana share kitchen din, fitowa tayi ta samu AbdulKadir din a zaune
"Yunwa nakeji nikam"
Ya fadi yana kallonta, dan zaman da yayi waje daya yasa yunwar taso mishi.

Nuriyya kamar zatayi kuka tace
"Nikam me zan baka?

Kaga abincin ne na dora ya kama, ko zaka yo mana takeaway?"
Kai ya girgiza mata, yanda yakeji bazai iya fita ba
"Ko indomie ki dafa mun, bazan iya fita ba Nuriyya"
Robobin lemukan ta karasa tsincewa dana ruwa tan komawa kitchen din, ranta inyai dubu ya gama baci.

Ita har ranta batayi niyyar cin indomie ba, batama tunanin tana da indomie din, dubawa tayi, sauran data rage matace ta dafa jiya.

Fitowa tayi tana kallon AbdulKadir din, muryarta can kasan makoshi tace
"Babu indomie"
Juyawa yayi yana kallonta da mamaki
"Baki siya bane wancen watan?"
Kai Nuriyya ta girgiza mishi, ita wancen watan kudin da ya batane gabaki daya ta tattara ta siyi zobon gwal karami, dubu biyu kawai ta cika.

Babu abinda ta siya, ta dauka ma shi zai siyo musu.

"Ki duba kitchen din Waheedah"
AbdulKadir din ya fadi da alamar gajiya a muryarshi.

Wucewa tayi ta dibo indomie din guda hudu ta dawo
"Masoyi"
Ta kira tana dorawa da
"Yaushe Waheedah zata dawo?

Jikinne har yanzun?"
Kai AbdulKadir ya jinjina mata
"Zata dawo, tana gida....data kara warwarewa"
Wucewa Nuriyya tayi batare da tace mishi komai ba.

Ranta ya kara baci ba kadan ba, ashe gida Waheedah ta wuce abinta saboda bakin hali.

Nan da nan ta dafa indomie din, dan zatace duk a abinci ita kadai take dafawa babu wata matsala, a plate ta zubo musu ta saka cokula tana fitowa da ita ta ajiye, cokalin AbdulKadir ya dauka, duk yunwar da yakeji bata hanashi fadin
"Baki dafa mana kwai ba?

Haka zamu ci?"
Batare da Nuriyya ta kalle shi ba tace
"Banda kwai ni"
Da alamar kosawa a muryarta, ta kula ba a iyama AbdulKadir din, ta samu waje ta zauna
"In zakiyi mana siyayyar azumi ki siyo mana, ina so ni fa"
Cewar AbdulKadir din yana fara dibo indomie din da tai mishi zafi yana jira ta huce, kallon shi Nuriyya take cike da rashin fahimta
"Bakai zaka siyo ba?"
Kai AbdulKadir ya girgiza mata
"Me yasa zan tura miki kudin idan ni zan siyo"
Hanjin cikinta Nuriyya taji sun tattaru sun kulle waje daya
"Wanne kudin?"
Ta tambaya cikin bayanannen tashin hankali, indomie din daya dibo yakai bakin shi ya tauna yana hadiye tukunna ya kalli Nuriyya
"Na tura miki dubu arba'in dazun, baki gani bane?"
Kai Nuriyya ta daga dan dakyar ta hadiye indomie din dake bakinta
"Na siyayya ne daman?"
Cikin rashin fahimta AbdulKadir yake kallonta kafin yace
"Nuriyya..."
Saboda yanayinta daya gani duk ta daburce, ya kirata ne yana tambayar ko lafiyarta, amman ita bata fahimce shi ba, ta dauka koya gane bata da gaskiya ne
"Wallahi bansan na siyayyar azumi bane Masoyi, nasan kana bani kyautar kudi"
Kallon nata AbdulKadir yakeyi, yana son fahimtar inda kalamanta suka dosa, kallon ne takejin yana kara rikitata
"Na siyi takalma a ciki, daman wancen watan akwai atamfofin dana dauka, shine na cika kudin....

Saina biya kudin dinki kuma"
Cokalin AbdulKadir ya ajiye cikin abincin yana kallon Nuriyya
"Bangane me kike cemun ba, kudin dana tura miki dazun dinne kika siyi su takalma da atamfofi?"
Kai Nuriyya ta daga mishi, cikin tashin hankali take fadin
"Dan Allah kayi hakuri, wallahi bansan na siyayya bane"
Kallonta AbdulKadir yake yana rasa abinda ya kamata yayi, ranshi da yake kokarin kwantarwa ne Nuriyya take ta batawa tunda ya shigo.

Tsaye yake akan gidan shi, indai kayan sawa ne duk bayan wata biyu ko uku yake ba Waheedah kudi ko zata siya, itama Nuriyyar ya fara bayan watanta biyu da zuwa, to tana yawan tambayar shi kudi, ko zatayi ankon suna kona bikin kawayenta, ko zata siyi wani abin, shisa ya daina bata.

Akwai kudin daya ware na siyayyar kayan sallar su daman.

"Kudin kayan abincinne kika siyi takalma dasu Nuriyya?

Abinda duk nake miki bai isheki ba saikin tabamun wannan kudin?"
Kai Nuriyya ta girgiza mishi
"Baki da takalma?

Baki da kayan sawa?
Chapter 69 · 0% Book details