← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 94

Sashe 56

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baisan me take so dashi ba, bayan bata jira shi ba, aure tayi abinta ta kyale shi, tunda batasan tana son shi ba sai yanzun.

Shisa bata samun amsar shi, bacin ran dayai tunanin ya binne a NDA ne ta taso mishi dashi gabaki daya.

Bakuma yaso ana taso mishi da abinda ya rigada ta wuce shisa.

Kusancin nan da Waheedah yasa yaji sanyi-sanyi.

Tunda ya shigo ya dora idanuwanshi akanta cikin rigar shi da tayi mata yawa yaji komai ya kwance mishi.

Nuriyya na manne cikin kan shi, amman Waheedah ta saka shi jin nutsuwar da ita kadai take saka shi samu.

Saboda haka bazai kulata ba, ta saba cewa zai karyata daman, ko hannunta ya riko sai ta fara cewa zai karyata.

Ko shi farkon auren su lallabata yake kamar yana tsoron da gasken zai karyata.

Amman zai iya rantsewa daman can Waheedah din dan shi akayita.

"Matar kowa daga kashin hakarkari ake cirota, na sha taba nawa hakarkarin Waheedah, kasusuwan nada kauri, ki kalleki dan Allah..."
Ya taba ce mata, lokacin daya kamo damtsen hannunta yaji shi kamar babu tsoka a jiki, tayi dariya kamar me ranar, amman fuskar AbdulKadir din ko alamar murmushi babu, dan daga zuciyarshi yai maganar.

Har saka mata ido yayi kan abinci, amman tanaci lafiya kalau, kawai jikin 'yan matan kenan.

Yanzun daya gane ba zai karyata ba, shikenan kuma.

Inma ta fada sai dai yayi dariya kawai.

Ture shi Waheedah tayi tana mikewa ta nufi kitchen ganin biyar hartayi.

Wake ta dibo ta dawo tana zama kan kafet hadi da fadin
"Ta so ka tayani tsince wake..."
Kafada ya maqale yana sake kwanciya cikin kujera
"Ni kibarni...

Nagaji.

Jikina ciwo yake mun"
Murmushi tayi, neman tsokana ne yasa ta cewa ya tayata din daman.

"Ko zakaje kaci abinci a wajen Hajja?"
Cike da rashin fahimta yake kallonta yana jiran karin bayani kan dalilin da zaisa yaje gida cin abinci bayan ga gidan shi, ganin tayi shiru yasa shi fadin
"Saboda ban tsince wake ba shisa ba zaki bani abinci ba?"
Dariya Waheedah takeyi tana girgiza mishi kai
"Abincina yanzun da mai da yaji ne, ko kana so kaci da miya, ko kamshin nama banaso...

Shisa nace ko zakaje can"
Kai ya girgiza mata
"Kome kika bani kinsan zanci ai, zanci da mai din nima"
Shiru tayi batace komai ba, tasan halin shi da abinci ne, shisa tace ko yaje wajen Hajja din yaji, har ranta hakan ba komai bane ba, indai zaici abinda yake so ya wadatar da ita.

Amman AbdulKadir ne, ko yana so din ba zaije ba, gani zaiyi tunda shine sanadin kin cin miyar tata, sai suci kome ya samu a tare.

Kallon suka ci gaba dayi, ta karasa tsintar waken taje ta wanke ta dora.

Da zai fita da magriba binshi tayi ta kulle kofar daga ciki, duk da akwai maigadi a bakin kofa.

Dan yace mata zaije gida ya g
aishe dasu Abba.

Tasan kuma zai iya kai karfe tara bai dawo ba, dan har wajen Yassar saiya biya.

Gidan Yassar din kuwa ya fara biyawa.

Kowa a gidan na mishi mitar baya zuwa a gaisa.

Banda Yassar babu wanda yake ganin shi, baya kulasu, ko Hajja ta mishi fada fushi yake mata.

In gaisuwa ce sunayi a waya, kuma sukan hadu a gida, idan anyi wani abu na rashin lafiya in yazo ta fada mishi yakanje ya duba su.

Baiga dalilin da zaisa a takura mishi da cewar sai yaje gidajen su ba, kuma da karamar sallah duk ana haduwa har wanda suke nesa ma suna zuwa.

A masallacin unguwar su Yassar yai isha'i, tukunna yahau babur zuwa kofar ruwa.

A hanya ya kunna wayar shi yana jin sakonni nata shigowa ya kuma san Nuriyya ce.

Jinta yake a wuyan shi, a rayuwar shi bayason abinda duk zai saka shi tunani, kuma ba zaima kanshi karya akan abinda yakeji a kanta ba.

Kofar gidansu babur din ya ajiye shi, ya sallame shi, yana saka canjin a wallet zai mayar aljihu ya hango Nuriyya tsaye ita da wani a bakin motar shi.

Ko babu fitilar kofar gidan su AbdulKadir din da ta haska mishi ita, yana da tabbacin zai gane ita din ce.

Wani irin tuquqin kishi da yajine idanuwan shi har lumshewa suke ne abinda bai tsammata ba.

Baisan kafafuwan shi na takawa ba sai da yagan shi tsaye a gabanta.

Ita kanta ta girgiza dan bata tsammaci ganin shi ba, tun da safe take kiran wayarshi a kashe, ga sakonnin duk da ta tura basu nuna alamar sun shiga ba, ya kirata jiya da dare ya dorata kan tsanin buri, da safen nan ya girgizata ta fado.

Har kuka tayi, tunanin shine yai mata yawa shisa ma ta fito zancen ko bakomai zata rage dare, inta koma ta sake kiran shi in bata samu ba ta hakura ta gwada kwanciya ko bacci zai saceta, shine tunaninta lokacin data fito
"Masoyi..."
Ta fadi murmushi na kwace mata, kallo daya AbdulKadir yai ma yaron da yake tsaye ya zagaya ya shiga motar shi yajata yana barin wajen.

"Me kike tsaye da wancan yaron Nuriyya?"
Ya bukata ranshi a matukar bace, saboda baiga dalilin da zaisa ta addabi rayuwar shi idan tasan zata dinga kula wannan yaran ba, baisan me yasa zata ce tana son shi ta fito tana kula kananun yara ba.

Kafin ta bashi amsa ya dora da
"Me kike so da ni?

Me yasa zaki dameni kuma ki fito kina kula wannan yaron?

Da wannan yaron zaki hadamun soyayya Nuriyya?

Raini kike son ja mun?"
Kai take girgiza mishi, gabaki daya yanayin shi ya tsoratata, muryarta a karye tace
"Ka aureni, ka aureni....in baka son ganina da kananan yara ka aureni"
Murmushi AbdulKadir yayi mai sauti da ko kadan bashida alaka da nishadi, tana maganar aure kamar abune mai sauqi, shisa ta zabi tayi auren tabarshi tun daga farko.

Magana zaiyi yaga ta matsa da sauri tana boyewa a inuwar shi.

Hakan yasa shi juyawa ya kalli inda idanuwanta suka bari, baisan waye ya shiga gidan su ba, amman bazai wuce wani cikin kannen shi ba.

Hankalin shi ya mayar kanta
"Me kike boyewa?"
Idanuwanta cike taf da hawayen da batasan ta inda suka taso ba ta tsinci kanta da fadin
"Naziru ne ya wuce..."
Lokacin da tace tana son shi, bata hango girman hakan ba, asalima idanuwanta a rufe suke da tunanin samun shi, ta manta alakar da take tsakaninta da Waheedah da zata iya saka auren shi ya zame mata abu mai matuqar wahala.

"Me yasa zaki boye?"
AbdulKadir ya sake tambaya, Nazirun ba bakonta bane, baiga dalilin da zaisa ta boye ba.

"Zai ganmu a tsaye"
Ta amsa a sanyaye, tana saka hannu ta share kwallar data taru a gefen idanuwanta, wata irin soyayyar AbdulKadir din na dafa ruhinta
"Me yasa kika ce kina sona idan kananun abubuwa irin wannan zasu dameki?"
Idanuwanta ta sauke cikin nashi tana rasa abinda zata ce mishi, numfashi AbdulKadir ya sauke, gabaki daya kanshi yayi nauyi, bayaso abu ya dame shi, yaga alama kuma Nuriyya zata dame shi
"Kina sona da gaske?"
Kai ta daga mishi, inta ce kalamai zatayi amfani dasu ba zasu isheta ba, kalar son da take mishi har mamaki yake bata.

Kai ya jinjina mata
"Zai zo karshe in na sake ganinki tsaye da wani, bana so, raina zai baci idan naganki da wani"
Kan ta sake daga mishi
"Bana so ana mun magana da kai, ki bude bakinki insan kin fahimci abinda nake fadi"
Wani abu dayai mata tsaye a wuya ta hadiye tana kallon fuskar AbdulKadir din
"Ba zaka sake ganina da kowa ba"
Wannan karin shiya jinjina mata kai, ya juya yana barinta a tsaye a wajen, sai da taga ya shiga gida tukunna itama ta wuce, zuciyarta na wata irin dokawa taban mamaki.

AbdulKadir kuwa wani irin yanayi yakeji da bai taba tunanin zaiji ba, cikin gida ya shiga yana wucewa bangarensu.

A daki ya samu Hajja da ko gaisheta baiyi ba, sallamar da yayi ma bai jira ta amsa shi ba yace
"Hajja ina Abba?"
Cike da mamaki take kallon AbdulKadir din
"Lafiya?

Me ya faru?"
Kai AbdulKadir ya girgiza mata
"Lafiya kalau Hajja, ina son magana dashi ne, yana ina?"
Ita ba girkinta bane ba, Mami ke da girki, dan haka tace ma AbdulKadir din
"Yana bangaren shi..."
Kai ya jinjina mata ya fice zuwa bangaren Abba, da sallama ta shiga, ya samu Mami tana hada kwanonin abincin da alama Abba ya gama ci.

"AbdulKadir....

An iso kenan"
Abba ya fadi da fara'a a fuskar shi.

Murmushi AbdulKadir din yayi shima yana gaishe da Mami da ta amsa shi cike da fara'a, kunya irin tata bata iya tambayarshi ya Waheedah ba, ta fice daga dakin tana barinsu.

Kan hannun kujera AbdulKadir ya zauna
"Abba..."
Ya kira yana dorawa da
"Ina wuni"
Gyara zama Abba ya sakeyi kan kafet din
"Lafiya kalau, ya aikin?

Ka samu kowa lafiya dai ko?"
Kai AbdulKadir ya jinjina yana tsintar kanshi da daburcewa a karo na farko a rayuwar shi
"Abba..

Daman zanyi magana dakai ne...

Zamuyi magana..."
Ya rasa kalaman daya kamata yayi amfani dasu.

Cike da kulawa Abba yace
"Allah yasa lafiya"
Numfashi AbdulKadir ya fitar da baisan yana rike da shi ba, sakkowa yai daga kan kujerar yana zama a kasa a gaban Abba din, muryarshi can kasan makoshi yace
"Aure zanyi Abba..."
Maganar Abba yaji kamar daga sama, yanda yajita yafi yanda maganar auren AbdulKadir din daga farko ta dirar mishi.

"Aure AbdulKadir?"
Abba ya tambaya cike da shakku, duk da matan shi hudu, hakan bai hanashi jinjina maganar AbdulKadir din ba, dan yasan yan zamanin su da zamanin su AbdulKadir din akwai banbanci, adalci nama yaran yanzun wahala, kuma da yawa sukanyi auren ne badan ra'ayin hakan ba, sukanyi ne saboda dalilai da kala-kala, da yawa dan suna samun matsala da matan su na gidane.

Maimakon su tsaya su fuskanci matsalar su shawo kanta, sai a dinga basu shawarar su kara aure, kamar hakan zai zama sanadin batan matsalar da suke fama da ita.
Chapter 56 · 0% Book details