Sashe 59
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amman naga alama yanda kasa kafa ka shure duk wata kunya da ake halittar dan adam da ita haka itama tayi fatali da tata"
Gefen Hajja AbdulKadir ya zauna yana fadin
"Hajja akan maganar ne kema kike so ki bata ranki?
Me yasa bazan aureta ba bayan addini ya halarta mun, me yasa kuke son haramtamun abinda Allah bai...."
Kara yaji cikin kunnen shi na haggu da ya katse mishi maganar da yake shirinyi, kafin daga baya ya fuskanci abinda ya faru.
Hannun shi yasa yana taba kuncin shi cike da tsantsar mamaki.
"Hajja...
Marina kikayi Hajja...
Mari Hajja"
Kai ta jinjina mishi tana fadin
"Ina gab da kara maka wani in baka bacemun dagani ba wallahi.
Tunda kai bakasan abinda ke maka ciwo ba, abinda duk kaga dama shi kake son yi....
Aure ko?
Auren cin amana, ayi lafiya AbdulKadir, wallahi ba baki nai maka ba, alhakin Waheedah bazai barku ba"
Hajja ta karasa maganar tana kokarin tarbe hawayen da takejin sun cika idanuwanta dan takaici, rokar mishi yafiyar Allah take da yanda ya bata mata rai kar wani abin ya same shi.
Mikewar yayi kuwa, baya niyyar bata hakuri koya ce mata ya fasa auren.
Muryar shi can kasan makoshi yace
"In kin huce kimun addu'a Hajja..."
Ya wuce yana fita daga dakin, yaja mata kofar a hankali, yanajin yanda ita kadaice zata mishi abinda tai mishi din.
Duk da ran shi yakai koluluwa a baci.
Daga jiya zuwa yau, abinda Abba yai mishi, Yassar, yanzun kuma ita.
Kamar tunzura shi sukeyi da son yin auren, dan yanajin bashi bane mutum na farko da addini ya halarta ma abu al'ada ta haramta mishi.
Zai dai zama cikin mutane kalilan da ba zasu taba barin al'ada tayi nasara akan su ba.
Yana fita daga gidan, machine ya tare yahau zuwa zoo road, rabon shi da gidan kanin Abba, Alhaji Ali da suke kira da Kawu Ali, harya manta.
Amman shi kadai ne mutumin da yake da yakinin zai tsaya mishi kan maganar, dan a gidan su Abba kaf shine yake dan boko na gaske, kuma mutumin da ko a yaran shi zaka fuskanci wayewar da suke tafiyar da rayuwar su a kai.
Duk da a baya AbdulKadir din kanyi tir da kalar tarbiyar tasu, yau dai Kawu Ali zai mishi ranar da bai zata ba.
Da yake ranar lahadi ce, babu aiki, ya kuwa yi nasarar samun Kawu Ali a gida.
Fada mishi abinda yake faruwa yayi, sosai Kawu Ali ya jinjina maganar
"Shima Alhaji yana da matsala wallahi, yanzun da kuzo kuna abinda bai kamata ba ai gara ayi auren.
Kayi hankali da kazo ka sameni da maganar, kaje abinka, zan kira shi muyi magana in shaa Allah"
Dan jim AbdulKadir yayi kafin yace
"Gobe in shaa Allah zan wuce ne Kawu, nafi so a gama maganar kafin in tafi"
Kai Kawu Ali ya jinjina yana fadin
"Bari in kira shi yanzun inji idan bai fita ba, sai muje gidan"
Gyara zama AbdulKadir din yayi, yana sauraren Kawu Ali ya kira Abba, bayajin me Abban yake cewa.
Amman da alama baya gida, Kawu Ali na sauke wayar ya kalli AbdulKadir
"Sai da dare, ya fita.
Amman karka damu in shaa Allah komai zaiyi dai-dai"
Godiya AbdulKadir yaima Kawu Ali tukunna ya wuce, gida ya nufa, a kitchen ya samu Waheedah tana ta aikin da baisan na menene ba, falo ya koma ya kwanta kan doguwar kujera.
Babu abinda yake so sai yaga an daura auren ya gama da wannan matsalar, ganin tunani zai mishi yawa inya kwanta yasa shi tashi yabi Waheedah kitchen din
"Me kike dafa mana?"
Kallon shi tayi tace
"Dambun shinkafa"
Murmushin da yai mata yasa taji gabaki daya wahalar dambun ta bace mata
"Ina son shi sosai"
"Nasani...
Harda zobo na dafa mana, shi zan hada yanzun"
Murmushin AbdulKadir ya sake yi mata, a cikin gidan su ya baro marin da Hajja tai mishi, dan bazai saka abin a ranshi ba.
Abu daya da kowa bai sani ba shine yana da Waheedah, babu wani abu da zai bata mishi rai fiye da rana daya.
Zatayi wani abin da zaishi ranshi kal, kamar yanzun din ma, gashi duk da hasken da yake ganin ta kara, ta mishi kyau cikin riga da skirt dinta, dankwalin ta daura shi simple, da jan jambaki a labbanta da tunda ta kula yana so take sakawa, dan ita kwalliya ba damunta tayi ba.
Ganin yana matsowa cikin kokarin hade space din sake tsakanin su yasa ta nuna shi da ludayin hannun ta tana matsawa baya
"Sadauki aiki nake wallahi, dan Allah kaje kayi zamanka, zobo zan hada kaga....
Kaji"
Dariya AbdulKadir yayi yana ja ya tsaya, har saida ta karasa wajen kantar kitchen din, tukunna ya taka yana taba fuskarta zuwa wuyanta
"Ni zanji ko da zazzabi a jikinki ne kawai..."
Murmushi tayi, tasan halin shi sarai.
Shiya miko mata robar sukari ta hada zobon da zallar shine yasha kayan kamshi, sai flavor din abarba da tadan diga na ruwa.
Da dumin shi haka AbdulKadir yace mata shi yana sha.
Dole ta zuba mishi tukunna ya fitar mata daga kitchen din yana komawa falo, taci gaba da aikinta.
Kafin isha'i Kawu Ali ya kirashi da su hadu a gida.
Dan haka yana fitowa daga masallaci yahau machine ya wuce.
Dakin Abba ya nufa, zuciyar shi a dake yake jinta.
Dan ya gama yanke hukuncin duk abinda zasu fada bazai canza ra'ayin shi ba.
Da sallama ya shiga dakin Abban yana samun shi zaune da Kawu Ali.
Wani irin kallo Abba yabi shi dashi da yake jin yana neman sanyaya mishi jiki.
Yana zama kuwa kamar jiran shi Abba yake
"Ni ban isa ba ko AbdulKadir?
Ban isa da kai ba kake son nuna mun, kuma nagani.
Allah yai maka albarka ya kuma shiryeka....
Aure ayi lafiya amman wallahi babu hannuna a maganar"
Numfashi Kawu Ali ya sauke, ya bude baki zaiyi magana Abba ya katse shi da fadin
"Ku biyun tashi zakuyi kubani waje, kai boko ta hanaka ganin aibun abinda zaiyi, shikuma taurin kai ko?
Allah ya bada zaman lafiya, sai kuje kuyi duk abinda kuke so, bana son jin kowacce irin magana indai kan auren nan ne..."
Ganin sun zauna yasa Abba mikewa ya shige bedroom din shi yana barinsu.
AbdulKadir kan shi a kasa yake, tunda yake da Abba bai taba ganin ranshi ya baci haka ba.
Shi kan shi Kawun jikin shi a sanyaye yake jin shi.
"Abbanka yace yarinyar nan makota take, kuma bazawara ce, abin bazaiyi wahala ba....da Babanta yana nan ma sai mu fara magana"
Mikewa AbdulKadir yayi yanajin shi kamar yana yawo a gajimare, komai yake jin yai mishi wani irin shiru.
"Sai mu duba mugani"
Ya fadi, muryar shi na dawowa kunnuwan shi da wani irin yanayi.
Tare da Kawu suka fita har kofar gidan su Nuriyya, sallama sukayi da Babanta, ya kuwa fito, yagane AbdulKadir din, amman yayi mamakin ganin su a kofar gidan.
Gaishe dashi AbdulKadir yayi yanajin Kawu Ali na mishi bayanin komai.
Sosai Baba ya nutsu yana sauraren su.
Duk yanda yake son sakama Nuriyya ido, zai karya idan yace matsalar yarinyar bata damun shi tana kuma bata mishi rai.
Alhaji Ahmad mutum ne da yake gani da matuqar mutunci, kuma yana taimaka mishi sosai da sosai.
Ba zaiso Nuriyya ta zama sanadin da wannan zumuncin da suka shafe shekaru suna ginawa ya zube ba.
A nutse yace ma kawu Ali
"Ku bani mintina biyar in dawo"
Cikin gida ya shiga ya sa aka kira mishi Nuriyyar, muryarshi babu alamun wasa yace
"AbdulKadir ne yaron Alhaji Ahmad da Kawun shi suka zo kan maganar auren ki"
Dagowa tayi ta kalli Baba tanajin ta kamar a mafarki, text din karshe da AbdulKadir yayi mata shine
'Karki kirani, ki jirani zanma Abba magana'
Bata kirashi din ba kuwa, da zullumi ta kwana fal ranta, ko abinci sai dazun da magriba ta tura
shi badan tana gane kanshi ba, haka kawai zuciyarta rawa take mata.
Gani take ko sama da kasa zasu hade ba za'a bari AbdulKadir ya aureta ba, yanzun kuma da Baba yazo mata da maganar sai take ganin kamar mafarki take.
"Kinga abinda kikai mana aurenki na farko, badan bana miki addu'a ba, amman wallahi ban taba tunanin zaki sami namijin da yake da masuyi mishi fada bayan yayi bincike yaji abinda ya fito dake daga gidan mijinki su barshi ya aure ki.
Idan za'ayi magana ta gaskiya ni bazan bari dana ya aureki ba.
Zuwa nayi in tambayeki dan idan kika kaso wannan auren ki nemi inda zaki wuce daga gidan mijin, wallahi Nuriyya ba zanyi kaffara ba, kika kaso auren nan ba zaki zauna mun a gida ba"
Kai ta daga mishi, haka kawai idanuwanta na cika da hawaye.
Juyawa Baba yayi ya koma kofar gidan ya samu su AbdulKadir yana fadin
"Idan yanzun kun shirya ma ana iya daura aure tunda ba budurwa bace"
Ware idanuwa AbdulKadir yayi, yana da inda zai ajiye Nuriyya, yana da kudin Sadaki da zai bayar, amman akwai su lefe da sauran kananun abubuwa, duk da an tayashi bikin Waheedah bazai manta kalar kudaden daya tara ba.
"Baba akwai su lefe"
Dariya Kawu yayi yana cewa
"Kayya AbdulKadir...
Ai ta taba wani auren, za'a iya daurawa yanzun, duk da gaggawa na daga shaidan, amman auren za'a iya daurawa sai kuyi maganar lokacin tarewa da sauran abubuwa"
Kai AbdulKadir ya daga yana fadin
"Babu kudi a jikina, sai dai inje banki in dawo yanzun"
Jinshi yake kamar a mafarki, kai Kawu Ali ya girgiza mishi yana fadin akwai kudi a wajen shi.
Mota suka koma Kawu Ali ya kirgo dubu hamsin suka sake fita, masallaci sukaje akayiwa Liman magana, da wasu manyan mutane da suke zaune a majalissa nan gefen masallacin.
Cikin kasa da mintina talatin aka daura auren aka gama komai.
Kawu Ali da kanshi ya sauke AbdulKadir har gida dan yace mishi bada mota yazo ba.
Ya shiga cikin gidan, ya dora hannun shi kan handle din kofa, amman ya kasa murzawa, komai daya faru yakeji yana danne shi, kamar wani mafarkine yakeyi sai yanzun ya farka ya samu mafarkin da gaske ne.