Sashe 16
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka kace kar in fito..."
Idanuwa Abdulkadir ya tsura mata, baiyi niyyar dukanta ba, haka kawai yaji yana son ganin ta tsorata haka.
"Wallahi Hamma kafata daya na cikin daki...
Dayace kawai a waje...
Wallahi"
Waheedah ta fadi, baisan dariya ta kubce mishi ba saida yaji sautinta cikin kunnen shi.
Zahra na da wauta, bayajin kuma a cikin gidan akwai wanda yakai Nabila rawar kai, amman Waheedah cikin sanyi take nata rashin hankalin, dariya yake daya kwana biyu baiyi ba, ita kanta Waheedah din kallon shi take da mamaki, bawai baya dariya bane, amman dariya irin haka da sauti ba zata tuna ranar karshe da taga hakan ya faru dashi ba.
Dayan hannunta tasa tana share hawayenta, dan karamin murmushi na kwace mata.
Hannunta Abdulkadir yaja zuwa cikin dakin, ya zaunar da ita kan kujera, da murmushi a fuskarshi ya nufi kitchen din, ruwa ya dibo a cup yazo ya kawo mata, karba tayi tana mamakin yanda batasan tana jin kishi haka ba, ta kusan shanye ruwan, ta ajiye kofin hadi da sauke numfashi, mikewa tayi
"Ina zakije?"
Abdulkadir da yake tsaye ta tambaya, muryarta a dishe tace
"Fuskata zan wanke"
Kai ya daga mata, ta zagaya ta bayan kujerar ta wuce, dan gani take inta wuce ta gaban shi zaiji yanda zuciyarta take dokawa.
Kofin ruwan ya dauke yana mayarwa kitchen ya fito ya koma kan hannun kujerar dake kusa da kofa ya zauna.
Fitowa Waheedah tayi, yabi fuskarta da ta kara mishi ja saboda kukan da tayi, yana tunanin kartai ciwon ido da yanda yaga idanuwan sun kumbura.
Wajen data tashi ta koma tana zama, wasa take da hannuwanta, ko zuciyarta zata rage gudun da take, lokaci zuwa lokaci takan dan dago ta saci kallon Abdulkadir din da yake zaune, kananun idanuwan shi na kafe a kanta, duk da alamun shi sun nuna yayi nisa a duniyar tunani.
Hakan ne a bangaren Abdulkadir din, in da zaka tabashi ka tambayeshi tunanin da yakeyi baisani ba, balle kuma azo dalilin daya sashi yake zaune a wajen, kukan da yaga tanayine ya dame shi, shisa ya dawo kota sake fitowa, yanzun din ma yana zaune ne karya tafi ta sake fita, yana kuma so yaga dawowar su Mami din ya duba jikin Amatullah, dalilan duka sun zauna mishi, dan baya tunanin akwai wani dalili baya hakan, numfashi yaja a hankali yana fitarwa, yana jinjina ikon Allah akan Waheedah din, yanda ta kubcewa fitowa a zabaya abin al'ajabine, hannuwanta da take wasa dasu ya tsayar da idanuwan shi akai, har faratan yatsunta farare ne.
'Wannan wanne irin haske ne?'
Ya tambayi kan shi yana sake sauke numfashin dayasa Waheedah kallon shi, duk cikin yayyen nasu shine basa hira dashi, bakama ga wannan fuskar ba, inba gaisuwa ba, saidai in shi da kanshi ya tambayeka abu zaka amsa, amman hira kam bayayi dasu, wani irin gudu taji zuciyarta ta kara, sautin na bugawa har cikin kunnuwanta, da labbanta da ta dagasu dakyar tana fadin
"Gobe In Allah ya kaimu zaka tafi ko?"
Da mamaki Abdulkadir din ya kalleta, yana dan daquna fuskar shi hadi da jinjina mata kai, wani abu Waheedah ta hadiye da takejin shi tsaye a makoshinta, batasan ya akai take son tambayar shi ba
"Hamma sai kayi shekara baka dawo ba ko?"
Kai ya sake jinjina mata, kamar bazaiyi magana ba kafin yace
"Menene?
Ba murna kuke zan tafi ba"
Wannan karin ita ta girgiza mishi kai, tana kallo ya sake kankance mata idanuwan shi kafin yace
"Karya ne..."
Yana sakata yin karamin murmushi
"Ki ban ruwa in sha Waheedah..."
Abdulkadir ya fadi yana kara gyara zaman shi akan kujerar, mikewa Waheedah tayi tana zuwa kitchen ta dibo ruwan ta kawo mishi, karba yayi yana shanyewa tas ya mika mata kofin data mayar kitchen, ta kai mintina uku a ciki tsaye batare datasan tunanin me takeyi ba.
Kafin ta fito tana komawa kan kujerar ta zauna, wannan karin tana kwantar da kanta a jikin hannun kujerar, agogon dake daure a hannun shi ya duba yana mamakin gudun da lokaci yayi dan har tara da rabi ta gota.
"Kinci abinci?"
Ya tsinci kanshi da tambayarta, dan yanda ta langabar dakai a jikin hannun kujerar yasa shi tunanin ko yunwa take ji, shi kanshi baici abincin ba.
A hankali Waheeda ta daga mishi kai, gyara zaman shi ya kara yi kan hannun kujerar.
Lumshe idanuwanta Waheedah tayi, batasan iya lokacin da suka dauka a haka ba, balle tasan bacci ya dauketa, cikin bacci taji muryar Abdulkadir din na fadin
"Ya jikin nata yanzun?"
A hankali ta bude idanuwanta tana kallon Mami, da sauri ta mike tana murza fuskarta
"Mami...
Ina Amatullah din"
Kallon ta Mami tayi
"Suna asibitin ita da Hajja, bacci takeyi, da sauqi ma sosai, zasu dawo da safe in shaa Allah..."
Numfashi Waheedah ta sauke, Abdulkadir da yake tsaye ya kalli Mami yana fadin
"Me yasa baku tafi da ita ba?"
Ware idanuwa Mami tayi tana kallon Abdulkadir din
"Asibitin sai munyi gayya Abdulkadir?"
Dakuna fuska yayi
"Da kun tafi da ita ai, ta zauna tanata kuka a waje"
Kallon ta Mami tayi, tana sakata sadda kanta kasa, sai yanzun take jin kunya ta lullubeta
"Harabar motoci Mami, ga sauro a wajen...nikam da kun tafi da ita"
Ya sake maimaitawa, yana kokarin tausasa harshen shi saboda Mami ce, dan murmushi Mami tayi, tasan halin yaron sarai, ta kuma san kokari yake kar maganar da yake tayi kamar yana mata fada ne.
"Ai mun dawo yanzun"
Mami ta fasi da murmushi a fuskarta.
Kai Abdulkadir ya jinjina mata
"Sai da safen ku.
Allah ya kara sauqi"
Yai maganar yana ficewa daga dakin kafin yace komai, kamar hakan Waheedah take jira ta karaso tana kwantar da kanta a jikin Mami data tureta tana fadin
"Ke yanzun meye na kuka?
Ke da zakiyi mata addu'a?
Ke komai na kuka ne?"
Dariya Waheedah din tayi tana jin hankalinta ya kwanta, bin Mamin tayi suna hira, kafin tai mata sallama ta wuce dakin su.
Sai taji dakin yai mata shiru, musamman data kwanta, da yanzun Amatullah din tana mata tsegumin juye-jujen da take inta yi bacci, dan da yawan lokutta tana cikin bacci zataji Amatullah ta dala mata duka, ta kwashe kafafuwanta data jibga mata ta warbar gefe tana fadin
"Adda Wahee ki kasheni saiki huta"
Dariya tayi ita kadai, mikewa tayi ta kashe wutar dakin, tana daukar yar karamar fitila mai batir ta maqala a cikin hular dake saman kanta, tukunna ta kwanta tana janyo littafin ta dan taci gaba da karantawa.
Idanuwanta da taji har zafi suke mata yasata lanqwasa shafin data tsaya din, tayi addu'ar bacci tana rufe idanuwanta, soyayyar Asma'u da Jikamshi na mata tsaye, soyayyar tasu na sata tunani kala-kala, kafin bacci yayi awon gaba da ita cike da mafarkin su.
Bangarensu ya nufa ya shiga kitchen tunda girkin Hajja ne ranar, tuwon shinkafa ne tayi da miyar taushe data sha albasa mai lawashi sai kamshi take.
Yanajin dadin girkin Anty da Mami, amman abincin Hajja daban yake jin shi, a wajen shi duk wani abinci da zaici bayan na Hajja zai biyo, baisan ko kaunar da ke tsakanin su bace ta rufe mishi ido.
Anan kitchen din ya tsaya yana dora abincin kan kantar kitchen din, hannun shi ya dauraye jikin famfon dake gurbin wanke-wanke.
A tsayen yaci abincin.
'Kaga zaka tafi wani gari da babu idanuwan mu akan ka, dan Allah ka rike addininka, karkai wasa da sallah, in har kana yinta cikin lokaci, kana kokarin yinta yanda ya kamata zata kare maka aikata abubuwan dabai kamata ba.
Kuma ka rage zafin zuciya, dan Allah Abdulkadir ka dinga sakama ranka salama'
Nasihar da Abba yai mishi ta dawo mishi, kai yadan jinjina yana karasa cinye abincin ya wanke hannun shi ya fice daga dakin.
Bangaren su ya koma, babu kowa a falon sai Yassar daya kalle shi cike da mamaki
"Daga ina kake haka kaikuma?"
Saida ya zauna tukunna ya daquna ma Yassar din fuska
"Hamma kana tsareni da tambaya kamar yaro"
Dariya Yassar yayi
"Nakai shekarun dazan fita in dawo sanda naga dama"
Dare yayi, dan sha daya harda rabi, gashi bayajin yana da karfin biyewa rashin kunyar Abdulkadir din da zuwa yanzun inda sabo ya kamata ace ya saba, in wani yaiwa a waje su Hajja yake jama zagi, mutane naganin bai samu wadatacciyar tarbiya ba.
Abin nama Yassar takaici, mutane nabashi mamaki, yanda sukan dora laifin yara akan iyayensu batare da kwakwwarar shaidar cewa laifin na iyayen bane na ci mishi rai.
A ganin shi burin kowanne iyaye dansu ya zamo nagartacce, ya zamo abinda zasuyi alfahari dashi.
Baice wasu lokuttan ba'a samun baraka daga bangaren iyayen ba, baice ba'a samun sakacin iyaye a kan tarbiyar yaransu ba, amman hakan baya nufin duk wani abu da yaro zaiyi saiya zamana laifin iyayen shine, kowanne dan Adam yana da zabi a rayuwa, cikin zabin harda fatali da tarbiyar da iyaye kan dora yaransu akai, a bangaren Abdulkadir din kusan zaice hakane, tun yana da karancin shekaru yake da wata irin zuciya, da ko laifi yayi in zaka kasheshi da duka bazai ko motsa ba ballantana yai tunanin gudu, ko wani yazo ya da nufin janye shi zai nuna bayaso.
Yana tuna lokuttan da Hajja ke dukan shi akan abubuwa da dama, kafin Abba yace tana binshi da addu'ar shiriya tunda dukan baya aiki, ga bakin shi bazai shiru ba, inka fadi daya saiya fadi goma, musamman in yana ganin akan gaskiyar shine, komin girmanka baka wuce Abdulkadir ya datsa maka maganar duk da tazo kan shi ba.
Kallon shi Yassar yayi yana fadin
"Dan Allah ka kula da kanka, banda fada da mutane, banda rashin kunya..."
Murmushi Abdulkadir din yayi yana sa Yassar tashi daga kishingidar da yayi a jikin kujerar yana gyara zaman shi sosai
"Nasan fada dai sai kayi, dan Allah banda fadan da babu dalili"
Kankance mishi idanuwa Abdulkadir yayi
"Nasiha kake mun?"
Duka Yassar yakai mishi da yasa shi ture Yassar din yana fadin
"Cin zali babu kyau"
Hadi da mikewa dan kan shi yakeji ya mishi nauyi
"Idan nabar gidan saika nemi wanda zakaci zali"
Ya karasa maganar yana wucewa hadi da turo kofar dakin shi, murmushi Yassar din yayi yana komawa kan kujerar ya kwanta yana sauke numfashi.