← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 94

Sashe 68

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Igiyar aurenki a hannuna take, yanzun kuma na fara rikon ta, kaya kuma Allah ya baki iko, kina jina?

Allah ya baki iko dake da duk wanda yake da tsautsayin shigomun gida da nufin tayaki kwashe su...

Aljanu ne kike dasu da bansani ba sai yanzun, to wallahi ko su ubansu yayi karya....ke da kanki ma kinyi karya kisani yin abinda banyi niyya ba"
Kallon shi Waheedah takeyi itama tana tsintar kanta da mikewa tsaye
"Ana dole ne?

Nagaji...

Nagaji da aurenka"
Cikin hargowa yace
"Ni bangaji ba, gajiyarki bata da wani muhimmanci"
Dariya Waheedah tayi tana jin duk wani kwanciyar hankali data samu a kwanakin nan na bace mata
"Abubuwa da yawa da suka shafeni basu da muhimmanci a wajenka daman, saboda haka banyi mamaki ba"
Cike da rashin fahimta AbdulKadir yake kallon ta
"Bangane abubuwa da suka shafeki ba suda muhimmanci a wajena ba"
Gyarama Ikram zama ta sakeyi a jikinta tana kara tallabeta
"Kwakwalwa ce a kanka duk da bako yaushe kake amfani da ita ba, sai kayi tunani ai"
Kallon ta AbdulKadir yakeyi, ya dauka ya gama shan mamakinta tunda ta iya bude baki ta nemi ya saketa, amman da duk wani gani da zai mata bayan haka da yanda take kara shayar dashi mamaki
"Zagina zakiyi Waheedah?"
Kai ta girgiza mishi, zagi ba dabi'arta bane tunda can, ko Fajr ma zata kirga lokuttan da ta zage shi balle shi AbdulKadir din
"Idan ba zagi ba, me maganganun ki suke nufi?

Rashin kunya kike neman yimun da bansan lokacin da kika koyeta ba"
Yake karasa maganar da wani irin bacin rai marar misaltuwa
"Nifa ban zageka ba, rashin kunya kuma in dai koya nayi bai kamata kayi mamaki ba tunda nayi rayuwar aure da kai"
Da hannu yake nunata
"Gashi nan...

Yanzun me kikayi..

Wani zagin ne wannan ai...

Wallahi Waheedah ki kiyayeni, kina gwada hakurina...

Kuma tashi zakiyi mu koma gida"
AbdulKadir yayi maganar yana son ture alamun da yakeji kamar na tsoro na son taso mishi, ga hankalin shi da yake a tashe kasan bacin ran da yake fama dashi, musamman da Waheedah tayi mishi wani irin kallo tana komawa ta zauna tare da fadin
"Saika daukeni ka dora saman kai ka mayar dani ai"
Kai AbdulKadir yake jinjina mata, inda take ya karasa, rashin hankali take nuna mishi karara, zai nuna mata duk abinda takeji dai-dai yake da ita.

Belt din da yake kafadunta na jakar goyon yake kokarin ballewa, ta ture hannun shi
"Me kakeyi?"
Ta tambaya muryata cike da tsoro, hannuwanta AbdulKadir ya kama duka biyun yana saka karfi ya rike su, belt din ya kwance duk ihun da Waheedah take mishi, da hannu daya ya zame Ikram yana sauketa daga jikin Waheedah din
"Sadauki ka sakeni, dan Allah ka kyaleni, kaga Ikram na kuka"
Waheedah ta karasa tanajin idanuwanta sun ciko da hawaye duk yanda ta fadama kanta ta gama yi mishi kuka
"Ashe muryarki na sauka haka, harna manta saboda yanda kike dagamun ita a kwanakin nan"
Cewar AbdulKadir din yana kama hannuwanta da yake rike dasu ya dagota ya mikar tsaye, zuwa lokacin ta daina kiciniyar kwacewa, dagata yayi yana sabata a kafadar shi kamar ya dibi kayan wanki, yasa hannuwan shi yana mata rikon da tasan ko da wasa ba zata iya kwacewa ba, ikon Allah take saurare kawai tana tabbar da AbdulKadir na da tabin hankali, bata sani bane tuntuni sai yanzun.

"Wallahi ka saukeni, wannan kidnapping ne, shekara goma sha biyar zakayi a gidan yari"
Dariya AbdulKadir yayi, wannan karin tana fitowa daga bangaren zuciyarshi daya kwana biyu baiji ya buga mishi ba.

"Ka saukeni, bana son haka, ka saukeni...ko ka kaini ba zama zanyi ba Sadauki...na fada maka nagama aurenka"
Hanyar da zata fitar dashi daga dakin ya nufa yana bude kofar yaci karo da Yassar da ya miko hannu da alama yana shirin kwankwasa kofar ne koya bude.

Dan tunda ta shigo gidan yakejin kamar maganganu shisa ya nufo bangaren Waheedah din, muryarta na tabbatar mishi da AbdulKadir na ciki.

Yanayin maganganunta ne ya hanashi bankada kofar kar yaga abinda bai kamata ba, tunda yasan AbdulKadir ba hankali gare shi ba ballantana kunya.

Sai dai baki a bude yake kallon AbdulKadir din
"Ka matsamun Hamma..."
Ya fadi yana gyara ma Waheedah zama a kafadar shi
"Me kakeyi AbdulKadir?

Me kakeyi?"
Yassar yake tambaya yana kallon AbdulKadir din kamar a film, dan bai taba ganin abinda yakeyi a zahiri ba, cikin kuka Waheedah take fadin
"Hamma kace ya saukeni, dan Allah kayi mishi magana, ni bazan koma gidan shi ba..."
Muryar Yassar har lokacin da mamaki yace
"Ka sauketa AbdulKadir....

Ka sauketa tun kafin ranka ya baci"
Kankance idanuwa AbdulKadir yayi
"Ita tace in dauketa a kai in tafi da ita..."
Waheedah najin hawayen dake digar mata, ga kanta daya fara tara jini saboda yanayin yanda AbdulKadir din ya riketa
"Ni bance mai ba Hamma...

Dan Allah kace ya saukeni"
Kokari Yassar yakeyi kar murmushi ya kwace mishi, idan AbdulKadir yaga alamar wasa koya take tattare da Yassar din bazai sauke Waheedah ba
"Ka sauketa nace maka AbdulKadir..."
Baisan ya akayi maganar Yassar din tayi tasiri akan shi ba.

Sauketa yayi tana dafa kofar wajen jin zata fadi, tana tsayuwa sosai tasa hannu tana goge fuskarta, dankwalinta batasan ma lokacin daya fadi ba, ga wata irin matsananciyar kunyar Yassar din da ta kamata.

Wani irin kallo ta watsa ma AbdulKadir din
"Aurenka ko na zobe ne sai ka rabu dani...

Kuma wallahi saina fadama Abba"
Ta karashe maganar wasu hawayen takaici masu zafi na zubo mata.

AbdulKadir kuwa Yassar ya kalla
"Kagani ko?

Hamma kanajin irin rashin kunyar da take mun"
Hannu Yassar ya daga mishi
"Ka wuce ka tafi"
Kafada AbdulKadir ya makale
"Ni bangama magana da ita ba"
Kai Yassar ya girgiza yana sauke numfashi, so yake yabar wajen kafin dariya ta kwace mishi.

"Ka tabbata zakai mata magana kamar mai hankali?"
Kai AbdulKadir din ya daga mishi, saida Yassar din yadan tsaya tukunna ya juya.

Kofar AbdulKadir ya tura yana mayar da hankalin shi kan Waheedah data dauki Ikram tana kokarin lallashin ta
"Babu ribar da zakici a fada dani Waheedah...

Ki taho mu koma gida, na baki hakuri..

Kiyi hakuri dan Allah.

Kizo mu koma...

Kinga ni bana son yin fada dake"
Ya karasa maganar yana sauke muryarshi, amman a idanuwanta yake ganin yanda maganganun shi ko kadan basuyi tasiri ba, ci gaba yai da fadin
"Kinji Wahee...

Kina ta dagamun hankali akan magana karama, Wallahi kwanana biyar a barikin sojojin garin nan, ki kalli fuskata, na manta rabona da wadataccen bacci balle abincin kirki..."
Yayi maganar yana kama rigar jikin shi ya daga mata, jinine yayi baqiqirin a gefen cikin shi da duka hakarkarin shi, tana kallo ya juya mata har bayan shi da nan ma jinin ne a kwance, kowanne irin duka akai mishi ba karami bane ba, zuciyarta takeji a bushe babu wani abu da take sonyi banda shakar numfashi batare da igiyar auren shi ta daure mata wuya ba.

Sakin rigar shi AbdulKadir yayi
"Ban shigo da nufin yin fada dake ba, har kudin hidimar gida na tura miki dazun..."
Kalamai yake nema da zai lallasheta dasu, amman ya rasa, saboda basu taba fada ya wuce yini daya ba, koyace bata taba fada dashi ya wuce yini daya ba, tunda ba biye mishu takeyi ba, ita ta saba lallashin shi, shisa komai ya kwance mishi.

Takawa yayi ya karasa yana kamo dayan hannunta da yake jikin Ikram yana sakata sake rike yarinyar sosai
"Kinga azumi ya kusa, saura kwanaki kadan, ana yafewa juna kafin azumi, bama kyau fada kafin azumi"
Cikin idanuwan shi Waheedah ta kalla
"Ka saukake mun kafin azumin...dan Allah Sadauki...kaji...ka sakeni in huta nima.

Nagaji da auren ka"
Ta karasa maganar tana zame hannunta daga cikin nashi ta share kwallar data zubo mata.

Wani irin numfashi AbdulKadir ya sauke yana juyawa ya fice daga dakin, bai tsaya ko ina ba sai cikin motar shi, tayar da ita yayi ya fita daga gidan Yassar, a gefen hanya yayi parking yana hade kan shi da abin tuqin motar.

Kan shi ciwo yake da bashida alaka da yunwa ko rashin bacci.

Wani irin tsoro yakeji da bai taba sanin akwai shi ba.

Kalaman Waheedah ke mishi yawo da wani yanayi naban mamaki.

Batayi mishi maganar da hayaniya ba, asalima idanuwanta cike suke taf da hawaye, da neman alfarma, bata taba rokon wani abu a wajen shi ba, yaune yake ganin alamar tana rokon shi, kuma rokon farko daya shiga tsakanin su shine na ya rabata da auren shi, si take ya bude bakin shi ya furta mata kalaman da zasu warware igiyar da bai yarda an kullata tsakanin su ba saida nufin mutuwa ce kawai zata raba.

Bai taba tunanin cewa zata roke shi wani abu da zai kasayi mata ba, kodan girman matsayinta a wajen shi, amman sai ta tambayeshi abinda yakejin duk duniya babu wanda ya isa ya sakashi yin shi.

Wani irin tsoro yakeji daya danne duk wani abu da yake damun shi.

Lumshe idanuwan shi yayi yana hango yin rayuwa babu Waheedah, da sauri ya bude su yana dagowa daga jikin motar, dan jin shi yayi duniyar tai mishi wani irin girma, ga kadaici naban mamaki daya lullubeshi.

Da aurenta yasan akwai abinda babu a rayuwar shi sai bayan ta shigota, daga randa igiyar aure ta hadasu zama a karkashin inuwa daya bai kara hasko wani lokaci a rayuwar shi da babu ita a ciki ba.

Ko tunanin mutuwa yake bai taba hango zata riga shi ba, abu ne da tunanin shi ma baya hasaso mishi.

Film idan yana kallo indai za ai mutuwa, yafi son yaga mijinne ya mutu yabar matar, dan baisan yanda zaiyi da sauran rayuwar shi idan babu ita a ciki ba.

"Bazan iya sakinki ba Waheedah...

Ko meye nai miki me zafi haka hakuri zakiyi ki dawo.

Inke zaki iya barina ni bazan iya barinki ba wallahi...

Bazan iya ba"
Ya karasa maganar yana dafa fuskarshi da duka hannuwan shi biyu.
Chapter 68 · 0% Book details