Sashe 41
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da gaske ya samu matsala, shine da maganar aure harda tunanin rayuwar yaranshi da yanda yake son ta kasance.
"Hakan yayi Abba...
Zan tara kudin sai in bama Hajja ta siyo abinda ya kamata..."
Murmushi Abba yayi, AbdulKadir din ya kalle shi yana fadin
"Waheedah ce Abba...
Waheedah zan aura"
Kallon shi Abba yake da mamaki shimfide akan fuskar shi
"Waheedah?
Waheedah ta nan gidan?"
Ya karasa tambayar da alamar rashin yarda a muryarshi da fuskarshi gabaki daya.
Akance sai halayya tazo daya ake zama guri dayama har a qulla alaqa, Abba na ganin karyar zancen a abinda AbdulKadir yake fada mishi, dan ta kowacce fuska AbdulKadir bai dace da Waheedah ba, halayyarsu da komai nasu ya banbanta, bai kuma hango ta yanda akai suka fara soyayyar ba.
"AbdulKadir ka tabbata?
Ita Waheedah din ita tace tana sonka?"
Kai AbdulKadir ya dagama Abba, inda batace tana son shi ba, bazai taba zuwa ya furta ma Abba zancen aurenta ba.
"Allah mai iko...
Oh Allah"
Abba yake fadi har lokacin da AbdulKadir din ya mike jinjina maganar yake, dan kai kawai ya iya daga ma AbdulKadir batare da yaji kome yace ba, harya fice daga dakin.
Sosai yake jinjina al'amarin auren Waheedah da AbdulKadir, shikam zai kira Waheedah ya tabbatar daga wajenta kafin ya yanke kowanne hukunci, dan jikin shi na mishi wani iri akan auren, sanyin Waheedah yai yawa, zafin AbdulKadir ko su da suka haifeshi addu'a suke binshi da ita, yana kaunar su biyun duka, yana jin Waheedah har kasan zuciyarshi, zai komai dan ganin ba'a cutar da marainiya da sa hannun shi ba...!
*#TeamAbdulKadir*
*#TeamWaheedah*
*#AnaTare*
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
Tun da ta kwanta tunanin abinda yaci takeyi, ko kadan zuciyarta taki samun nutsuwa, ita kanta Amatullah ce ta dafa musu taliya, da bata zuba musu tare ba, tana da tabbacin babu abinda zata saka a cikinta.
Dan ta nemi yunwar data kwaso tun daga makaranta ta rasa, duk da tasan ba lallai ya amsata ba, bai hanata daukar waya ta bude manhajar sada zumuntarta na whatsapp ba.
Sunan shine a sama dan shine mutum na karshe da tayi magana dashi.
'Me kaci?'
Ta tambaya, tana dorawa da
'In dafa maka indomie?
Ko zaka sha Tea?'
Amatullah dake kusa da ita ta gyara kwanciyar ta tana fadin
"Adda Wahee...
Ki rage hasken wayarki mana"
Hannu takai tana rage hasken wayar hadi da fadin
"Yi hakuri..."
Bargo kawai Amatullah taja tana rufe jikinta har kai batare da tace komai ba.
Hakan ya ba Waheedah damar mayar da hankalinta gabaki daya kan wayar, dan ba surutun take so ba daman.
'Shine baka fadamun zaka zo ba ko?'
Ta sake rubutawa tana tura mishi, da tasan zaizo din da ta dafa mishi wani abu, lumshe idanuwanta tayi tanajin da dare bai farayi ba ita kam ko indomie ce data dafa takai mishi, a kasan zuciyarta take addu'ar karya zauna da yunwa.
Alamar shigowar saqo da taji yasata ware idanuwanta kan screen din wayar da wani irin bugun zuciyar da bazai misaltu ba
'Waheedah...'
Lumshe idanuwanta tayi data karanta sunan nata da muryarshi, tana bude idanuwan da murmushi a fuskarta
'Waheedah...'
Taga ya sake rubutowa, saida ta goge hannunta jikin wandon kayan baccin da take sanye dasu saboda zufar da taji ya mata, tukunna ta iya amsa shi da
'Hamma'
Rubutu taga yayi, babu shiri ta tashi zaune, da ita kadaice a dakin tsaf zata yi dan ihun murna ko ya yake, yanzun ma gudun tashin Amatullah daga barcine kawai ya hanata yin hakan, amman kanta har wani lilo yake, kamar tana saman gajimare haka take jinta, kafin ta karanta saqon shi daya shigo da wani yare daban da ya saka komai yi mata tsaye cik
'Kina so na?'
Karantawa takeyi tana kara maimaitawa cike da son fahimtar kalmamomin da take jin kamar ba'a yaren da take fahimta yayi su ba, bai bari ta gama fahimtar su ba ya kara mata da
'Ba so na yan uwa ba Waheedah...
So na aure.
Kina so na?'
Wayar ta ajiye jin kamar ta dauki wani irin dumi da yake barazar qona mata hannuwa, sauka tayi daga kan gadon, fankar dake cikin dakin takejin ta mata kadan, zafi takeji bana zazzabi ba, zafi take ji daya girmi ta dora shi akan tsantar girgiza da mamaki.
Littafin Amatullah da tayi assignment tagani a ajiye, da sauri ta dauka tana fifita fuskarta da duk wani waje a jikinta da zata iya.
Zuciyarta kanta ta nutsu wani waje a cikin kirjinta dan taji abinda basu taba mafarkin ji ba su dukansu.
Sakon da taji ya sake shigowa ya sata dauki wayar saidai ta kasa zama sam
'Ki amsani, zan kirga daya zuwa goma.
Karki amsa sai kina da tabbaci, idan bakida shi karki amsa, nida ke zamuyi kamar ban tambaya ba, maganar ba zata sake hadamu ba har abada'
Gefen gadon ta zauna tana mayar da numfashi a hankali, ta runtsa idanuwanta ta budesu kan saqonnin nashi yafi sau ashirin, so take ta tabbatar ba mafarki takeyi ba.
Ba kuma tunaninta yake hasaso mata abinda zuciyarta take burin ji ba, amman duk sanda zata bude sakon AbdulKadir din yake sake mata sallama.
'Daya...'
'Biyu...'
'Uku...'
Ta karanta kafin zuciyarta ta fara mata ihu tana sanar da ita yanda take musu wasa da dama kwara daya tal da suka samu a wajen AbdulKadir din.
Tasan shi, kamar yanda ya fada ne, idan harya gama kirga goman da yace maganar ba zata sake hadasu ba har abada.
Sai dai yanzun ma batasan yanda akai maganar ta hadasun ba, ko a mafarki bata taba tunanin hakan zata faru da ita ba
'Hamma...
Hamma kace wani abu, ka gayamun ba mafarki nake ba, kabani wani tabbacin banda wannan...'
Ta rubuta, sai ta tsinci kanta da gogewa
'Hudu...'
'Biyar...'
'Shidda...'
Kai take girgiza mishi tana soma rubuta
"Ina sonka, bansan ko tun yaushe nake sonka ba, ina sonka fiye da yanda zan taba fada maka Hamma AbdulKadir, tare dakai zuciyata ta fara bude idanuwa, kai zuciyata ta fara dokawa...'
Batasan meyasa ta sake gogewa ba, kalamai take nema, amman ta rasa, har lokacin jin komai take kamar a mafarki, kamar tana tura mishi amsar zata farka
'Bakwai'
Kai ta sake girgiza wannan karin a fili tace
"Ka tsaya Hamma, dan Allah ka tsaya..."
Idanuwanta ta lumshe tana sake budesu kan wayar tata
'Takwas..."
Wani irin yanayi ne ya bayyana kan fuskarta, muryarta a karye tace
"Hamma mana, dan Allah ka tsaya..."
Nutsuwarta take son tattarowa ko da abinda yake faruwa zai kasance mafarki, bataso ta manta komai, sakkonin nashi ta sake karantawa tana lumshe idanuwanta ta adana su wajen da tasan ba zasu taba bace mata ba koda ta farka tukunna ta bude idanuwan nata.
'Tara...'
Ta karanta
"Bansan yazan ci gaba da rayuwa bayan abin nan ba Hamma, idan mafarkine ka tabani ta fannin da banajin zan koma dai-dai wannan karin...
Ka fifitamun wutar burina ka dawomun da komai baya..."
Ta karasa maganar da wani irin sanyin murya, sosai take jin in har mafarki take a gefen soyayyarshi da take wahalar da ita, burin samun shi zai zauna, zata dinga kallon shi tana jiran ya sama mata wajen zama a rayuwarshi ko da bata samu a zuciyarshi ba.
'Ina son ka, ina son ka da aure Hamma AbdulKadir'
Ta tura mishi tana jiran taji ta farka daga baccin da take, alama tagani na cewar ya karanta sakon, kafin taga ya sauka daga kan WhatsApp din, wani irin numfashi da batasan tana rike dashi ba ta saki, itama kashe data din tayi ta ajiye wayar hadi da mikewa.
Bandaki ta shiga ta tara ruwa tana wanke fuskarta, har lokacin numfashi take mayarwa kamar wadda tayi gudu.
Zuwa yanzun bata da kalaman da zata fassara abinda takeji.
Takai mintina goma tsaye a bandakin ta dafe sink, amman idan ka tambayeta ba zatace ga asalin abinda take ji ko take tunani ba.
Alwala ta daura ta fito daga bandakin, doguwar hijab din da take sallah da ita ta dauko ta saka jikinta.
Dardumar da tayi sallar isha'i tana shimfide bata nade ba, kai tahau ta fara jero salloli tana rokon tabbatar alkhairi a koma menene yake shirin faruwa tsakaninta da AbdulKadir din, dan tun daga yanda take son shi tasan abin yafi karfinta, yanzun ma ba zata iya ba, ba kuma zata bata darenta tana tunanin abinda baya karkashin ikonta ba, gara ta bude ma Allah zuciyarta, sosai kuma ta samu nutsuwar da take jin ta kwace mata, akan dardumar bacci mai nutsuwa ya dauketa.
Tana da darasin safe, gashi ta tashi da wani irin sanyin jiki, har iskar da take shaqa daban take jinta yau din, bata sake shiga wani yanayi ba saida taci karo da sakon Abba
'Aslm.
Waheedah ki sameni kafin ki wuce makaranta'
Haka kawai taji zuciyarta na mata rawa, duk da ba yau bane ranar farko da Abban yakan mata irin sakon ko idan zasuyi magana ko kuma zai bata wani abin.
Yau dinne dai takejin kiran kamar zai zamana daban.
Sanda tagama shiryawa saida ta biya dakin Mami tai mata sallama tukunna ta fita zuwa bangaren Abba.
A bakin kofa ta tsaya ta kwankwasa, saida taji yai magana tukunna ta tura dakin da sallama tana shiga.
Waje ta samu kan kafet din ta zauna dan shima anan yake zaune ya miqe kafafuwan shi.
"Ina kwana Abba..."
Ta gaishe dashi cikin sanyin muryarta
"Waheedah..."
Ya kira yana dorawa da
"Kin tashi lafiya?
Ya makarantar?"
Hijab dinta da taji ta danne ta dan daga tana gyara zamanta sosai
"Alhamdulillah..."
Wani numfashi Abba yaja yana kallon yanda take komai nata cikin sanyi.
Da tunaninta ya kwana a ranshi, har zuwa safiyar ranar yana jinjina ma kaddarar data hadata da AbdulKadir, dan ko a tunaninshi ya kasa dai-daita dacewarsu.
Idan zabi za'a bashi na ya aurar da ita cikin yaranshi, yanajin Yazid kadai zai iya aura ma ita hankalin shi a kwance, yana da tabbaci akan Yazid zai riketa da amana, dan bazaice ga rana daya da yaji anyi wata hayaniya dashi ba tun yarintar shi.
Muryarshi dauke da nauyin da yake jin dukkan jikin shi yai mishi ya soma magana
"AbdulKadir ya sameni jiya.