← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 94

Sashe 7

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bazan cire ba..."
Ya fadi a fili, da Waheedah yake, dan ita ce bataso yana shigo mata da takalma har daki, abinda take so shi take mishi yau, shima abinda yake so zaiyi, hannu yasa ya dafe kan shi, yana kuma saukewa hadi da ajiye numfashi mai nauyi.

Idan matsalar kwakwalwa ce ta samu Waheedah, yaga alama harshi takw son gogawa tunda ya fara magana shi kadai.

Hoton su dake durowar gefen gadon ta ya dauka yana tsayar da idanuwan shi akai.

So yake yagane wanne kalar kayane a jikin Waheedah din, yadai ga farare ne, dankwalin da ta nade kanta dashi ma farine, zai iya tuna da wayarta ta dauke su hoton, tana lafe a jikin shi, ya zagayo da hannunshi daya kan cikinta data dora nata hannun akan nashi, ya kankance mata idanuwan shi daba girman kirki ne dasu ba daman, da dariyar nan tata a fuskar shi.

Dan yatsan shi ya saka ya shafi dai-dai fuskarta, yasha ganin hoton a ajiye a gurin, hade da sauran hotunan shi da bazaice ga lokacin data dauke su ba, amman zai karya idan yace ya taba tsayawa ya kula da hoton da yake hannun shi, balle ya tambayeta lokacin data kai aka wanko hoton har aka saka shi a frame hakan, baisan meyasa sai yanzun yake son tambayarta ba.

Sake shafar fuskarta yayi
"Me yake damunki yau?

Me kike son janyo mana Wahee?

Me kike son janyo mana haka?"
Ya tsinci kan shi da tambaya, shirun dakin na saukar mishi da wani irin yanayi daya saka shi ajiye hoton inda ya dauka.

Baisan abinda ya kamata yayi ba, wani abu makamancin wannan bai taba faruwa da shi ba, asali yau ce rana ta farko da rikici ya soma hadashi da Waheedah, shisa yake jin komai ya kwance mishi, ba zaice baya fada da ita ba, ita dince dai bata taba biye mishi, komin fadan dazai sauke mata hakuri kawai zata bashi, baisan me yake damunta ba yau.

Aljihun shi ya taba, wayarshi bata ciki, waige-waige ya fara yana neman inda ya ajiye ta, babu shiri ya mike, duka inda tunanin shi zai iya kaiwa cikin dakin saida ya duba amman bai ganta ba, takawa yayi zuwa falon su, zuciyar shi na wani irin dokawa da ya sauke idanuwan shi kan table din da Waheedah ta fada kai, ga jini da harya fara bushewa kan kafet din, kafafuwan shi da yake ji sun soma rawa yaja zuwa hanyar kitchen, wani karamin bokiti yagani ya dauka ya tara ruwa a ciki, kan window din kitchen din ya dauki omo ya zazzaga a ciki.

Abin goge-goge yake nema, bai gani ba sai wani towel karami.

Shi ya dauka ya saka cikin bokitin yana daukowa ya fito daga kitchen din, gefen da jinin yake akan kafet ya ajiye bokitin yana tsugunnawa, towel din ya fiddo ya matse yana soma gogawa a wajen, sosai jikin shi ya dauki dumi da alamar zazzabin da yake da alaqa da dana sanin da ya lullube shi, yana mayar da towel din cikin bokitin yaga yanda ruwan ya sake launi yaji wani abu na tattarowa daga zuciyar shi ya hadu a wuyan shi ya shaqe shi, a hankali kuma shige da ficen numfashin shi ya fara canzawa.

Towel din yake gogawa a wajen da dukkan karfin shi.

'Jinin Waheedah ne duka anan'
Wata karamar murya ta furta cikin kunnuwan shi, numfashin shi na fita da sauri-sauri kamar wanda yai gudu.

'Bana bata lokaci akan abinda ya riga ya wuce, bana tunani akai saboda bazan iya komawa in canza ba'
Yake fadi cikin kwakwalwar shi ko zuciyar shi zata taimaka ta bashi hadin kai.

Iya abinda zai iya gogewa daga jikin kafet din ya goge yana daukar bokitin ya mayar kitchen, wajen wanke-wanke ya juye ruwan, kalar shi nasa cikin shi yamutsawa, baisan lokacin da jini ya fara daga mishi hankali haka ba, fanfo ya bude kan ruwan dan ya wuce da wuri, bayason ganin shi, ya tara hannuwan shi a jiki ya wanke, har fuskar shi ya wanke ko zata rage mishi zafin da yaji tanayi, ya kashe fanfon ya fito.

Tunawa yayi wayar shi yake nema, yaci gaba da duddubawa, baisan lokacin da yace
"Waheedah!

Ina wayata?"
Idanuwan shi ya runtsa, bai gama tunanin yanda shima yake gab da samun tabin hankali ba yaji karar wayar.

Hakan na sashi bude idanuwan shi babu shiri, inda yake jin karar wayar yake bi, harkan kujera daga gefe, hannu ya saka ya janyo wayar da rabin ta ya fara shigewa cikin lokon kujerar, sai dai kiran harya yanke, dangwala jikin gilashin wayar yayi tunda babu wani mukulli a jiki ta kuwa bude, mamakine bayyane a fuskar shi ganin Abba ne ya kira, bawai dan baya kira ba, lokacin daya kira dinne yaji ya mishi wani iri.

Yana shirin bin kiran sai gashi ya sake shigowa, amsawa yayi yana kai wayar kunnen shi da fadin
"Abba..."
Daga dayan bangaren Abba ya amsa
"Abdulkadir, kome kake kazo gida yanzun"
Zuciyar shi yaji tai wata irin dokawa
"Abba lafiya?"
Ya bukata yanajin sautin muryarshi daya fito a tsorace
"Ka dai zo..."
Kai ya girgiza
"Ni dai ka fara fadamun ko menene a waya tukunna"
Abdulkadir ya fadi, dan yanda zuciyar shi take bugawa sam bai aminta da kiran Abban ba.

"Abdulkadir..."
Abba ya kira cike da kashedi
"Ba zanyi tuqi a nutse bane idan bansan meye dalilin kiran ba Abba, ni dai ka fadamun dan Allah.

Kaji"
Ya sake fadi
"Bari in aiko a dauke ka to"
Cewar Abba da alamun ranshi ya fara baci, kai Abdulkadir ya girgiza yana jin komeye yake shaqe da wuyan shi yana kara shaqe shi.

"Akan Waheedah ne ko?"
Ya tambaya muryar shi can kasa, yana kuma jin bugun zuciyar shi har cikin kunnuwan shi, idanuwa ya runtse yana jiran amsar Abba, a ranshi kuwa rokon Waheedah yake
'A'a Waheedah, bakimun wannan tonon asirin ba, baki mun haka ba, ba zaki taba mun haka ba'
Bude idanuwan shi yayi dajin Abba yace
"Akan ta ne, kazo yanzun ina jiran ka"
Kafin ya furta wani abu Abba ya kashe wayar, tayi yar karar alamun an kashe daga dayan bangaren cikin kunnen shi, sauke wayar yayi yana fadin
"Abba mana, Abba banaso ana kashe mun waya cikin kunne, da gaske bana so..."
Ya karasa maganar da furta
"Yaa Ilahee..."
Komai yake ji ya kwance mishi, takawa yayi yana fita daga dakin, gurin motar shi ya nufa, budewa yayi yana jefa wayar a ciki, harya daga kafarshi daya ya saka cikin motar yaji an kira sallah
"Ni sai nayi Sallah wallahi"
Ya furta kamar wani yace kar yayi sallah, cikin gida ya koma ya daura alwala, sai dai bayajin yana da nutsuwar da zai iya zuwa masallaci, anan dakin baccin su ya nemi darduma ya shimfida yana tayar da sallah.

Sai dai ga mamakin shi kokawa ya soma yi sosai da nutsuwar shi, dakyar ya samu yai sallar tunani fal cikin ranshi, ko addu'a baiyi ba ya mike yana barin dardumar anan.

Fita yayi ya shiga motar yana kunnuwa hadi da janta ya juya, maigadin kofar nashi ya bude mishi gate ya fice ya nufi hanyar da zata kaishi da gidan nasu da yake a kofar ruwa.

Dakyar Anty ta samu likitan yabar su suka taho gida, shima da alkawarin cewa zata dawo da Waheedah a ranar, komai a asibitin suka baro shi.

Ita kanta Antyn taso koma menene abar shi sai Waheedah ta samu sauqi sai ayi, amman ita da Abbanta sunki yarda da hakan.

Har suka shigo gida addu'ar Allah ya kawo musu sauqi takeyi.

Waheedah da kanta ta fara jan Anty zuwa bangarenta, badan bata son ganin Mami ba, bata son kowa yace tayi hakuri ko tabi komai a hankali, batason jin duk wannan.

Kujera ta samu tai zamanta a dakin Anty, lokaci zuwa lokaci take saka hannu ta share hawayen dake biyo fuskarta, Ikram ma data qara bata tasha Anty ta miqama yarinyar.

Tana nan zaune Abba ya shigo da sallama, tana sauke idanuwan ta cikin nashi wani irin kuka ya kwace mata, a hankali Abba ya karaso cikin falon yana neman waje ya zauna.

"Waheedah..."
Abba ya kira sunanta muryar shi cike da rauni, kanta da yake nade da bandeji ya fara bi da kallo, tukunna ya tsayar da idanuwan shi kan fuskarta da duk kumburin da tayi da alamun kukan da tasha bai hana yanda ta rame matuqa nunawa ba.

Kukan da take yasa ta kasa amsa shi
"Waheedah kiyi hakuri kinji..."
Abba ya furta yana jin yanda zuciyar shi take a jagule, muryar Waheedah a dishe ta dago jajayen idanuwanta tana kallon Abba, kai take girgiza mishi tana sauke ajiyar zuciya a hankali
"Dan Allah Abba..."
Ta soma fadi tana jin zuciyarta kamar zata fado
"Dan Allah...

Karkace in koma...

Karka ce inyi hakuri Abba...

Wallahi nagaji...

Inajin idan na koma zuciya ta Abba..."
Tai maganar tana kai hannunta a kirji inda take jin zuciyarta kamar zata fashe, numfashi take ja tana fitarwa amman iskar bata kai mata inda take so, dakyar take iya magana
"Abba zuciyata ina jin kamar zata fado, dan Allah karkace inyi hakuri, karka tambayeni me ya faru...

Bansan ta inda zan fara maka bayani ba, kawai nagaji ne, nagaji sosai"
Anty dake tsaye hannu tasa tana share hawayen da taji suna shirin zubo mata, a muryar Waheedah take karantar kuncin da Allah kadai yasan tun yaushe take danne shi, a muryat Waheedah take jin ciwon da take ciki, ya kuma taba zuciyarta ba kadan ba, sosai tayi niyyar lallaba yarinyar takoma dakin mijinta domin sh
i aure dan hakuri ne, kowa kaganshi zaune a gidan mijin shi komin dadin zaman su akwai hakurin da suke da juna ta fannin da bazai bayyanu ba.

Sai dai kuma batasan har yaushe za'a dinga labewa a bayan hakuri ana cutar mata a zamantakewa ta auratayya ba, batasan sai yaushe mutane zasu fahimta shi kan shi hakurin yana da qa'ida ba, a al'adance ma hakuri na da iyaka, balle addini daya sauqaqa matakin komai, batasan lokacin da mutane zasu fahimci duk da hakuri jigone na zaman aure bai sa ya zama ibadar auren gabaki dayan ta ba.
Chapter 7 · 0% Book details