← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 94

Sashe 61

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sallamar da Baba yayi yana kiran Mama ya katse mata tunanin da takeyi, duk da hakan baisa ta daina jinta kamar a mafarki ba.

Mama ta fito tana kallon Baba da farin cikin dake fuskar shi.

"Auren Nuriyya aka daura yanzun a masallaci"
Cike da mamaki Mama take kallon Baba, tasan kullum zancen shi baya wuce na Nuriyyar duk sanda zasu kebe, amman bai mata zancen ya samo mata miji ko kuma akwai wanda ya same shi da maganar aurenta ba.

"Ban fahimta ba, aure fa kace Baban Nuriyya..."
Kai Baba ya jinjina mata
"Fitar da nayi dazun da maganar suka zo, to a shirye suke ashe"
Har lokacin da mamaki a fuskar Mama tace
"Duk da a shirye suke, kuma ba auren farko bane abin da mamaki, badan baya faruwa ba har a auren budurwar, amman gaggawa na daga shaidan fa, wanene yaron?

A musulunce ya kamata ayi bincike kafin a daura"
Murmushi Baba yayi
"Nasani, nima nayi tunanin, amman ganin dan gidan Alhaji Ahmad ne shisa ma banki ba"
Da wani sabon mamakin karara a fuskar Mama take kallon Baba
"Dan gidan Alhaji Ahmad kuma?

Wanne daga ciki?"
Gyaran murya Baba yayi tukunna yace
"AbdulKadir"
Wannan karin da tashin hankali bayananne Mama take kallon shi, cike da yanayin da yasa yaji gabanshi ya fadi
"Lafiya kuwa?

Me ya faru?"
Kai Mama take girgizawa
"AbdulKadir naji kace, AbdulKadir dan gidan Alhaji Ahmad"
Da sauri Baba yake jinjina mata kai.

"Eh shi nace"
Bango Mama ta laluba tana samun kujera ta katako ta zauna akai tana wani irin mayar da numfashi hadi da fadin
"Nuriyya me kikayi?

Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
Sosai Baba yake kallon Mama
"Kimun bayani yanda zan gane...

Me yake faruwa wai"
Kai Mama ta daga tana kallon Baba da idanuwan da suke cike da hawaye, ko da fada mishi tayi ba lallai bane ya fahimta, abune da 'ya mace kawai zata fahimci ciwon shi, dan ita zuciyarta wani irin zugi take mata, batajin zata dauki abinda akai ma Waheedah din, batasan hawayen ta sun zubo ba sai da taji su kan kuncinta, muryarta na sarqewa tace
"AbdulKadir dinne baka sani ba?

Baban Nuriyya AbdulKadir dinne baka gane ba kafin ka biyewa son zuciyar 'yarka ka wakilci daurin auren nan ko me?"
Kafafuwan shi Baba yaji sunyi sanyi, tsugunnawa yayi, yasan matarshi farin sani, a tsayin zamansu, abinda zai sakata zubar kwalla babba ne.

"Maryama na kasa fahimtar ki, kimun magana yanda zan gane, kaina ya daure"
Wani irin kallo Mama take mishi da duk ya kara dagula mishi lissafi
"Kasan yana da aure ko?"
Kai Baba ya jinjina yana kallonta cikin kaguwa da jin sauran zancen
"Kana so kace mun baka san wacece matar shi ba"
Kai Baba yake girgiza mata, zai iya tuna lokacin da akai auren AbdulKadir din, su uku ne ko fiye da haka aka daurama aure ranar in zai tuna, dan a makare yaje, ko cikin masallacin bai samu shiga ba saboda cikowar mutane, ya tsayane har Alhaji Ahmad ya fito yai mishi Allah yasa alkhairi ya wuce.

Wani irin daci Mama takeji har kasan zuciyarta, bata shiga harkar Nuriyya ne saboda batason rainin yarinyar, shisa a lokutta da dama take binta da ido, tasan tana da halaye marassa kyau, amman bata taba zaton ko zata nunawa kowa zai fada kan Waheedah ba.

"Amman kasan Waheedah ai"
Kan dai Baba ya sake daga mata
"Ya zakice nasan Waheedah...

Waheedah fa"
Baba ya maimaita, yarinyar da aminiyar 'yar shi ce, kaunar dake tsakaninta da Nuriyyar ta kara karfin zumunci shi da Alhaji Ahmad din har yake samun alkhairai da dama daga shi har 'yar tashi.

Hankali da nutsuwar yarinyar yasa duk shekarun shi yana ganin girmanta ba kadan ba.

Kuma ko da Nuriyya tayi aure duk idan Waheedah tazo gida saita biyo ta gaishe dasu ko baya nan, yakan dawo ya samu sakon abin alkhairin da ta kawo musu.

"Hmm..."
Mama ta fadi zuciyarta kamar zata baro kirjinta, sai da ta hadiye wani abu dayai mata tsaye a makoshi tukunna tace
"Mijinta ne ka aura ma 'yarka"
Cikin tashin hankali Baba yake kallon Mama, yana son tace mishi abinda yaji ba gaskiya bane ba.

Yasan Nuriyya daya daga cikin yaran Alhaji Ahmad ta aura, amman harga Allah bazai ce wanne bane a cikinsu, kuma bai taba kawo ma ranshi AbdulKadir din bane ba, tunda da kan shi yazo neman auren Nuriyyar, kuma itama Nuriyyar tasani, ko a mugun mafarki kuma bai hango cewar zasu hadu su biyun suyi wannan cin amanar da addini bai haramta ba, amman kunya da kara ta haramtashi ta kowacce fuska.

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Baba yake fadi yana maimaitawa, idan hankalin shi yayi dubu gabaki daya yagama tashi.

Ya rasa abinda zaice, mikewa Mama tayi tana kara share kwalla kafin tace
"Bansan abinda kikayi ba Nuriyya, bansan da idon da zaki kalli Waheedah a matsayin kishiya bayan duk halarcin da taimiki da zumuncin dake tsakanin ku ba, wallahi bansani ba.

Nikam nasan bazan iya kallon idanuwan yarinyar nan ba....

Duk da ina son tasan bada sa hannuna kikai mata wannan cin amanar ba"
Mama ta karashe maganar tana barin wajen, Baba kuwa har lokacin ya kasa magana, hannu yasa cikin aljihunshi ya zaro sadakin Nuriyya da tunda aka fara maganar kanta yake a kasa, hawaye kawai suke zubar mata badan zata iya cewa ga asalin dalilin zubar tasu ba.

Duk da ta daina jin duk wata magana da ta biyo bayan an daura aurenta da AbdulKadir, sai yanzun da tabi kudin da Baba ya ajiye mata da kallo.

"Wallahi da nasan mijin Waheedah ne sai dai ku nemi wanda zai daura muku auren nan Nuriyya...

Bansan me kikayi ba, daga ke har shi, ban kuma san dalilinku nayin abinda kukayi ba.

Amman in kunyi da son zuciya amana ba zata taba barinku ba..."
Baba ya fadi yana tashi shima.

Dakin shi ya wuce yana jinjina al'amarin da kuma daukar da Waheedah zatayi musu ta mutanen da basu san darajar zaman tare da girman alkhairi ba, kuma bazai ga laifinta ba.

Da gaske ne gaggawa a komai daga shaidan take, yanda ya kaqu ya rabu da Nuriyya yasa shi amincewa auren batare da tunanin komai ba.

A karo na farko da yabi son zuciyarshi gashi tun ba'a je ko ina ba ya fara dana sani.

Nuriyya kuwa kudin ta dauka tana komawa daki ta kwanta, har lokacin bata daina jinta kamar a mafarki ba.

Wayarta ta dauko, duk da tana shakkar ta kira AbdulKadir din, text ta tura mishi
'Nagode Masoyi, duk da na kasa yarda na zaka matarka, wallahi ina jina kamar a mafarki'
Sai da taga sakon ya shiga tukunna ta sauke wayar kan kirjinta tana jin wani irin nishadi da bata tabaji ba a rayuwarta yana lullubeta, kafin bacci ya kwasheta cike da mafarkin rayuwar da zatayi a matsayin matar AbdulKadir.

Komai bai sake hade mishi waje daya ba sai bayan komawar shi Lagos.

Duk wani wanda yake sama dashi a gidansu saida ya kira yai mishi tas kan maganar auren, gabaki daya babu wanda ko Allah yasa alkhairi yai mishi, ya manta rabon da yayi kwanaki da bacin rai haka.

Har kannen nashi ma Zahra sai da tayi mishi text
'Hamma baka kyauta mana ba, zaka zageni nasani, amman bai dameni ba wallahi.

Abinda kayi baka kyauta ba'
Ya kuwa kira din ya sauke mata masifa kamar zai cinyeta, kukan ta daya ishe shine yasa shi kashe wayar shi, daman wanda zai huce akan shi yake nema.

Gabaki daya ya rasa yanda zaiyi ko inda zai saka ranshi yaji sanyi, ga Waheedah duk waya ko video call din da zasuyi sai yaga ta kara mishi wani irin kwarjini da ko maganar kirki sai yayi da gaske yake iya hadata balle har yai mata zancen auren.

Nuriyya ma kullum suna waya a gajarce, a satika biyun da yayi a Lagos doguwar waya daya sukayi, shima bayan ya kira Anty Talatu da tunda yake a rayuwarshi bai taba tunanin akwai ranar da zai bukaci wani abu daga wajenta ba.

Amman babu yanda zaiyi, babu wanda zai tambaya tunda duka yan gidansu basa magana dashi dan ya kara aure, itace ta fara zuwa kan shi.

Ko ita din ma mamakine bayyane a muryarta da ta daga wayar, suka gaisa tana dorawa da
"Lafiya dai ko AbdulKadir?

Kowa lafiyar shi kalau?"
Kai ya daga kamar tana ganin shi
"Lafiya kalau Anty, zan tambayeki ne daman"
Yanajin sauke numfashin da tayi kafin ya dora da
"Idan ka auri bazawara zakayi akwatuna duka ko?"
Dariya Anty tayi daga dayan bangaren
"In kana da halin hakan, ai kyautatawa ce, amman bakowa yakeyi ba gaskiya.

Zaka iya magana da ita kaji, wasu sunfi son a basu kudin ma akan a sai musu kayan, kai ma kuma zaifi maka sauqi"
Jinjina kai AbdulKadir yayi, dan bai fahimci maganar Kawu Ali kan lefen ba, ita kuma Nuriyya batayi mishi zancen ba.

Shisa ya kira Antyn dan yaji in sai yayine sai yasan yanda zaiyi
"Kaman nawa zai isa"
Ya tambaya
"Gaskiya bazance ba, daga dubu dari in kana da hali har dari biyu ma, ko kasa da hakan.

Iya aljihunka iya abinda zaka yi"
Shiru AbdulKadir yayi
"Idan nace banda dubu dari biyu nayi karya, amman akwai hidindimu a gabana nikam, matata nada ciki"
Yar dariya Anty tayi
"Bakayi tunanin akwai wata hidima a gabanka ba kake shirin kara aure, na dauka halin naku na mazane ya motsa ai, aljihunka kaji a cike da kudin da bakasan yanda zakayi dashi ba sai karin aure..."
Dan murmushi AbdulKadir yayi
"Nasan ba zamu gama wayar nan lafiya ba Anty...

Dole sai kin fadamun maganar da zanji daman ban kira ba"
Dariya Anty tayi sosai
"Allah ya shirya mana halinka AbdulKadir..."
Sallama yai mata hadi da godiya kafin ya kashe wayar.

Da gaske yake da yace mata hidima ce a gabanshi, akwai kudaden da yake ajiye da sai dolece take sakawa ya tabasu, yana ajiyewa ne saboda tsaron lalura.

Dan sai da aka haifi Fajr tukunna yasan kula da yara ba abu bane me sauqi.

Saima daya fara haqora, ga kyanda.

Shisa baya wasa da ajiye kudi dan irin lalura haka.
Chapter 61 · 0% Book details