Sashe 49
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko musha Tea?"
Tun kafin ta karasa kalmar Tea din yake girgiza mata kai, ana zaune lafiya bazai sha shayi ya kwanta ba, yunwar da yakeji ma tafi karfin shayi.
"Wani abu dai banda shayi"
Shagwabe fuska tayi tana sauke muryarta cike da kissa
"Kamar me?
Ka zabi wani abu mai sauqi"
Dakuna fuska AbdulKadir yayi, yanayin na mishi baqunta, shifa sam bai saba fadar abinda zaici ba, dafawa Waheedah takeyi ta kawo mishi
"Ki dafa komai ma, ni ban saba zabar abincin ba, kome kika bani zanci, amman banda shayi"
Numfashi taja tana saukewa
"Ko mu fita muci a waje?"
Kallonta yayi yana kankance mata idanuwan shi
"Saboda me?"
Ya bukata yana jiran jin dalilin da zaisa su fita waje suci abinci.
Haka kawai tunani ya watsa shi washegarin auren su da Waheedah.
"Me zakici in siyo mana?"
Ya bukata bayan tafiyar su Anty, yana kallon yanda take dakuna mishi fuska tana tambayar shi
"Muna da abinci a kitchen, me yasa zaka siyo?"
Kafadu yadan daga mata
"Sai an dafa..."
Ya amsa a taqaice
"Nasani, amman akwai"
Kai ya girgiza
"Amarya bata girki"
Murmushi tai mishi tana mikewa ta nufi kitchen din, binta yayi.
Tare sukaita bude-buden abubuwa a kitchen din harta gama dauko wanda take bukata, da wani gari daya gani kamar yaji, sai dai yafi yaji ja yaga ta jiqa a ruwa, sai tumatir na leda, macaroni tayi musu jalof da sauran kajin da aka kawo musu da su Anty basu cinye ba suka saka mata a fridge.
Sosai yaci abincin dan ya mishi dadi.
"Masoyi..."
Nuriyya ta fadi tana riko hannun shi, ganin yayi shiru kamar yana tunani
"Ki soya mana ko dankali saiki mana sauce"
Ya fadi da wani nisantaccen yanayi a muryarshi, ranta taji ya baci saboda zaman fere dankalin da zatayi
"Banda dankali fa, sai dai in siyowa zakayi"
Kai ya girgiza mata, bayajin fita sam
"Ki duba kitchen din Wahee...
Tana dashi"
Mikewa tayi tana nufar bangaren Waheedah din da tunanin yaushe zata dawo gidan.
Dan ita ba zata iya wannan bautar ba sam-sam, rabonta da wani girki harta manta.
Gashi ta kula da AbdulKadir din nada mugun cin abinci, kuma tana da tabbacin Waheedah ta lalata shi haka.
Kwando ta samu ta kwashi dankalin da take tunanin zai ishe su ta koma nata bangaren.
Ta wuce AbdulKadir zaune inda ta same shi, wayar Waheedah ya kira a kashe, hakan yasa shi ajiye tashi yana jin ranshi a jagule.
"Masoyi ba zaka zo ka tayani ba?
Da yawa fa dankalin..."
Nuriyya ta fadi daga bakin kofar kitchen din kamar zata fashe da kuka, gashi bata iya
saka peeler ba, dole sai dai da wuqa.
"Ban iya ferewa ba nikam"
Yai maganar da iya gaskiyar shi, yakan dami Waheedah da zai tayata aiki in tanayi, amman banda Maggi bata bashi komai, sau daya ta bashi yankan albasa, yajin daya cika mishi ido yasa har ya yanke hannu, bata kara ba, da yayi magana zatace ya rufa mata asiri, kafin azo a kamata taba soja aiki ya yanke hannu.
Sai dai yakan miqo mata su cokali ko kwano.
Jin Nuriyya bata kara mishi magana ba yasa shi zamewa ya kwanta kan kujerar, ya dora hannun shi saman goshin shi yana lumshe idanuwan shi.
Baifi minti biyar ba ya bude idanuwan shi, sai dai me, yanda tunanin Waheedah ya addabeshi da ya rufe idanuwan hakan ma daya bude su.
Tashi zaune yayi, tunani bakon abune a tare dashi, babu abinda ya isa ya saka shi tunani haka, Waheedah tasani, bazai iya kwana baisan matsayar matsalarsu ba.
Wayar shi ya dauka ya wuce ya dauko mukullin mota tukunna ya dawo yana fadin
"Nuriyya bari in dubo Waheedah, zanyi sallah a hanya..."
Kai ta daga mishi daya saka shi dakuna mata fuska, babu shiri tace
"Tam a dawo lafiya, kayi mata sannu"
Nashi kan ya jinjina mata, ita bata isa tai mishi ba, tana kuma lura da Waheedah na amsa shi da kai baya ce mata komai, amman ranar farko data kwatanta magana yai mata, data gwada yi mishi shiru ma saida ya sauke mata masifarshi har kuka tayi ranar.
Akwai abubuwa da yawa da take lura Waheedah kawai take yinsu yana dauka, hakan kuma na mata quna har kasan ranta.
Tana jin takun tafiyar shi har ya bace mata.
Kamar yanda ya fada, a hanys ya tsaya yai sallar magriba, sannan ya karasa gidan Yassar.
Ya gwada kiran wayar Waheedah bai samu ba, hakan yasa shi shiga gidan kanshi tsaye hadi dayin sallama.
Hauwa ta amsa mishi suna gaisawa, AbdulKadir din ya dora da
"Waheedah fa?"
Dan jim tayi na minti daya, batasan me yake faruwa ba, ba kuma tason shiga koma menene, idan akwai abinda zama da Yassar ya koya mata bai wuce kin shiga abinda babu ruwanta a ciki ba.
Dan haka ta nuna mishi hanyar dakin da Waheedah din take ciki, tana ci gaba da hidimar da takeyi ta fito musu da abincin dare.
Sauri AbdulKadir yakeyi yana godema Allah da baiga Yassar ba, dan zai iya cewa bazai ga Waheedah din ba.
Dakin ya tura ko sallama baiyi ba yana mayarwa ya rufe.
Tsaye yaganta ta goya Ikram tana jijjigata, kallon mamaki take mishi, dan ta dauka ma Fajr ne ya shigo mata daki babu sallama haka, juyowa tayi tai mishi fada taga AbdulKadir a tsaye.
Lumshe idanuwanta tayi ta bude su akan shi tana jiran soyayyar shi da takanji ta taso mata duk lokacin da zai bayyana a gabanta, amman shiru, babu abinda takeji banda son kara yin nisa dashi.
"Waheedah..."
Ya kira muryar shi na fitowa a karye da ganin nisan da tayi mishi cikin idanuwanta duk da tana tsaye a gaban shi
"Ba zan iya bacci bansan me kike so dani ba..."
Murmushi tayi, kallon ta yake, da gaske murmushi tayi, shi kam ko kadan baiga abin nishadi a yanayin da suke ciki ba
"Da wanne yare kake so in fada maka?
Na maka da Hausa, in maka da turanci ko da larabci?
Su kadai nasan kana fahimta...
Sakina nake so kayi Sadauki, ka fadamun idan akwai abu mai wahala cikin gane hakan"
Tabbas ranar tazo mishi da abubuwa naban mamaki, Waheedah yake kallo yana son ganin ko da gaske matar shi ce a gabanshi, da gaske Waheedahr shi ce da ko murya bata taba daga mishi ba, balle ta tsaya idanuwanta cikin nashi tana gaya mishi magana irin hakan.
Ji yake kamar an watsa mishi ruwan sanyi an kunna mishi AC.
Jikin shi ba la'asar kawai yai ba, isha'i yayi makararriya.
"Waheedah?"
Ya iya furtawa yana kallonta, ganin taki sauke idanuwanta, kuma bata da alamar amsa shi yasaka shi fadin
"Nine fa, Waheedah ni ne?"
Kai ta jinjina
"Naganka ai...
Kaga na nuna alamar bakai bane?"
Wannan karin dariyar takaici mai sauti ta kubce mishi
"Yaushe kika koyi rashin kunya?"
Maganar da yai zaton cikin kanshi yayi ta fito fili, sautin muryar shi na dukan kunnen shi da wani yanayi.
Kafadu tadan daga mishi
"Zama da madaukin kanwa..."
Waheedah ta fadi tana zama gefen gadon
"Me kike nufi?"
Cewar AbdulKadir cikin bacin rai, kallon shi tayi wannan karin tana ganin yanda yake gab da birkice mata.
"Karka tasar mun da yarinya, Sadauki bazan iya hayaniya ba, dan Allah inba takarda zaka bani ba ka fita...sanda ka shirya bani kasan inda nake"
Kai kawai ya iya jinjinawa, yana juyawa ya bude kofar ya fice daga dakin, a falo ya samu Yassar da alama lokacin ya shigo
"AbdulKadir..."
Ya kira cike da mamaki, ko inda yake AbdulKadir bai kalla ba, hanyar da zata fitar dashi daga dakin kawai yake nema, saboda yanajin yanda wani agogo yake harbawa cikin kanshi yana mishi kashedin saura kiris ya cika, bayaso lokacin da koma meye ya dibar mishi ya cika a cikin mutane, kar a samu matsala.
Rabon da ranshi ya baci irin haka harya manta, dan har wani duhu-duhu yake gani.
Ganin hakan yasa Yassar kara kiran shi
"AbdulKadir..."
Gani yai ya fice daga dakin, babu shiri Yassar yabi bayanshi, ko takalma bai tsaya ya saka ba.
Kafadar shi ya dafa yana juyo dashi
"Magana nake maka"
Ya fadi yana yawata idanuwan shi kan fuskar AbdulKadir din, bakuma yason abinda yake gani shimfide akai.
"A haka zaka shiga mota kai tuqi?
Saboda baka da hankali"
Numfashi AbdulKadir ya sauke yana jan hancin shi da yake ji kamar yaji-yaji a ciki, muryar shi can kasan makoshi yace
"Me yasa igiyar aure ta shiga tsakanina da Waheedah?
Hamma me yasa?"
Runtsa idanuwa Yassar yayi, cikin alamar rarrashi ya ce
"AbdulKadir..."
Kai AbdulKadir din ya girgiza mishi yana jin kaman zai kama da wuta da yanda jikin shi ya dauki dumi saboda bacin rai.
"Na mareta da safe, bansan ya akai ba Hamma, wallahi ban sani ba, amman cikin idona ta kalla tai mun rashin kunya...
Yanzun ta kara...
Bansan meya faru ba, bansan me nai mata haka ba....amman a karo na farko inajin igiyar auren da ta hadamu batai mun adalci ba.
Da ta bani damar da zan daketa yanda raina yake so da ta dawo hayyacin ta ta fadamun me nai mata sai in san yanda zanyi in gyara..."
Dafe kai Yassar yayi, baisan abinda ya kamata yayi ba, a yini daya yana ganin AbdulKadir din na shirin susucewa, baisan me zai faru in aka dauki kwanaki a haka ba, tsintar kanshi yayi da musu addu'ar samun maslaha su duka biyun, dan sun saka shi a tsakiya ta yanda bazai iya zaben bangare ba.
Motar shi AbdulKadir ya bude tukunna ya sake juyowa
"Ka fada mata, wallahi bata isa ba...wallahi bata isa ta birkitamun lissafi ina zaune lafiya ba...idan rigima take so Hamma ka fada mata AbdulKadir ne...taga wajen kwanana shisa ta rainani haka..."
Da idanuwa yake bin AbdulKadir din da kallo, murmushin da baisan ta inda ya taho ba yana shirin kwace mishi.
AbdulKadir na kiran Waheedah bata isa ta birkita mishi tunani ba, amman hauka yake tuburan, tsaye yayi saida yaga yanda AbdulKadir din ya birka mota kamar zai takashi tukunna ya matsa da sauri.