Sashe 83
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murza idanuwanshi yayi da hannu yana kara runtsa su, kafin ya bude su cikin tashin hankali yana mikewa zaune babu shiri, hasken da yagani cikin dakin bai saka shi ya yarda ba, saida ya dauki wayar Nuriyya da take gefen shi ya danna, yana ganin shidda saura minti goma.
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
AbdulKadir ya furta yana kai hannu ya jijjiga Nuriyya
"Ki tashi mun makara"
Ya fadi yana hasaso kalar yunwar da zaiji a yinin yau, dan shi azumi baiyi suhoor ba rayuwar shi na cikin tashin hankali.
"Nuriyya..."
AbdulKadir ya kira yana bubbugata, idanuwanta ta bude dakyar tanayin mika
"Dilla ki tashi karfe shidda fa"
Wata irin mikewa Nuriyya tayi tana kallon shi
"Karfe shidda?
Shidda fa?
Bamuyi Suhoor ba, baka tasheni ba"
Wani irin kallo AbdulKadir ya watsa mata yana jan tsaki
"Ban tasheki ba?
Bake ya kamata ki tashi ba, ki dafa mana abinda zamuci, nine zan tasheki?"
Shagwabe fuska tayi, tanajin idanuwanta na cika da hawayen bakin ciki, duk yanda sukai zaman rashin mutunci da Anas yana tashinta lokacin azumi, tunda yaga randa batai suhoor ba ta zama abin tausayi, a kwance ta wuni shame-shame.
Shine AbdulKadir zai sauke mata fada kamar akwai inda aka rubuta cewar ita ya kamata ta tashe shi dole dole.
"Kaima idan ka tasheni ai ba wani abu bane Masoyi"
Ta fadi wani abu na tokare mata wuya, kankance idanuwan shi AbdulKadir yayi
"Magana zaki fadamun?"
Ya bukata cike da neman ta furta wani abu ya sauke mata fadan shi, kai ta girgiza a hankali, hawayenta na kara taruwa, qwafa yayi yana sauka daga kan gadon ya wuce bandaki, abin na hade mishi waje daya, ga bakin cikin rashin suhoor ga asuba daya rasa, ga Nuriyya da zatai mishi kukan rashin dalili.
Saida yadan watsa ruwa a gaggauce tukunna yayi alwala ya fito, bama shida kaya a dakin nata, dole sai yaje bangaren Waheedah.
Nuriyya ya kalla da bata ko nuna alamar tashi ba
"Ke ba zakiyi sallah ba?"
Kafafuwanta ta sauko daga kan gadon
"Ba zakiyi wanki ba kuma?
Bandakin ki baya shigar miki ido, me yasa bakya wankewa ne?
Dakyar nayi wanka a ciki"
AbdulKadir ya karasa yana wucewa ta fice daga dakin.
Wannan karin hawayen ta taji sun zubo.
Wani malolon bakin ciki na tokare mata kirji, a haka ta dauro alwala ta dawo ta gabatar da sallar asuba.
Tana idarwa ta koma bandakin, tasa tsintsiyar da take a ciki ta wanke shi sama-sama, ko omo bata saka ba.
Ba zata fara karar da karfinta a bandaki tun yanzun ba, dan wani sharri ma, cikinta harya fara murdawa da alamar yunwa.
Wani zaninta ta dauka ta hada duka kayan wankin da suke cikin bandakin ta kulle su, ta dawo ta cire zanin gadonta dan yayi dauda sosai shima takai bandaki ta ajiye akan wancen kayan wankin, zata fitar dasu tunda Waheedah ta dawo.
AbdulKadir kuwa dakin Waheedah ya wuce yana turawa wani kamshi ya cika mishi hanci, dakin a gyare yake tsaf.
Ta sake zanin gado, ko ina tsaf tsaf, tana zaune kan gado ta mike kafafuwanta, ta goya Ikram ta gaba tana kwance akan kirjinta, hannunta daye rike da Qur'ani.
Ba zaice ga kalar dinkin jikinta ta yanda take zaune ba, amman atamfa ce, ta daura dankwalin atamfar, fuskarta fayau babu kwalliya.
Amman ta mishi kyau har zuciyar shi dokawa take.
Sai da ta idar da ayar da take kan karantawa, tukunna ta dago idanuwa ta sauke su kan AbdulKadir din
"Ina kwana"
Ta furta cikin sanyin muryarta tana dan mishi murmushin da yaji zuciyar shi ta dan nutsu
"Wahee...
Ya kuka tashi?"
Dan langabar da kai tayi
"Alhamdulillah..."
Idanuwan shi AbdulKadir ya kankance mata
"Shine baki tashe mu ba?
Mun makara, yanzun fa muka tashi, ko sallah banyi ba"
Ware mishi idanuwa Waheedah tayi, ita ba Suhoor takeyi ba, sai dai inta tashi tayi brush tasha ruwa, in tana da kankana ta dan sha dan samun ladan suhoor din, ko taci dabino wasu lokuttan, yau dinma hakan tayi.
Zatai karya idan tace batayi tunanin duba ko AbdulKadir din ya tashi ba, tunda tasan yanda yake wahala idan baiyi suhoor ba, kawai dai ta tsinci kanta da share koma meye yake son yin tasiri a kanta
"Na dauka kun tashi, kasan ni ba Suhoor nake ba"
Kai kawai AbdulKadir din ya iya jinjina mata, ba sai ta fada mishi ba, yasan fushin da takeyi dashi ne, koya tashi Waheedah zata kara kiran wayar shi ta tabbatar da hakan, wahala take son yasha, kuma zai shata din yau ya sani.
Kaya ya wuce ya dauka, yana ganin yanda Waheedah batace ya bari ta dauko mishi ba
"Ka dauki na kwana biyu ka wuce dasu Sadauki, inka dauki kaya kaje dasu bangarenta ka cire acan kabar mata acan, karka dawo mun dasu nan dan Allah"
Ta karashe maganar da rokon shi kamar yana da wani zabi
"Ki zo ki dauko mun to"
AbdulKadir yace kamar karamin yaro, Qur'anin ta ajiye tana tallabe Ikram ta sauko daga kan gado, kaya ta dauko mishi, riguna da gajerun wanduna, harda na ciki kala bibbiyu, tunda shi ba manyan kaya yake sakawa ba, yana dasu, in tayi magana kan ya saka bakinta ne zai tsini, ba zaisa ba, bayason manyan kaya.
Hannun shi ta dago tana saka kayan a ciki, tayi mishi murmushi har hakoranta suka fito, idanuwa AbdulKadir ya kankance mata
"Ko turare baki fesa mun ba"
Kallon shi tayi
"Bafa kayi sallah ba, lokaci na wucewa kuma"
Wani irin shagwabe mata fuska yayi, ta wuce tana komawa tayi zamanta, tana daukar Qur'ani taci gaba da karantawa a bayyane da muryar data tsaya dai-dai kunnuwanta.
Da kan shi yaje wajen mudubinta yana daukar turaruka ya feshe kayan dashi, ko inda yake ma Waheedah bata kalla ba, balle yai tunanin zatai mishi magana.
Harya gama ya fice daga dakin, ta sauke numfashi tana cigaba da karatunta.
Ko da ta idar, bata fita ba sai wajen karfe goma, da Ikram ta fita karta ajiyeta ta farka taita kuka dan wanki zatayi kafin su dauke wutar su.
Sai da ta fara share dakin wankin tukunna ta koma dakinta ta dauko jakar da suka dawo da ita da.
Tana cikin firfito da kayyakin wankin sai ganin Nuriyya tayi kamar mikiya, ta diro dakin wankin, da katon zanin gado da alamar kayan wankine a ciki
"Lafiya?"
Waheedah ta tambaya tana tsare Nuriyya da idanuwa cikin yanayin da yasa Nuriyyar jin duk ta daburce, Waheedah din na mata wani irin kwarjini naban mamaki, dan ko babu fara'a a fuskarta bata hade girar sama da ta kasa haka.
"Ina kwana"
Nuriyya ta fadi saboda ta rasa abinda zatace kafin tayi saurin dorawa da
"Ya jiki?"
Sai da Waheedah ta kalleta na wasu dakika, tana sata jin duk ta tsargu, kafin ta amsa da
"Lafiya"
Tana cigaba da hidimarta, tsaye Nuriyya tayi mamaki duk ya gama cikata.
Kayan wankin ta ajiye tana juyawa ta fice daga dakin.
Wankin ta Waheedah tayi dan bashida yawa, ta kwashe ta zuba a wata babbar roba, Ikram tazo ta kwantar akan doguwar kujera tana saka pillow din ta tareta, dan yarinyar ta cika juye-juye, karta fado.
Tukunna ta koma ta dauki robar ta fita bayan gidan inda igiyoyin shanya suke, ta shaya kayan ta dawo.
Wanda Nuriyya ta ajiye ta kwashe tanajin nauyin shi, bangaren Nuriyyan da tunda ta shigo gidan zata kirga lokacin da kafafuwanta suka taka ta nufa, a tsakiyar falo ta ajiye mata kayan tana juyawa, dakin wankinta ta janyo ta saka mukulli ta rufe ta dauki Ikram suna shigewa ciki.
Nuriyya kuwa fitowa tayi dan ta kawo wata hijab da tagani da datti, taci karo da jibgin kaya ajiye a falo.
Tsaye tayi turus tana kallon kayan cike da mamaki, ba rashin lafiya bace take damun Waheedah, wani hali na banza ne ta dauka da ba nata ba, dan bata santa dashi ba.
Ranta a bala'in bace ta dibi kayan wankin tana komawa dasu ciki ta ajiye a tsakiyar bandakin, itama tana da injin wankin ai, bawai bata dashi bane ba, kitchen ta koma ta dauko ledar omo ta dawo tana kallon AbdulKadir da yake a kwance yana danna waya
"Masoyi..."
Ta kira shi muryarta na fitowa a karye, hakan yasa shi dago idanuwan shi ya kalleta
"Ya ake amfanin da abin nan?"
Dakuna mata fuskar shi yayi
"Wanne abu?"
Ya tambaya, yana sa kunya ta rufeta, dan ta tsani ace duk irin wannan abubuwan na gayu ita bata iya ba, muryarta can kasan makoshi tace
"Na wanki"
Mikewa zaune AbdulKadir yayi yana kallonta cike da rashin fahimta, hakan na sata sake fadin
"Injin wankin, ya ake amfani da shi"
Har lokacin kallon ta AbdulKadir yakeyi
"Da ina kikaje da kayan?
Ba naga kin fita dasu ba"
Maganar shi nasa ranta kara baci
"Bangaren Waheedah..."
Ta amsa a taqaice tana kin mishi bayani, wannan karin fuskar shi ce dauke da tsantsar mamaki
"Me kike nufi da bangaren Waheedah?"
Kanta ta saddar kasa ganin irin kallon da AbdulKadir din yake mata
"Ita kika kai tayi miki wankin saboda baki da hankali?"
AbdulKadir yake fadi yanajin ranshi na kara baci fiye da yanda yake a bace, dan bai taba ganin irin wannan rashin hankalin ba, shisa ya sai mata nata injin wankin itama, yanda ma ba sai taje bangaren Waheedah din ba gabaki daya akan maganar wanki.
Yana daukar abubuwa da yawa a rayuwar shi amman bayason raini
"Ajiyeta kikai da zaki kai mata wanki Nuriyya?"
Kanta ta kara saddarwa, hawaye na tarar mata cikin idanuwa a karo na biyu daga wayewar garin yau, ko kadan bata saba a sakata a gaba ana mata fada ba, ko a gida daman Baba ne yake mata fada in tayi wani abin, to sai tayi abu goma, Mama bata fada mishi ba.