Sashe 33
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zata iya cewa shima tun bayan Sallah da canjin wajen aiki ya dauke shi zuwa Abuja.
Sai kwanaki da akace mata ya shigo, ita kuma taje gidan kanwar mahaifinta, kuma ba sosai take kwana ba, ranar dai rabon ba zata hadu dashi bane yasa ta kwana din, taji takaicin abin.
Ta kuma yi mamakin da Yazid baije can din ya sameta sun gaisa ba, Yazid din data sani zai nemeta, bazai zo Kano bayan watanni masu yawa ya koma basu gaisa ba.
Sai dai Zahra tace mata da Asuba ya wuce, a cewar shi ayyuka sun mishi yawa.
Abdulkadir din kuwa text tai mishi tana fada mishi itace, tukunna ta sake tura mishi wani tana tambayar lafiyar shi.
Kasa hakura tayi duk da bai amsa mata sauran sakkonin ba, ta tura mishi wani tana cewa bata ganshi a Whatsapp ba, ya bude.
Bata samu amsa ba sai bayan kwana wajen biyar tsakani, a kwanaki duk lokacin data samu tana duba wayar taga ko ya amsata bata gani bane.
Sosai zuciyarta ta matse lokacin da take dubawa.
Ba wata doguwar amsa bace.
'Na bude' kawai ya tura mata a taqaice.
Amman zuciyarta ta mata wani irin sanyi.
Tun lokacin suke magana ta WhatsApp din, ko tace take mishi magana, dan tana iya tura mishi sakonni sama da ashirin bai amsata ba, lokutta da dama zata ga ya bude ya karanta.
Amsawar ce takan mishi wahala.
Bai dameta ba a lokacin, har zuwa yanzun kuma baya damunta.
Saboda bashi yake son magana da ita ba, itace take son magana dashi.
Indai yagani ya karanta, har kasan ranta ya wadace ta, duk rana zata bashi labarai kala-kala, abinda akai a makarantar su, me tayi a ranar, me ya faru da yan gida.
Wani lokacin zai karanta ya turo mata Emoji din murmushi, randa ta wuni batai mishi magana ba zai sake turo mata da Emoji, idan yaga ta jima bata amsa shi ba zai kira sunanta.
Zata rantse akwai yanayin yanda yake rubuta sunan da takan gane idan a gajiye yake ranar, idan ranshi a bace yake, ko idan yanajin fadan shi.
Takan yi murmushi a dukkan yanayoyin tukunna ta bashi labari kamar ko da yaushe.
Bata taba gwada kiran shi ba ko sau daya.
Takan tura mishi voice notes a whatsapp, a kasan zuciyarta tana fatan shima zai fahimci tana kewar muryar shi ya tura mata.
Hakan bai taba faruwa ba.
Sai dai lokacin da tayi wani zazzabi mai zafi, ta kwana biyu bata ko samu karfin duba waya ba.
Kuma randa ta duba din bata da katin da zata siya data ta duba whatsapp din.
Har washegari, tana kwance a daki ya kirata, tana dagawa ta kara a kunne, kafin tace wani abu muryar shi ta daki kunnenta
"Me ya sameki?"
Lumshe idanuwanta tayi, muryar shi na nutsar da wani abu cikin kirjinta da batasan a tashe yake ba.
Kafin ta amsa ya dora da
"Meyasa ba zaki fadamun kina wani abu ba?"
Murmushi tayi
"Hamma..."
Bai bari ta karasa din ba
"Karki sake mun haka, bana so Waheedah"
Numfashi ta sauke a kunnen shi
"Bani da lafiya ne Hamma"
Ya kai dakika talatin kafin ya sake magana cikin wata irin murya da ta dinga shigarta har kwanya.
Duk da hirar batai tsayi ba tai mata dadi.
Satin saida ya jera kullum saiya kirata yana jin ya jikinta.
Da zata iya mishi karya zata ce bata warke ba dan yaci gaba da kira.
Amman ba zata iya ba, daga lokacin kuma idan harya kirata to ta dawo makaranta a gajiya tana bashi labari tace kanta na ciwo, yana kira yace mata tasha magani ta kashe waya ta kwanta.
Amman ba zai amsa maganar tata a whatsapp ba.
Mutane da yawa zasuyi mamakin badaudaden halin shi, ita kam babu wani abu a tattare dashi da bai mata ba, ko yake bata mamaki.
Numfashi ta sauke tana samu ta miqe dakyar, dan inta zauna tunane-tunane ba tashi zatayi ba.
Kayan da tazo dauka ta saka cikin wata yar jakar biki da aka ba Mami wajen Walima, ta dauke.
Ficewa tayi daga dakin, tana cin karo da Mami a falo
"Badai tun shigowar da kikai ba?"
Kai Waheedah ta langabar
"Wallahi Mami jikina ciwo yake...
A gajiye nake jina"
Yar dariya Mami tayi
"Ai dole, tunda kune kirjin biki"
Dariyar itama Waheedah tayi, tana fadin
"Kirjin biki kam nashan wahaka Mami"
Ta karasa maganar tana ficewa daga dakin.
Gidan su Nuriyya ta shiga da yake cike da mutane, tana samun Mama ta bata kayan da ta dauko.
Tukunna ta sake komawa gidan nasu, wannan karin bangaren Anty.
Tana shiga dakin da sallama.
Idanuwanta na sauka kan Nuriyya da ake ma kunshi.
"Wai har yanzun ba'a gama ba?"
Waheedah ta fadi tana karasawa ta samu waje ta zauna.
Nuriyyar bata amsata ba, ko dagowa batayi bama.
Bata tsammaci amsa ba, ita kanta zuciyarta ta mata wani irin nauyi dan zata ce ita kadai tasan halin da aminiyarta take ciki.
Dan a watannin nan biyu yanda take tashi ta gabatar da sallolin dare kan matsalar Nuriyya, ko ita da Nuriyyar bata tashi tayi addu'a kan matsalar irin haka.
Watannin su shidda da fara zuwa makaranta dukkan su, sunyi jarabawar zango na farko a cikin biyun da yake a shekara daya.
Dan Nuriyya ma ta riga Waheedah gama jarabawarta ta farko.
Duk da lokacin wata irin wayewa taban mamaki ta shigi Nuriyyar.
Wasu irin samari take tarawa da Waheedah bata san daga inda ta kwasosu ba.
Ko wayar hannunta Nokia C2, daya daga cikin samarin da tayi ne ya kawo mata.
A gida tayi karyar cewar Anas ne.
Waheedah kawai tasan asalin gaskiya, har fada sukayi akan wayar.
Dan Waheedah taga rashin kyautawar abinda Nuriyyar takeyi.
Kowa yasanta da Anas, duk da tana tare dashi ne har lokacin saboda yana da yake wahala da ita.
Tayi wasu samarin da suka fishi kudi, kyau, da komai, amman a cikinsu babu wanda yake dawainiyar da Anas din yake mata, shisa ta kasa rabuwa dashi.
Duk da ya dameta da maganar aure, hakan yasa tayi kuskuren cewa ya gaida mahaifinta.
Tasan Baba yasan da Anas, dan Mama kan nuna mishi inya siya mata kaya, koya kawo musu wani abin.
Yakanyi hakan, idan lokacin doyane ko dankalin Hausa, da yawa yake siyowa ya kawo musu, haka kayan marmari.
Baba ya fara mata fada kan tara samari, duk da tsoron shi da take kamar ranta, dan Baba baya wasa.
Tsayayyen mutum ne, bai hanata cigaba da tara samarin ba, sai dai takance suzo da yamma idan Baba bayanan.
Tashin hankalin duniyarta ya farane randa Baba yazo ya sameta da wani dan makarantar su, da sai yayi magana ne zaka san bahaushene, idan kaji sunan shi kasan musulmine saboda yanayin shigar shi da kuma askin da yake kanshi.
Ranar dukanta ne kawai Baba baiyi ba saboda fada.
A ranar ne kuma yace tai ma Anas magana idan da gaske yake ya turo.
Tsaye duniyar tai mata waje daya, saboda ko kadan Anas baya cikin tsarin mazan da take son aure, a rikice da wuni ranar tana jiran Magriba tayi, Anas yazo ta bashi hakuri ta gaya mishi ba zata aure shiba, kafin ya jaza mata masifa.
Magriba nayi kuwa sai gashi yazo, sai dai bata samu damar fada mishi ba, Baba ya fito ya same su yana gaya mata ta koma cikin gida.
Da kanshi yaima Anas din magana.
Abu kamar wasa washegari sai ga dangin Baban Anas din a gidansu aka tsayar da magana aka kuma saka biki wata uku kacal.
Dan shi daman a shirye yake.
Baba kuma yana dan tanadi, tunda yasan auren Nuriyyan zai iya zuwa kowanne lokaci, duk abinda ya samo yakan ba Mama ta ajiye, ita kuma adashi ta shiga irin na talakawa dan a taru a rufama kai asiri.
Har da Abba aka karbi kayan sa ranar Nuriyyan aka kuma tsaida magana.
Babu kalar tashin hankalin da bai faru a watannin ba, da kukan ta shabe-shabe, da duk yanda take tsoron Baba ta same shi tana tsugunnawa kan gwiwoyinta akan cewar ita bata son Anas.
Baba yace ta makara, dan shi bazai zama karamin mutum ba, idan bata san shi meyasa tasa yaje ya gaishe shi.
Me yasa ta dinga karbar mishi kaya?
Tabbatar mata Baba yayi idan an fasa auren sai dai idan shine ya kwanta dama, ko Anas yazo gidan da kanshi yace ya fasa aurenta.
Tun daga ranar tashin hankalinta ya fara, a watannin babu kalar wulakancin da batayiwa Anas, duk da har fada mata yayi zata cigaba da karatunta, shi zaiyi kokari ya biya mata komai, duk dan hankalinta ya kwanta.
Amman kamar duk wani abu dazai dan kyautata mata yana kara tunzurata ne.
Haka zasu zauna ita da Waheedah susha kuka.
Ita kanta Waheedah din saida tai zuru-zuru a yan lokuttan.
Tayi-tayi da Nuriyya ta kwantar da hankalinta, taci gaba da addu'a, batasan abinda Allah ya boye a auren ba, amman taqi.
Kullum Anas cikin kiran Waheedah yake ya kawo mata karar Nuriyyan, amman ko maganar takan kasa yima Nuriyya saboda halin da take ciki.
Abin harya fara bama Waheedah tsoro dan wayar karshe kan karar Waheedah da Anas ya kawo mata, maganganun shi sun tsaya mata
'Nima akwai zuciya a kirjina Waheedah, nima na iya fushi.
Wulakancin da Nuriyya taimun jiya yasa naji kamar in samu Baba a fasa auren nan.
Sai dai kinsan me?
Wallahi bata isa ba, bata isa ta mayar dani dan iska ba, har gardama nayi da Mamana akanta da tace mun ita auren bai kwanta mata ba.
Ta hakura saboda na nuna mata bazan iya barin Nuriyya ba.
Zaman wulakancin take so muyi aiko?
Ki fada mata a shirye nake da ita, wanda duk ya gaji saiya sauko ayi zaman lafiya.
Amman ko zata mutu sai an daura auren nan'
Sosai maganganun shi suke ma Waheedah yawo, bata gani ba, amman takan karanta wulakancin da namiji a litattafan Hausa, takan kuma ganina fina-finai.
Shisa take gujema wulakanta mutane ko yaya suke kuwa.
Musulunci ma yai hani da hakan, duk mazan dakan bita a makaranta takan fada musu an mata miji, dan bata son fara abinda ba zata iya karasawa ba.