Sashe 8
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Dan Allah Abba..."
Roqon da Waheedah tayi ya katse ma Anty dogon tunanin da takeyi, wani radadi takeji zuciyarta nayi, kuncin Waheedah na tuna mata da duk hakurin da tayi a nata gidan auren, yana sa tana tuna rashin sauqin da yake tattare da hakuri, sai mai matuqar karfin zuciya ake yiwa ya kauda kai.
Abba kan shi numfashi ya sauke yana furta
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un...
Abdulkadir...Halima kinga yaron nan saida ya kure hakurin ta ko?"
Abba ya karasa maganar yana jinjina kanshi, a raunane Anty ta amsa shi da
"Ai shikenan, ya kyauta, ya kuma yima kan shi wallahi"
Hajja ce ta shigo dakin da sallama, tana kare musu kallo, dan sallah take lokacin da Abba ya aika a kirata.
Mami daman da Anty taje da kanta catai duk suna wajen ita kam bataga zuwan me zatayi ba, ta san zasuyi yanke duk abinda ya kamata akan Waheedah din.
Duk kawaicin Mami, Anty tasan Waheedah ta ninka ta, yau kam tura takai bango.
"Allah dai yasa lafiya..."
Hajja ta fadi bayan Anty ta amsa mata sallamarta, kafin ta zagayo ta samu waje gefen Abba ta zauna, sai lokacin ta kula da Waheedah da tun shigowar Abba ta sauko daga kujerar da take ta zauna kan kafet din dakin
"Subhanallah, Waheedah?
Ashe dai ciwon da yawa haka...
Zainab tazo tana fadamun, yanzun nake shirin in idar da sallah saimu koma asibitin gabaki daya.
Amman kamar bai kamata su baki sallama da wuri haka ba..."
Anty ce ta amsa Hajja da
"Basu bayar da sallama ba suma, zamu koma zuwa anjima..."
Da mamaki Hajja tace
"Ikon Allah...
Lafiya dai ko?"
Tai tambayar tana kallon Abba daya girgiza mata kai
"Abdulkadir ne..."
Zuciyarta Hajja taji tayi wata irin dokawa jin sunan dan nata
"Yau kam dai ya kure hakurin yarinyar nan.
Saki take nema..."
Cikin tashin hankali Hajja tace
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un...saki kuma Alhaji?
Meya faru?
Me yai mata?"
Dan rausayar dakai Abba yayi, dan baida wannan amsar, ba kuma shi da karfin zuciyar da zai tambayi Waheedah din tunda har roqon shi tayi dakar ya tambaya.
Waheedah dake share kwalla Hajja ta kalla
"Waheedah me ya faru?"
Batare data dago ba ko hawayenta ya daina zuba tace
"Dan Allah Hajja karki tambayeni meya faru, kiyi hakuri, duk kuyi hakuri, takardata kawai nake son a karbar mun a wajen shi..."
Maganar daga zuciyar ta takejin tana fitowa, ta dauka rashin Abdulkadir a kusa da ita zai barazana da rayuwarta, bata taba tunanin zama dashi ne abinda zai haifar da hakan ba, in baya kusa da ita ko numfashi batajin tana fitarwa dai-dai, amman yanzun tunanin kusanci dashine yake barazana da dai-daiton numfashin ta.
Ba tasan lokacin da rayuwa ta bude musu wannan shafin ba, sai dai ko ba zata iya wuce shi ba, zatai duk wani kokari da zata iya ko dansu Fajr.
Salati Hajja take tana kara wani
"Ke kam Waheedah kiyi hakuri mana, kinji tunda duk muna nan kibari a kira shi in shaa Allah koma menene yake faruwa zamuji sai a dai-daita ku...tunda haihuwa ta shiga tsakani ko dan yara sai a duba lamarin..."
Kai Abba ya girgiza ma Hajja
"Karkuyi amfani da yaranta ku danne ta..."
Rai a jagule Hajja ta kalle shi
"Karka cemun kana tunanin yin abinda take so ne batare daka duba lamarin ba?"
Kafin ya amsa Abdulkadir ya shigo dakin, kallo daya zakai mishi kasan babu nutsuwa a tattare dashi ballantana ai maganar kwanciyar hankali.
Ko sallama baiyi ba, zagayowa yayi yana zama kan hannun kujera, zuciyar shi kamar zata fito daga kirjin shi saboda tsallen da takeyi
"Abba me tace na mata?"
Ya tambaya, rashin gaskiya shimfide a fuskar shi.
Kallon shi kawai Abba yakeyi, Hajja ce ta watsa mishi harara
"Me kai mata Abdulkadir?
Me ka sake yi mata?"
Cike da rashin fahimta yace
"Bangane me na sake mata ba Hajja?
Na mata wani abune banda nayau?"
Girgiza kai Anty tayi tana fadin
"Hmm..."
Dan batason tayi magana, Abdulkadir rashin kunya zai mata tasan shi sarai
"Dan ubanka baka san me kai mata ba?"
Fuskar shi babu walwala yace
"Hajja mana..."
Ko kadan bayaso a saka shi a gaba ana mishi fada, ko dacan ma bayaso balle yanzun da ba yaro bane shi, sai dai baiga laifin su ba, Waheedah ce, duk laifin nata ne da tai mishi wannan tonon sililin, tafi kowa sanin yanda yake son sirri a rayuwar shi, abinda ya faru yau din tsautsayine da zasu iya magance shi tsakanin su, baisan me yake damunta da ta kwaso matsalarsu tana fadama su Abba da baiga ta inda abin ya shafe su ba.
"Ka kyauta Abdulkadir...
Ka ji...
Ka kyauta"
Hajja ta karasa muryarta na karyewa, idan ranta yai dubu a bace yake.
Abba ya sake kallo
"Dan Allah Abba me tace nayi mata?"
Kai Abba ya girgiza mishi
"Batace kai mata wani abu, aurenka ne kawai ta gaji dashi"
Cikin wani irin tashin hankali Abdulkadir ya kalli Waheedah da ta sauke mishi rinannun idanuwanta.
Da nashi idanuwan yake tambayarya me take?
Me take yi musu haka?
"Abba zanyi magana da ita...
Kaji...
Hajja kunji..."
Ganin suna kallon shi yasa shi dorawa da
"Dan Allah..."
Abba ya fara miqewa, shikam batun yanzun ya sallama da lamurran Abdulkadir ba, tsakanin shi da yaron idone da addu'a, amman shikam yace yayi ko kar yayi bakin shi ya daina wannan asarar.
Ganin da gaske bar musu dakin zasuyi yasa Waheedah fadin
"Abba dakun zauna...
Kome zaice bazai canza komai ba...
Takardata kawai nake so ku amsar min tunda ni na mishi magana yaki..."
Basu ce komai ba suka fita, ko karasa barin dakin Hajja batai ba, Abdulkadir ya bar inda yake zaune yana dawowa kusa da Waheedah ya tsugunna, hannu yasa yana tallabo fuskarta
"Me nayi miki da zafi haka Waheedah?
Dan Allah me nayi miki haka?
Hankalina kike son ganin ya tashi?
Nutsuwata kike son rabani da ita?
Duk kinyi nasara, wallahi kinyi nasara, kibari haka ki tashi mukoma gida...
Idan ma kina so raina ya baci ne kamar yanda na bata miki rai duk ya faru..."
Saida hawaye suka zubo mata tukunna tasa hannuwanta tana zame nashi daga fuskarta, kallonta yake yana ganin kamanninta nata ne, amman gabaki daya yanayinta yasa ta zame mishi baquwa, bai taba sanin tana da wannan bangaren bama balle yai tunanin ganin shi wata rana.
"Aurenka nake so ka saukake mun"
Ta furta da wani irin yanayi daya sashi zama.
Ko dai Waheedah nada aljanun da baisani bane sai yau, ko kuma watakila batasan yanda kalmanta suke mishi kamar ta watsa mishi garwashin wuta bane shisa
"You are hurting me...Waheedah dan Allah...
Kiyi hakuri...
Shikenan?
Hakuri kike so in baki?"
Kalaman suka kwace mishi batare daya sani bama, kallon shi take, yaune rana ta farko a tsayin shekarun data sanshi da taji kalmar hakuri ta neman afuwa akan labban shi, sai dai zuciyarta kamar dutse take jinta, babu abinda hakurin shi ya motsa a kirjinta balle yai tasiri.
Muryarta na rawa tace
"Ka sakeni...
Shi nake so"
Ciwon kan da yake ta fama dashi yaji yana karuwa, ya kasa gane kanta, ko kadan ya kasa gane kanta balle yasan ta inda zai bullo ma abinda yake faruwa.
"Kinsan girman kalmar da kike fada?
Kinsan babu kyau mace ta furta ma namiji kalaman nan?"
Duk da hawayen dake zubar mata saida murmushi ya kwace mata
"Zakafi kowa bada tabbacin naje islamiyya Sadauki, kaman yanda zan bayar akanka, an halarta mun neman sakina idan bazan iya zama dakai ba...
Zan biyaka sadakinka karka damu..."
Ta karasa tana sa wata irin dariya kubce mishi, ya lallabata, yayi duk iya abinda zai iya, baisan me take son samu daga wajen shi haka data zabi wannan hanyar ba, mamakinta yake sosai, ance kana sanin halayen mutum fiye da ko yaushe idan zamantakewa ta aure ta hadaku, Waheedah nason karyata kowaye ya fara fadin kalaman, dan yanzun bazai iya bada shaida akan halayyarta ba, da wani yanayi a muryar shi yace
"Me kike so daga wajena?"
Dan in bayau ba, shi bai mata komai ba, wata rigima bata hadasu da zata zabi daga mishi hankali haka ba.
A gajiye ta amsa shi da
"Sau nawa zan maimaita?
Ka saukakemun auren ka"
Tashi yayi daga kasa yana komawa kan kujera, yaga alamar tashin hankalin shi take son yi, nata kuma babu yanda za'ai ya kwanta, baisan kalar wasan da takeyi dashi ba, amman zai biye mata harya gane kan wasan, sai yasan hanyar dazai bi yai nasara akanta.
"Ko meye yake fada miki zaki samu abinda kike nema yaudararki yake yi..."
Ya fada mata yana tabbatar da kalaman sun zauna mata, zaiga wanda ya isa yasa shi sakinta tunda igiyoyin a hannun shi suke.
"Abba..."
Waheedah ta kira idanuwanta cike da hawaye, zaman shi Abdulkadir ya gyara kan kujera yana jin shigowar su.
Suka zazzauna banda Anty datai tsaye inda take kafin ta fita daga dakin.
Kallon su Abba yayi, fuskar Abdulkadir tana tabbatar mishi basu cimma wata matsaya mai kyau ba, duk da yayi wannan addu'ar, bayason Abdulkadir ya rasa Waheedah din, amman ba za'a hadu dashi aci gaba da zaluntar marainiya ba.
Baida karfin daukar zunuban nan kam.
"Abba ku fada mata, ni ban shirya rabuwa da ita ba...
Ku fada mata"
Abdulkadir ya fadi yana kara gyara zaman shi, karyar hauka Waheedah take, aure yanzun yakejin ya fara yinshi da ita, dan bai amsa karbar aurenta a masallaci ba saida niyyar mutuwa ce kawai abinda zai raba igiyoyin da suka qulle su a ranar.
Baiga meye zai canza wannan ba.
"Kaji shi ko Abba?
Bazan iya komawa gidan shi ba nikam...
Dan Allah ku bashi hakuri ya saukakemun..."
Waheedah ta fadi cikin tashin hankali, cikinta har yamutsawa yake da tunanin komawa gidan shi, karfinta ya gama karewa gabaki daya.
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
Anty ta fadi, tana sa Abdulkadir juyawa ya kalleta
"Kifa daina salati tunda auren bai mutu ba, ba kuma mutuwar zaiyi ba"
Idanuwan Hajja a waje tace
"Abdulkadir..."
Ranshi a bace yake, sosai ranshi ya jima bai baci irin na yau ba
"Salatin me take yi to Hajja?