← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 94

Sashe 38

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kan kafet suka zauna, cokali AbdulKadir ya saka cikin abincin yana jujjuyashi, yanayin taliyar bai mishi ba sam, yakanci kome Waheedah ta dafa ta bashi, bai saba fada mata ga abinda yake son yaci ba, idan unguwa taje ma saita gama mishi girki take fita indai yana nan.

Zubawar kan zame mishi aiki, da lokacin cin abincin yayi zata kirashi a waya taji ko yaci.

Lokutta da dama zai saka mata rigima saita baro duk inda take ta dawo sunci tare, ko yace shi baisan yanda zai zuba ya isheshi ba, haka zata fada mishi ludayin dazai amfani dashi, ko guda nawa zai zuba, miya tasa ya samo wajen zubawa ya zuba tace ya dinga diba yana sakawa a abincin inya rage saura ya saka mata a fridge.

Sai dai Waheedah ce, tasan abinda yake son ci, tasan abinda bayaso, taliya na daya daga cikin abincin da bawai ya dameshi bane, gara da miya, amman jalof haka tsuranta bata dameshi ba.

Idan Waheedah tayi tana hada mishi salad sai yaci, idan yace ta dafa taliya, takance mishi tana son ya dinga cin komai saboda inya koma wajen aiki bata kusa.

Sosai yake cakuda taliyar yana tunanin sakata a bakin shi, naman ma ko kadan bai mishi ba, idan a wajene babu yanda zaiyi saiyaci, amman cikin gidanshi bai saba da abinci irin hakan ba.

Bayason yin wani dogon nazari ya nannado taliyar yana sakata a bakin shi.

Nuriyya yake kallo da take cin abincin hankalinta a kwance, kamar yana mata dadi, abinda baisani ba, bawai abincin ya mata dadi bane, ita kanta taji yanda gishiri yadanyi yawa.

Sai dai yunwa takeji ta fitar hankali, inda baya nan ma zataje ta hada shayi.

Amman batason nuna mishi yanda abincin bai mata ba.

Dakyar Abdulkadir ya hadiye taliyar dake bakinshi yana dubawa danya dauki ruwa, bata kawo mishi ba
"Baki bani ruwa ba..."
Ya furta, sai lokacin ta dago tana kallon shi, mikewa tayi ta dauko mishi ruwa a fridge tazo tana kawo mishi.

Ganin ya kalleta yasa ta komawa ta dauko kofi tazo ta ajiye, budewa ruwan tayi tana zuba mishi, dauka yayi yasha, ruwan ya kulle mishi ciki lokacin daya dira cikin hanjin shi, ko kadan bazai iya cin taliyar nan ba, ganin ya bai dauki cokalin ba yasa Nuriyya fadin
"Har kayi me?"
Daquna mata fuska yayi
"Bana son taliya Nuriyya..."
Da rashin fahimta take kallon shi
"Idan Waheedah ta dafa kana ci"
Kai ya jinjina mata da taji kamar ya watsa mata garwashin wuta, tabbatar mata yake tata ce bazai ci ba, amman yanacin ta Waheedah, magana zatayi ya dora da
"Ba irin wannan bace"
Cokalinta ta ajiye itama, tana danne kishi da tuquqin bakin cikin daya taso mata tayi mishi wani murmushi
"Kaci naman to"
Baiyi musu ba, cokalinshi ya dauka yana kokarin sabulo tsokar naman, amman yaji abu ya gagara, idan abincin Waheedah ne yana saka cokali a jikin naman yake raboshi da kashin shi saboda ya dahu.

Ajiye cokalin yayi yasa yatsun shi ya tsamo cinyar yana kaiwa bakin shi ya kafa hakori a ciki, qiri-qiri yaji naman, kona waje yafi shi dahuwa, gutsura yayi yana taunawa, ruwan naman na sauka bakin shi da wani dandano marar dadi, gashi ko maggin kirki bai kamashi ba.

Ajiye na hannun shi yayi yana dakuna fuska
"Wanne irin nama ne wannan?

Bai dahu ba..."
Abdulkadir ya fadi yana ciro na kora wanda ya gutsura da ruwa
"Bangane bai dahu ba..."
Nuriyya tai maganar a kufule, kankance idanuwan shi yayi yana kallon ta
"Kici a bakinki..."
Naman ta sa hannu ta dauka ta gutsura, ita kanta taji bai dahu ba, ajiyewa tayi kunya na kamata, tasan bata iya girke-girken nan ba, girman kanta kuma bazai taba barinta tace Waheedah ta koya mata ba, shisa take ta damun shi daya dauko mata 'yar aiki, kuma ko da ta iya ma, Allah ya dora mata ganda, ba zata iya girke-girken da Waheedah ke yini tana yi ba.

Duk ranar girkinta takanja jiki, kota jashi tace suje bangaren Waheedah din su tayata hira, dan suci abinci acan din.

Farko-farko ta dauka Waheedah din kan basu saboda Abdulkadir din ne kawai.

Saida taga ko baya nan taje bata hanata, wani lokacin takan aika Fajr ya kirata tazo ta dibi abinci.

Yanda Abdulkadir din bai taba kula tana gujema girki ba har mamaki yake bata.

Addu'a take Waheedah karta jima a asibitin, dan taga alamar zasu samu matsala da Abdulkadir kan abinci.

Mikewa yayi da alama ranshi a bace yake, yana sawa ta mike itama
"Dan Allah Masoyi kayi hakuri, cikin sauri nayi girkinne dan naga yamma tayi..."
Baice mata komai ba ya rabata ya wuce, ranshi a bace yake, kuma yunwa yakeji, idan yai magana baida tabbacin abinda zai fito daga bakin shi, addu'a yake kartai kokarin binshi dan baisan me zai faru ba...!
*#TeamAbdulKadir*
*#TeamWaheedah*
*#TeamYassar*
*#AnaTare*
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
Tunda suka shiga gidan Yassar ta gaisa da matar shi Hawwa da yar kanin Abba ce ya aura, ta samu kujera a falon ta zauna.

Batasan me Yassar din yace mata ba, taga dai tazo tace mata ta tashi taje ta huta, daya daga cikin bedrooms din dakin ta rakata.

Fajr kin binta yayi saboda yana kallon cartoon, da yake Yassar din ma yakan je ya dauko shi yai hutun karshen mako a gidanshi wasu lokuttan, yaron ya saba dasu.

Tana shiga ta kwantar da Ikram, bandaki ta shiga ta daura alwala dan ko sallar azahar batayi ba.

Ta fito ta gabatar da sallah, zaune tayi akan kafet din tana dora kanta a jikin gadon, kanta a cunkushe take jin shi, ta rasa abinda yake mata dadi a gabaki daya duniyar.

Tunani ne ya dauketa yana watsata shekaru Shida da wasu yan watanni da suka wuce, kafin rayuwa ta kawota inda take.

Tun bayan bikin Nuriyya, sai ya zamana babu abinda Waheedah ta saka a gaba banda karatunta, takanyi kwana biyu bata leqa gidan Nuriyyar ba, duk da ba wani nisan kirki ne a tsakanin su ba, ita tana cikin Naira da kwabo, su kuma su Waheedah din a kofar ruwa, ko da kafa zata gangara.

Amman suna yawan waya, kusan kullum zasuyi chatting, wani lokacin kuma inta riga Nuriyya tashi daga makaranta takan biya ta FCE dinsu sai su gaisa.

A yanayinta take fuskantar yanda har lokacin taqi kwantar da hankalinta da auren Anas din.

Sai dai fadan da Waheedah take mata yasa ta daina gaya mata komai, inta tambaya ma sai dai Nuriyyan tayi murmushi tace mata lafiya kalau, duk da tasan karya take, bata takurata, kullum Nuriyyar na cikin addu'o'inta akan ta samu kwanciyar hankalin da kowacce mata take samu a dakin aurenta, tare da mata addu'ar nutsar da hankalinta da auren Anas din.

A bangaren samarin da suke kawoma Waheedah tayin soyayya ma babu abinda ya canza, dan bata fasa gaya musu cewar an mata miji ba, kamar yanda bata fasa bama AbdulKadir labarin yanda ranarta ta kasance a kullum ba.

Duk da yanzun saqqonin nata na zuwa, suna kuma nuna alamar an karanta.

Amman tun kafin bikin Nuriyya rabon da ta samu amsar shi.

Batasan ya akai ba, amman a shirunshi take karantar akwai abinda yake damun shi, tana kuma jin hakan har kasan zuciyarta, kuma koma menene yake damun shi din, tare suke cikin damuwar, dan itama nata hankalin ba'a kwance yake ba.

Daina kirga kwanakin zuwan shi tayi, zasu fi mata sauri idan bata kirga ba, sosai ma tayi mamakin kanta da bata taba tambayarshi yaushe zaizo ba.

Tana alaqanta rashin yin hakan da yanda jikinta yake bata ba lafiyar shi ba.

Haka rayuwa taci gaba da tafiyar mata har bayan shekara daya, shekarar da tayi dai-dai da lokacin fitar AbdulKadir daga NDA.

Lokacin da har a fuskar Mami takan karanci damuwar da ta kasa furta mata akan rashin wani da za'a nuna ace yau yazo zance wajenta.

Musamman da aka sa bikin Zahra, dan wannan karin yara uku Hajja zata aurar, Zahra, Mubarak da kuma Yazid da sai yanzun da alama surutun kowa ya ishe shi ya fito da matar aure, duk da sukan jima basu sakashi a idanuwansu ba, da alama yabar Kano din kenan kuma sai dai ziyara.

Duk da gidan nasu Allah yai musu fahimta kan cewa shi aure lokaci yake dashi.

Duk yanda kaso ka kawar da yaro, idan lokacin shi baiyi ba dole zaka hakura, shisa sam Abba baya jira, wanda duk Allah ya fitowa da miji aurar dashi yakeyi, ko Nusaiba akwai wanda ya fito cikin yan uwa da nufin aurenta, takiya da cewar ita karatu take so tayi, tunda ko sakandire bata kammala ba, babu yanda basuyi akan a tsayar da magana ba, Abba ne yaki, cewar shi su dai jira in zasu iya, yarinyar ta kara mallakar hankalin da zata yarda da auren dan su, karya yanke hukunci da zai zamana kowa baiji dadinshi a gaba ba.

Ita kanta Waheedah zuwa lokacin tana so ace ta fara kula wasu, tasha fadama kanta daga yau duk wanda yazo mata da tayin soyayya zata amsa shi, amman saita tsinci kanta da kasa yin hakan.

Ko wani ta tsaya dashi takanji kamar tana cin amanar AbdulKadir ne, tanajin rashin hankalin dake cikin hakan, tunda bai furta mata kalmar so ba, asalima bai san tana haukanta ba, amman haka take ji.

Zuwa yanzun azumi ta fara da tsayuwar dare akan neman zabin Allah, sai take jin da duk rana kamar ana kara rura mata wutar son AbdulKadir dinne a zuciyarta.

Yau ma a gajiye ta dawo daga makaranta, dan bata dawo ba sai yammaci liqis, har a kasusuwan jikinta take jin gajiya.

Da sallama ta shiga dakin tana zare takalmanta a kofa.

"Mami..."
Ta kira tana cilla jakar hannunta kan kujera, da hijabin ta nufi hanyar kitchen inda ta samu Mami tana tace zobo.

Kanta ta dora a bayan Mami din tana fadin
"Mami kashina kaman zai fito waje..."
Dariya Mami tayi tana ture Waheedah din
"Dagani nikam...

Kashin ne kaman zai fito waje?"
Kai Waheedah ta daga mata, cikinta take jin ya tattaru waje daya saboda yunwa.

"Nagaji sosai, gashi yunwa nakeji"
Robar sugar Mami ta dauko tana zubawa cikin bokitin zobon.
Chapter 38 · 0% Book details