← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 94

Sashe 42

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nasan halin shi, nasan bazai sameni batare da amincewarki ba, amman ina so in tabbatar daga bakinki Waheedah, amana ceke a wajena kamar yanda suma suke amana, banma kowa maganar ba tukunna, ki fadamun idan kin amince da auren shi..."
Kanta a kasa yake tunda ya fara magana, bata taba tsintar kanta cikin kunya irin wadda takeji ba, wasu zasuce kamar kasa ta tsage su shige, a irin kunyar da take ciki ba tajin zata iya jiran kasar ta tsage, ita take so ta narke ta sulale tabi kasar ta shige cikinta.

Ga zuciyarta da take wata irin dokawa kamar zata fito daga kirjinta
"Kimun magana Waheedah, karkiji nauyina, idan har baki amince dashi ba yazo ya sameni ki fadamun, wallahi indai ina numfashi babu wanda zai miki dole akan komai na rayuwa..."
Shirun ta sakeyi tana kara sadda kanta kasa, numfashi Abba ya sauke
"Aure ba abu bane da akanyi dan kowa nayi, ba kuma abu bane da ake fatan idan anyi a fito, aure abune da ake fatan idan har anyi ya zamana har muddin rai, shisa ba'a son gaggawa a cikin duk wani abu daya shafe shi, ba'a kuma son tursasawa, da fahimtar juna ma dole sai an hada da hakuri a zamantakewar da za'a tashi a kwana karkashin inuwa daya.

Kimun magana Waheedah, bazan samu nutsuwa akan maganar nan ba..."
Kanta da takejin yaima siririn wuyanta nauyi naban mamaki yau ta samu ta motsa tana dagashi a hankali, da ace nutsuwar Abba bata kanta da bazai ga daga kan ba
"Kin amince da auren shi?"
Abba ya tambaya yana son tabbatar wa, kan ta sake daga mishi a hankali.

Wani numfashin ya sauke, yana jinjina ma karfin kaddara da take zuwa karkashin ikon Allah.

Kai ya jinjina
"To Alhamdulillah, Allah ya tabbatar mana da alkhairi..."
Kafafuwanta Waheedah ta tattara, har lokacin ta kasa dago fuskarta, jikinta gabaki daya ya dauki dumi da kunyar Abba da takeji, mikewa tayi dakyar tana juyawa cikin sauri da nufin barin dakin
"Kizo ki karbi kudin makaranta..."
Abba ya fadi yana saka hannu a aljihun shi, amman kamar maganarshi ta kara tunzurata, da gudu ta fice daga dakin tana ja mishi kofar.

Murmushi Abba yake
"Oh Allah mai iko..."
Ya fadi, ya jima wani abu bai bashi mamaki ba irin na daren jiya zuwa safiyar yau.

Da gaske AbdulKadir da Waheedah sukeyi, yanda yake jinshi zai kwana biyu yana jinjina al'amarin.

Wayarshi ya dauka ya kira Mami dan ya sanar da ita kafin ya samu dangin Baban Waheedah din da maganar, duk da sun jima da nuna mishi yana da damar yanke hukunci akan rayuwar Waheedah din bazai hanashi nuna musu godiya da halaccin da sukai mishi ba, zai samesu da maganar duk da yasan ba zasuki kowa yake son hadata dashi ba, balle kuma idan sunji jinin shi ne.

"Ina zaki je?"
Muryarshi ta sauka cikin kunnuwanta, tana sakata gyara zaman jakar dake kafadarta tukunna ta juya tana sauke idanuwanta akan shi.

Jikin shi sanye da riga fara kal, sai wandon sojoji gajere da silipas din wanka a Kafafuwan shi.

"Hamma..."
Ta kira da wani yanayi a muryarta, wani irin son shi taji ya taso mata har yana ma numfashinta barazana.

Tasan ya kamata ta sauke idanuwanta daga kanshi, ta daina kallon shi, amman zuciyarta ce da iko kan idanuwanta wannan karin, ta kuma nuna mata bata gaji da kallon shi ba.

Shima idanuwan shi ya kankance akanta da dakyar take ganin kwayar cikin su, fuskarshi a kumbure take har idanuwan da alamar rashin wadataccen bacci.

"Ina zaki je?"
Ya maimaita tambayar yana kallonta, tsaye yake ya hango hijabinta da yake share harabar gidan, blue ne mai hasken da yai mishi kyau sosai.

Badan baya ganin masu saka hijab ba, amman kowa zai gani da hijab itace mace ta farko da take zuwa mishi a rai, kuma bai taba ganin wanda hijab yake ma kyau kamarta ba, zai rantse yanayin tafiyarta a cikin hijabanta daban yake.

Kamar hijab din na bata wani asirtaccen confidence da idanuwa basa iya gani, sai yaga kamar ba Waheedah mai sanyin halin nan ba, kwarjininta daban yake mishi in tana cikin hijabanta.

Idanuwanta take raba mishi, wannan karin cike da wani yanayi da ya saka jikinshi daukar dumi, kalar hijabin ta kara mata farin da yasa shi furta
"Wanne irin mai kike shafawa?"
Da mamaki
bayyane a fuskarta tace
"Vaseline..."
Kankance mata idanuwa ya karayi
"Yana kara haske?"
Dariya tayi tana girgiza mishi kai
"Hamma Vaseline fa"
Kafadunshi yadan daga mata, bazai sani ba, tunda haske take kara mishi a duk ganin dazai mata.

"Ina zaki je?"
Ya sake tambaya a karo na uku.

Da murmushi a fuskarta har lokacin tace
"Makaranta..."
Ta dauka wani abu zai canza tsakaninsu da maganar auren, amman bataji komai ba ita kam, banda soyayyar shi da duk lokacin da zata dauka babu wani waje a jikinta daya rage wanda baya dokawa da soyayyarshi, sai ta sake jinshi a wani wajen da batasan yana motsi ba.

Babu abinda ya canza, shidinne dai, Hammanta, Sadaukinta, ko babu maganar auren batajin akwai inda zatakai soyayyar shi.

"Da sassafen nan?

Waye zai kaiki?"
AbdulKadir ya fadi yana katse mata tunanin da takeyi
"Ina da class, nama makara, napep zan hau..."
Kai ya fara girgiza mata yana sata dorawa da
"Ina zuwa Hamma, ba kullum ake kaini ba"
Kan AbdulKadir yake girgizawa har lokacin, yaushe Waheedah din tai girman da zataje makaranta, ta tafi ita kadai bai zauna mishi ba sam
"Na iya zuwa Allah"
Ta fadi ganin shakkun dake cikin idanuwan shi
"Ki jirani ina zuwa..."
Cewar AbdulKadir din yana juyawa da sauri.

Binshi tayi da kallo harya shige bangarensu, idanuwanta akan kofar tana jiran fitowarshi da dukkan zuciyarta.

Baifi mintina biyar ba taga ya fito yana takowa zuwa inda take, tari tadanyi da yanda zuciyarta ta matse cikin kirjinta kamar akanta yake tafiyar.

"Muje..."
Yai maganar yana yin gaba, tabishi a baya har wajen motar Yassar, mukullin yasa yana bude kofar, ita kuma ta zagaya, saida ya zaro wayarshi daga aljihun bayan wandon tukunna ya shiga ya zauna, hannu ya mika ya bude ma Waheedah dayar kofar ta shigo itama.

Wayarshi ya dora kan cinyarta kamar babu inda zai iya ajiyewa a cikin motar gabaki daya.

Daukar wayar tayi ta rike a hannunta, tanajin shi ya tayar da motar yana jansu suka fice daga gidan.

"BUK, old site..."
Tace mishi
"Nace miki bansani ba?"
Kai ta girgiza mishi
"Me yasa kike fadamun to?"
Ya sake maganar yana dan kallonta kafin ya mayar da hankalin shi kan tuqin da yakeyi.

Har malamansu gabaki daya yasani, bazai ce ga course din da take dashi ba a ranar, amman idan ya duba wayarshi zai iya fada mata, a cikin labaranta gabaki daya yasan hakan, me yasa take tunanin bai rike ba?

Dan bai amsa ba baya nufin bai karanta ba, baya nufin hankalin shi baya kai.

Shiru tayi bata amsa shi ba, tunda tasan halin shi.

"Bakici abinci ba...bakici komai ba kika fito"
Yai maganar kamar tunanin ya fado mishi.

Girkin Mama ne har ranar, da yunwa ya tashi ya kuma je bangarenta bata gama ba, lokacin daya shiga ma ake fere doya.

Ko da yayi maganar da alamar tambaya ne, Waheedah batajin zata amsa shi, bazai sauke mata fadanshi da sassafe ba.

"Kinsan yanda abincin safe yake da muhimmanci?"
Murmushi taji ya kwace mata, ba abincin safe bane kadai yake da muhimmanci a wajen AbdulKadir, duka abinci nada muhimmanci dan baya wasa da cikinshi ko kadan.

Wani shago ya hango hakan yasa shi tsayawa, batare dayace mata komai ba ya fice daga motar.

Wayarshi dake hannunta ta latsa dan taga ko karfe nawa, zuciyarta nayo tsalle zuwa makoshinta ganin hoton dake kan wayar.

Hannuwanta ne babu tantama, da kunshinta da bata manta ranar daya dauka ba.

"Hamma..."
Ta fadi da wani irin yanayi a muryarta tana shafa screen din wayar.

Dai-dai lokacin da AbdulKadir ya bude motar ya shigo yana dora mata leda akan jikinta da kashedin
"Karki sake fitowa bakici wani abu ba"
Bata abinci takeyi ba, kallon shi take tanajin wani irin yanayi da bazai fassaru ba, har suka karasa makarantar babu wanda ya sake cewa wani abu.

Har department dinsu ya kaita yana zaune cikin motar saida yaga ta shiga aji tukunna ya sauke numfashin da baisan yana rike dashi ba, kafin yai wata irin hamma, ba wani bacci ya samu ba jiya, yana kwance yana tunanin yanda akai rayuwa ta kawo shi inda yake yanzun.

Sai dai zuwa safiyar yau komai ya mishi dai-dai.

Tana son shi, zai aureta, ya rigada ya gama duk wani tunani da zaiyi akan hakan.

Yanzun yaga garin da aka kaishi ne abinda yake ranshi, sai yai magana da Hajja dan yaji ko nawa ne zai tara.

Juya motar yayi yana nufar gida.

Sallar azahar ya dawo, yana kwance a daki yaji an turo kofar kamar za'a karyata
"AbdulKadir me kayi?"
Yaji muryar Yassar din ranshi da alamun a bace yake.

Sai dai a iya tunanin AbdulKadir din baisan ya mishi wani abu da zai bata mishi rai ba.

A nutse ya tashi daga kwanciyar shi ya zauna yana dakuna ma Yassar din fuskarshi cike da rashin fahimta.

"Kajini ai, me kayi?"
Yassar ya sake fadi yanajin yanda yake gab da kwashe AbdulKadir din da mari.

Aiki ya fita, yau da wuri yake tashi, yana dawowa yakejin ana maganar auren AbdulKadir din da Waheedah cikin wata shidda tare za'a hada da nasu Yazid.

Maganar yake ji kamar wasa, saida ya tambayi Mama tace mishi da gaske ne, Abba da kanshi ya fada musu.

Yasan halin AbdulKadir zai iya cewa fiye da kowa a gidan, yasan yanda yake son kanshi fiye da tunani, amman bai dauka yakai haka ba.

Bai dauka yakai yai amfani da soyayyar da Waheedah din take mishi ta wannan fannin ba.

"Kaimun magana yanda zan gane Hamma..."
AbdulKadir ya fadi a kasalance, bacci yakeji, kuma da niyyar yin baccin ya kwanta
"Waheedah...

Me kayi AbdulKadir..."
Dan dafe kai AbdulKadir yayi yana fadin
"Oh...
Chapter 42 · 0% Book details