← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 94

Sashe 26

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallo Waheedah tabi shi dashi harya shiga mota yaja murfin ya rufe, da ido ta rakasu har gate suka fice, ko sau daya Abdulkadir din bai juyo ba balle tayi tunanin ko hannu zai dan daga mata cikin alamar bankwana, jikinta take jin kamar an mata allurar rashin kuzari, saida taga mai gadi yaja gate din gidan ya rufe tukunna ta dago hannunta da take jin har zufa-zufa yake ta bude tafin hannun tana juyo dashi saboda taga meya rubuta.

Lambar wayar shi ce da adireshin shi na email, dayan hannunta tasa tana shafar rubutun hadi dayin yar dariya, sosai Abdulkadir yana da kokari ko da suke islamiyya da boko, a ajinsu kaf babu wanda yake kamo shi, amman baida rubutu me kyau, zaka rantse dan firamare ne yayi duk idan kagani.

Hannunta ta sake dubawa tana kallon lambobin hadi da rufe idanuwanta ta karanta su cikin kanta inda suka samu wajen zama daram.

Adireshin email din ta duba '[email protected]' ta hada da lambar wayar tana samar musu waje me kyau ta adana, hannun dake da rubutun ta daga tana dorawa a kirjinta inda zuciyarta take dokawa da wata irin nutsuwa tukunna ta juya tana nufar bangaren su, tana jin tafiyar da take kamar akan gajimare.

Idanuwan shi kofar gidansu Nuriyya ya sauka suna fita, saiya tsinci kan shi da sauke wani numfashi da baisan yana rike dashi ba, bazai ce ga asalin abinda yake ji ba, amman idan da Nuriyya zata kasance tsaye a kofar gidan hakan zai mishi dadi, gyara zama yayi cikin kujerar yana lumshe idanuwan shi, numfashi ya sake ja, kafin ya fitar dashi Yassar yace
"Meke damunka?"
Idanuwan shi ya bude yana juya kanshi bangaren Yassar din daya dan juyo ya kalle shi yana sake mayar da hankalin shi kan tuqin da yake
"Kai ido kaman an saka ma sakwara dan yatsa, kaita qara kankance su..."
Dakuna mishi fuska Abdulkadir yayi
"Kana cewa Ma shaa Allah Hamma, kyawun idanuna yasa kuka cinye mun tun ina karami..."
Dariya Yassar yayi
"Banza.

To har kai shekara wajen hudu in za'ai hoto idanuwanka basa fitowa"
Murmushi Abdulkadir yayi yana fadin
"Allah ya yafe maka..."
Dariya Yassar ya sake yi, muryar shi wannan karin babu alamun wasa yace
"Da gaske, me yake damun ka?"
Dan daga kafadu Abdulkadir din yayi, baisan me yake damun shi ba shi kanshi, kawai dai wani sanyin jiki yake ji naban mamaki, kuma ba zai cema Yassar yaso yaga Nuriyya a tsaye a kofar gidan ba, saboda bashida dalilin da zaiji hakan, bai kuma san abinda yasa yake jin hakan ba.

Shiru Yassar yayi, dan ta gefen idon shi yaga Abdulkadir din ya daga mishi kafadu, ya kuma san ba sake wata magana zaiyi ba, idan wani abin ma yana damun shi sai yaga dama zai fada mishi.

"Kardai kabari koma menene ya dameka"
Yassar yace, wallet din shi Abdulkadir din yake wasa da ita, maballin yake ballewa yana mayarwa, kafin ya sauke idanuwan shi akan wallet din lokacin daya balle maballin, karamin hoto yagani a jiki, bayan shi a juye, daquna fuska yayi, a hankali yake furta
"Ba duka na bata ba?"
Dan kallon shi Yassar yayi
"Magana kake?"
Dagowa Abdulkadir yayi yana girgiza ma Yassar kai, kafin yasa dan yatsan shi ya zaro hoton yana juya shi, daquna fuska ya sakeyi ganin hoton Waheedah, kafin dariyar da baisan daga inda ta fito ba ta kwace mishi.

Yana da tabbacin ko gawayi aka shafama Waheedah a fuska sai idanuwanta sun nuna alamun farinta, yanda akai ta kubcema zama zabiya abin jinjina ma Ikon Allah ne.

Juya hoton yayi yasaka shi dai-dai a cikin wallet din, haka kawai ya tsinci kanshi da saka dan yatsa ya shafi fuskarta dake jikin hoton, kamar zaiga tsoron shi ya cika manyan idanuwanta.

Jiyai an fisge wallet din, da sauri ya bita da shirin kamowa, Yassar ya mayar da ita dayan bangaren yana daga cinyar shi ya saka wallet din
"Tuqi nake Abdulkadir..."
Harararshi Abdulkadir yayi
"Hamma bana so, bana so, kabani wallet dina"
Murmushi Yassar yake yi
"Meye kake shafawa da dan yatsa?

Dariyar me kake kuma?"
Kankance idanuwa Abdulkadir yayi
"Ina ruwanka?

Karka bude, kabani wallet dina..."
Gudun motar Yassar ya rage yana zaro wallet din daga karkashin cinyar shi ya bude, dan kallo yayi tukunna ya mayar da idanuwan shi kan titi, wannan karin shi ya daquna fuskar shi da take dauke da bayanannen mamaki ganin hoton Waheedah din
"Kabani Hamma, ni banason irin wannan.

Ai zubda girma ne kana daukar abin kaninka.

Ba saika ja in rainaka ba"
Abdulkadir din yake fadi yana miqa jikin shi ya fisge wallet din daga hannun Yassar ya balleta yana dan daga jikin shi ya saka a aljihu.

Kallon shi Yassar yayi yana rasa abinda zai fada, sosai mamaki yakeyi.

"Karka fara abinda ba zaka iya karasawa ba Abdulkadir, karka fara"
Yassar yace da wani yanayi a muryar shi da yasa Abdulkadir din kallon shi cike da rudani
"Kar in fara me?"
Wannan karin sosai Yassar ya rage gudun motar, yana jin wanda suke bayan shi suna danna mishi hon, alamun idan shi baida gurin zuwa su suna dashi, amman bai damu dasu ba, Abdulkadir ya kalla sosai yana son karantar gaskiyar abinda yake tunanin, amman banda confusion babu abinda yake fuskar Abdulkadir din.

Murmushi Yassar yayi yana girgiza mishi kai.

Idan soyayya ce take shirin qulluwa a tsakanin Abdulkadir din da Waheedah bazai kara mata gudu ba tun kafin Abdulkadir din ya fahimci akwaita.

"Ni banaso a fara mun maganar da bangane ba, kasani kuma"
Gudun motar Yassar ya kara, tukunna ya amsa Abdulkadir din da
"A shaqeni a fito da sauran mana"
Wani kallo Abdulkadir din yai mishi, tukunna yakai hannu yana kunna radio din cikin motar, maganar yake qurewa da yasa Yassar bugar mishi hannun daya janye babu shiri, maganar ya rage yana fadin
"Ka qarata sai naci ubanka wallahi, ba zaka cika mun kunne ba"
Daquna fuska Abdulkadir din yayi kasa-kasa yace
"Matsala kake da ita Hamma"
Murmushi Yassar yayi
"Idan ma zagine bazan zagu a fili ba, kuma bazan daku ba..."
Gyara zaman shi Abdulkadir din yayi cikin kujerar, yana jingina kanshi da jikin kujerar.

Idanuwan shi ya lumshe, hoton Nuriyya na tasowa daga inda ya samu wajen zama cikin kan shi yana bayyana a bayan idanuwan shi cikin yanayin daya sashi bude idon shi babu shiri, kallon hanya yaci gaba dayi zuciyar shi ta mishi nauyi naban mamaki.

A kasan zuciyarta take jin wani irin fili da tafiyar Abdulkadir tabar mata, zata rantse da Allah akwai wani bangare nata da ya tafi dashi, sai dai ba zata iya dora dan yatsa akan bangaren ba, da duk kwanakin da yake karawa da yanda take jin filin na qara mata girma.

Yanzun ma hakan take ji, komai baya mata dadi, har littafin da ta fara karantawa na Biebee Isa (ke Alheri ce) tana kwasar dariyar Nenne da dinkum dinta, yau ta kasa karasawa.

Sosai take jin kewar shi na danne ta.

Ga ranar Alhamis ce babu islamiyya balle taje ta rage zafi.

Nuriyya kuma bata nan, taje wajen dangin mamanta sada zumunci.

Kujera ta dauko ta saka a harabar gidan ta zauna, tunanin ya hadar mata biyu.

Gana Abdulkadir, gana Nuriyya da takeyi, dan ta jima tana mata maganar tsoron faduwa jarabawar aji shidda, kasancewar makarantar gwamnatin ba wani tabbacin kirki gareta ba, duk da Nuriyya na da kokari, gashi tunda suka shiga aji hudu su biyun, banda darasin ingilishi da lissafi, babu abinda suke iya samu suyi ita da Nuriyyan, tunda ita Waheedah bangaren Art take, Nuriyyar kuma commerce, a cewarta tana son karantar bangaren kasuwanci dan tayi aiki da wani kamfani babba.

Ita kuwa Waheedah turanci take son karanta, ta kuma koyar in ta samu hakan.

To satin aka fara biyan jarabawar aji shiddan ta Waec, batasan ta inda zata fara yima Abba maganar Nuriyyan ba, saboda batason dora mishi nauyi fiye da wanda yake kan shi, amman ta tambayo wata makaranta da babu nisa dasu, Green olive, kudin jarabawar kuma kadan zai cika a wanda zai biya mata ita kadai a Sheikh Bashir su zana anan Green Olive din ita da Nuriyya.

Kamar daga sama taji an tafa hannuwa a saitin fuskarta daya katse mata tunanin datai zurfi a ciki, tana sauke idanuwanta kan fuskar Yazid dake mata murmushi har dimple din gefen fuskar shi ya bayyana.

Kaf dakin Hajja, har matan babu mai kyawun Yazid, ga sumar dake fuskar shi ta kara mishi wani kwarjini naban mamaki, abinka da wanda yake da haske fata
"Hamma Yazid..."
Waheedah ta fadi tana mayar mishi da murmushin da yake mata
"Tunanin me kike haka?"
Kai Waheedah ta girgiza mishi a hankali, daga mata girar shi duka biyun Yazid yayi, alamar bai yarda ba.

Inda kujerun robar suke ya karasa yana dauko guda daya ya dawo da ita ya kusa da Waheedah ya zauna.

"Bansan kanwar tawa da karya ba"
A kunyace Waheedah ta sadda kanta kasa tana wasa da yatsunta, sosai yake jin kominta har ranshi.

Shi ba mutum bane maison hayaniyar duniya, shisa jininsu ya hadu da Waheedah din, sanyin halinta ya mishi.

"Kinsan zaki iya fadamun damuwarki ko?"
Ya bukata a tausashe, numfashi Waheedah ta sauke
"Da gaske babu komai Hamma"
Kai Yazid ya girgiza mata
"Aikam zamuyi fada yau"
Dan murmushi Waheedah tayi
"Ina son inma Abba magana ne, kuma ina jin nauyi"
Sake gyara zaman shi Yazid yayi
"To ni kimun maganar"
Dagowa fuskarta tayi tana kallon yanda ya bata gabaki daya hankalin shi, idan wani yagani zai rantse bashida wani abu mai muhimmanci daya wuce saurarenta.
Chapter 26 · 0% Book details