← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 94

Sashe 12

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asalima ko gidan ta shiga gaisuwarta ma can kasan makoshi yake amsawa kamar ta mishi dole.

Yanzun ma amsa ta yayi da
"Lafiya..."
Yana tsayar da idanuwan shi kan Waheedah da ko ina cikinta bari yake
"Ban hanaku tsayawa wani waje in kun fito islamiyya ba?"
Dagowa idanuwanta da suka tara hawaye tayi tana kallon shi, ko batai wani abuba ya kafeta da idanuwan shin nan masu kama dana yan Japan saboda kankantarsu ji take komai ta kwance mata batare da wani dalili ba.

"Ka...ka hanamu"
Ta fadi a daburce, kai ya jinjina yana wuce su, hannun juna suka kama ita da Nuriyya suna wucewa suma, wani irin sauri suke zumbudawa kamar zasu tashi sama, Waheedah nada tabbacin in ya rigasu isa makaranta zai kirki dalilin dazai mata dukan biyawa gidansu Nuriyya, ita kuma Nuriyya laifin Waheedah din tasan shi zai shafeta, juyawa Nuriyya tayi taga ko yana gab dasu, ta sauke idanuwanta cikin nashi da yasa wani irin yanayi tsirga mata daga dayan tsakiyar kafarta zuwa dan yatsan kafarta, kafin da sauri ta juya tana kiran duk wani sunan Allah dazai zo bakinta ko zuciyarta zata daina rage gudun da takeyi.

Tana sake damke hannun Waheedah hadi da janta dan su kara sauri...!
*#TeamAbdulKadir*
*#TeamWaheedah*
*#FWA*
*#AnaTare*
[7/27, 1:13 PM] +234 816 124 4732:
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
Da yawan lokutta idan aka tashe su daga makaranta sukan fi mintina sha biyar suna jira kafin azo a dauke su.

Yazid yafi kawo su yazo ya dauke su, amman kowa in za'a tambaye shi zaice yafi son Mubarak yazo, dan duk gidan babu dan raha irin shi, kudin duk da yake aljihun shi kuma ranar akan su zai karar, duk abinda zasu nuna suna so sai an tsaya an siya.

Yanzun basa komawa lokaci daya da Abdulkadir, saboda yana tsayawa extra lesson din da zai taimaka mishi wajen zana jarabawar aji shidda.

Yau din kuwa sa'a sukaci Mubarak ne yazo daukar su, kowa ka duba fuskar shi kar take
"Ina Commander din naku?"
Ya bukata yana sa Amatullah jan wani numfashi a tsorace
"Hamma..."
Suka kira kusan gabaki daya, dariya Mubarak yayi
"Bansan ya akai baiji sunan nan ba har yanzun"
Jinjina kai Zahra tayi, tana hasaso kalar drama din da za'ayi duk randa yaji suna kiran shi da Commander din nan.

Mubarak ya rigada ya juya motar ya hango mai yalo a tsallaken titi
"Wazai siyo mana yalo?"
Ya bukata yana kallon Waheedah dake zaune a gaba, dan kafin ma ta ja kafarta cikin sanyin tafiyarta da mutane da yawa zasu iya kuskurewa da yanga sun gaggama shiga motar, gaba kadai ya rage.

Jakarta ta ajiye tana cewa
"Kawo a siyo....

Wanne iri?

Farin?"
Daga baya Nazir yace
"Nidai bana cin fari..."
Yana sa Mubarak juya ya harare shi
"Kaji mun yaron nan fa, nace zan siyo dakai ne?"
Yana zaro dari biyu ya miqama Waheedah
"Kowanne na dari..."
Motar ta bude ta sauko, baya tadan yi tana tsayawa daga bayan motar, abubuwan da take tsoro a rayuwarta basu da yawa, tsallaka titi na daya daga cikinsu, bataso tai magana ne su isheta da tsokanar su da bata karewa shisa ta karba, amman zuciyarta dukan uku-uku kawai take.

Dakyar ta iya tsallaka hannu daya, tana tsaye a tsakiya, ganin motocin da mashina take suna wucewa da gudun da take tunanin ko suna da niyyar tashi sama ne.

Banda zare idanuwa babu abinda takeyi, juyawa tayi dan ta tsallaka ta koma, amman abin ya gagara, data sani tace wani yaje, yanzun take jin gara tsokanar su da wannan tashin hankalin da take ciki.

Yana daga dayan bangaren shida Imran da Nawaf da suka jashi suna fitowa dashi, kasancewar basa fara extra lesson din sai biyu da rabi cif, ana nada rabin awar dan sallah da cin abinci.

"Lokaci yana tafiya, wanne iskanci ne wannan wai?

Ku siyi kome zaku siya mu koma dan Allah"
Cewar Abdulkadir yana duba agogon dake manne a hannun shi.

Imran ne ya kalle shi, dan Nawaf bai niyyar asarar bakin shi ba
"Karka daga mana hankali Malan, ka koma abinka mana"
Wani kallo Abdulkadir ya watsa ma Imran din
"Ai kuma karya kake, ku biyun, yanda kuka janyoni na fito haka zamu koma tare..."
Ya karashe maganar yana gyara tsayuwar shi, kamar ance ya daga idanuwan shi, ya kuwa sauke su kan Waheedah, duk da tana juyawa zuwa dayan bangaren hadi da bashi baya bai hanashi ganeta ba, akwai farare a makarantar sosai, harda yaran kwarori da suke makarantar, yana tunanin da kalar farin sune kawai zai iya kwatanta na Waheedah, yanzun ma yanda ya shigar mishi idone yagane itace, sai kuma yanayin sirantakar.

Sake kankance kananun idanuwan shi yayi ganin ta sake juyowa ta fuskanto inda yake tsaye, da alama a rikice take.

Apple din dake hannun shi ya juya yana tunanin abinda ya tsallako da ita titi.

Bai amsa Imran da yake tambayar shi ya sake shawarar tafiya babu su ne, dan abarba suka siya ana fere musu.

Titin ya tsallaka yana takawa harya karasa inda take.

Saboda a daburce Waheedah take ko kula batayi dashi ba
"Uban me ya tsallako dake?"
Muryar shi ta daki kunnuwanta tana tsoratata, baya tayi saboda yanda zuciyarta tai wani irin tsalle, da zafin nama Abdulkadir ya riko hannunta daya yana mata wata irin damqa kamar zai karyata, bakin shi da take ganin yana motsi ya tabbatar mata da ba magana kawai yakeyi ba, fadan shi yake mata da baya karewa, amman batajin shi, ta tsorata har cikin ranta, da bai riketa ba da labarin ya banbanta, tana jin yajata suna tsallakawa bangaren titin daya baro.

Hannunta ya saki yana kai nashi hannun ya dan goge wani abu a goshin shi da yake jin ya taru.

Badan yanda zuciyar shi take dokawa ba daya dauke ta da mari
"Me zakiyi a tsallaken titi?"
Ya bukata yana kafeta da idanuwan shi da suka saukar mata da wata irin nutsuwa
"Ya...

Yalo zan siya"
Numfashi Abdulkadir yaja yana saukewa, wani irin yanayi yakeji da bayason alaqanta shi da tsoron da yaji, runtsa idanuwan shi yayi yana sake bude su, sam bayason tuna yanda ta kusan fadawa titi
"Hamma Mubarak yace in siyo..."
Waheedah ta fadi a tsorace, ba tsoron titin data kusa fadawa ba, tsoron yanayin da take ganin Abdulkadir din a ciki, yanda ya dago da idanuwan shi yasata kai hannuwanta duka biyun tana rufe kuncinta dasu, wani irin dogon kallo yai mata yana kai hannun shi wajen fuskarta, matsawa tadanyi a tsorace tana rufe idanuwanta gam, cikin yanayi biyu zuciyarta take dokawa, yanda take cike da tsoron shi, da kuma yanda takanyi duk idan yana kusa da ita haka.

Dari biyun da ke cikin hannunta yakai yan yatsun shi yana fisgewa hadi da nufar inda mai yalon yake, baisan me take tunanin zaiyi ba, dukanta ne karshen abinda yazo mishi.

Mai yalon ya mika ma kudin yana tsayawa
"Na nawa?"
Mai yalon ya tambaya
"Na duka..."
Kai ya jinjina ma Abdulkadir ya dauko leda hadi da sake fadin
"Wanne iri"
Wani irin kallo Abdulkadir ya watsa mishi, yalo duk ba yalo bane da zai tsare shi da tambayar banza
"Malan ka sakamun yalo, karka isheni da tambaya dan Allah..."
Ya karasa maganar da jan karamin tsaki, daya miko mishi ma a hasale ya karba, ranshi a bace yake jin shi.

Waheedah na tsaye inda ya barta, ta sauke hannuwan ta daga kuncinta saboda bataji marin da tai tsammani ba.

Batare da yace komai ba yasa dayan hannun shi ya damqi nata dashi yana janta batare da yace komai ba, hannun nashi tabi da kallo, wani irin yanayi na lullubeta, kafin ta kalli fuskar shi da take a nutse, yanda wani abu ke motsi a kuncin shi dake nuna alamar ciza hakoran shi yake ta cikin bakin shi tasan ranshi a bace yake.

Yan gidan duka sukan ce kullum ma ran Abdulkadir a bace yake.

Tasan ba dariya yakanyi ba, in kuwa yayi takan ga baquntar yanayin akan fuskar shi, amman ita tana gane idan ranshi a bace yake ko ba'a bace yake ba, batasan ya akai take ganewa ba, tunda ta taba gwada yi musu bayani sau daya suka sakata a gaba da dariya bata sake kwatantawa ba.

Fuskar shi take kallo tana binshi duk inda ya jata, batasan sun tsallaka duka titin biyu ba saida ya saka ledar yalon a hannunta yana sakin hannun tukunna.

"Idan na sake ganin ko da wasa kin nufo kusa da titi saina zane jikin ki Waheedah, Allah saina zane ki, kina jina ko?"
Kai ta daga mishi a hankali, bai jira amsarta ba, duk cikinsu ita kadaice baya damuwa da saita mishi magana da bakinta, inta ware mishi idanuwanta haka tana kallon shi da farar fuskarta yasan ko kasheta zaiyi ba iya magana zatai ba.

Dan haka ya juya yana zagaya wa inda Mubarak ya fito daga motar ya tare mai yoghurt yana zaba yana sakawa a mota
"Hamma idan kasan zaka siyi wani abu tsallaken titi ka daina aiken yara, in ba zaka tsallaka da kanka ba ka hakura"
Dago kai Mubarak yayi yana kallon Abdulkadir din da in zasu gwada tsayi a kafadar shi kan shi zai tsaya.

Duk da ba wani nisa bane a tsakanin su ta bangaren shekaru, amman ya girmi Abdulkadir din, yanda yai tsaye yana bashi umarni yasa shi yin dariya da fadin
"To Abba..."
Cikin ido Abdulkadir ya kalle shi
"Da gaske nake, karka sake aiken su tsallaka titi, bana so..."
Kai Mubarak ya daga mishi, dan bazai iya masifar Abdulkadir din ba, juyawa yake da shirin tafiya, Mubarak yace
"Kazo ka dauki yoghurt"
"Bana sha..."
Kallon shi Mubarak yayi
"Daga abin arziqi?"
Daquna fuska Abdulkadir yayi
"Nima bance wani abu ba, bana sha kawai nace"
Hannu Mubarak ya daga mishi
"Naji, sai anjima, jeka abinka"
Tafiyar kuwa yayi yana nufar hanyar da zata mayar dashi cikin makarantar.

Waheedah kuwa dakyar ta iya jan kafafuwanta ta shiga cikin motar.

Kan sit din da Mubarak ya tashi ta dora mishi ledar yalon, hannunta take murzawa inda take jin na Abdulkadir har lokacin, zuciyarta na mata wani irin yanayi da ta kasa fahimta.
Chapter 12 · 0% Book details